Showing 30001 words to 33000 words out of 108344 words
Chapter 11 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt
D'ago kaina yayi da hannunsa.
Had'iye yawu yayi cikin nutsuwa yace.
"Shi kenan!?"
Gyada mishi kai nayi,
Rungume Ni yayi sosai, tare da saukar kanshi a kafadana ya sumbaci gurin.
"Ina son cin abinci da naci a gidan ranar."
Tura baki nayi, saka yatsar hannunshi yayi shafa kan lips dina, saka min dan yatsar yayi cikin bakina, kallon shi nayi naga ya narke min. Zaro harshena nayi na fara lasar yatsar, d'ago kaina nayi. Ya haɗe fuskarmu dukda.
"Bani nasha."
Girgiza kaina nayi cikin son na janye daga abinda muke aikatawa.
"Karka lalata mana aurenmu domin cire mana albarka nifa kai."
"Ni kike so ko!?"
Girgiza kai nayi ina lumshe idanuna.
Had'a baƙin mu yayi wani irin kiss yake min wanda ya kusan tafiya dani baki daya, rike rigarshi nayi cikin wani irin yanayi.
Numfashi nane ya shiga fita da sauri, komawa jikinshi nayi na zub'e, dan kafaffuna bazasu iya daukata ba,
Rungume Ni yayi, shima zubewa yayi akan kujera, b'are mishi baki nayi na fara mishi kuka.
"Har yanzu baki daina kukan banza ba, meye na kuka Ni ban miki hakan dan sha'awar ki ba, abun da nayi dabi'armu ce, haka."
"Ni kam ka mai dani gida."
"Sai kin min abinci ko kuma na cinyeki"
"Toh ba kaine ka rike Ni ba "
"Ta ina!?"
Sake ware baki nayi zan fashe da kuka, ya zira min yatsarshi a bakina.
Ni kuwa na gatsa mishi cizo tare da turo hannunshi daga bakina.
Murmushi yayi tare da d'aga ni, ya riko hannuna muka nufi kitchen, ina shiga kitchen ɗin na zama bakauyiya, dan abinda yafi bani dariya, shine ties din kitchen ɗin wanda aka yi shi kamar kwalba a saman ruwan, muna shiga na dawo da baya ina zare ido, wai yau sai ga Ashraf yana dariya sosai, tsayawa nayi ina kallon ikon Allah, haushi ya bani na kama dukanshi ina kuka, dan na fahimci shi Mutum ne me son shagwaɓa.
Inayi ina dire kafana, hannunshi yakai k'uguna na tare da had'ani da jikinshi, kuka na kara ina dukan kirjinshi.
"Kiyi hakuri kinji bazan kuma ba."
Goge min hawayen fuskana yayi, sannan yajani zuwa cikin kitchen ɗin ya fidda waken kwali sai shinkafa basmati sai kuma kwai, duk abinda ya kawo min sai ya kalle ni, garin barkono ya ciro na kamfanin Gino, ya ajiye min, a hankali yayi ta ciro min abinda zan mishi hatta gishiri.
A hankali na fara aiki shima kuma wai sai ya tayani, nuna mishi abinda zai min nayi, dake daga Ni harshi ba gwajen magana bane, shiru ne ya wanzu a tsakanin mu har na kusan gama dafa shinkafa, yana kallona.
"Ka buɗe min tukunyar kwan nan" nace mishi,
Ba tare da yasaka safan taba abu me zafi ba, Ni kuma ina kallon shi. Ya kamo kan murfin tukunyar, dama murfin glass ce, ai kuwa ya saketa akan kafarshi, yana yarfe hannun da dangale kafar.
Dariya ya sake mara sauti, da sauri na kamo hannun nasaka a bakina, ina tsotsa sannan na cire ina hura mishi iskar bakina nace.
"Kai a wata duniya ce aka taba sauke girki ba a saka abun kare zafi ba."
Langwabe min kai yayi yana yarfe hannunshi, duka na kai mishi ina cewa.
"Rago kawai "
Da naga zai bata min lokacin sai naka kujerar na ajiye shi sannan na cigaba da aikinsa.
"Amma da kin cire mayafin nan kar ya kama da wuta."
Sam ban wani damu ba, na cire tare da cigaba da aikina.
Bina yaƙe da kallo duk inda nayi, yana lumshe idanunshi.
Ta madubin durowar kitchen ɗin na hango yadda yayi min k'uro.
Da sauri naja mayafin na rufe ina tura bakina nace.
"Dama aka sani na cire ne dan kayita kallona."
Tab'e baki yayi sannan ya gyara zaman shi akan kitchen Island.
Ya cigaba da jirana, wasa wasa sai gashi nayi dare a gidan Ashraf ba tare da na halkanta ba, shima tun a mota ya kashe wayar
Shi, sannan muna shigowa gidan ya kashe min nawa, ba tare da na fahimci hakan ba.
Ina gamawa ana kiran magbri, kiran sallarce ta dawo dani daga shirya mishi dinner ɗin, a tsorace na juya muna kallon juna, yana tsaye a jikin kofa.
"Gida!!!"
Lumshe idanunshi yayi sannan ya buɗe akan agogon kitchen ɗin, shida da arba'in.
"Sai na dawo sallah"
Yace min, yasa kai ya fita daga gidan, ina tsaye a gurin.
Ji nayi an rike hannuna zuwa waje, sama ya haura dani ya buɗe min daki ya shigar da Ni, a bakin gado ya zaunar da Ni, yace.
"Kiyi sallah yanzun Zan dawo."
Fita yayi Ni kuma na cigaba da zama can na mike. Zuwa ban daki, ina shiga nayi arba da pant dina da na bari a Oman, dafe goshina nayi ina girmama iskanci Ashraf ko wata uwar zai da dan kanfena (🤣😂😆 Queen Hafsy tace wai shinshinawa yake bani na gaya ba)
Tsaki nayi na ciro abata ina mita, halin Ashraf gaba mutum sai shege jaraba.
Ina fitowa na tsaya niman gabasa, d'uka ke nayi na tadda sallah.
Ina idarwa na fito falo zaman jiran Ashraf, wanda babu shi babu labarin shi.
.....
Ashe bayan fitar shi a masallaci Ghaniyu yake gaya mishi Nannah tana nimanshi, shine bai dawo ba suka wuce.
Koda suka isa asibitin. Ya samu ita da Natashah a cike ban. Bai damu ba ya zauna yana tambayar Natashah nuna jikinta, sai kauda kanta tayi tare da ja mishi tsuka.
Jikin shine ya kama rawa sabida ɓacin rai, ya mike zuwa gabanta ya mari baƙinta sai da ya fashe zai kuma Nannah ta dakatar dashi ta hanyar gaya mishi magana.
"Idan ka kuma tab'ata sai na gaya maka Maganar da zai habaka sukuni a rayuwar ka. Ita SAFINAH da muka zo ance banga lokacin da tayi maka tsaki bane sai yarinyar da ba ruwanta. Kuma wallahi baka isa aurenta ba matukar Ni na haifeka."
Kura mata ido yayi al'amarin uwa alamarine mai girma da daraja, dan haka ba zai taba yin dalilin da Safinah zatayi bakin jini a gurin Mahaifiyarshi.
Cikin shagwaɓa yace.
"Shi kenan amma Ni dai sai na dawo da Uwar yarana kuma ai kin fi kowa sanin baiwata ce, na yantatta, toh yanzun na dawo da ita matsayinta, tunda bazan aureta ba.".
"Wallahi ba zai yiwu ba! A baiwa ma kasamu damar makale mata missing Ammih kece mu koma Oman." Inji Natashah,
"Eh ai dole can zamu koma, tunda na fahimci wannan munafukai ta fara kawo mishi kanta, dan haka kaje ka shirya muku kayan ku Oman zamu wuccin." Inji Nannah
"Yawwa Ammih gwara ki gaya mishi muyi komawar can, kuma zan rike yaranta da amana ko Ammyn"
Ta fada a shagwaɓe, tare da kwanciya a jikin Nannah.
Aikuwa inda Nannah ke shiga ba nan take fita ba, shiru yayi yana jinsu suna zagin hasken rayuwar shi, bai ce mata kome ba, haka suka gama masifar su, yana kallon su.
Kallon daya yayi musu ya sake murmushin mugunta.
Iska yaja tare da fesarwa yace.
"Toh Ni zan tafi."
"Ammyn ina zashi, baki ji dazun iyayen wancan yarinya sun kiraki wai bata dawo ba."
Gabanshi ne ya fad'i ya duba agogon hannunshi,. Tara saura dan ko sallah isha suna shigowa asibitin yayi suka je masalaci sallah Isha.
Tsare Natashah yayi da idonsa, tura mishi baki tayi, abinda ya fahimta zuwan Nannah ya kuma sata fallewa da rashin kunya, cizon lips dinshi nayi cikin ɓacin rai.
"Da fatan ka mai da musu da ita gida dan naga kana shishige mata."
Had'iye yawu yayi cikin b'oye abin yace.
"Baki yarda dani bane."
Ya juya ya fita daga d'akin ya fita da sauri abinda bai wani saba dashi ba sauri.
Duk yadda yaso ya zo da wuri abin yaci tura, haka dai yaja motar yadda ya saba, har ya iso gidan.
Ina zaune na zabga tagumi da hannu biyu, hankalina yana kan agogon falon.
Yana shigowa na kauda kaina bansan ya aka yi kwalla suka shiga bin fuskana ba,
Yana zuwa ya durkusa a gabana tare da zuba min hannuwan shi kan cinyata, kuka ne ya kwace min tare da ture hannunshi ina shasheka.
D'ago Ni yayi tare da rungume ni, yana shafa bayana, sai da yaji ina ajiyar zuciya sannan ya janye Ni daga jikinshi muka fita daga gidan.
Gabana sai Fad'uwa yake dan bansan me zan fad'awa Ummi ba, da girma da babu saurayi gidansa, wannan abin da kunya yaƙe, da wani fuska zan kalli iyayena.
(Kuskure da yan mata suke kenan dubi samarika gida ayita abin da bai dace ba, kuma karku ga laifin Iyaye dan wallahi suna bakin ƙoƙarin su amma haka zaku ga yaran suna ha'intarsu Allah ya kyauta)
Duk ya rasa yadda zai dani, dan ya lura bani cikin nutsuwa balle nasan me zance masa kuka nake sosai.
"Toh kiyi hakuri mana!!!"
Yadda yayi maganar sai da ya kashe min jiki, kallon shi nayi dan ban taɓa jin kalmar hakuri a bakin shi ba, sai yau nice Ashraf yake iya bawa hakuri.
Share kwalla nayi kaina a sunkuye yake.
Gabana bai tsananta Fad'uwa ba sai da muka nufi hanyar unguwar mu, nan naku cikina ya cire guri guda dan dare yayi kusan goma da rabi, bansan me zancewa Ummi ba, dama Abba baya gari.
"Sauke Ni anan zan shiga da kaina."
Kallona yayi cikin damuwa ranshi a jagule yace.
"Ummu Marhus!"
A hankali na d'ago kaina ina kallon shi.
"Kiyi hakuri kinji" gyada mishi kai nayi, zan fita riko hannuna yayi yana cewa.
"Ko zamu shiga ne, na gayawa Ummi na saki kiyi min girki ne."
Zaro ido nayi cike da mamaki Ashraf bai da sense inji bature Ni zai bakowa teku, ya gayawa Ummi ina gidan shi ta tsine min sauran albarka........
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
15.
Abinda mugun rikitarwa wai Ni SAFINAH aikawa Miji, ban daga hankalina ba, sai dai nasan tabbatar ba dani zaayi auren ba.
Cikin ruwan sanyi na kwantar da hankalina na kuma bi yarima Asha kida.
Mutumin da akace zan aura babba ne ba laifi. Sai dai a halin yanzun Ni Uban Y'ay'ana nake so! Inda hankalina da mutuncinta za a kare min, yazo sau biyu dan bai cika zama a kasar ba, sam bai min ba wallahi duk yadda naso gwada cusa shi na kasa karshe na watsar dashi na huta, zuwan shi na biyu ne ya amshi number na ba musu na gaya mishi amma nace mishi wayar tana kashe sai da na shiga na gayawa Ummi ya amshi number na, bata yarda ba sai da ya kirani da wayar a
Abba bayan mun gaisa ne har munyi sallama, shine ta bani wayata tare da gargadin karya ji karka gani na kira Ashraf,
Karku manta nifa ba Yarinya nace tunda na bawa 32 baya amma ake zabga min sharad'i.
Tunda na kunna wayar sakonshi yake shigowa, tsabar fada da masifa. Anyi da Larabci anyi da turanci.
Ban daki na shiga tare da kunna, ruwa sannan na kira shi a wayar. Bugu daya yayi pick ajiyar zuciya yake ajere ajere tsabar ranshi ya baci.
"Kayi hakuri!?"
Shiru yayi na kuma ce mishi yayi hakuri,
Sai da na dauki lokaci ina rarrashinsa sannan yace min.
"Kin manta muhimmanci alƙawari ko? Laifin meye nawa Ajali ki suke bani wahala haka"
"Don Allah kayi hakuri Wallahi baka da laifi Nah ce tace su ja min kunne na fita harkan ka, amma wallahi da kai nake kwana da kai nake tashi"
"Indai haka ne kifito ina jiranki!" Yace min,
"Ashu!!!"
"Babu wani Ashu! Kifito kawai indai da gaske ina ranki"
"Ka rufa min asiri! Wallahi tsine min zasu yi."
"Babu wani tsine miki, SAFINAH ki fito, ina jiranki."
"Don Allah! Nace wallahi zaka ja su Kore Ni a gidan ne.,"
Magana ya fara min jikina ne ya ɗauki rawa, kashe kiran nayi ya kuma kirana, cikin dakiya yace.
"Kina da zabin indai wancan ne kike so toh idan kuma wannan ne. Ranar juma'a yau saura kwana huɗu toh ki fito idan kika ki kuma Wallahi zan saka a satin min ke."
"Don Allah ka rufa min asiri wallahi wannan karon kashe Ni Abba zai yi, kuma ga Ummina Don Allah ka kyaleni"
"Shi kenan tunda ban isa dake ba, kije Amma wallahi bazan fasa abinda nayi niyyar tunda haka kike so"
Gabaki d'aya na rude na kuma shiga damuwa sosai, gashi ya kashe wayar shi duk yadda naso abu ya faskara....
★★★
*★Jordan★*
Al'amarin ya sabon Sarki a ranar da ya iso masarautar ya fara gabatar da nashi tsarin
Aikuwa Marhum ya miqe tare da daga murya yana cewa.
"Kai waye da zaka gindaya mana sharuddan muku ma mubi, Ashraf ma yake mana yadda muka so bai tsira ba sai kai da muke maka kallon bakon haure."
Bilal mugune fitar farko, kanshi a sunkuye, bai kalli kowa ba ya sauke hannu tuni aka fitar da Marhum suka je aka yanke mishi harshen aka barshi baki duk jini.
Tunda akaga abinda ya aikata take kowa ya shiga hankalinsa kuma yace.
"Daga yau ko da kiyashi za a cire a sanar min sannan anabi jadawayen shigowa da abincin cikin masarautar,dan bana son ana kawo kome."
Take hankalin kowa ya tashi musamman barayin Masarautar. Bilal yasanya su a cikin uku Bala'i.
Dan rufe asusun bankin kowa tare da kwace min wasu takardun su masu darajar, sannan ya shiga bin yan mata cikin masarautar, ana kawo masa su yana kwanciya wasu. Duk wanda yayi magana toh Allah ya yarda za'a kashe shi daga shi har yar tasa, ga bayi basu tsira ba.
Shi kanshi Ukshe sai da ya tattara jikokinshi mata, yasa aka tsallaka dasu Saudiya, sannan zuciyarshi tasami nutsuwa, duk wasu manyan fada sai da Bilal yasa aka sauke mukamansu, daga cikinsu har da Uzaif da Ammar.
A fujajjan suka fara niman Ashraf.
(anya zasu same shi🤔🙄)
★★★
Oman...
Natashah sun dawo, cikin nan ko wata uku bai yi ba, aka kusan cika daki da kayan baby. Tsakaninta da Aamih da Aanih hantara da kyara, tun can ma yaran sun san ba sonsu yake ba,