Showing 99001 words to 102000 words out of 108344 words

Chapter 34 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt

27 Nov 2024

4840

D'ago Ni yayi daga jikinshi yace.
"Kina da hankali kuwa! Taya zan cire cikin jikinki bayan ina son shi kamar sauran yan uwan shi."


Rike hannuna yayi sosai sannan yace.
"Yarima William matar shi kartine ta girme shi, sannan suna da yara har uku, Safinah sai Musa muke musulmai ne bazamu iya ba, Safinah koda bani da dukiyar da zan rike ki kodan Albarkacin yaran da kika haifa min zan nemi abin yi, don Allah karki kuma cewa a cire min cikina."


"Kayi hakuri bazan kuma ba."
Hmm abinda nasani daga bada hakuri ya nemi wani abu, kwace kaina nayi. A gajiye nace.
" Dan girman Allah, ka barni haka"


Kyale ni yayi ya shiga ban daki yayi sakewa kanshi ruwa, a raina nace.
*Yafi maka wannan jarabar*


A cikin kwanaki shida muka tattaro shirgin mu zuwa jordan, wa Ghaniyu ya bawa sakon ajiye mulkin, shi kuma ya kasa kaiwa shine ya ajiye sakon.


Ranar jumma'a muka iso jordan, kusan watan mu uku fa, tun da muka shiga masarautar, nake kallon shi, duk wata walwalar shi ta dauke, jingina kaina nayi a jikinshi, tare da matse hannun shi nace
"karka manta ina tare da kai."


"Na sani SAFINAH! Tsoro nake ji kar na rasa farin cikin da nake fatar samu"
Kamo hannun shi nayi na daura akan cikina nace.
"Idan zaka yi kewar farin ciki ka tuna da wannan an same shine ta hanyar farin ciki da soyayyar gaskiya."


"Ubangiji ya kuma baki wasu Yan matan dan ni nafi son ki haifa min Y'ay'a Mata masu albarka."


Shiru nayi, dan bani da tacewa, har muka iso cikin gidan. Da gudu su Aanih da Aamih suka fito kodan sun san da zuwan mu ne, da sauri na fita daga motar.
Na dauki Aamih na sumbaci goshinta, sannan na koma ga Aanih wacce ta cika dam, itama daukarta nayi na mata kamar yadda nayiwa Yar Uwarta.


Bata wani nuna farin cikin ta ba, kamar Yar uwar, sai ma komawa tayi gurin uban tana b'ata rai tana kallon Yar uwan, irin kallon k'iyayyar nan, ita kuma Aamih ta manne a jikina, tana leka yar uwar.


Ɗaukar Aanih yayi yace mata.
"Ammyna me ya faru!? Kike fushi ?"


Tura baki tayi tare da harara Aamih sannan tace.
"Appa! Ni na tsaneta ne! Ta kwace min Ummuna"

Miko min ita yayi naki kar b'arta nace.
"Dan gidan ku ki mutu ma, kuma na kamaki sai na cire miki kunne da shegen idanu kamar na b'eraye"


Daukar Uwata nayi muka shige cikin gidan, inda muka samu Natashah itama tana hararar Aanih.


Dakyar ta mike tazo ta rungume mijinta, tana jan kumatun Aanih, tace.
"Wallahi idan baki bar mugun hali ba nida kece a gidan nan, Kuma na ganki a wancan bangaren sai na karya kafarki da kananun idanunki irinta kadangaru."


Zaro ido yayi tare da kallona yace.
"Meye Husnah tayi da kuke zafin idanunta?!"


Tsaki Natashah tayi cikin masifa tace.
"Wallahi yarinyar nan tasan kan mugunta, duk lokacin da taje wancan bangaren zaka ga ta fito da mugun hali, d'azun Maryam nashan ruwa tazo ta tureta sai da ruwan ya fito ta hanci, hakan bai isheta ba, dake taga Ammyn tana hanani hukunta ta, shine daga jin kun iso nace suke su tarbuko, shine ta ture yar Uwarta,"


Sauketa yayi sannan ya kalleta, cikin rarrashin yace.
"Ki daina babu kyau yar uwarki ce, ki daina mata mugunta."


Gyad'a kai tayi tare da maida hannunta baya tace..
"Appa! Toh kace ta daina kallona."
A zuciye na kaiwa bakinta duka, wani baƙin ciki na kara rufe Ni, taya Husnah tazama haka yarinyar da bata fi hud'u ba har tasan k'iyayya.


Rike hannuna yayi, yana kallon yadda bakinta yake fidda jini, abinka da girman burodi.


"Amma baki da hankali! Taya zaki mata irin wannan dukar yarinya ce fa, bai dace kici da zuci ba."


"Kwas-kwas-kwaas" shine takun takalmin da muka ji ban juya ba, sai tsakin Natashah da naji taja tace.
"Maman Ablah! Muje ki huta, Ammyn sun tafi Oman da Ablah, muje ciki kafin matar cushe ta fara miki iyayi."


"Barka da dawo Sultan!" Ta fad'a cikin murmushi.
"Hmm mun same ku lafiya."
Yace mata yayinda ya dauki, Aanih, tayi maza tasha gaban shi zata amshi yar, Natashah ta riga ta.
Yanzun na kara fahimtar maganar shi, cikin kissa ta janye jikinta, ganin Natashah ta amshi yar sai ta koma jikinshi ta narke tare da jan shi zuwa part ɗinta, har shashina Natashah ta rakoni, ajiye Aamih nayi na karbi Husnah, ina kallon yadda take cira, kishi na cizonta, sai taune lips ɗinta take.


"Don Allah Kiyi hakuri ki bar damun kanki da zuciyarki, cikine dake ko kina son jininki ya haura ne, akan kishin banza a yanzun a daina wannan kishin da kike yi, ki nemi Allah yaye miki kishinta sai ki daina jin zafinta."


Gyad'a kai tayi kawai bawai taji hakan bane, shigo da kayanmu akayi na mikawa Natashah na Ashraf nace mata.
"Dakinki ya kamata ya sauka, tunda daga nata ya fita muka ya tafiya dashi, da ya dawo sai ya sauka a naki."


Kamar dama jira take sai ta fashe da kuka, rike hannunta nayi cikin tausayawa nace.
"Share hawayenki yanzun zai zo kije ki shirya mishi abinda zai ci."


Dakyar ta mike, har ta isa bakin kofa sai ta juyo tare da cewa..
"Nagode sosai!"
Murmushi na mata, tafita da sauri, wayarshi dake jakata na dauka, na rubuta mishi sako kamar haka.
"Kaji tsoron Allah! Ba iya mulkin al'umma ke jiran adalcinka ba hatta iyalinka suna niman adalci daga gareka. Natashah tana jiranka."


"Maryam Zo kije can shashin ki buga kofar karki shiga, sai an baki izni, sannan Kiyi musu sallama, ki kaiwa Appanku kice ya duba kan wayar inji Ni."


Gyad'a min kai tayi tafita da sauri. Ihun ta naji tana kara kamar ranta zai fita. Natashah da take can tana shiryawa ta rigani fitowa. Ina isa na sameta ta saki fitsari a jikinta, sai rawa yaƙe, ta kasa cigaba da kuka.


"Ashraf!!!"
Na kira sunan shi a haukace, tare da dukar kofar, buɗe kofar da yayi da sauri ya fito jikinshi duk kumfa, daga shi sai towel. Yasa yarinyar zub'ewa na gabanshi ragwab, Natashah zata kai hannun na riƙe ta, sai lokacin Zoyah ta fito rike da wayar shi a hannunta, bansan me yasa duk abinda zaka min zan iya jurewa amma banda tab'a min Yarana. Mai dashi gefe nayi, bayan ya dauki Yarinyar, naje gaban Zoyah na tsinke mata mari, sai da wayar ya kwace, na kuma tsinke mata wani marin, sannan na riko gashinta, nace.
"Wallahi kika kuskura aka ce min ta Karye, Allah sai na shayar dake mamaki dan karyaki zanyi, muguwar banza kawai."


Juyawa nayi na kalle shi, sannan na amshi yar, na sakata a kafad'ana, riko shi nayi har shashin Natashah na kai shi, sannan na fito.


Tana tsaye rike da kumatun ta, harara na watsa mata, sannan na wucce da y'ata, ina sauya kayana ya shigo.


Bai ce min komai ba ya fita da yarinyar, nima dake ina jin haushinsa ban ko kalle shi ba.


_Na fahimci wasun ku basu san yakana ba, Pages biyu nake baku idan na bada d'aya Uzuri ne ya riƙe Ni, amma baki fahimci haka ba🤦🏾‍♀️ jiya da na baku Page 44 sai da na baku hakuri amma hallau wasu na tambayata 45 da dare fa, wallahi abin bani mamaki karfe goman zan muku typing? Ko yaushe?! Ki ji a ranki ke Marubuciya ce, kina da miji da yara, ki kalle abin a kanki mana kiji, wallahi a duk lokacin da zan saka buk din kudi abinda nake fara karo dashi shine na sauke nauyin ku dake kaina, na huta, da yawanku sunan ban tab'a jan labari haka ba, sabida bana dogon labari idan naja labari 56, yar yadiko 46' da ciwon a rsyuwata 58, matar malam 59 toh da sauran books dina bans rike labari duka duka labarin MJ pages 105 ne. A cikin kwana arba'in da uku, Ni bana son haka, duk wacce ta gaji ko take sauri tayi min magana na mai da mata kuɗin ta marubuta yan kasuwa suna dayawa, sabida ranki ke ɗaya bazan batawa Nawa Iyalin ba Please muyiwa juna Adalci. Idan nayi kuskure kuyi hakuri_🙏🏻👏🏼
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


4️⃣6️⃣
Tun da suka dawo da yarinyar, naga yadda aka daure shi da bandaji, naji zuciyata na ta fasa mik'ewa nayi zan fita dawo dani yayi tare da zaunar dani cikin b'acin rai yace.
"Wallahi kika kuma dukar musu Y'a har gidan nan zasu zo su miki mugun duka, kuma babu abinda ya dame ni, dan su ƙabilar su suna da had'in kai."
Yadda ya gama maganar cikin zolaya, na kwace hannuna na fita zuwa gurin Natashah. Har na fita na kuma dawowa.
"Wallahi sai na rama mata abinda tayi mata ka ajiye maganar, matukar ina gidan nan sai itama an daurata."


Gyada kai yake kamar kadangare, bowl d'in da na yanka kankana da Grape, mutumin ku, ya shanye tass dake na zuba madara da zuma, sai da ya gama shanyewa sannan ya ce min.
"Hmm dazun kina magana me kika ce ma?!"


Abinda Ya faru lokacin da Aamih ta kaiwa Baban su Waya, koda ta isa kofar buga kofar tayi tare da sallama, tana kiran Babanta, dake ya shiga wanka. Zoyah ce taji buga kofar, tana fitowa ta kalleta bayan ta zaro mata ido tace.
"Me ya kawo ki?! Da zaki dame mutane da buga kofa."


Dake tana tsoronta jikinta na rawa ta mika mata wayar tace.
"Appa na kawo mishi jin Ummuna wai ya duba."


Nuna mata ciki tayi ita kuma ta rab'a ta shige, bata gan shi ba shine ta ajiye tazo fita, har ta fita da ta kuma kiranta, ta kamo hannunta ta tare da rufe mata kofa akan yatsunta, ta kuma tayi maza ta shige d'akinta kamar bata san komai ba.


Shigewa nayi na barshi a gurin, amma naji ciwon abinda Zoyah tawa Mariamah koda nayi magana cewa yayi zan fara taurin kaina kenan, shi yasa nayi shiru ban ce mata komai ba, sai dai na hana Aanih fita gabaki d'aya saboda itama na lura bata kaunar Mariamah, abin ya bani mamaki yadda ko zama muci abinci yarinyar bata yarda ya zauna kusa damu. Dan haka ban dauki alamarin da wani muhimmin ba, tunda nasan basa shiri da juna.


...
Kwanan mu biyar da dawowa su Nah suka dawo, ita da Ablah da Zakiya. Yarinyar tayi wayo abinta, dake itama bata da hasken fata, amma bata kai Aamih ba. Toh har ita Ablah bata bari ta tab'ata idan kuwa tab'a ta, zata shiga bayi tayita wanke gurin, kamar wacce ciwo ya tab'a ta, a hankali ta fara tsantsar yan uwan, da zaran ina kitchen zata hanasu tab'a komai na falo ko daki tana gani na zata koma kamar ba ita ba.


Ban a sannu sai Ablah ta shiga jin tsoron ta, da zaran ta ga Aanih zata shiga niman b'oya. A nan na fara lura da takurawa da Aamih take na yawan zama ita d'aya ko kuma ta biyo NI kitchen, Husnah itace amma lokaci d'aya na shiga tambayar kaina a ina ta dauko mugun hali, dan nasan daga Ni har Ashraf bamu da wannan dabi'ar, sai da na fahimci baya nan, na kama kamar zaneta nace.
"Maza gaya min meye yan uwanki suka miki haka da baki son su."

Ruwa idanunta ya kawo cikin tsoro tace.
"Ummuna! Su basu da kyau Ni nafi su kyau shine, Ummu Zoyah tace kar na zauna dasu zasu goga min baƙi, ni ki mai dani gurin Ummu Zoyah, tana sona."


"Wallahi sai dai ki mutu baki zuwa gurin wata banza naga kafarki a gurin kafin Ummunku ta dake ki nice zan fara miki duka, da manyan idanunta nan kamar na Habibi."


Wato da manyan idanu kamar na Ashraf,(😂🙄 keda shi)


★★★
Tun daga ranar da Nannah ta dawo, gidan mu ya rikid'e, a hankali Nannah ta shiga jin haushin mu, da zaran yana dakin Natashah tayita nishi da tari, dasu haki dasu wani irinsa na numfashi, kamar me cutar Asthma, kar kuce Natasha ka dai ce a'a har dani ai nawa yafi muni, domin da zaran ya shigo gurina ajima kad'an ta turo a kirashi, idan yaje sai yafi awa biyu sannan ya dawo, bayan kamar minti arba'in zata kuma kiran shi, idan yaje sai yafi kusan awa uku, wasa gaske sai kiran asalatu ke fidda shi, daga shashinta, abin tausayi ya fito yayita hamma, dake kwana d'aya d'aya yake mana.


Dan haka girki ya dira kan Zoyah.


Na fito ina karkad'a jina nayi tsifar kitso hud'u da nakewa kaina, kallon gashin tayi yadda ya sauka kamar yadda nata yake, har yafi nata ma da cika.


Wucce Ni tayi abinta bata ce min kala ba, nima kuma ban d'ago nasan tana gurin ba, dan Ni banda Natashah da Yarana Ni bana surutu, idan kaji surutuna da dariyana, Ashraf ya sani a gaba da wasan, banza nan kan ko kana daga waje zaka ji dariyata.


Falon Nannah ta shiga ta zauna, tashi zaune Nannah tayi. Sannan Zoyah tace mata.
"Ni ban damu dake kin nan ki baki nan! Ni abinda nasani kin haifi d'an kuma ina auren shi, naga abinda kikawa Yar d'an uwanki balle kuma wacce ta sadaukar da Rayuwarta domin ki, wallahi kika kuskura mijina yazo d'akina kika min wannan tsiyar da kika musu, wallahi."


Mik'ewa tayi tazo dai dai fuskar Nannah sannan tayi mata magana kasa kasa.
"Tabbas zan baki kyauta na musamman."


Murmushi Nannah tayi sannan tace.
"Ban haifawa kowacce a cikin ku d'an ba, dan haka kome zaki yi ki yi bazan fasa ba."


"Lallai zaki sha mamaki, daga kaina baki kuma tab'a wata."


Sam abin ba dad'i tsakanin Nannah da Zoyah, dan kowanne su ya tsaya akan maganar shi, ina muka san budirin da suke,har akaci aka cinye


..,....... Yau da ya dawo dama yanka tsaya a gurinta su fara gaisawa, sannan yabi kanmu sannan ya wucce d'akin me girki, sai gashi ta rike shi, aka shiga bashi labarin Bara taci wanke, gashi yau a matsa yake da lalura. Wasa wasa, Nannah bata bar Ashraf ba. Sai karfe biyu saura shima zuwa Zoyah yasa ta hakura ta bar shi, cikin idanunta Zoyah ta kalla sannan ta nuna mata wani alama da hannun.


Nah bata bu takanta ba, ita ba dai ta kuntattawa Zoyah ba, burinta ya cika,


Suna shiga zoyah ta sha gaban shi dan a gajiye yake zai kwantar.
"Sultan meye Mahaifiyarka take nufi ne damu?! Taci lokacin ta akan me take shiga hakkinmu, don Allah duba karfe nawa ka shigo biyun dare wannan wata irin Uwa ce mata adalci?! Toh wallahi an gama idan ta kuma zan kai ta kara gurin iyayena."


Mika mata hannu yayi sannan sannan yace..
"Kiyi hakuri?! Zo mu kwanta,"
Fir taki yarda karshe ma, kunna wutar rikici suka yi sosai, abinda ya masifar daga mishi hankali kenan, duk rigimar SAFINAH bata tab'a hanashi barci yau gashi Sabida Ammyn yau Zoyah ta hana shi barci, dake yasan tafishi gaskiya bai ja al'amarin ba, sai ma Kyaleta da yayi tayita masifa har goshin Asuba.


Mu dai muna cikin damuwa dan wallahi Nah ta hanamu mijinmu, shi kuma ya ki fahimtar abinda Mahaifiyarshi take aikata mana, sai na kudiri aniya a raina zan mishi tsiya, dan ma Allah ya taimaka cikin jikina babu laulayi shi yasa babu wanda yasan ina da ajiyar shi, a cikin yan tsakanin ya saka Yaran shi makarantar, nafi tunani sabida halin da yake ciki na bukatar kebewa damu, ga Mahaifiyarshi ta hana shi kwana bamu, sai ya saka yaran a makaranta.


Toh a haka da ya samu yara na makaranta shi kuma sai ya baro pada yazo ya turmushe wacce take da girki, da wannan hikimar aka same zaman lafiya, Amma saboda bin diddigin matar nan sai da yasan yadda ta kamashi a dakin Natashah. Bayan fitar shine ta kira Natashah wacce cikinta ko yau ko gobe, sannan tasata ta kiramu, duk muka hadu a falonta.


"Toh munafukai na tarakune na gaya muku cewa duk wacce na kuma ganin Ashraf ya fito d'akinta sai na sashi ya rabu da ita." Inda take shiga ba nan take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login