Showing 54001 words to 56271 words out of 56271 words
Chapter 19 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt
nata da kirjinta duk sun zube kamar mai fama da wata lalura,"
Aneelerh tace"abun da yafi ɗaure min kai da ita ummi, kwata kwata bata da natsuwa, ko magana take yi yatsun hannayenta zaki ga suna kerma kamar wadda sanyi ya kama"
Ummi tace"Muje muji meke damunta," gaba dayansu suka nufi kitchen din gidan, Koda suka shiga basu ganta ba, Har ta kamma aikace aikacen da take Yi, tayi wanke wanke tayi mopping dinsa.
Ummi tace"baiwar Allah gata da ƙoƙarin yin aiki, banji dadin halin da take aciki ba"
Fitowa sukayi daga kitchen din suka nufi bedroom din Ana.
Abakin Door room din Suka dakata da yin tafiyar, Aneelerh ta kwankwasa mata kofa, kusan sau uku Tana buga kofar kafin suka jiyo motsinta ta cikin dakin, buɗe kofar tayi tare da leƙowa tana kallon su
Fuskarta a yamutse, idanunta sun yi jajir da su.
Murmushin yaƙe ta ƙaƙalo akan fuskarta, cikin girmamawa ta gaishe dasu tana ƙoƙarin 6oye damuwarta
"Wurin ki muka zo mu shiga daga ciki" mami ce tayi maganar, da sauri Ana ta matsa masu hanya suka shiga dakin, Daga tsaye suka tsaya tace mashi su zauna saman gadonta
Ummi tace"ba zama ya kawo mu ba, zuwa mukayi don muji meke damunki Ana, meke faruwa dake ne? Duk kin canza mana kin rame kinyi baƙi! Baki da lafiyane"?
La66anta na kerma ta furta"babu komai lafiyana lau madam, wallahi babu abun dake damuna"
Cikin kwantar da Murya mami tace"Kada ki 6oye mana komai, Ki ɗauke mu tamkar iyayenki, dan Allah ki fada mana damuwarki, In sha Allah zamu share maki hawayenki,
Mami na rufe baki Aneelerh tace"Ana please kada ki bani kunya, Saboda mun ɗauke ki da daraja shiyasa muka damu da damuwarki, Kina gani dai mami da ummi da kansu suka zo dakin ki yau duk don saboda sun damu dake, Idan kika ce babu abunda ke damunki, kinyi mana karya saboda babu yadda za'ai ki rame batare da ciwo ko wani abu ba, dole da akwai wani abu da baki son mu sani"
Gaba ɗaya sun ɗaga mata Hankalinta, Cikin kwantar da murya suke yi mata magana amma sai ta dinga ganin kamar suna yi mata faɗane, Dafe kanta tayi da hannu biyu tana ambaton sunan Allah tamkar musulma.
Muryarta na rawa take fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, na roƙe ku ku ƙyaleni, ku tafi kawai, nagode da kulawarku agare ni,nagode"
Hankulansu atashe suke ambaton sunanta haɗi da tambayarta meke damunta.
Gaba ɗaya ta rikice masu, sai sambatu takeyi tana rokonsu akan su tafi subar dakinta, a karshe ta watsa da gudu ta shige toilet taja ƙofa ta datse. 😳
Kallon juna suka somayi da tsantsar mamaki da rudani aka fuskokinsu,
..mami tace"to fa, Anya kuwa lafiya"?
Ummi tace"bafa lafiya, Ni dai inaga kamar hada aljanu ke damunta.
Jikin Aneelerh yayi sanyi, tun datake da ana bata ta6a ɗaga mata murya ba sai yau da ta rikice masu tana korarsu daga dakinta, tabbas babu lafiya!
"Yanzu ya zamu yi da ita"? Mami ce tayi maganar,
Ummi tace"yakamata mu sanar da su Abie, dangane da halin da take aciki"
Sun jima a dakin Ana suna yi mata magiya akan ta fito daga toilet, amma taki fitowa a karshe dole suka hakura suka bar mata dakinta..
*Daular Obie Estate*
Gaba ɗaya Manyan matan Family din sun hallara a gidan Hateem domin yi masu bangajiyar tafiyar da su ka yi, musamman saboda zuwansu akayi masu shimfiɗa ta alfarma a katafaren Garden din gidan hateem, garden ne na alfarma cike ya ke da tsiro da furanni launuka daban daban masu ban sha'awa, ga wata irin ni'imtacciyar iska mai ratsa fatar jikin mutun, daga can cikin garden din akwai wani ƙaramin tafki wanda ke acike da tsaftaccen ruwa launin blue sky, inda fararen agwagi suke shawagi acikin sa, an tsara komai da kyau, a tsakiyar garden din akwai wani katafaren wurin zama, kewaye da ciyawar da aka yi wa ado, Lallausar darduma ce mai wani irin laushi a jikinta irin ta sarakuna, An kewayeta da tuntuye, yayin da suke a zaune kowaccensu ta ɗauki wanka na kece raini na mutunci, mata ne masu duniya, ajin farko, waɗanda suka gaji arziƙi tun kaka da kakanni, wayayyune masu ji da ilmin da Allah ya basu, mace ta farko Gimbiya mujeedat ce a kishingiɗe saman dardumar tayi shiga ta alfarma cikin tsadaddiyar Arab gown launin Ash colour anyi mata adon sparkling stones, masu ɗaukar ido, ta yafa mayafin saman kafaɗarta, baƙar sumar kanta ta sauko har saman dardumar da suke, daga gefenta First Lady ce Hajiya Malikat Sarauta ƴar sarkin Yarbawa jihar Lagos, Mace mai ji da kanta, mahaifiyar Chief Owais, A launin fata chocolate colour ce, taji hutu, bata da yawan fara'a, tana da ƙaramin baki ga dogon hanci, idanunta masu kyan gaske sunyi kama da Asian eyes, kayan jikinta Na yarbawa ne, Wrap around skirt ta sanya tare da farar shirt, anyi mata naɗin head akanta, tun daga kan wuyanta har hannayenta adone na zinarai, bayan Hajiya Malikat sai Hajiya Laurat uwar ji da izza, ƙanwar Alhaji Musa, Idan ka gansu atare da Hajiya malikat baka ta6a gane cewa kishiyoyine saboda kowaccensu bata ɗaukar raini, ita malikat arziki da sarauta ta gada, ita kuma Laurat Arziƙine gare su na fitar shari'a, sai dai daga ganin fuskarta zatayi rashin mutunci idan aka ta6a, daga ka kalli fuskarta zaka shaida ƙanwar Alhaji musa ce, Kamanninsu har sun 6aci da shi, hatta launin fatarsu kala ɗaya ce, Hausa fulani ce, ta ɗauki wankan shadda launin dark brown anyi mata ado, Wuyanta na asanye da sarƙar diamond, haka yatsun hannayenta zabban diamond ne masu kyalkyali da daukar ido.
Mace ta gaba, Hajiya Madina ce matar senate Lateef, barumaya ce, tana da hasken fata da tarin sumar kai, hatta gefe da gefen fuskarta akwai tsagensu na rumawa, Tana da kyau iya gargado sutura tanayi mata kyau, daga ganin fuskarta tana da kyakkyawar zuciya ko ba'a faɗa maka ba, Hadaddiyar atampa chiganvy ce a jikinta tabi shape din jikinta, Itama ta dauki nata adon na zinarai.
Bayan Ita sai matar His excellency Deen, Hajiya Jamila, Bafullatanar usili ce, Ƴar sarkin Jihar adamawa state, Fara ce jawur da ita, tsabar kyanta kamar ba'indiya.
Daga ita sai Matar Abdul Razak, Her excellency Muhibbat, Shuwa Arab ce ƴar mai duguri, fara doguwa ga gashi har gadon baya, family dinsu sunyi ƙaurin suna a 6angaren Arziƙi, Mace ce mai ji da kyawu da wadatar arziki, tana sanye cikin shiga ta bubu gown ta lace, ta kashe ɗaurin kallabi, awarwaron dake a hannayenta na zallar zinari ne.
Mace ta karshe basai nayi maku bayaninta ba, Kun riga da kun santa, bakowa bace face Aunty Masifatu Hajiya saratu, mutuniyar, wankan material ta ɗauka, gaba ɗaya ƙamshin turarensu Ya karaɗe iskar garden din hakan ba ƙaramin ƙara ma yanayin ni'ima yayi ba.
Daga tsakiyarsu Katafaren Faranti ne na azurfa, mai girman gaske wanda masu hidima suka kawo masu shi, An cika shi da Soyayyun Kaji jar suya, da kayan marmari nunannu, tare da juice masu sanyi.
Fira su ke yi atsakaninsu cikin harshen turanci tamkar ba su son furta magana.
"Naji daɗin ziyarar da kuka kawo min, kuma naji daɗin ganinku, Sai naji dama A ƙasar nan nake zaune, saboda mu runƙa sada zumunci a tsakaninmu akai akai" gimbiya mujeedat ce tayi maganar tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
"Ni kaina naji dadin haɗuwar da mu ka yi, bazan Iya musalta farin cikin da nake a ciki ba, Allah Ya ƙara Haɗa kawunanmu da zuri'armu" hajiya malika ce ta fada, tare da kai hannu ta ɗauki Yankan Tufa tana sha.
"Canada tamkar gida take awurina ina yawan zuwa saboda business din da nake yi Acan, In sha Allah zan dinga zuwa Ina kawo maku ziyara, Har sai kun gaji da ganina" hajiya Laurat ce ta faɗa tana duban gimbiya mujeedat, murmushin gefen fuska Mujeedat ta sakar mata tare da lumshe idanunta.
Hajiya Jamila tace"naji kamar kuna Bankwana, Tun Kafin jibin tayi ko kun manta da family dinner da zamu Yi a gobe?
Hajiya saratu tace"Kamar kin shiga zuciyata, nima tun ɗazu maganar da nake ta so Inyi masu kenan, ai gobe muna da gagarumin shagali In Allah yakaimu da rai da lafiya, dole kowa ya halarta" ta faɗa tare da kai hannu cikin faranti Ta yago cinyar kaza ta tura abaki tana tauna
Hajiya jamila na dariya tace"daɗina dake saratu baki wasa da cikin ki, Zaman mu anan kin cinye fiye da rabin kaza, shiyasa gaki nan kullim ƙara ƙiba kike yi,"
"Kinsama kanwar nan tawa ido" acewar Gimibiya mujeedat.
"Kibarni da ita aunty, da duk wani mai sanya min ido akan cin abincina, nasan maganinku, zanyima yayyena magana su ƙara maku kishiyoyi, ƙwara ku lalla6ani ku dinga lallashina idan ba haka ba kun san sauran" dariya su ka yi gaba dayansu,
"Meya yayi zafi, nayi shiru bazan ƙara tanka maki ba, Ci ki ƙoshi, Idan ma kina buƙatar ƙari zansa akawo maki" hajiya jamila ce ta faɗa tana tura mata farantin agabanta, Hajiya sarah tayi dariya da zolaya tace"Bari naja bakina nayi shiru, naga wasu sun fara haɗe min fuska saboda nayi maganar kishiya"
Murmushi kowannansu ya saki,
Gimbiya mujeedat tace"ko kaɗan banji fargababa, because I know who my husband is. He doesn't want to remarry; I'm enough for him." She said proudly and gently.
Hajiya laurat tace"ai dama irinku ba'ayi maku kishiya, wane mutun, ballanta kuma mijinki da gaba ɗaya rayuwarsa acikin turawa yayita, ba lallai Yana da wannan ra'ayin ba, tun da suma mace ɗaya su ke aure"
Her excellency Muhibbat ta murmusa tare da cewa"ni dai koban fada maku ba kun riga da kun sani, ba'ayi mana kishiya, Mijina bai ta6a gigin kula wata ƴa mace ba"
Hajiya malikat dake sauraransu tace"nima nan bada jimawaba zansa mijina yayi waje da wata" ta faɗa da zolaya tana kallon Hajiya laurat, dariya suka sanya gaba ɗayansu.
Hajiya Laurat tace"Ni da sharafudden mutu karaba takalmin kaza, badai mutun ba sai Allah, me raba ni da shi sai mutuwa"
Yamutsa fuska Hajiya malikat tayi"alfarma fa nayi mashi ya aure ki, saboda yana jin shakkar tunkarata da zancen auranki yasa shi ƙin sanar dani sai dai naji daga saman an shafa fatihar auranku, wato yanzu kin samu wurin zama shiyasa har kike da bakin fadin mutu karaba takalmin kaza," cikin raha suke Yin firar tasu.
Hajiya Muhubbat tace"ai ni ina mamakin dauriyarku da har kuka Iya haɗa kanku, babu mai jin sirrinku, Gaskiya kun burgeni, amma ni fa wallahi bana tunanin zan Iya zaman lafiya da kishiya, shiyasa tun kafin abdul razak Ya aureni saida muka ƙulla yarjejeniyar bazai yi min kishiya ba, mahaifina ma saida Yaja mashi kunne akan hakan"
Jinjina kai Hajiya madina tayi'lallai abun naki azimin ne, ni kuwa dai bana jin zan Iya hana Mijina Yin aure, tun da Allah ya Halasta masu auren mata har huɗu, Idan Ya nuna yana so zan goyi bayanshi, kuma Idan Ya aurota zamu yi zaman lafiya da ita idan har ba ita bace ta bijirema hakan ba"
Wani kallo her excellency Muhibbat Ta yi mata"babu zuciya a kirjinki, Shiyasa bakya kishin mijinki"
"Bawai don bani da kishi bane, nafiso idan ma kishin zanyi inyi irin na matan manzon Allah SAW, ni fa da ace mijina Yana bin matan banza ƙwara ya auro mata uku a lokaci ɗaya, amma idan nace zan tauye mashi hakkin shi in hana shi auran abunda yake so to fa zan jefa shi ga halaka ne, sannan ban Isa In hana zuciyarshi son wata ƴa mace ba"
Jinjina kai su kayi jin bayanin Hajiya madina badan sun fahimce ta ba.
Hajiya Jamila tace"godiya yakamata muyiwa Allah daya bamu mazaje nagartattu, nagari masu ƙaunarmu tsakani da Allah, Har Yau Ina alfahari da kasancewata ɗaya daga cikin surukan dattijon Arziƙi, Allah Ya saka mashi da gidan Aljanna, Ya haifa mana zaratan maza sadaukai, Tsakaninmu dashi sai son barka" Murmushi hajiya saratu tadinga saki jin ana yabon mahaifinsu, wani irin dadine Ya lullu6eta
Hajiya Muhibbat tace"Ai Zuri'ar Obi komai sun haɗa Allah Ya basu, kyau, nasaba, ilmi, wadatar arziƙi, ƙawayena har tambayata sukeyi wai babu sauran ƴa'ƴan shi da suka rage? Don su aura suma su shigo daga ciki, nace masu sai dai Jikokinsa ƴa'ƴan cikin su in suna so" dariya sukayi gaba ɗayansu.
Bayan sun lafa, kowaccensu Ta sanya hannu a faranti ta dauki abunda take son ci, wasu nama Wasu kayan marmari wasu kuma lemu suke sha.
_______________________🌹✍️
A hankali Motar Sir Mubarak Tashigo Gidan Hateem, A Harabar ajiye motoci yayi parking dinta, fitowa yayi daga front seat ya zagaya ta back seat Ya bude ma mom turai kofa, A hankali ta fito ta sanya atampa riga da skirt sunyi mata kyau, Ta yafa mayafi saman kafadarta, yayin dashi kuma yake asanye da Shadda.
Kallon juna sukayi, da sauri ta kau da idonta gefe, hannunta ruƙe da ƴar handbag dinta
Muryarta ƙasa ƙasa ta furta"dan Allah kabarni in koma gida, bansan meyasa ka tursasa min akan inzo gurinsu ba, na faɗa maka basu ƙaunata, wallahi ci mun mutunci zasuyi"
Ɗaure mata fuska yayi"kar na kuskura nasake jin kin furta maganar nan! bana jin dadin yadda kike ware kanki daga cikinsu! Dame suka fi ki? Tsoron su kike ji? Baki Iya mayar masu da martani in suka gaya maki magana"?
Tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace"Ina da banbanci dasu, Har Yau har gobe sunƙi mantawa da matsayina agidanku, Suna yi min kallon ƙasƙantacciya Ƴar aiki, babu abunda Ya canza"
*DAGA ALƘALAMIN HAFSAT BATURE✍️*