Showing 9001 words to 12000 words out of 56271 words
Chapter 4 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt
amsa masu sukayi da toh, Jiki asanyaye suka zauna duk basu ji dadin abunda khadeeja ta aikata ma sojojin ba
"Dan Allah kuyi hakuri Idan mun 6ata maku rai" sarah ce tayi masu maganar
Murmushin yaƙe suka sakar mata"kada ku damu, ai munyi maganinta yanzu" juyawa sukayi atare suka nufi kitchen, abun da suka daura kan gass harya fara ƙonewa shaf shaf suka ƙarasa Yin girkin.
Khadeeja dake adaki, Sai kuka takeyi tana bubbuga ƙofa da hannunta kamar zata 6alleta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta
Gajiya tafara Yi da buga ƙofar, Ta Juya zata je ta kwanta karaf idanuwanta suka sauka akan Wayar dr jazz da suka bari kasa, Ga kayanshi daya bari riga da wandon shadda, jiki na 6ari taje ta dauki wayar, duk da bata Iya amfani da ita ba sai da tayi ƙoƙarin kunnata, saboda ta haddace Yadda jazz yake latsawa agabanta, Cikin sa'a ta kunna wayar haskenta Ya kawo,
Gefen gado ta zauna tana yin shessheƙar kuka
Ta soma kacaccala mashi wayar, kasancewar babu password a wayar Yasa ta samu damar dannata son ranta, batare da saninta ba ta shigar mashi contact dinsa adai dai kan sunan My Mom ta latsa Kira, Ringin wayar ta fara Yi, Khadeeja ta natsu tana jiran jin wazai Yi magana kamar yadda taga Ana yin amfani da ita ayi communicating
Kiran wayane Ya shigo layin Mom turai, a lokacin tana acikin bedroom dinta ita da sir mubarak akwance saman gado, ita kadai ce idonta biyu, shi Sir mubarak Ramuwar baccin dabaiyi ba jiya yake Yi.
Jin wayarta na ruri ne Yasa ta sauko daga kan gado, taje gaban mirror ta duba sunan mai kiranta
Mamakin ƙarara akan fuskarta ganin sunan My Own Son Ya bayyana akan screen din wayarta
Murmushi tadan saki tana fadin"Allah Sarki My son, Ciwo Ya hana kazo inda nike shiyasa ka kirani awaya, bari Naji me Yake buƙata" ta faɗa tare da ɗaga wayar ta kara a kunnanta, hada ƙoƙarin yin sallama.
Shessheƙar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruɗani ta furta"Wacece ke kuka"?
*Daga Alƙalamin Boss Bature🫶*
*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*
_~*✊💋BOSS LADIES WRITERS✊💋✊*~_
_🔥💫THE PRISONERS🔥💫_
~TAKUN ƘARSHE~
Daga Alƙalamin Boss Bature
Dedicated To Aunty Kubra💋
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty❤._
_______________________✍️
Shessheƙar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruɗani ta furta"Wacece ke kuka"?
"Khadeeja ce, Ina Jazz ɗina Yake" kafin Turai ta bata amsa kiran Ya katse, abun ya ɗaure mata kai, Ya akai wayar Jazz taje hannun mace? Maimaita sunan khadeeja tayi aranta kafin da sauri ta fito daga dakin ta nufi bedroom dinsa.
A lokacin suna daga zaune gefen gadon shi, Shi da Ibad dake bashi abinci abaki, hannun ibad ruƙe da plate with spoon, har yayi wanka ya sanya jallabiya a jikin shi.
Shigowa mom Turai tayi dakin gaba daya suka dago suna kallonta.
Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da fara'a ta ce"My son, how's your body? I hope you're getting better now."
In a cool voice yace"Mom da sauki, ina samun kulawa a wurin ƴan uwana, yaya Zaki ma bai jima da fita ba"
Murmushi tasaki tana kallon Ibad tace"our last born, Sannu da ƙoƙari, kana Ji da ɗan uwan nan naka"
Ta6e baki yayi kafin yace"to ya zanyi mommy, daddy ya 6allo mana aikin Jinya, Yana can kwance Kinyi mashi wanka Yana bacci, Ya ya Zaki kuma ya gudu ya barni da aikin bashi abinci abaki"
Tuntsirewa tayi da dariya, shima jazz ɗin dariyar yake Yi, shi kuwa ko ajikin shi bilhakki dagaske Yake Yin maganarshi.
Tsagaiwata tayi da yin dariyar tace"Ibad na fahimci maganata ta tsaya maka aranka, Nifa ba daddynku nayi ma wanka ba, Taimaka mashi nayi ya rage kayan jikin shi, idan ba haka ba ni taya zan Iya yi ma shi wanka ƙato dashi, Kallarni ka gani Ƴar ƙarama dani" hura mata hanci yayi batare da yace komai ba
"Jazz where's your phone"? Ta faɗa tana kallon shi.
He was silent for a while, Yana ƙoƙarin tuna inda Yabarta.
"Mom, kamar nabarta a gidan Yaran da nake Kula da lafiyarsu"
Miƙa mashi wayar tayi"Duba ka gani, wata yarinya ta kira da layinka, tana kuka, wai jazz dinta take nema"
Da mamaki akan fuskarshi Ya kar6i wayar, Yana duban Kiran da akayi da layinshi, tunkafin Ya danna kiran ranshi ya bashi cewar Khadeeja ce.
Da sauri Ya kira layin, ringing uku ta ɗauko tana fadin"Ni ku ƙyale ni tun da ba zaku bani muyi magana da Ya jazz ba, kun wani isheni da kira,"
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa, jin muryar deejan sa, mom turai da Ibad sun tsareshi da ido suna kallon fuskarshi.
"Khadeeja ni ne fa" a kwance take kan gado Jin muryarshi Yasa Ta yi zumbur ta miƙe zaune tana fadin"Ya Jazz dama baka mutu ba"? da wani irin farin ciki ta furta maganar.
Murmushi ya saki tamkar yana a gabanta yace'ban mutu ba My deeja, lafiyata qalou, Yanzu haka ina agida, wannan layin da kika kira, Na mom ɗina ne"
Shagwa6a ta sanya mashi" I hate U ya jazz, Shine ka manta dani, duk nabi na tashi hankalina akanka ashema kana gida"
"No, it's not like that, Khadeeja. I miss you. I've been thinking about you tun time din dana dawo hayyaci na"
Kallon juna mom Turai da Ibad su ka yi alokaci ɗaya, kafin suka maida dubansu gare shi.
"Faɗamin Kin yi breakast da safe kuma kin sha maganinki"?
"Ni ban sha uban komai ba, babu wanda ya bani, waɗancan ƙattan da aka bar mana agida jiya suka cinye mana abincin mu, yau kuma na sanya su dole su girka mana, aiko suka shiga kitchen suna yi, basu sani ba na ɗauki bindigarsu nadinga tsoratar dasu hawwa......." hankalinta kwance take kora mashi jawabi, a firgice ya ɗago da ido yana kallon Mommyn su, ga dukkan alamu suna jin maganar da deeja take Yi mashi,"
Muryarshi a ruɗe ya furta"Dagaske kike ko wasa"?
Dariya tasaki kafin tace"Wallahi dagaske nake maka, don ma sun min wayau sun kulleni a ɗaki, ai da tuni na kakkashe su"
Zaro Ido Ibad Yayi, Mom Turai tayi dariya, gani su ke yi kamar zolaya ne abun da yarinyar take faɗa ma jazz, shi kuwa yasan zata aika, Fiye da haka ma shiyasa ya ɗauki maganar ta serious.
"Khadeeja, Ina fata baki raunata kowa acikinsu ba"
"Wlh ban kashe kowa ba, ai na faɗa maka sun ƙwace bindigar"
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke
"Dan Allah My baby girl kada ki ƙara yunƙuri ɗaukar bindiga kinji ko?
"Toh,"
"Yawwa ai nasan kina jin magana ta, idan har kina so na zo gidan karki ƙara rashin ji," muryarta a ladab ce tace"In sha Allah" kamar wata mai hankali
"Good Girl, Kafin nazo kiyi wanka, Kici abinci ki ƙoshi," tace "Toh"
"Namanta ban tambaye ki ba, Where did you find my phone?"
"Aɗaki kabarta saman kayanka, nan na ɗauke ta"
"Okey, pls Ki ajiye min inta, kada kice zaki yi wasa da ita"
"Toh, Idan kazo gida zaka gyara min gashin kaina kuma kayi min kalar kitson kalaban nan da ka ta6a yin min"
Da sauri ya ɗago suka hada ido da mom Turai.
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Eyyeh, Lallai ashe Jazz har kitso ka Iya yi ma mace, gama wayar ka bani labari"
da zolaya ibad yace "mommy kin huta, da zuwa saloon, daga yanzu Jazz zai dinga yi maki gyaran gashi" miƙa mashi hannu tayi suka tafa kamar wasu abokai.
Duƙar da kai Jazz yai"Khadeeja sai anjima, please take care of your self for me"
"You too," sallama su ka yi da ita.
Kunya duk ta kama shi, sai faman sunnar dakai ƙasa Yake Yi.
"Jazz kai muke sauraro ni da mommy" ibad ne yai maganar.
Fuskarshi a yamutse ya furta "Khadeeja ce yarinyar da daddy ya baku labarin ta, She's mentally ill. There's no love between us. ina kula da ita ne saboda rashin lafiyarta"
mom turai da raha tace "Don't lie to me. I'm your mom and I understand you. Yarinyar nan dai sonta kake Yi" shiru yayi bai ce komai ba, don yasan da wuya ta fahince shi, zolayar shi suka dinga yi tun yana ɗaure fuska har yakai ga sakin dariya.
______________________✍️
A hankali Motar su Ta shigo gidan, bayan jami'in yayi parking, Salsabeel Ya fito daga ciki Yayi mashi sallama kafin ya nufi ƙofar shiga falo.
Yana shiga falon ya hango su Hawwa zazzaune kan carpet, An jera masu kayan abinci saman Tray, komai da Khadeeja ta ba sojojin Umarnin su girka masu saida suka girka shi, tun daga kan Chicken pepper soup, fried fish, Chips, wainar kwai, Doya da kwai.
Gyaran murya yayi masu tare da buɗe baki Yayi sallama, A hanzarce suka ɗago suna kallonshi, aiko da sauri suka miƙe da sauri hada gudu suka nufeshi, ɗaya bayan ɗaya yake rungumarsu a jikinshi.
"Ya salsabeel Ina kaje tun jiya baka dawo ba, Ka tafi kabar mu da kewarka"
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Eyyah am sorry, nima nayi kewarku, ay min afwa wani uziri ne Ya ruƙe ni, amma tunda na dawo yanzu komai ya wuce"
Yayi maganar idanuwanshi akan fuskokinsu
"Ina Khadeeja"?
Nan fa suka haɗa baki suna bashi Labarin Ta'asar da Khadeeja tayi ma sojojin da aka bar masu.
Hankalin shi ya ɗan tashi sai dai baiyi mamakin abun da Khadeeja ta aikata masu ba, ya riga daya san halin kayanshi.
Jin motsin tafiyar mutane yasa shi saurin kai idonshi inda suke.
Fitowarsu kenan daga kitchen, wanke wanke Suka tsaya yi a kitchen din sun gyara komai da suka 6ata, har sun maida suturarsu.
Wani ɗan iskan kallo suka watsa ma Salsabeel, Hakan Ya tabbatar mashi da ransu Ya 6aci sun harzuƙa.
Tamkar mai jin shakkarsu ya furta"Am...dan Allah Kuyi haƙuri, Yanzu na shigo gidan su Hawwa suke bani labarin abun da khadeeja ta aikata maku, banji dadi ba, Yalla6ai ne bai bani damar dawowa da wuri ba, da duk hakan bata faru ba....."
Fuskokin su babu annuri ko miskala zarratin
Tiger yace"malam bamu buƙatar Jin komai daga bakin ka, tun da ka dawo gidan falillahil hamdu, Ka ci gaba da kula da ƴa'ƴanka, Mu kaga tafiyar mu sannan duk abun da ka gani badai dai ba kada ka tuhumi kowa, Khadeeja ce sila" Rai a6ace Ya ƙare maganar, Ya nufi Dining table Ya duƙa ya dauko masu bindigoginsu.
Army boy yace"Zan baka shawara, Yarinyar nan ku gaggauta kai ta Gidan Mahaukata, can ne Yafi dacewa da ita, Idan ba haka ba wata rana zaku kuka da kanku, don wannan tafi bomb bala'e"
Army na kammala yin maganar suka nufi ƙofar fita daga falon, da sauri salsabeel Yabi bayansu yana basu haƙuri.
"Dan Allah Ku tsaya, bai kamata muyi irin wannan rabuwar ba, nasan ban kyauta maku ba, amma dan Allah kuyi hakuri kada ku ruƙe mu aranku"
Ta6e baki su ka yi, Tiger yace"hmmm bakasan masifar da yarinyar can taso taja mana ba, shiyasa har kake da ƙwarin gwiwar Yi mana magana, Badan Allah Ya kawo mana mafita ba, da yau mu dukan mu zamu baƙunci lahira"
Jiki asanyaye Salsabeel Yace"ina ƙara baku hakuri, Allah Ya huci zuciyarku"
"Dama ahuce take, bamu hanya mu wuce" matsa masu hanya yayi, duk bai ji ɗadin abun da ya faru da su ba. har suka fuce bai daina bin bayansu da kallo ba.
Sai da yajiyo tashin motarsu, tukunna ya sauke ajiyar zuciya, Ya juya ya kalle su Hawwa.
"Awani ɗaki suka Kulle ta"? Sarah ce Ta nuna mashi kofar dakin, Azafafe Ya nufi upstairs, Yana isa bakin ƙofar Ya sanya hannu ya murɗa key din.
Tsabar 6acin rai ko sallama baiyi ba ya faɗa ɗakin, a gaban mirror ya taras da ita zaune, ta sanya undy ta jashi har saman kirjinta, ga dukkan alamu wanka tayi shine ta zauna tana gyara jikinta kamar wata mai hankali.
Gyaran murya yayi mata, zumbur ta miƙe tana faman ƙyafƙyafta idanuwanta, hannayenta biyu ta ɗaura asaman kanta kafin tace "sun faɗa maka abunda na aikata"?
Takaici ne Ya ishe shi wato har tasan ta aikata badai badai ba.
"Meyasa"! Aɗan tsawace Ya jefa mata tambayar, Ta6e mashi baki tafara yi alamar zata fashe mashi da kuka da sauri Ya zare mata ido haɗi da cewa"Yi min shiru! kar in kuskura Inji kukan ki," da buɗar bakinta sai cewa tayi"ai dama ba ka so na, Kafi son su hawwa, shiyasa kake min fada" sassauta fushin fuskarshi yayi tunawa da karancin hankalinta
"Am sorry, raina ne Ya 6aci, bawai bana sonki ba, pls ki daina rashin ji dan Allah"
Washe mashi baki tayi "Nadaina, bari na ɗauko maka wayar Ya jazz, na kira shi har mun gaisa ashe bai mutu ba Yana nan da ranshi" ta faɗa tana dariya ta juya ta nufi gado ta dauko wayar taje ta miƙa mashi Yasa hannu Ya kar6a.
da mamaki yace "Taya akai ki ka yi waya dashi"? Watsa hannu tayi"nima bansani ba, na daddana saina kira,"
Call log Ya shiga, numbar farko data bayyana ta Mom turai, Ya danna ma Kira, Bayan ta ɗaga wayar cikin girmamawa salsabeel Ya gaishe da ita, daga bisani Ya tambayeta Ya jikin jazz, tace mashi da sauki, bata tambayi wanene shi ba sai ta ba Jazz wayar suka cigaba da yin magana,
Hankalin shi ya kwanta Jin muryarshi raɗau tamkar bai ta6a yin ciwo ba, sun jima suna yin wayar har jazz ya tuna mashi da maganin khadeeja kafin suka yi sallama Ya adana mashi wayar a hannun shi
Tattara Yaran yayi a falo, hada shi suka zauna suna kwasar girkin da Su Tiger suka Yi masu, dama da yunwar shi Ya dawo, aikuwa dai sunyi kullu wash rabu hani'an, su mama Tiger An Iya girki, sai santi su ke yi, musamman khadeeja, bakinta dama dama da maiƙo.
*🌹ZEENATU🌹*
Baiwar Allah, Ta hana zuciyarta sukuni, tun lokacin da tayi masu Benazir la6e a toilet, kunnuwanta suka jiyo mata maganganun da suka tsaya mata aranta, haƙiƙa tayi danasanin sauraransu, don tun safe take faman jinyar zuciyarta, kiri kiri taki cin breakfast dinta, har lunch bata ci ba, yini tayi a cikin bedroom dinta da raɗaɗin abun azuciyarta, Tani tayi ƙoƙarin shawo kanta donta faɗa mata meke damunta taƙi ta sanar da ita, ba irin lallashin da ba ta yi mata ba amma taƙi sakin jikinta.
A yanzu haka tana daga kwance saman prayer mat, ta lullu6e jikin ta da dogon hijabinta launin milk, daga gaban dardumar qur'anic stand ne an bude shi alamar karatu take cikin yi bacci yayi awon gaba da ita.
Damuwar halin da take aciki Ya hana Tani samun sukuni, fargabanta kada ace wani abunne ke shirin faruwa da ita shiyasa ta canza mata.
Shigowa ɗakin tayi domin gyara mata bedroom din, karaf idanuwanta suka sauka akan zeenatu dake ƙudundune tana bacci.
Cikin takun sauri Tani ta nufi dardumar, aranta tana fadin'baiwar Allah, daɗina da ita duk halin da zata shiga bata mantawa da yin ibadarta"
Zuƙunnawa tayi agaban prayer mat din, muryarta ƙasa kasa ta ambaci sunanta.
"Zeenatu! Zeenatu! Ki tashi ki koma kan gado ki kwanta, kwanciya kan prayer mat, bai da amfani jibi yadda ki ka ƙudundune kanki duk kin takure kanki"
Tani sai zuba takeyi babu alamun zeenatu zata farka,
"Oh Oh ni wannan baccin naki bame ƙarewa bane da alama, dan Allah ki tashi" still bata tanka mata ba.
Hannu ta ɗaura saman jikin zeenatu ta bubbugata, nan ma taƙi farkawa, lokaci ɗaya Tani ta fara Jin fargaba acikin zuciyarta, hankalinta yayi mugun tashi, a ruɗe ta ɗaga murya tana ƙwala mata kira da sauti mai karfi"Zeenatu! Zeenatu! Nashiga uku, Wayyo Allahna, meke faruwa dake ne, Zeenatu dan Allah ki tashi" jikinta na rawa ta soma kiciniyar tu6e mata hijabin data ƙudundu ne kanta aciki daƙyar ta samu ta yakice hijabin ta nannaɗeta gefe daya kan darduma, koda Tani ta ɗaura idanuwanta akan jikin zeenatu saida gabanta Ya faɗi, ganin wata irin zufa dake tsastsafo mata ta ko'ina, Rigar jikinta ta manne ma fatarta, sumar kanta kuwa duk ta yamutse babu gyara, shafa wuyanta Tani tayi nan fa taji yaɗauki zafi sosai.
A gigice ta miƙe ta watso da gudu ta nufi babban falon gidan, a lokacin Dr shureim Yana daga zaune kan Sofa, Benazir tana a gefenshi, fuskarta ɗauke da murmushi take kallon shureim dake bata labarin ƙuruciyarta.
Kamar mahaukaci haka Tani ta nufo su ta zagayo ta gaban Sofas din, kusan atare suka dago suna kallonta da alamun ruɗani akan faces dinsu
Dr shureim Yace"Tani! Lafiya? Meke faruwa"?
Sai faman yarfa hannu take yi duk tabi ta ruɗe.
"Pls ki buɗe baki kiyi mana magana" acewar Benazir, daƙyar ta iya tattara natsuwarta wuri guda, da karfin hali ta furta"Zeenatu ba lafiya! Tana acan daki rai hannun Allah, kwata kwata bata motsi..." kafin ta ƙare maganar, da gudu Dr shureim da Benazir suka nufi part dinta, tsabar sauri mayafin jallabiyar Benazir har faɗuwa yake yi kan kafaɗarta da sauri take sanya hannu ta gyarashi, Tani tana abiye da bayansu.
Suna shiga ɗakin idanuwansu suka sauka akan zeenatu dake a kwance magashiyan tamkar bata numfashi.
Slowly dr shureim ya zube agabanta kan gwiwowinsa, ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo da kanta ya ɗaura saman laps dinsa, Benazir ta zuƙunna gefenshi, fuskokinsu da alamun ruɗu suk soma ambaton sunanta"Zeenatu! Zeenatu"!
"Tani, bata da lafiya ne"? Benazir ce ta jefa mata tambayar
Muryar Tani tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi ban sani ba nima, yanzu nashigo ɗakin na taras da ita a kwance, nayi tsammanin ko bacci ta ke yi, amma dana