Showing 45001 words to 48000 words out of 56271 words

Chapter 16 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt

23 Nov 2024

3616

suna fira, ta cikin window din motar Yake dubansu, Ranshi yayi mugun 6aci, dama fuskar babu annuri ko miskala zarratin.


Bayan motar tasu tayi parking a harabar Ajiye motocinsu, Bai jira Security guard din Ya buɗe mashi mota ba, da kanshi Ya buɗe murfin Ya fito Yana faman haɗe rai, fitowa daga cikin motar Alhaji Ubaid Yai, idanunsa akan Musa yace"wai meke damunka ne? Tun dazu da muka fita taron jam'iya babu annuri akan fuskarka, mutane sai rububinka sukeyi amma kai ko kaɗan basu agaban ka, Ka haɗe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa... " kafin Alhaji Ubaid Ya ƙare maganar, Alhaji musa Ya ɗaga mashi hannu babu mutunci Ya furta"Ya isa haka! Bana son jin maganar nan," da sauri Alhaji ubaid Yaja baki yayi shiru, Cikin Takun Isa da izza Alhaji musa Ya haura ƙafa Ya nufi Cikin gidan.

Hajiya Layla dake hangen su Alhaji ubaid tun da suka fito daga mota, da zolaya tace ma mom sarah"Matar so Ga mijin So can Ya dawo, Naga kamar ranshi a6ace Yake yakamata kije ki lallashe shi"


sai data furta maganar Hankalin Sarah Ya kakarta akan su, A lokacin Har Alhaji musa Ya shige Ciki, miƙewa tayi da sauri tana fadin"Nasan bai wuci gajiya bace ta dameshi, dama da safe kafin ya fita Ya faɗa min baya jin dadin jikin shi, " tana ƙare fadan hakan Tabi bayan Alhaji musa.


Bayan tafiyarta, Hajiya layla bata motsa daga inda take a zaune ba, Alhaji ubaid take Jira Ya ƙaraso inda take ganin Yana tunkarota sai faman sakar mata murmushi Yake Yi, Ita ko ta haɗe mashi fuska, don ba ƙaramin haushin shi take ji ba tunda yaƙi amincewa da zancen Komawarsu Joss.


Kujerarar dake fuskantarta Yaja ya zauna.
Fuskarshi da fara'a yace"uwargida ran gida, fatan na sameki Lafiya"
Banza tayi da shi batace komai ba, sai ma cup da ta dauka tana shan sauran coffee dinta
"Layla kina ji ina magana kinyi banza kin ƙyaleni, Ko sannu da dawowa babu"


Ta6e baki tayi tare da hararar shi tace"hmmmm, me kakeso nace"? Shiru yayi baice mata komai ba, sai dai binta da idanu da yakeyi.


"Ka bani mamaki, nayi tunanin mijina Namiji ne, ashe ba haka bane nayi kuskure, Ka nuna min kai ba komai bane wai ƙaninka shike juya ka son ranshi, baka jin maganar kowa In ba ta shi ba, kamar wani ubanka" rai a6ace tayi maganar.


Tuni yanayin fuskar Alhaji ubaid ya canza zuwa matsananciyar damuwa, baya son mitar da Hajiya layla take yi mashi kullum haka ya ke fama da ita.


"Layla bai kamata Kina gaya min magana ba, Har yanzu ni mijinki ne matsayina agareki bazai ta6a canzawa ba... "
Murmushin takaici tasaki tana dubanshi tace"Ubaid! Duk abunda na faɗa maka Kaine kaja, wallahi ka 6ata min rai, bana jin daɗin ƙasƙantar damu da ka ke yi awurin musa, baya ganin girman kowa daga kai har ni, burinshi mu zama tamkar bayinshi shi kuma uban gidan mu, na rasa gane da wani yare zanyi maka magana yadda zaka fahimce ni...." muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye tuni sun cicciko idanunta.


Girgiza kai yai cikin sanyin murya yace"bani da amsar da zan baki, duk abunda kika faɗi gaskiya ne layla, bawai bana fahimtar ki bane, sai dai bani da yadda zaniyi, yakamata kiyi min uziri, Ni ina girmama musa ne saboda halaccin shi agareni, yayi min abubuwa da dama waɗanda bazan ta6a mantawa ba, duk wani cigaba da kika ga na samu arayuwata musa shine sila....." kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon dariyar da layla ta saki tamkar wata zararra, jikinta har jijjiga yake yi.
da mamaki akan fuskarshi yace"meyasa kike min dariya? Kin maidani mahaukaci ko"?


Tsagaitawa tayi da yin dariyar ta soma yin magana.


"Mijina Ina tausayin rayuwarka, Sannan Ina jiye maka ranar da zaka yi danasanin yarda da kayi da ƙaninka musa, saboda ya riga daya gama dakai! tarkon daya ɗana maka Yayi tasiri a zuciyarka, Wai kai baka amfani da ƙwaƙwalwarka ne? Idan har don Allah yake kyautata maka meyasa baya yi maka biyayya amatsayin shi na ƙaninka"!? A faɗace tayi maganar, Alhaji ubaid Yayi shiru Yana sauraronta, kalamanta sun yi mashi tsauri suna neman ruguza mashi lissafin ƙwalwarsa.
"Kasan ni bana 6oye ta cikina! Idan abu yana damuna kai tsaye nake faɗi ma mutun koda kuwa bazata yi mashi daɗi ba" Ta faɗa tana mai ƙara jaddada kalamanta.


"Yakamata ka farka daga baccin da ka ke yi, tunkafin lokaci Ya ƙure maka, Ni dai zan faɗamaka gaskiya koda kuwa zaka ji haushina ne, Alhaji musa ƙaninka ba ƙaunarka yake yi ba dakai da iyalanka, Baya sonmu ba don Allah Yake kyautata mana ba face sai don saboda wata manufa tashi, na faɗa maka hakanne bawai don ina zargin shi da wani abu ba, sai don saboda babu gaskiya a lamarin shi!"


A zafafe Ta ƙarasa maganar, tare da kai hannu ta daki gaban table din, Bata jira amsar da zai bata ba tayi saurin miƙewa zuciyarta na tafarfasa ta nufi cikin gidan ta shige.


Gaba ɗaya Alhaji Ubaid Ya rasa meke yi mashi daɗi a duniyar nan, Har cikin ranshi bayason 6acin ran layla, A cikin ƴan kwanakin nan kusan kullum sai sun samu sa6ani da ita saboda Alhaji musa, baisan ya zai yi da ita ba, a ganin shi itace ta tsani Alhaji musa shiyasa take neman 6ata mashi suna a wurinshi duk don su bar gidansa.


Ya jima zaune kan kujera Hannin shi ɗaya dafe da kanshi sai daga bisani Ya miƙe Ya nufi cikin gidan.


*ALHAJI MUSA💪*


Bayan shigarshi bedroom dinsa, rage kayan Jikin shi yayi, ya rage saura farar shirt da short, Sai faman Cika ya ke yi yana batsewa, zuciyarshi Ta kai maƙura awurin 6aci.


Hajiya sarah tana ƙoƙarin shigowa bedroom din nashi, ba zato ba tsammani taji Ya furta"Kada ki kuskura ki shigo min nan!" Ras taji gabanta Ya faɗi, abakin kofar ta tsaya tana dubanshi Yana daga tsaye Ya dafe sofa din dakin da hannayenshi.


"Meyasa zaka hanani shigowa"? Cikin kwantar da murya tayi mashi maganar
Tamkar bazai tanka mata ba yace"zonan"! Kamar wata ƙaramar yarinya haka ya kirata, bayan ta shiga dakin daga gaban sofa din ta tsaya tana kallon shi.


Zagayowa yayi ta gabanta, ya sassauta fushin fuskarshi.


"Meya hana ki zuwa wurin Aiki yau"?
Cike da jin shakkar shi tace "Namanta ne ban faɗa maka ba, Jiya na ɗauki hutu saboda Hajiya layla inaso muna samun lokacin da zamu dinga zama muna fira harma mu dinga fita" daƙyar ta ƙare maganar ganin irin kallon da yake jefa mata, tuni tasha jinin jikinta.


"Saboda ita kawai kika ɗauki hutun aiki? Kin fara shaye shaye ne"? A ruɗe take kallon
"Kin ci sa'a bani da ɗabi'ar ta6a lafiyar mace, da kuwa yau saikin yaba ma aya zaƙinta, " mamakin maganarshi ne yasa ta zaro idanunta waje har saida ta maimaita kalmar sai kin yaba ma aya zakinta.
Adabarbace ta furta"bangane me kake nufi ba"?


"Bani da lokacin Yi maki bayani, amma Inaso in ja maki kunne akan matar can, bana son ganin kina sakar mata jiki kuna yin fira, wannan umarni ne daga gare ni, ban amince ki rinka ke6ance kanki da ita ba"!


ɗaure mashi fuska hajiya Sarah tayi"akan me zaka hana ni yin fira da ita? Haramunne yin hakan? Ko tayi maka laifi ne? Ina buƙatar hujja.


Da kakkausar Murya Ya furta"Umarni nake baki ba shawara ba, ki koma aiki gobe sannan kada in ƙara ganin kin ke6ance da ita" Ya faɗa yana furzar da huci ta hancin sa.


Ta fahimci bayason hajiya layla, ta daɗe da sanin rashin jituwarsu sai dai batayi tsammanin abun yakai haka ba.
Ƙwara tabi Umarnin shi ta zauna lafiya idan ba haka ba, Ita zata jama kanta"
Yana ƙoƙarin juyawa tayi saurin ruƙo hannun shi acikin nata, kallo ya jefa mata mai kama da harara.


"Ka yi hakuri idan ranka ya 6aci, in sha Allah zanyi maka biyayya bazan ƙara zama yin fira da ita ba"
Lumshe idanunshi yayi kafin ya buɗe su Ahankali Ya furta"me kuke tattaunawa ne da ita"?
Tayi mamakin tambayar daya jefa mata, saboda tasan halin shi, mutunne da bai Iya shiga shirgin mutane ba, idan yana zaune a wuri baka isa ka yi mashi gulmar wani ba, amma sai gashi yau yana neman ta fada mashi abun da suke tattaunawa da Hajiya Layla.


Bayan ta kammala faɗa mashi calmly ya furta"bansan meyasa ta sanya min ido ba, bata son ganina kamar na kashe mata wani"
Matsawa Sarah tayi dab da shi ta ɗaura hannayenta saman fadadan kafaɗunsa
"Kada hakan ya dame ka, ni dai shawarar da zan baka, dan Allah ka basu damar da zasu koma Joss, saboda ta nuna batason zama a gidan nan" ta faɗa tana mai tausasa kalamanta.
Jinjina kanshi yayi"zanyi tunani akan hakan,"
Ya faɗa tare da juyawa Ya nufi Katafaren gadonsa, Ya haye ya kwanta idanunsa suna fuskantar ceilling.


Duk sai taji ba daɗi, ganin yanayin shi da damuwa akan fuskarshi, tasan bai wuci ƙiyayyar da hajiya layla take nuna mashi bace tasa shi shiga yanayin.


"Babe, kana buƙatar wani abu ne In kawo maka"?


Batare daya kalleta ba Ya furta"Bana buƙatar komai, ki zo ki kwanta a gefe na" taji dadin maganar daya furta mata da sauri ta nufi gadon tare da hayewa ta zauna kan mattress din, sai da tafara zage zip din rigarta, ta cireta kafin ta kwanta saman kirjin shi, ya ruƙo waist dinta da hannun shi ɗaya, ɗagowa tayi da blue eyes dinta tana kallon sajan fuskarshi.
"Bana gajiya dakai, banƙi mu kasance har Iya ƙarshen rayuwarmu atare da kai ba, Idanunsa dake a lumshe yaɗan buɗe su A hankali yana duban fuskarta ba tare daya ware su ba.
Sumbatar cheek dinsa tayi, tamkar zaiyi murmushi sai dai bai bari Ya bayyana ba, ta fahimci yaji dadin abunda tayi masa, kallon juna suka cigaba da yi, tunawa tayi da layin dake akan wayar Zeenatu, har ta buɗe baki zata fada mashi kiran da akayi da bakuwar mumber da sauri ya ɗaura mata yatsa sama lips dinta.


"Ina buƙatar hutu!" murmushi tasakar mashi, tare da rungumo shi suka ƙanƙame juna, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da shi.


Idan muka koma 6angaren Zeenatu tun da ta watsa da gudu ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta haye saman gado ta kwanta tare da rungumo pillow a ƙirjinta, fuskarta ɗauke da murmushi, wani irin so da ƙaunar yaya shureim take ji, taso ace Benazir bata katse mashi hanzarin shi ba, da yau ta kar6i first kiss dinta a wurin hubbinta, wani irin nishaɗi take ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, sai faman juyi take yi a tsakiyar gadon kamar me fama da ciwon ciki.


Jefar da pillown hannun tayi tare da saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, after some mins ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa ta nufi glass wardrobe dinta, suturar jikinta ta canza zuwa riga da skirt launin dark brown, ta dawo gaban mirror ta zauna tana kiciniyar ɗaure gashin kanta da ribbom.


Jin motsin shigowar mutun ɗakinta ne yasa tayi sauri juyowa don ganin wanene
Benazir ce a tsaye ta goya hannayenta saman kirjinta,
Kamar mara gaskiya haka zeenatu take kallonta, duk tabi ta kame kanta wata irin kunyar Benazir ce ta kamata gani take yi kamar taga abunda suke yi ita da dr. shureim.
Muryarta da in'ina ta furta"am.. um.. aunty Benazir kece" dariya Benazir tayi tare da shiga ciki tana fadin"Zeenatu kenan, dole ki ruɗe babyn shureim"
Waro ido waje tayi jin ta kira ta da sunan babyn shureim hakan na nufin tagansu ɗazu, da sauri ta miƙe daga kan mirror chair din tana faman duƙar dakai ƙasa
"Kin bani mamaki zeenatu, Ki rasa dawa zakiyi soyayya sai yaya shureim! Kamar kin makance, May be bakisan shekarun shi ba, Ki daina ganin shi kyakkyawa kamar matashin saurayi, ya kusa sa'an daddynki... " har saida gabanta ya fadi jin abunda Benazir ta faɗa mata.
Muryarta na rawa ta furta"am... aunty Benazir kina nufin yaya shureim da daddyna sa'annin juna ne"?


"Eh mana, kema in banda abunki taya zaki yi soyayya da wanda Ya girme maki? yafa haife ki" Da biyu Benazir take fada matan hakan duk don tacanza mata ra'ayinta na son ya shureim, don ita aganinta bai kamata yaso ƴar cikinsa ba, badan bata son shi da zeenatun ba, sai dai bata jin zata iya bari ya auri mace mai ƙaramin shekaru amatsayinshi na tazurun daya daɗe baiyi aure ba, zaifi dacewa Ya auri babbar mace wadda takai shekara talatin.


Bubbuga ƙafafu zeenatu tayi akan floor, voice dinta da shagwa6a tace.


"Aunty Benazir ai ba haramun bane, cos The Prophet Muhammad, peace be upon him, married Aisha when she was very young," ta faɗa tare da sanya hannu ta rufe fuskarta cike da jin kunyarta.


Dariya Benazir tayi tana dubanta da mamaki wato bazata kar6i shawararta ba tafi son Sugar daddy irin Ya shureim.
"Zeenatu Ki fahimce ni, Kinfi buƙatar saurayi wanda baifi shakara ashirin da bakwai ba, Ina zaki kai Ya shureim"?


"Aunty benazir dan Allah kidaina fadin haka, wallahi bana so, Inason Ya shureim ɗina, koda tsohone shi" tamkar zata fashe da kuka tayi maganar.


Gyaɗa kai benazir tayi"its Okey, babyn shureim, Naji nayi shiru bazan ƙara magana ba, hakan yayi maki"
Tana faman zumbura baki tace Eh, dariya Benazir tayi da zolaya take fadin"lallai ya shureim yayi kasuwa, Irin wannan So haka? Ta fada tare da samun wuri gefen gadon zeenatu ta zauna.


"Ina wayarki take"?


"Nabarta A cikin wandon jean dina dana cire, Bari na dauko maki" da sauri ta juya ta nufi inda ta rataya kayan.
Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da wayar ta miƙa ma Benazir, bayan ta kar6a, zeenatu ta zauna agefenta.


Screen din wayar ta ƙurama ido hoton Fatiman shureim ne, nan take yanayin fuskarta ya canza, da sauri ta furta"Zeenatu! Meyasa kika daura hoton nan a wallpaper dinki"?
"Saboda inason hoton ne, yaya shureim ne ya tura mun hotunanta"
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, aranta ta ayyana bazai yiwu ba, dole in sa zeenatu ta sauke hoton fateema daga wallpaper dinta.
"Aunty Benazir, Ɗazu An kirani da wata baƙuwar number lokacin na shiga toilet, bansan wanene ba, har mommy nakaima wayar tace ita batasan ma da layi akan wayarba, Nima kuma bansan da layin ba"
Cikin kulawa Benazir tace"waye ya siya maki wayar ne"?
"Daddy ne Ya siya min, amma bani yaba ma ita ba, saboda bayason ina yawan amfani da waya zata Iya ɗauke min hankali daga yin ibada, shine yaba mommy wayar, ita kuma ta ajiye min ita, dama ni ban damu da ita ba, sai da naga hotunan fatiman ya shureim awayarsa shine naje nace ma mommy ta bani wayata zan yi amfani da ita" tunda tafara yin maganar Benazir bata kau da ido daga kallon ta ba, tayi mamakin da har shureim ya iya faɗama Zeenatu sirrin shi, hakan ya ƙara tabbatar mata da irin Ƙaunar da yake yima zeenatu.


A hankali ta kau da idanunta daga kan Zeenatu, ta ɗaurasu kan screen din wayar, Call logs ta shiga, nan take tayi tozali da bakuwar number da aka kira zeenatu da ita kusan 2 missed calls, Aranta ta ayyana Uncle musa ne ya siya mata layin awaya ko kuwa tare da sim din aka siya mata wayar? Tayaya ma haka zata yiwu? Idan shine ya sanya mata sim din meyasa bai sanarma mom sarah ko ita zeenatun da akwai sim a wayar ba? Sannan babu yadda za'ai companyn da aka sayi waya su bada ita tare da sim"


Zeenatu dake kallonta ganin ta ƙurama screen din ido babu alamun zatayi magana ne yasa tace"ko dai in kaima daddy wayar ya duba min mommy ma tace idan ta shigo gidan zata bibiyi layin"!


"A'a zeenatu, Kada ki kai mashi wayar, nafi tunanin shine ya sanya maki sim din aciki ba tare dasanin ki ba may be ya manta bai faɗa maki ba, sannan layin da aka kira ki da shi ina da tabbacin wrong number ne suka kira"


"Nima raina ya bani hakan, to ki goge min layin daga kan wayata"


Benazir tace"A'a, kada mu yi saurin goge number, Mu jaraba kira don mu faɗa ma mai layin wrong number ne ya kira, Kinga ta hakanne zai iya gyara number din ya kira wanda yake son yin magana da shi"


Jinjina kai zeenatu tayi alamar gamsuwa da bayaninta.
"Yaushe zamu kira su"?
"Yanzu zan jaraba"
Danna kira Benazir tayi, duk sun ƙagara da son jin me layin ya ɗaga sai dai kash Kiran yaƙi shiga"
"Ki bar min wayar a hannuna, tunda ba amfani kikeyi da ita ba, Zuwa anjima zan jaraba kiran layin"
Amsa mata tayi da toh
"Amma idan mommy ta tambayeni ina wayar ya zan fada mata"?


"Sai kice mata ni na kar6a, ina wani amfani ne da ita" amsa mata tayi da toh.


"Namanta wayata a hannun mutumin da na zauna awurinshi can ƙasar Canada" benazir ce tayi maganar
Zeenatu tace"aunty dama a canada kika zauna? Ya sunan mutumin da kika zauna a wurin shi"?


Shiru ta yi tamkar bazata tanka mata ba tace"hakane a canada na zauna, mutumin daya ruƙe ni sunan shi Zaki Mubarak Obinna, ɗan gidan chief of army staff bansan ko kin san shi ba"


Murmushi zeenatu tayi tare da cewa"nasan ƴan family din obinna sosai, tun kafin in mallaki hankali na muna yawan zuwa estate dinsu nida mommy na, da yake suna mutunci da Hajiya saratu daga bayane daddy ya hanata zuwa Yawo dani, tun da na kammala secondry school Ya garƙameni agida, bai bari tana fita dani, har sai da Ya shureim Ya dawo da zama gidanmu sannan Ya kyaleni ina fita tare da shi.
Murmushi benazir tayi"Allah sarki, kada ki damu ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login