Showing 33001 words to 36000 words out of 56271 words

Chapter 12 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt

23 Nov 2024

3615

da lallausar bargonsa, kafin ta kashe switch din dakin yai duhu, ta kunna mashi bedside lamp, tamkar karta bar ɗakin haka take ji, addu'o'i ta tottofa mashi tun daga ƙasa har sama kafin tabi bayan su suka nufi bedrooms din su.


Sai da big guy ya tabbatar kowan nan su Ya shiga dakin shi, tukunna Ya nufi hanyar da zata kaishi part din da room dinsa Yake agidan.


Fitarshi keda Wuya, Unaisah da Batool, suka fito daga ɗakin su, Hannayen su ruƙe da plates sun rufe su, abincin da suka ajiyema Ummi ne, tun ɗazu suka shirya zuwa dakinta don su kai mata abinci sun kasa saboda fargabar awani hali zasu taras da ita, duba da yanayin da ta shiga ɗazu na ganin sheikh Imam, Batool ce ta bada shawarar su ɗebi abinci su kai mata, tun lokacin da aka kawo masu dinner dinsu, Suka ɗibar mata plate biyu na abinci, A ɗakinsu suke 6oye mata shi sai yanzu su ka samu damar fito da shi.


Cikin sanɗa suke yin tafiya suna ƴan waige waige kamar wasu munafukai, fargaban su kada wani ya gan su, basu san cewa duk wani motsin su akan idon jami'an isod dake kula da CCTV room ɗin gidan.


A hankali suka haura second floor kaitsaye suka nufi ƙofar dakin ummi, cike da fargaba Batool take zazzare ido, don har yanzu mugun jin tsoron ummi take yi, gashi ta damu da ita kamar yunwar cikinta.


"Sister, Ni zan jira ki awaje, ke sai ki fara shiga" cikin muryar raɗa batool tayi ma unaisa maganar.


Harara unaisah ta jefa mata" waye ya kawo shawarar mu kawo mata abincin"? Yamutsa fuska batool tayi"Ni ce,"


"Don haka ke zaki fara shiga, Ni dama hankalina bai kwanta da mu zo kawo mata abinci ba, wata'ƙil ma taci abincinta tun ɗazu, mu ne ba mu sani ba"


"Shikenan, Mu koma ɗaki sai mu cinye"


Dariya Unaisah tasaki tana kallon batool tace"ai wallahi yadda kikasa muka ajiye mata abincin nan sai mun kai mata shi, Kuma ke zaki miƙa mata da hannunki" ta faɗa tana nuna ta da girar ta, jikin Batul harya fara kerma tsabar tsoro, idanunta suka ciko da ƙwalla.


"Nidai mu koma ɗaki, sai in cinye abincin" a tsorace ta faɗa.


da zolaya Unaisah Tace"You are just a coward, ai na lura shakkar aunty ummi kike ji, gashi duk kin damu da ita, Yinin yau tun bayan data shige daki kika ga bata fito ba shikenan kika addabe ni da tambayar Aunty ummi, bata ci abinci ba, tana adaki, ko awani hali take aciki, ni narasa gane meyasata kuka, yen yen yen haka kika isheni, shine yanzu kuma mun kawo abincin kike kokarin zillewa" murguɗa mata baki batool tayi batare da tace mata ƙala ba.


Knocking ƙofar Unaisah tayi daga ciki suka jiyo Muryar Ummi ta furta"Come In"


Tura ƙofar Unaisah tayi kafin ta shiga da sallama abakinta, Batool tana abiye da ita sai fama 6oye kanta take Yi.


Kusan atare suka ɗaura idanunsu akan shimfiɗeɗan gadonta, tana daga kwance ta ɗaura kanta saman pillow, yayin da eyes dinta ke akan apple laptop dinta da ta ajiye saitin inda take fuskanta, wata yar gown ce a jikinta, shara shara kana Iya hangen inners dinta, tsayin rigar bai wuci gwiwar ƙafarta ba, gashin kanta a yamutse yake mai uban yawan gaske, ya cunkushe wuri guda, yanayinta da kasala a jikinta babu kuzari.


Kamar an danna masu full stop haka suka dakata da yin tafiyar suna faman binta da kallo, jin shiru sunyi mata sallama basu shigo bane yasa taɗan ɗago da idanunta waɗanda suka rikiɗa suka koma launin Ja, Su kansu da su ka yi tozali da idanunta saida suka sha jinin jikinsu, wani ɗan iskan murmushi tasakar masu haɗi da ɗage masu gira ɗaya tace"meyasa ku ke kallona? Ba zaku shigo ciki bane"? Kallon juna su ka yi cike da al'ajabin jin sautin muryarta tamkar ta gardin ƙato wanda yasha ya bugu da giya.


"Aunty Ummi baki da lafiya ne"? Unaisah ce ta furta maganar, a kasalance ta miƙe zaune haɗi da jingina bayanta kan gadon, kafin ta furta"Lafiyana Lau, menene ku ka kawo min"


ta tambaya yayin da take kallon Batool data 6oye kanta bayan Unaisah.


"Abinci ne" buɗe ido ta yi alamar tadan yi mamaki .


"Wanene Yayi tunanin kawo min abinci acikin ku"? Ta faɗa tana nuna su da yatsanta.


Cikin muryar raɗa Batool tace"Dan Allah ki ce mata ke ce bani ba"


Murmushin mugunta Unaisah tayi jin abun da ta raɗa mata,


Da gangan tace "Batool ce, tun ɗazu da kika tafi ɗaki kina kuka ta hana kanta sukuni, ta dinga damuna da tambaya akan Aunty ummi shiru bata fito taci abincin ta ba, ta tafi tana kuka bansan awani hali take ba, Pls sister mu ajiye mata abinci mu kai mata"


Lumshe idanu ummi tayi, har cikin ranta taji dadin jin hakan.


"Ku shigo daga ciki," ta faɗa tana nuna masu gadonta da hannu, Unaisah ce tayi gaba Batool tana abiye da bayanta kamar wata mara gaskiya, taji haushin faɗa matan da unaisah tayi

"Bani plates din" ta fada tare da mike masu hannu ta kar6i plate din hannun Unaisah, ta ajiye akan gadon, ta kar6i na hannun batul ta ɗaura shi kan side drawer tana fadin"tun da kun kawo min abincin, ku zaku bani a baki in ci"


duk idan tayi maganar sai sun kalli fuskarta, bakomai ne yake ɗaure masu kai ba, face sautin muryata daya canza kamar na wadda tasha giya, ga idanuwanta sun yi ja.


"Aunty Ummi sautin voice dinki Ya canza, Idanunki ma suna yi ja sosai, ba ki jin daɗin jikin ki ne"? Cikin kulawa Unaisah tayi mata tambayar, ƙamshin turaren ummi duk Ya buɗe ɗakin.

"Nothing is bothering me. Maybe it was my crying that made my voice change." She said, trying to bring her voice back to normal.


"Meyasa ki kuka ɗazu da kika ga sheikh Imam"? unaisah ce ta ƙara jefa mata tambayar


da zolaya tace"Unaisah kin cika bin ƙwaƙƙwafi, Kina min tambaya kamar Ƴar jarida, Ku zo ku zauna Yau muyi fira" ta faɗa tana nuna masu mattress.


Unaisah ce ta fara hawa gadon, Kafin Batool ta haye gadon tana mai jin shakkar haɗa ido da ummi, suna fuskantar juna da ita, Batool tana agefen Unaisah, Ummi tana fuskantarsu.


ta lura kamar Aunty Ummi batason tambayar da take Yi mata dangane da sheikh Imam hakan yasa taja baki shiru.


da fara'a akan fuskarta tace"Banyi tsammanin kun damu dani ba, har na fidda rai da zanci abinci, gashi wata iri yunwa nake ji kamar inci ƴan hanjin cikina...." ta ƙare maganar tana ya mutsa fuska ta buɗe plate din gabanta, ashaƙe yake da tsiran nama, yanka yanka yaji kayan haɗi sai maiƙo yake yi ga kayan lambun da aka yayyanka mashi, sai ƙamshi yake yi, sun kura mata ido suna kallon ta.


"naji daɗin tsiran nan da ku ka kawo min, wa zai fara bani abaki" da sauri Unaisah tace"Batool" ta faɗa tare da ruƙo hannun batool ta ɗaura shi kan plate din, Hankalin batool ba ƙaramin tashi yai ba, fuskarta duk ta yamutse itafa atakura take jin kanta har yanzu bata manta abunda ya faru tsakaninta da ummi ba a daren Jiya, gani takeyi kamar bata ƙaunarta.


"Babe, Ki bani tsiren miyau na Ya gwada" ta faɗa tana ɗage mata gira, hada sakar mata murmushin gefen fuska
Daurewa batool tayi, ta ɗauki tsiran hannunta na kerma takai shi bakin ummi, Unaisah na dariya tace"wlh batool tsoron ki take ji aunty ummi," ruƙo hannun batul ummi tayi ta ƙarasa tura naman abakinta, har wani lumshe ido takeyi, tana taunarshi ta ce.


"Na lura da hakan, Amma kada ki damu zamu saba ne" Ummi ce tayi maganar, sanya hannu unaisah tayi cikin plate din tsiren ta dauko ta tura ma ummi abaki, Idan batul ta bata ita ma sai ta bata abaki, wani irin ƙaunarsu ce ta ɗarsu acikin zuciyarta, A hankali take satar kallonsu afakaice, don bata son su gane tana kallonsu.


Bayan sun kammala bata tsiren suka buɗe dayan plate din me ɗauke da chips, shima suka bata har tana tambayarsu sunci nasu abincin ne? Suka ce mata Eh sun ci, duk da haka saida ta ɗebi chips ta tura ma kowan nan su abaki, Cike da nishadi suke tauna.
bayan sun gama, Unaisah ta ɗauko masu Juice me sanyi suka sha.


Ganin sun fara yunkurin tafiya ne Yasa tace"why baza ku tayani kwana ba"? Waro ido batul tayi tunawa da abinda Ya faru Jiya, Murmushi Ummi ta sakar mata, Ta fahimci tsoro take ji kada ta ƙara Yi mata irin na jiya hakan yasa tace


"Asaman gadona zamu kwana, kafin muyi bacci har kallo zan kunna mana a laptop," jin hakan yasa batul taji hankalinta ya kwanta.


gaba ɗayan su suka haye gadonta, unaisah ta takura ma Ummi akan tana son ta gyara mata gashinta, adole ummi ta ɗauko mata comb, da ita da batool suka kama gashin kanta suka dinga sharce shi bayan sun kammala, ta basu ribbom babba suka ɗaure mata gashin daƙyar saboda yawanshi gashi taurine dashi donma tana gyarashi da mayuka masu sanya laushin gashi.


Gefe da gefenta suka kwanta, ta kunna masu kallo a laptop, cikin nishadi su ke yi, da zarar anzo wurin da za'ae kiss ko makancin hakan take yin saurin rufe masu idanuwansu da tafukan hannayenta, hakan ba ƙaramin dariya yake basu ba, Saida dare Ya fara nutsawa ta kashe kallon, a lokacin bacci mai nauyi yai awon gaba da su, ta sauko daga kan gadon ta kunna masu bedside lamp kafin taje ta kashe hasken ɗakin ya rage saura na fitilun gefen gadon, ta dawo ta kwanta a tsakiyarsu.


A jiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura eye balls dinta tana kallon fuskar batool dake ta sharar baccinta, A hankali ta daura hannunta kan hular batul ta zameta, gashin kanta ya bayyana, shafashi taci gaba dayi tana binta da kallon ƙurulla, gani take kamar ta ta6a sanin mai kama da ita, sai dai ta gaza tuna wanene ko wacece ke kamanceceniya da ita cikin mutanan da tayi tarayya da su.


Lumshe idanuwanta tayi yayin da ƙwalwarta ke tariyo mata wani abu can daya ta6a faruwa a arayuwarta wanda yayi silar tarwatsewar Farin Cikinta, baƙin tarihin da har bada bazata ta6a mantawa da shi ba, Ya lalata darajarta da ƙimarta Ya zubar mata da mutuncinta a idon jama'a, wasu kalmomi ne suka soma yi mata yawo acikin kanta.


_Nayi danasanin kasancewarki Ƴata, wallahi da ace nasan da zuwan wannan ranar da tun kina acikin ciki zanyi silar da za'a 6arar dake_


Tuna wannan maganar yasa ta fashe da wani irin matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, sham ta manta da su Unaisah dake bacci.


Cikin muryar bacci batul ta furta"aunty ummi kuka ki ke yi"? Da sauri ta haɗiye kukanta, Hannunta ɗaya atoshe da bakinta, ta runtse idanuwanta.


Idanun batul biji biji ta buɗesu, akan fuskar ummi, hankalinta ya tashi matuƙa ganin yadda fuskarta ta jiƙe da hawaye, muryarta na rawa ta furta"aunty.... ummi, baki da lafiya? Meke damunki"?


Daƙyar ta iya buɗe ido ta kalli batool dake kallonta batare da tace mata komai ba.


Duk da shakkarta da Batool take ji hakan bai hanata jin tausayinta ba, hankalin ta ya tashi matuƙa da ganin yanayin da ummi take aciki.


Hannunta na kerma ta ɗaura shi saman fuskar ummi a hankali take share mata hawayen dake sintiri kan kuncinta.


"Aunty ummi ki daina kuka dan Allah, bana son ganin ki cikin damuwa"


Muryarta adisashe ta furta"meyasa kika damu dani? Ko Kin manta abunda nayi maki jiya"?


"A'a ban manta ba, ni kawai ina ƙaunarki kuma bana son ganin kina kuka"


tayi mamakin abunda batul tace mata.


"Don't worry, I'm feeling better. Go back to sleep." ta faɗa tana ƙoƙarin danne damuwarta.


"Bazan Iya bacci ba, idan bakiyi ba," kalaman batul sun sanyaya mata zuciya.


"Ki sanyani inyi baccin" matsawa batul tayi dab da ita.


Da ƙarfin hali ta rungume ummi sosai tayi tighting dinta, ta daura hannayenta saman bayanta, itama ummi ta daura nata hannun asaman bayan batool ta ƙanƙameta, wani irin yanayi ta soma ji mai wuyar fassaruwa hatta bugun zuciyarta ya canza, ta rasa gane dalilin faruwar hakan, Yau ne karo na farko data fara rungume Batool ajikinta amma wani iko na Allah sai ta dinga jin kamar ta ta6a rungumarta, ita kanta Batool din sai da taji canzawar bugun zuciyarta daurewa kawai take yi amma sai take ji kamar su dawwama ahaka ita da ummi batare da sun raba jikin su daga na juna ba.


Ƴan addu'o'in da Unaisah ta koya masu, ta soma karantowa tana tottofa ma ummi.


Wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta nemi damuwarta tarasa, Ahaka bacci mai nauyi yayi awon gaba da su rungume da juna kamar zasu koma mutun ɗaya.....


(Nima kuma na rungumi Alƙalamina)




Mu haɗu Gobe Idan Allah yakaimu da rai da Lafiya🌹




*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*


3196407426


First bank


Bature Hafsat Muhammad,


*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*


~TAKUN ƘARSHE~










_______________________Boss Bature✍️










*The Unexpected call📞📲*










*❤CHIEF OWAIS✊*










A tsaye yake a gaban dressing mirror, cikin shiga ta pajamas Maroon colour, yayin da baba obie dake zaune saman gado ya ƙura mashi ido yana kallon shi, A hankali yakai hannu ya ruƙo roban massage oil Ya juya suka haɗa ido da shi, murmushi baba obie ya sakar mashi yana fadin"sannu da ƙoƙarina, tun ɗazu nake kallon ka, kanata laluban mai bayan ga abunan akusa dakai bansan me kake tunani ba daya ja hankalin ka.




Murmushin gefen fuska chief owais ya sakar mashi, kafin ya nufe shi yana fadin"grandpa, kaima kaso ka wahalar dani, maimakon ka fadamin ka ganshi sai ka barni ina ta neman shi" dariya Obie yai cike da nishaɗi yau jin shi yake tamkar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna saboda zuwan Owais Ya faranta zuciyansa.


Daga gefen shi chief owais Ya ɗaura Massage Oil din, Baba obie Ya juya mashi bayansa ta yadda zai ji dadin yi mashi tausar dama daga shi sai short a jikin shi.


"My Grandpa, Ka tsufa sosai, bayanka yayi tamoji tamoji" da zolaya chief ya furta maganar.


"Ba dole na tsufa ba, shekaru sun ja Owais" in cool voice ya fada
A lokacin Owais Har Ya fara shafe mashi bayan shi da message oil din tare da yi mashi tausa, A hankali yake matsa fatar bayan shi yana murzata Runtse idanunshi yai haɗi da cije la66ansa Chief har leƙen fuskar baba obie yake yi, ya fahimci kamar yana jin zafin tausar da yake yi mashi ne.


"Wash! Allah na! Owais kabi A hankali, wannan hannaye naka kamar na samudawa, kana murza min baya kamar yadda kake damƙar mugu idan ya aikata laifi" ƙumshe dariya chief yai jin sambatun da baba obie Yake yi mashi.


"Baba, saboda lafiyarka nake yi maka hakan, naga kana runtsa ido kuma kana cizon la66anka, Hakan na nufin kana jin zafin tausar, Amma idan na gama yi maka zaka ji daɗin jikin ka......" ɗaga muryarshi yayi da ɗan ƙarfi ya furta"toh.. Toh.. Naji yanzu saura ƙafafuwan da ƙirjina amma dan Allah kabi a hankali kada ka shaƙe min zuciyata, dama ya lafiyar gwiwa"


"Kana bani nishaɗi My Grandpa, Amma kayi min laifi...." kafin Ya ƙare maganar Baba Obie yace"Laifin me kenan"? Ya fada tare da Juyawo Yana fuskantar shi, Ya ɗaura bayan shi kan pillow, tare da miƙe ƙafafuwan shi yana duban Owais.


"Kafin In bar Nigeria ka yi min alƙawarin Zaka dinga kula Min da lafiyarka, Har family doctors din mu nayi ma magana akan su dinga duba ka akai akai, dama tun time dana faɗa masu hakan sai da dr Alex Ya faɗa min cewa kaine baka basu damar da za su duba ka, da zarar sunyi yunƙurin bincika lafiyarka sai kace masu kashe ka suke son yi meyasa"?


Ya jefa mashi tambayar Yana bin shi da kallo, hands dinsa na akan ƙafafuwan baba obie da yake yima tausa


Shiru yayi mashi batare da ya furta komai ba.


"Ba ka da abun cewa, shiyasa ka yi min shiru kana kallo na ko"? da zolaya yayi mashi maganar, baba obie yai murmushi tare da hararar shi yace"Bawai na rasa abun cewa bane, kawai ina tunanin yadda kake nuna damuwa akaina, Idan kaga na faɗa masu haka toh ni lafiyana ƙalou bana buƙatar a bincika ni," ya faɗa yana shafa gemun shi da hannu ɗaya
Shiru Owais yayi mashi batare daya furta komai ba, ya maida hankali akan tausar da yake yi mashi.


"Nayi kewarka sosai, Meyasa ka yi nesa dani? Abun da baka ta6a yi min ba owais, ka riga da kasan yadda na ƙwallafa rai akanka, sai da takai ga ko bacci nake yi ina sambatu a kan ka, ko na kira layin wayarka baka ɗagawa meyasa Owais? Ko dan kaga na damu dakaine" ya faɗa yana kwa6e mashi fuska kamar zaiyi mashi shagwa6a, chief owais dake kallon shi aranshi ya ayyana rigimar tsufa ta motsa, A fili kuma ya furta"Ba haka bane, Kamar yadda ka damu dani nima haka na damu dakai, ko aiki nake yi kana arai na, Grandpa kasan yanayin aikin mu ɗaga waya wuya yake min wasu lokuttan ma bana sanin an kira ni.... " bai kai ƙarshen maganar ba ya dakata yana kallon ikon Allah ganin baba obie yana kwaikwayon maganar shi, gaba ɗayansu suka sanya dariya.


"Are you making fun of me? I won't speak anymore" obie na dariya yace"ka yi haƙuri jikana, Muryarka ce da daɗin sauraro, shiyasa ƴan mata suke haukan su kai kuma kana yi masu rowar kan ka, faɗa min menene Sirrin ko akwai wani abu da kake sha wanda yake ƙara mata daɗi" calmly ya furta a'a, daga Allah ne"


"Amma kasan wani abu"? Girgiza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login