Showing 102001 words to 105000 words out of 108344 words

Chapter 35 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt

27 Nov 2024

4834

fita ba cin mutuncin kamar me, tana gamawa nace.
"Nannah! Iya girmamawa muna baki muna mutuntaki, muna kuma miki biyayya, Nah Ashraf d'anki ne mu kuma matan shine, Nah abu daya zuwa biyu, Ashraf dai ba sauran shi zaki yi ba!? Sannan babu abinda zaki iya mishi, mu matan shine sabida nutsuwar shi da jin daɗin shi yana gare mu, iya biyayya yana miki amma tunda kin nuna ke din surukar zamani ce tabbas zamu nuna miki zamanci."


"Toh mara kunya! Kuma nace kar na kuma ganin Ashraf a dakunarku."


"Wallahi bakin isa ba, Dole ya dawo mana." Inji Natashah


Abin Nannah yayi yawa, ta addabi rayuwarmu akan wata shirmenta na daban, shi.


★★★
Ina kwance a falo, sai gashi ya shigo yana hucci tunda naga haka nasan itace ta gaya mishi abinda muka mata.
"SAFINAH! Har rashin kunyar ki takai keda Natashah ki zagar min dan baki da tarbiya."


Wani kallon banza na mishi sannan na kauda kaina nace.
"Toh su tarbiya manya! Ai matukar tace bazata fita harkan mu da kai, wallahi abinda muka mata baya ga komai ba"


"Mahaifiyar tawa?! Safinah kike gayawa Maganar banza."


D'aga hannun shi yayi da niyyar zai mare Ni, sai ga Zoyah tashigo tare da rike mishi hannu.
"Haba Sultan , taya zaka d'aga hannunka akan fuskar mace, nida nasan gaya maka abinda suka yi zai kara tun zuraka da ban fara ba, na zata bazaka ji ciwon abinda suka aikata bane."


Riko hannunshi tayi suka fita ina zaune a gurin ashe kuka rahama ce, domin kuwa ban tab'a daukar al'amarin an ci ba, Amma ba komai.
Kiran Ummina a waya, kuka nasaka mata, sosai ina bata labarin abinda Nannah takei mana. Murmushi tayi sannan tace..
"Ina SAFINAH take, ajiye miji a gefe kiji da kanki in cikin wannan karon babu matsala."


Gaya mata abinda mukayi nayi ta min fad'a sosai, sannan ta kuma ce na bashi hakuri, sannan tace.
"Ki kwantar da hankalinki"
Wayyo na dakyar na gama wannan pagen nayi gyangyadi yafi sau biyar😂🙄
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


4️⃣7️⃣


"Ummina! Ya dauki zafi fa sosai."


" Eh mana ai dole ya dauki zafi Mahaifiyarshi ce fa! Kuma duk d'a nagari dole yayi kishin Mahaifiyarshi, dan haka ki bashi hakuri sai a wucce gurin"


Ciki sanyin jiki nace mata.
"Toh shi kenan zan yi yadda kika ce Ummina"


"Yawwa yar albarka! Wancan watan abokin mijinki da wasu mutane sun zo niman auren Batul."


"Toh wa kenan a cikin su?!"
"Fahad?!"
"Laa! Aukuwa ta more miji, dan bai da matsala, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya."
"Amin Ya Allah"
Munyi hira da ita sannan na kashe wayar.


Ina ta zuba ido naga shigowar shi ko Natashah babu su babu labarin su.


Can wajen maraici sai gashi ya shigo, ko takaina bai bi ba. Ya shiga dakin yarana ya fara diban kayan Aanih zai fita dashi.
"Wallahi ka kaiwa wata mace Y'ata sai naci mutuncinta sannan na tattara yarana mu bar maka gidan, idan kuma kana ganin bazan iya bane bismillah"


Na cigaba da abinda nake a falon, zuwa yayi gaba kamar zai rufe Ni da duka, d'ago kaina na kalle shi a tsanake sannan nace.
"Wallahi duk ranar da zuciyarka ta baka shawara ka tab'a Ni da sunan duka."


Gyara zama nayi ina rike kofin zumar da nake sha. Cikin isa da na koya daga gare shi, hannunshi naga ya kawo dai dai wuyata.
"Lallai Ashraf! Toh ka tab'a Ni ka gani idan baka da hankali! Wallahi Ni ba Natashah nace da zaka daketa tayi hakuri dan tana sonka. Idan ka tab'a Ni sai kayi dana sanin yin haka har karshen rayuwarka, dan kaga ina kyale ka ba tsoronka nake ji ba, igiyar auren tsakaninmu nake girmamawa, sannan inda akan abinda nayiwa Nah ne kaje Ni na yafe mata kai Ni ka sallame Ni dan ko baka sake Ni ba zan fita na bar maka gidanka."


Ina gama fad'ar haka nabi gefenshi na wucce, hakurin da Ummi tace na bashi ma na fasa, dani dasu shege ka fasa.


....... Ashe a lokacin da ya shigo ya Same Zoyah a falon Nah, tana bata hakuri tare da cewa.
"Kiyi hakuri Ammyn wallahi sai yanzun na fahimci abinda yasa kike rike shi, Ashe ba lafiya ce dake ba, kuma daga yau bazan kuma niman shi ba ya cigaba da kula dake Ni farin cikiki shine nawa."


Zama yayi kusada Nah cikin gajiya kwantar da kan shi yayi jikin kujera, zuciyarshi tana cikin kewar SAFINAH, yasan da itace da tuni ta cire mishi takalmin kafar shi da Safar ta shiga matsa mishi, mik'ewa yayi zai bar falon. Zoyah tace,


"Tunda ka shigo kaga yadda muke ai ka tambayi lafiya, amma baka yi ba. Sai ma tashi da kayi zaka Duba wata kaskantaciyar matar ka wacce bata san daraja kanta ba balle na iyayenta, dan duk wanda zai bud'e baki ya zagi Uwar wani toh bai san darajar tasa uwar ce ba."


Ware idanunshi yayi akanta mamaki na kama shi, ince itace ranar ta hana shi barci akan ya zo gurin Ammyn shi yau itace ke ihun.


Nad'e hannunshi yayi a kirji sannan yace.
"Ina jin ki!"
"Toh wancan bakar da lafiya al'amarin ta akan na kowa ce ita da Natashah suka zagi Ammyn."


Kuka tasaka tare da girgiza kanta sannan ta gaya min shi komai bayan ta gama sannan ta kara da cewa..
"Banga amfanin zama da su ba, amma kayi hakuri idan na maka shishigi, sai dai Ammyn ba Mahaifiyarka bace kai d'aya nima Uwata ce."


Ko gama jinta bai yi ba, ya shige dakin Natashah ya sameta tana kwance, shine ya maka mata duka a cinya, ya karta mata rashin mutunci sannan yace.
"Kar na kuma ganinki a shashin SAFINAH, tunda kina da komai na buƙatarki kar na ganki ko a waje."


Dake tana tsoron shi hakuri ta bashi, Ni kuwa yar tawaye shine da yazo wai zai mare ni, na gama lura dashi hannunshi kaikayi yake mishi. Zan dauki kowacce iskanci amma abinda duka, dan baka isa ka tab'a Ni da rana da dare ka biyo NI kana min dan murya ba, Allah kayi kadan.
Tun daga lokacin da baki ya taba lafiyata sai ya daina shigo min, ranar da yake guna ma baya shiga, tattara shi nayi na watsa gefe.


Hhhhhh mayen mata dagaske zuciya yayi akan babar shi, ganin munyi kwana uku bamu hadu da Natashah ba, bayan Sallah la'asar na shiga gurinsu. Zoyah da Nannah suna zaune ana gulmar. Suna ganina suka firgice, Salam kawai nayi musu, sannan na wucce inda zai sadani da shashinta, tana kwance da katon ciki a gaba.


"Sannu Kyautar Allah! Irin wannan zungurerren cikin ko sojoji biyu zaki haifa mana."


Tashi tayi ta zauna tana murmushi, gashinta da ya barbazu take tattarawar.
"Maman Ablah! Ai nazata kinyi fushi dani ne baki gani na kenan kinki zuwa."


Tashi nayi na amshi bam din hannunta na daure gashin ta, sannan na zauna kusada ita.


Mik'ewa tayi zata kitchen nace.
"Dawo Ni na koshi, indai ba wahalar da sojojina zaki yi ba."


"Wallahi ba sojoji bane yan mata ne, irinsu Aamih."


Can sai gata da katon bowl me dauke da ya-yan itace ta ajiye min a gabana, sannan ta zauna a kasan capter.

Kallon kofar da nashigo tayi, sannan ta kalle ni, akwai magana a bakinta, sai dai kamar tana cikin tsoro, dafa kafad'arta nayi cikin kwanta da hankali nace.
"Banzo dan na sanyaki damuwa ba, ya hanaki zuwa gurina ko?! Gashi Ni nakasa hakuri na biyo ki. Amma tunda kina lafiya zan koma yanzun."


"A'ah Maman Ablah, kawai nice bana son fita. Amma Insha Allah zaki ganni."


"Toh shikenan tunda kince haka, amma."


Mun jima muna hira kafin na mike zan bar gurinta, mik'a min kayan fruit din tayi. Amsa nayi tare da godiya.


Inda nabar Nah da surukarta suna zaune, haka na ficce abina.


★★★
Da dare ina zaune nasaka laptop a gabana ina aiki. Zama shirun ba dad'i shine na nemi aiki da wata gidan jarida amma a Internet. Bai sani ba na nemi aikin kuma, kuma iya editing kawai suka dauke Ni nake musu.


Kuma zasu biyani kudi me kyau, dan haka na amshi aikin hankalina kwance, yanzun ma sun turo min da editing labarin da zasu yi amfani dashi shi. Ban ji shigowar shi ba, sai rufe min laptop din da aka yi.
Ban d'ago kai na mishi magana ba na buɗe abuna na cigaba da aikina.
"SAFINAH! Natashah bata gaya miki nace kar na kuma ganinta a shashinki ba, kenan kar na kuma ganin ki a shashinta."


"Ai kace yanzun mun shiga zamanin da za a hanaka walwala kenan?! "


Dake hankalina yana kan aikin da nake, na bashi amsan ashe yaji haushi na, daukar system din yayi zai buga da bango.
"Wallahi kana bugawa, na gama zama da kai har duniya ta tashi. Wallahi da ka fasa min shi gwara ka sallame ni, zai fi sauki akan ka fasa."


K'arban abina nayi sannan na cigaba da cewa.
"Ba zai yi kaki sauke hakkin da ya rataya akanka bayan ka hanamu walwala da juna sannan kayi tsammanin zan zauna bakin cikin ka ya kashe ni, bana fatan cigaba da zama cikin wannan kuncin rayuwar, kaje ka zauna da matar so da kuma Nah, sai dai kasani idan bakayi a hankali ba, hakkinmu Allah bazai kyaleka ba, kaje mun Barka da Allah."


Duk yadda yaso ya kuntatta min naki sabida na gama fahimtar shi na kuma san halin su.


Saima nice ke kuntatta musu, domin a gabansu zai gaya min magana baki kula shi, a bayan idanun su kuwa fasa juna muke, kuma har zuwa wannan lokacin bai shigowa dakina. Nima kuma bai dame Ni ba, dan baya gabana. Sai dai nasaka a raina matuƙar na haife cikin jikina, sai na bashi mamaki, dan ajiye mishi jaririyar zanyi na koma gida abuna na gaji da iskancin Nah da Zoyah, sun juyar mishi da hankali, baya gane me kyau ko mara kyau, shi dai burin ya ci min mutunci.


Bayan wata guda.....
Ina ƙoƙarin fidda su Aamih, su tafi makaranta, sai ga Zoyah. Dan har yaran sun fito, saura shi, yana dakin Zoyah. Nazo wuccewa, sai da nazo wuccewa kawai tazo zata bangaje Ni nayi maza na kauce sharrinsu ya koma kansu, ta fadi a gurin, ta fasa ihu.


Fad'uwar ba wata babba bace, amma tana kaiwa ƙasa sai ga jini.


Ashe yaji muryan ta, shine ya fito a guje.


Gani na a tsaye ya sashi yiin kanta yana tambayarta, cikin kuka take gaya mishi ai nice na tureta, gashi nan na zubda mata cikinta da tasamu, dan na tsaneta.


D'ago jajjayen idanunshi yayi akaina banji komai ba, sai ma kauda kan da nayi....




*Don Allah kuyi hakuri tun jiya rabonmu da wuta! Shi yasa zaku pagen dan mitsitsi idan muka samu wuta zuwa dare Insha Allah zan yi 48🤔 Wannan labarin yayi tsayi da yawa, da alamu sai mun shiga book 3 kenan Allah yayi mana jagora yasa mu dace duniya da lahira*
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*


5️⃣0️⃣
Ganin har lokacin Aamih tana aman kumfa, na shiga cikin kitchen da mugun gudu na dauko mangyad'a na d'ura mata, komawa kan Aanih nayi, itama na juye mata, ita Maryamah tana amai, Husnah shiru, banga Ablah a falon ba.
"Ablah!!!!!!!"
"Ummu"
Naji muryan ta, a sukwane na juya, jikina na rawa.
Ganinta nayi rike da wani apple, kuka ne ya kwace min, na janyo ta sannan na dauki wayata, tsabar rawan jiki, dakyar na sami Number shi, yana ɗauka na fashe da kuka.
"Kazo yaran suna cikin hatsari, kowani lokaci zasu iya mutuwa."


Kashe wayar nayi yi ina kuka, bai yi cikakken minti biyar ba sai gashi. A gigice shida Ghaniyu, suka dauki yaran. Ni kuma na dauki Ablah har na kwace apple din sai na saka kuka kuma baci zata yi ba, dole na bar mata, muka bi bayan su.


Tunda muka shiga motar nake kuka, ina kallon yaran.
Har muka isa asibitin aka shiga dasu d'akin gaggawa, haka su Dr Fu'ad suka yi takaiwa da komowa.


Zuwan wani likita dan kasar Lebanon, yazo wuccewa ya kallemu. Har ya tafi sai ya dawo yasaka hannun ya amshi, kuka tasaka tana ihun ya bata abinta, tafiya yayi da apple din, babu wanda yayi Wani yunkurin, dan muna cikin tashin hankali.


Jaririn Natashah aka fara fito mana da shi, yaron me kyau kamar Ashraf.
Muna cikin wannan halin Dr Fu'ad, ya fito tare da kiran Ashraf zuwa Ofishin sa, yana shiga yace.
"Fu'ad ya jikin su?!"
Girgiza kai Dr Fu'ad yayi sannan yace.
"Kayi hakuri! D'aya ta rasu"
Zaman dirshan yayi a Office d'in, tasirin kiran sunayen Allah ya rike shi, kafin ya d'ago kai yayi yace.
"D'ayar fa?!"

"Sakamakon bata mai da akayi ya karya ƙarfin gubar, tana nan sai dai ta jikata sosai."


Bai kuma ce komai ba yafito daga Office d'in.

Tunda ya fito ya tsare Ni da ido, gabana ke faduwa, kukan da nake toshewa ne na shiga yin shi sosai.
Kauda kanshi yayi sannan yaje gurin Ghaniyu yayi mishi magana, fitowar Likitan da ya karbi apple a hannun Ablah yazo zai magana, Ashraf ya hana shi yace yaje yace yaje ya sami Dr Fu'ad.


Nannah ya gayawa mutuwar Husnah, a fusace ta mike, shi kuma ya bar gurin zuwa dakin da gawarta take ciki,
Ina cikin damuwa Nannah yazo zata kara min, dan d'aga hannun tayi zata mare ni na riƙe hannun.


Sosai ta nemi duka na, na hana faruwar, haka Rigima ya kaure a tsakanin mu, fitowa da gawar na kurawa Yarinyar ido, naje kan gawar na sake wani Irin kuka, me mugun cin rai.


Rike hannunta nayi nace.
"Wani irin laifi nayi haka da nake fuskarta hukunci haka, Ya Allah na tuba ka yafe min zunubi na."


Fitowar Nurse daga d'akin gaggawar, tace.
"Yallabai d'ayar ma ta cika."

Ji nayi zan fad'i yayi maza ya sake jikin gadon ya rike Ni, gam nake rigarshi ina sauke ajiyar zuciya, kafin nace.
"Alhamdulillah."
Cak naji hawayena ya kafe, tabbas lokaci yayi da zan bar Ashraf, dan Natashah tana cikin mawuyacin hali itama, haka suka fidda yaran, muka nufi gidan.


Anan aka kira masu wankar gawa, suka musu shi kuma Ashraf ya kira su Ummi ya gaya musu, zazzaɓi ne ya rufe ni. Dakyar yasani a gaba naje naga gawarsu, nayi musu addu'a. Sannan na fita, wani irin dangana nake ji a raina, sai dai bana jin zan cigaba da rayuwa a jordan.
Tun daga ranar ban kuma ganin Ashraf ba, har sai dasu Ummina suka zo naga idanunshi, abinda nake gani a cikin idanunshi yana kara rikita min lissafi, domin kuwa k'iyayyar da ban san da ita ba yake nuna min, Ummi da Umma suka zo sai Abba, Dudu yana Ukraine yana karatun da matar shi.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login