Showing 12001 words to 15000 words out of 108344 words
Chapter 5 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt
yasani shafowa, wani bakin ruwa ne me mugun wari, d'aga Kaina saman nayi.
Wani uban salati nayi gaskiya ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai bayan kwanaki biyu, sannan na farka na ganni a kwance a d'akin Ummina,
A hankali na bud'e idanunshi, tana zaune akan abin sallah, a hankali nake addu'an tashi barci...
Tasowa tayi tazo inda nake tace.
"Sannu SAFINAH, ya jikin naki."
Gyada mata kai nayi "da sauki." Nace mata a sanyayye,
Kallona tayi taga ina son ƙarin bayani, ruwan wanka ta fara haɗa min sannan ta dawo ta kama hannuna muka shiga ban daki nayi wanka da taimakonta dan zata fita na riƙe hannunta, shine ta dawo ta cude min bayana tare da kaina Ni kuma nayi sauran ina gamawa ta miƙa min towel.
Muna fitowa ta bani kaya nasaka sannan na zauna, tace.
"Naga kinyi alola a ciki ko Zaki yi sallar kafin na kawo abincin."
"Toh Ummina!"
........ Bayan naci abinci anan na zuba mata ido tace.
"Shekaran jiya! Abdulhameed, ya kiramu wai kumar suma da harbe harbe kamar me cutar jinmu, kuma daman kafin ya kira Ashraf ya fara mana maganar cewa zai dawo yana jin baki da lafiya dan yaji haka a jikinshi. Toh da muka ki nashi sai ya tattaro ya biyo jirgi, inda ko tsayawa ayi bikin shi bai yaƙi, a ranar da ya dawo. Yaje gidanki a daren. Mijinki ya kiramu. Toh a daren Abbanku ya gayawa Ashraf, shi Kuma dama yana unguwar ku, dan haƙa ya shiga gidan, dan yasamu Kofar gidan a buɗe. Shima yasha wuya sosai kafin ya shiga cikin gidan dan duk jikinshi ya ji ciwon. Koda ya samu ya shiga tare da mijinki suka fito dake kina fisge fisge, shi yaso a dawo dake gida amma mijinki yace scale kuje asibiti.
Tunda aka kai ki banda allurai, ganin. Har muka zo jiya, shine Wani mutum da Abdullahi ya taimaka, yazo ya ganki yace ba ciwon asibiti bane, na gidane, abin mamaki mutumin na fita mota tabi takanshi. Toh dai Abbanku yasa aka dawo dake gida dazun nan inda aka kira wani malami ya baƙi magunguna."
Lumshe idanuna nayi, sannan na gyara kwanciyata akan cinyarsa,
***
A sannu sai da nayi sati biyu a gida kafin aka mai dani gidana, sosai naji sauki,
Sati na biyu da dawowa, hmm wani sabon lamarin ya faru, kaina na bisa cinyar dr, yana wasa da gashina.
Haka kawai naga gidan yana juya min tare da ciwon ciki, buɗe idanuna nayi zan gaya mishi, sai ganin wannan abu ranar. Ihu nayi tare da yunkurin mikewa. Ji nayi abu mazuna daga kasana, aikuwa na kafe mishi a gurin.
Faɗan irin wahalar da nasha, tun Dr na nuna damuwarsa har ya fara ganin kamar da gayya nake kome, ƙarshe Sa'ima ta gayawa Uwarta, kuma dama ba wani shiri muke ba, gashi bana son zama Ni ɗaya amma haka zasu fita abinsu Ni ɗaya a gidan, haka zan dimauce. Na fita hankalina.
Watanni mu biyar, ina fama da wannan matsalar, hmm a sannu Kowa ya daina damuwa da halin da nake ciki, Ashraf ne yaƙe ƙoƙari a kaina. Shima kuma ba kaunar ganinshi nake ba, idan kuma ya kawo magani daukewa ake.
Nayi imani haka shine tawada kaddaran, dan kuwa nasha mugun wahala. Babu wani kulawa nake samu gurin Dr ba, ga rashin mutunci da yar uwanshi take min,
Ban tashi fahimtar abinda ke faruwa ba, sai da aka kawo min Kayan fadar kishiya, nan na fahimci mijina yayi min nisa, domin gefe ina fama da wahalar ciwo, suma kuma suna bunkasa masifa, sai gashi na zama marainiya da iyayena, na zama kamar mahaukaciya, ko me tambotsa, toh bana barci ido biyu nake ganin masifa, ba dole kai ya kunce ba. D'akina kaca kaca.
Ni kaina kana ganina zaka sanyani a class din mahaukata masu degree a cikin hauka,
Gidan kam zan iya cewa sun manta dani ma gabaki d'aya, a cikin zuri'arsu, dan babu me tunanin.
Abinda na iya ganewa shine Dr ba a gidan zai zauna ba, kuma a Cikin wannan lalura bai hanashi idan masifar ta Ciyo shi yazo yayi min wasa wai nan ya biya bukatarsa,bana hmm bana humm. Ina nan dai ido kawai nake bin kowa dashi, dan bakasan wata irin rayuwa nake ba, zan kwanta amma ba barci nake ba,
...... Haƙa aka yi bikin Dr, ya tattara yabar min gidan, Ni kuma na cigaba zama da shaidanin da yaƙe juya rayuwata. Gidan ya koma hunturu house, bakome sai buruntun aljanu
(🤣😂😎🙄😜 Na woh go rakani 🧗)
..... Haka nayita fama Ni ɗaya, watan dr biyu sai gashi nan ranar abin baya Ciyo shi, yazo zai murkushe ni, Ni Kuwa naki, murdeni yayi ya biya bukatarsa ya sakai zai fita, cikin wani irin murya me dauke da gajiya nace.
"Tafiya zakayi kabarni cikin bala'i Hameed me nayi maka da zafi."
Jikinshi ne yayi sanyin shima dai bazai ce ga abinda nayi mishi sai dankaren kazamtar da na keyi,
"Idan kina son zama lafiya dani dole ki daina haukacewar da kike kuma ki daina kazamtar da kike banda ina da da hakuri waye zai zauna dake, ki gyara nima zan dawo miki Hameed dinkin."
Haka yasa kai ya fito, nayi kuka iya karfina, nayi danasanin haka, tun bayan tafiyarshi ban Kuma ganinshi ba sai kwanciya sabon jinya dan cikin shine ya shigeni me mugun wahala, dan tun watanin baya da nayi bari ban kuma samun ciki ba sai yanzun, wani irin wahala nake sha, gashi duk kayan abinci na ya lalace, haka zan debi lalataceccen na dafa ina gamawa, zan zauna naci sai kawai naga jini ko tsutsotsi.
Ruwa wannan idan zan sha, sai nayita kuka dan jini ke zuba a fanfon,
Rayuwa ba dad'i baƙin cikin ya cika min zuciya. Yau ma haka aka min Cikin kuka nace.
"Idan wani abu nayi toh a fito a gaya min, bawai ana mai dani mahaukaciya ba."
Aikuwa aka fara wargaza kayan gidan, tare da makeni na fadi can, bayan wasu lokuta na farka Dr na gani zauna a kan kujeru, tashi nayi zan zauna ya bini da mugun kallo dole na koma na kwanta.
"Ban san laifin da namiki kike shirin jawo min masifa ba, akan me zaki kunna gas ki barshi yayi ta ci, gashi an kinji min gobara a gidan duk wasu abina masu daraja na rasa, hatta cikin jikinki kin min sanadin sa, amma Alhamdulillah tunda kema kinyi asarar wasu abubuwan zaki ji yadda nake ji."
Takowa yayi har gabana ya buɗe tafin hannuna ya ciro takarda daga aljuhun wandonshi yace..
"Kije dama zuciyarki bata tare da Hameed, tana can gurin kwartonki, ace duk abinda ya faru kafin wani naki ya sani shine akai toh na barshi ke dama banda budurwa zuciya me zaki da sa'an Dr Kyari, kije can ku karanta.....
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
MJ
BOOK-2
17-2-2020
Page.🖐️
Allah Sarki Dr kowa fatar mutuwa yake maka Ni kuma banjin zan dura maka fiya fiya 🤪🤓
______________________
"Wayyo wallahi bani kumawa ka barni haka,"
Sai da ya ganni cikin farin ciki, sannan ya d'ago tare da rungumana, ajiyar zuciya nake ta saukewa sabida dariyar da nayi.
Shafa cikina yayi cikin wani irin yanayin yace.
"Yaushe zan yi ajiyata? Na kosa naga kin fara laulayi fa."
Fari nayi da idanuna, tare da tausaya kaina, nace.
"Kai nake jira!"
Murmushi yayi cikin farin ciki, yace.
"Beauty! Idan Allah ya bamu haihuwa dake, kunsa sunan da zan saka?"
Girgiza mishi kai nayi cikin son jin sunan waye zai saka, jan hancina tayi sannan Yace.
"Sunanki idan mace ce, idan namijine sunan Dr Kyari zan saka."
Murmushi nayi tare da gyara kwanciyata a jikinshi nace.
"A'a sai dai mu saka sunan Baba! Mace kuma musaka sunan Amman mu!"
Birkitoni yayi yana kallon cikin idanuna, hura mishi iskar bakina nayi. Aikuwa ya riƙe haɓɓana da hannunsa yana gogan min hancinsa akan nawa,
Babban arzikine mace ta samu namijin da zai bada lokacinsa domin ita, ya shirirince sabida ita, ya lalace saboda ita dan ya nunawa duniya bayan ita babu wata, eh tabbas Dr baya kai min, amma farin cikin da nasamu dashi har abada bazan taɓa mantawa ba, Dr ya soni kuma yana cigaba da soma, dan haka babu ta inda zanyi kuka dashi, sabida ya toshe wannan hanyar.
Sannan Dr Mutum ne me hakuri sosai, koda yake bazan bada shaidan haka ba tunda bamu wani zauna can ba.
***
Dagaske bikin Ashraf ya kankama a Oman, yayinda Ango fit yaki zuwa sai da Abba da Ummi suka sashi a gaba suka tafi, tare da Dudu da Batul Khalil da Khalilah, Har da Abba lawan wanda ya gama jami'arshi. Aka bar Umma da Mamie a gida, sabida Umma tana kasuwanci, Mamie kuma yar zauna gari banza, masu jiran miji ya basu (🤭🤫🤧Ashe Irinsu oo suna nan a duniya🤒)
Sun sami karba Irinta alfarma, tare da hidima sosai. Aka shiga yi musu, abinda ya daure musu kai ba kome bane sai yadda akewa, girmama su, musamman ahali masarautar. Su Aamih kuwa Yaran kamar sunsan suwaye su, dan wani mugun miskilancin sukewa su Ummi, duk sabon su dasu kuwa. Daga Batul sai Khalilah, sune kaɗai suka same yardansu har suke Iya zama a jikinsu.
***
Satin mu biyu, muka shiga shiri bai gaya min inda zamu je ba, sai da muka isa Airport sannan ya mika min jakata, wanda ya riko tun a hotel.
Yaje ya mika ina zaune, yana gamawa yazo ya riko hannuna muka shiga mall ɗin da yake cikin airport ɗin, Banda kayan kwalama babu abinda yake jida sai abubuwan wasan yara, kome kala biyu pink da purple, daga nan na fahimci gida zamu koma, muna gamawa yaje gurin da ake sayar da wasu gown, jan hannuna yayi zuwa inda aka jera su, zaba min wata yayi tare da kaini bakin dakin sauya kayan, nasaka, shiga nayi na cire najikina. A cikin sati biyu da muka yi, sai naga nakara kumatu. Nayi cike d'akin da ake, kalar fata ta ya kuma fitowa sosai.
Saka kayan nayi na fito daga cikin d'akin,👌🏾 yayi min da hannunsa. Alamar nayi kyau, sannan ya kuma mika min wani rigar itama dai ba laifi.
Sai a na ukune yace.
"Wannan yayi! Dan yafi su kyau."
Riko hannuna yayi muka nufin inda ake biyan kudi, mika musu katinshi yayi suka diba iya kudin su. Kallon agogon da yayi sannan yaja hannuna muka fita.
Muna zuwa aka fara shiga jirgin, kallon shi nayi cikin zakuwa nace.
"Ina zamu? Naga sai sayayya kake!"
Na kura mishi ido ina son jin karin bayani. Ba tare da damuwa ba yace.
"Bikin Babansu Aamih!?"
Ji nayi kaman abu zai fado daga kirjina, nayi maza na dage kirjin. Zufa ne ke yanko min ta ko'ina, Allah ya taimakeni bai ga halin da nake ciki, kafin ya juyo na kirkiro Faransa dole.
"Baki ce kome ba"
Cikin ƙarfin hali na turo bakina nace.
"Allah ya bada zaman lafiya."
"Amin beauty."
Yace min, babban takaicina ɗaya ne me yasa ya gaya min, ji nake kuka na taso min, amma haka nayi shiru hiran da yake hana naki, biye mishi na cigaba da lumshe idanuna har barci yayi gaba dani,
Murmushi yayi tare da shafa fuskana cikin walwala, riƙon hannuna yayi yana kallon yadda sumar yatsuna suka kwanta, sake kallon fuskana yayi a karon na uku ya ga yadda na ajiye kumatu, kamar bani ce Hajja ke cewa a dauri kashi ko a bata igiyar ba.
Hannunshi ya kai cikin rigana da sauri na bud'e idanuna. Kallon juna mukayi, nice na fara janye idanuna daga gare shi, zuciyata tana tsawatar min abisa butulcin da nake shirin aikatawa, meye haɗin da Ashraf? Da nake shirin fad'awa hallaka sabida shi.
Innalillah nake mai-maitawa, har na samu saukin, daura kaina nayi a kafadar shi, daura kanshi yayi a gefen nawa.
***
Oman...
Tunda Dr ya turawa Dudu sakon gasu nan zuwa, shi kuma ya gayawa Ashraf. Dama yaki ya shirya zasu fita jin zamu zo ya miqe ya fara da wanka.
Ya jima a ciki sannan ya fito, shirya yayi cikin kananun kayan wanda suka fidda yarantashi sosai.
Turare ya fesa sannan ya koma gurin da agogon shi yake, ya dauka tare da zobensa na azurfa.
Takalmin kamfanin Mamata, ya saka sannan ya fito, a hankali yake fitowa. A sannu yake takawa cikin izza da kasaita, uwa uba kuruciya, na dibanshi da wani mugun miskilancin da ya kwanta a fuskar shi tare da tsare gida, yana fitowa ya kalli Dudu.
Sannan ya Basar da shi, kallon wayar shi yayi. Sannan ya turawa Ghani sako.
*Ka tambayi kawunsu Asma'u, karfe nawa jirgin zai sauka.*
Ba tare da ya kalli Ghani ba, ya cigaba da tsayuwar shi.
"Dr karfe nawa jirgin su Uwar d'akina zai sauka."
Cikin ko in kula Dudu yace.
"Saura minti ashirin."
Gaba Ashraf yayi suka take masa baya, mamakin Irin mulkin da Ashraf yaƙe nunawa Dudu yake.
(🙄🙄Dudu kenan ai Yayarka ta aikatu, mutumin da baya iya dogon magana.)
***
Mun iso lafiya sai narkewa nake a jikin shi, har muka shigo a arrival.
"My Man! Na gaji."
Na fada mishi a sanyayye, dan na gajine.
"Toh! Bari muje masauki sai ki kwanta ki huta, ina yaso sai na miki tausa."
Gyada mishi kai nayi, jikina a mace.
Muna fitowa muka haɗu da Dudu, da sauri ya zo ya amshi, jakar hannun Dr, sannan yayi ɗan murmushin jin dadin yace.
"Yallabai me kake bawa Didina ne haka tayi kumatu?".
Murmushi Dr yayi masa, sannan yace.
"Tayani gani, nima dazun a cikin jirgin sai da naso tambayar ta."
Kallona Dudu yayi cikin son ƙarin bayani,
Ban kulasu ba, na cigaba da binsun da murmushi, gabana ne yayi mugun Fad'uwa sakamakon ganinshi ya tsare Ni da ido. Komawa jikin Dr nayi ina tura bakina cikin kunkuni nace.
"Wallahi Ni da anyi shawara dani, bazan zo nan ba."
Shafa fuskana Dr yayi cikin rarrashin yace.
"Bazamu wucce sati ba!?"
"Sati!!! Fa wallahi Ni bazan zauna har sati ba."
Ayya SAFINAH kiyi hakuri mana ko kwana biyar muyi."
"Nifa na gaya maka gaskiya bazan zauna ba."
Dai dai munzo inda yake, kasa kasa yayi Magana yadda babu wanda ya isa yace sani yake domin kuwa, hankali shi na kan Dr da suka riƙe hannun juna suna gaisawa yace.
"Ba sai kin nunawa duniya mijinki bai isa dake ba."
Watsa mishi harara nayi raina a bace banga dalilin zuwana wannan bikin ba, haka kawai an dauko Ni zuwa wani gayyato soɗi, kunun bayan ludayi.
Mota muka shiga, nida Dr da kuma Dudu, sai nashi tare da ghani.
Muna isowa gidan, ya fita tare dayiwa Dr jagora har masauki su, Ni kuma Dudu ya