Showing 30001 words to 33000 words out of 56271 words
Chapter 11 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt
lalurar dake atare da shi, bana so wani abu ya cutar min dakai...." gyaɗa kai yai"bakomai baba nagode" cikin sanyin murya ya faɗi hakan.
Murmushi sheikh imam ya saki yana fadin"aminina yakamata kaga yaron nan da Hateem ya ƙwallafa rai akai, dama sauran yaran, zaku sha mamakin kamanninshi da Hateem, daku kanku" ya faɗa yana nuna su Deen, ba yabo ba fallasa suka dube shi batare da sun ce ƙala ba.
Baba obie ya ɗan yi jim na wani lokaci kafin yace"aminina, acigaba da bashi kulawa ta musamman, Idan yaji sauƙi Allah ya raba shi da abun dake damun shi, in sha Allah zamu je mu duba shi, zamu taya shi da addu'a, Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi"
Sheikh imam ya amsa mashi da ameen aranshi yayi mamaki yadda suka nuna basu buƙatar ganin yaran duk da ya fahimci kamar suna gudun haɗuwa da danish ne saboda lalurar shi.
Duba agogo sharafuddeen yayi"dare yana ƙara yi, Ina so zan wuce"
Baba obie ya dube shi"zaka iya tafiya tun da inada madadinka," ya faɗa yana nuna chief Owais da cup din hannun shi
Murmushi sharafudeen yasaki tare da kallon Owais a fakai ce ya kashe mashi ido ɗaya, murmushin gefen fuska chief ya saki ganin abunda daddynsa yayi masa, ba tun yau ba ya saba yi mashi hakan sometimes tamkar aboki yake ɗaukar shi.
Gyaran murya Senate lateef yai hankalinsu ya dawo kanshi, fuskarshi babu walwala ya furta.
"Hateem, kada ka manta, akwai taron da zamuyi a National Assembly, domin gabatar da jawabi da kuma ganawa da kakakin majalissar wakilai"
"Ina sane da wannan" atakaice Hateem ya furta hakan.
Sharafuddeen yace"bayan haka zamu ziyarci national Mosque, da kuma National Christian Centre, akwai kuma ganawa ta musamman da zaka yi da sarakunan gargajiya daga sassan kasar mu, after that zaka halarci State Dinner (Liyafar cin abincin dare) tare Ni A Villa"
Sheikah Imam yace"babu hutu kenan Hateem zai fara yawo, ko da yake haka ya dace tun da ba kowani lokaci ake samun damar zuwa ƙasar ba, ƙwara ka za gaya gari nima dai hadani za'a je villa wurin liyafar ko ba agayyace ni ba sai na je don nasan za'aci kaji" da zolaya sheikh imam ya fada yana murmushi
maganar shi ta ba su nishaɗi, gaba ɗayansu suka sanya dariya.
Sharafudeen yace"aikune kan gaba baba, kai zaka buɗe mana taro da addu'a" sheikh imam yace masha Allah nagode da karramawarnan"
Baba obie yace"Idan da hali ma, yakamata ku leƙa masarautar yarbawa ku gaishe da dangin mariganya ƙudirat, da kuma masarautar kano suma yakamata aje masu da Hateem, sannan zaka ziyarci National museum dake a lagos, da kuma Yankari Game reserve.... "Tunkan baba obie ya ƙare maganar, Hateem ya furta"baba duk ni zan halarci waɗannan wuraren daka lissafa? Bani da isasshen lokaci, On saturday next week zan koma canada, ina buƙatar hutu" fuskarshi a yamutse yayi maganar.
Senate yace"dole ne kaje ko kana so ko baka so, mu zamu jagorance ka, Tun da ka shigo ƙasar tamu, dole ka zaga dangi, ka kuma ziyarci wuraren buɗe ido,"
gyaɗa kanshi yai har cikin ranshi baison yawace yawacen nan badan komai ba sai don saboda Danish baisan yayi nisa da estate din, duk da an yanke alakarshi da yaron zaifi mashi kwanciyar hankali idan har yana akusa da inda yake rayuwa.
"On friday zamu shirya maka family dinner, na bankwana" acewar Deen.
Muryarshi asanyaye ya furta "Allah yakaimu lafiya" suka amsa mashi da ameen.
Sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa a tsakaninsu har wuraren ƙarfe sha ɗaya Na dare, Kafin daga bisani sheikh Imam ya rufe masu taron da addu'a, daga nan su ka yi wa junansu sallama, Har bakin entry Hall, Baba obie yayi masu rakiya, Hateem Ya shiga mota tare da sharafuddeen, Sheikh Imam tare da Boss man suka shiga mota ɗaya, suma sauran kowa Ya nufi Gidan shi dake a estate din, banda chief Owais, baba obie Ya ruƙe shi, yace shi zai taya shi kwana yau tunda shi yakawo abunda ya tsoratar da shi babu musu owais ya amince mashi domin shima yayi kewar kakan nashi.
Tun acikin mota, Sharafuddeen yake tausar Hateem akan yayi haƙuri dangane da hukuncin da baba Obie ya yanke mashi na raba shi da yaron, sannan ya kwantar da hankalin shi, ya yi mashi alƙawarin ko bayan baya ƙasar zasu kula da rayuwar yaron, ba zasu ta6a bari ya wulaƙanta ba, kalamanshi sun tausasa zuciyar Hateem, shi abinda yafi damunshi raba shi da akayi da yaron, yanzu shikenan bazai sake zuwa inda yake ba, har ya koma canada , abun ya ta6a zuciyarshi baiso haka ba, har cikin gidanshi sharafuddeen ya shiga, suka gaisa da gimbiya mujeedat, ita kadaice bata runtsa ba saboda rashin dawowar mijinta, Su Yazrin tuni sun nutsa a baccin su, bayan sharafuddeen yayi masu sallama ya fito daga gidan security detail dinshi suka buɗe mashi mota ya shiga, batare da 6ata lokaci ba, suka nufi Aso Villa domin komawa ga muhallinsa.
Bayan barin su gidan da kusan mintuna talatin, Hajjaty ta lalla6a taje ta ɗauko wayarta data ajiye ƙasan table, jiki na rawa ta nufi dakin don ta kaima pravin, tana shiga ta taras da shi yanata faman yin zarya adaki kamar mai fama da ɗan kanoma da basir, duk ya ƙagara da son jin abunda suke tattaunawa, jin sallamarta yasa shi yin saurin tambayarta ina wayar, da sauri ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a tare da kunna recording din, ya soma sauraron tattaunarsu, hajjaty dake kallon shi, ganin yadda yake tsuma zufa ta wanke fuskarshi yasa tace mashi lafiya, rai a6ace ya jefar da wayar saman gado yana fadin wannan wace irin masiface? Wato dole dai sai yaran nan sun zauna a estate din nan, wallahi bazai yiwu ba, duk yadda zanyi saina yi silar barin su, nasan owais ne ya tunzura obie har ya amince da zaman su, saboda ya makance akan ƙaunar shi, Idan sunsan wata basu san wata ba....." yana huci yai maganar, hajjaty dake kallon shi, tsantsar mamaki ne akan fuskanta, harta fara kokwanton anya pravin baida wata manufa akan yaran? Meyasa ya tada hankalin shi akansu? Tayi zurfi a tunaninta taji ya buɗe kofar ɗakin Ya fuce waje, Jiki asanyaye ta nufi gefen gadonta ta zauna tare da kwantar da kanta, tayi tsammanin zai dawo dakin amma sai taji shiru, ranta ne ya bata cewar ko ya tafi dakin hajiya saratu ne hakan yasa ta ja bargo ta lullu6e jikinta....
*❤EX-PRISONERS❤*
Bayan Sun kammala Cin dinner dinsu, sam sun kasa runtsawa saboda tunanin ɗan uwan su Danish, ɗazu da marece sun je duba shi, Yanzu ma kuma Bayan sun sanya kayan bacci a jikin su sun yi shirin kwanciya, ɗakin shi suka nufa, gaba ɗayan su ne a kawaye da gadon shi, sun yi tsaitsaye cirko cirko suna kallon shi.
Unaisah da Batool sun sanya kayan bacci kala ɗaya Riga da wando launin black gray, rigar tana da hula duk sun lullu6e kawunansu da ita, Jemimah da Azeeza ma kalar nasu sleep dress din iri ɗaya ne Yar gown ce dai dai gwiwa ta tsaya masu launin pink colour, sun daure kawunansu da head scarf, Praveen da Hanna launin nasu farare ne riga da wando masu zanen flowers ajikinsu.
Hala zalika Mazan ma kowan nan su yana sanye da kayan baccin sa.
Tun suna daga tsaye har dai suka kaiga samun wuri gefe da gefen gadonshi suka zazzauna, banda Gabriel dake atsaye ya goya Azeeza a bayan shi saboda makantar daren ta, duk da lalurar ta fara sauki yanzu, tana gani ba laifi saboda hasken dake gauraye da gidan tamkar da rana, yana ƙara ƙarfafa mata ganinta sai dai babu clear amma takan iya shaida fuskokin su, shiyasa bata damuwa yanzu bama kowa yasan tana da lalurar ba sai ƴan uwanta.....
Fuskokinsu babu walwala, yayin da suke kallon shi, musamman Haris hawaye tuni sun jiƙe fuskarshi.
"Allah ya baka lafiya ɗan uwana rabin raina, Danish na tausaya maka, Ina jin raɗaɗin da ka ke ji acikin zuciyarka, In sha Allah ƙarshen wahalarka ne Yazo"
murya arauna ce Haris Ya furta maganar, idanunsa akan fuskar Danish dake akwance tsakiyar gadon kamar matacce.
"Danish, ban sani ba ko kana ji na, dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka ta6a sanya damuwa akan abunda ke faruwa dakai, ko jiya da muka guje ka don ba mu san kai bane, amma Yanzu mun riga da mun sani, kuma in sha Allah, a kowani hali na rayuwa duk runtsi duk wuya muna a tare dakai, har ƙarshen rayuwar mu" Batool na ƙarasa faɗar maganar ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ta kifa kanta saman mattress din daga gefen hannun shi, ta ɗaura nata hannun akan nashi.
"Batool ki daina yin kuka, zaki ƙara karya mashi zuciyarshi, saboda Ina ji araina yana sauraron mu ba bacci yake yi ba" cikin kwantar da murya Unaisah ta furta maganar, idanuwanta akan Batool cikin shesshekar kuka tace"ya wahala sosai, ko motsi bai iyayi, mu kallon shi kawai mu ke yi, shi ka ɗai yasan raɗaɗin da yake ji acikin zuciyar shi, sai yaushe ne zaiji dadin rayuwarshi"? Cikin jin ƙunar rai ta furta maganar tare da dago da kanta idanuwanta sun kaɗa jawur..
Fashewa da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, sautin su ya karaɗe ɗakin, Naufal Yace"Dallah meye haka? Kuka shi zai mana maganin damuwar ɗan uwan mu ne? Ku bar mu muji da abunda ke damunmu mana" zuciyarshi a jagule yayi maganar,
Muryar Jemimah da shessheƙar kuka tace"Ni wallahi tausayinshi nake ji, bawan Allah, lokacin da muna a daji bamu lafiya shi ya rinƙa ɗawainiya damu har muka ji sauƙi....." kafin ta ƙare maganar, parveen cikin raunin murya ta katse ta da cewa"Idan muna jin yunwa shi yake sama mana abinci, sannan Ya hana idonshi bacci duk don saboda mu, amma meyasa mu muka kasa taimaka mashi awannan halin"? Muryarta na rawa ta jefa masu tambayar.
"Saboda bamu da yadda zamuyi Parveeen, addu'a ce kadai zamu Iya taimaka mashi da ita," acewar Javed shima fuskarshi ayamutse take.
"Ba iya addu'a ba javed, Idan muka tona asirin miyagun mutanan can da suka ƙasƙantar da rayuwarmu, Ina da tabbacin zamu Yi nasarar kawo ƙarshen matsalar Danish damu kan mu, don kuwa nasan har Yanzu suna nan suna bibiyar rayuwarmu bazasu ta6a ƙyalemu ba kodan saboda kada mu tona masu asiri dole subi diddiginmu" sajeed ne Yai maganar..
Unaisah ta natsu tana kallonsu, ba tare data tsoma baki ba, saboda ita a halin yanzu ta fahimci wani abu, tun da har jami'an isod suka gano salsabeel to kuwa tana da tabbacin sun san komai game da rayuwarsu!! Kallonsu kawai su ke yi.
"Ƙwara kowa yasan me suke aikatawa, mu faɗa masu kawai, su taimaka su rabamu da su, Su ƙyale ɗan uwanmu yayi rayuwarshi cikin salama" Hanna ce ta faɗa tana faman tada jijiyoyin wuyanta.
Calmly Unaisah ta furta"ku daina surutu kuna hana shi natsuwa, yakamata mu je mu kwanta, tun da mun ganshi inyaso gobe da safe sai mu dawo mu ƙara duba shi"
Shiru su ka yi, ba tare da sun motsa ba saboda basu sun yin nesa da shi, da da halima a ɗakin shi za su kwana, yayin da su ke cigaba da kallon shi tamkar zasu haɗiye shi, tsananin tausayin shi suke ji ga wata irin ƙaunarsa da su ke ji.
Parveen da Jamimah sai hamma su ke yi, ita jamimah hada gyangyaɗin bacci.
"Please ku tashi mu tafi ɗakunan mu" Nawfal ne yai maganar, tare da miƙewa ya zagaya ta 6angaren da garkuwa yake akwance ya duƙar da kanshi ya manna mashi sumbata akan forahead dinsa, ganin hakan yasa Jemimah yin sauri rarrafawa tsabar iyayi saman chest dinshi ta haye tukunna ta manna mashi sumbata kan cheek dinsa har sau biyu, murmushi kowan nan su yasaki abun ya ƙayatar da su.
Ƙarasa hawayewa gadon Batool tayi har zuwa gefen Garkuwa in a cool voice ta furta"ɗan uwana rabin raina, idan kana saurare ni, nayi kewarka sosai, Allah ya baka Lafiya sanyin idaniyata" gefen fuskarshi ta manna ma kiss, kafin ta sauka daga kan gadon, da sauri Haris ya zagaya ta inda su nawfal suke a tsaye daga gaban gadon ya russina tare da ruƙo hannun Danish ya buɗe tafin hannunsa A hankali ya sumbace shi kafin Ya furta"ko ban faɗa maka ba, nasan kasan da irin ƙaunar da nake yi maka jinin jikina, Allah ya tashi kafaɗunka" bayan Haris Ya saki hannun shi, Javed Ya miƙe ya nufi Side da danish yake, Ya manna mashi kiss a forehead nashi.
"Big bro, our guardian, Allah ya baka lafiya" ya faɗa cikin nuna tausayawarshi.
Sajeed dake agoye da Azeeza, Ya matsa kusa da Danish,Ya sauketa daga gefen gadon, da rarrafe ta lalubo Danish ta ɗaura fingers dinta saman fuskarshi ta shasshafa shi, duk suna ta kallonta.
Haris da zolaya yace"kada ki lashe mana ɗan uwa, Kiss ɗaya zaki manna mashi ya wadatar" kusan sau uku ta sumbace shi, biyu kan cheek dinsa, ɗaya kan tsinin hancin shi, bayan ta gama nata, Sajeed ya ruƙo Hannun shi kamar yadda Haris yayi, a hankali Ya sumbace shi gently ya furta"ka kula mana da kanka our super star, zamu kwana da tunaninka, gobe da sassafe zamu zo duba lafiyarka, garkuwar mu"
Murmushi duk suka saki, wani irin daɗi suke ji, mayar da goyan Azeeza Sajeed yayi akan bayan shi.
Hanna ma ta sumbace shi, Ya rage saura Unaisah, dake zaune tayi zugudun kamar mai tunanin wani abu.
"Genie saura ke" acewar jemimah idanuwanta sunyi luhu luhu saboda baccin da take ji.
"Unaisah we are waiting for u, ki yi mashi kiss kamar yadda muka Yi mashi kafin mu tafi" Sajeed ne yai maganar, tamkar bata ji me suke cewa ba, tayi kasaƙe tana faman wurwurga eye balls dinta.
Dafa shoulder dinta Batool tayi"Sister, Kin yi shiru, ki motsa mana, Ko kin manta abun da muka ce zamuyi idan mun fita daga ɗakin Danish"
Haris Yace"menene za ku yi" da sauri tace"karatu ne zamu yi kafin mu kwanta bacci" Ya furta okey,
Jiki asanyaye Unaisah ta ƙarasa haurawa kan gadon, crowling slowly ta nufi Danish, koda ta ƙarasa inda yake a kwance, saita sanya hannu ta zame hular kanta, nan take nannaɗaɗɗiyar sumar kanta ta warwaro ta sauko kan kafaɗunta, rumfa tayi mashi da gashinta ta yadda ba zasu Iya ganin sumbatar da za ta yi mashi ba.
Sajeed Ya buga ƙafa yace"ba mu yarda ba wlh, You are trying to be smart Unaisah, dole ki janye sumar kanki mu gani da kyau" Ya faɗa yana sakin murmushi.
Haris yace"kiyi yadda kowa yayi" Batool da su javed sai murmushi suke saki, shiru tayi bata tanka masu ba.
Babu Mai Iya ganinta acikinsu, ɗaura tsinin hancinta tayi akan nashi, numfashinsu ya soma kokawa dana juna, hatta bugun zuciyarshi saida ya canza, dogon wuyan shi ta fara manna ma sumbata har zuwa kan chin dinsa ta sumbace shi a hankali kafin slowly ta ɗago da kanta, ta sumbaci forehead dinsa, ta dawo kan eye lids dinsa ɗaya bayan ɗaya ta sumbace su, tana ƙoƙarin kai mashi sumbata kan soft lips dinsa ba zato ba tsammani taji an damƙo sumar kanta, da ƙarfi ya ɗago da ita, A firgice ta juyo don ganin wanene Ya katse ta......
Rass taji gabanta Ya faɗi ganin Big Guy, wata irin kunya ce ta rufeta, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe face dinta, su Haris dake atsaitsaye sai tiƙar dariya suke yi, ashe tunda ta dukufa tana sumbatar danish suka jiyo motsin buɗe ƙofa, suna kallon shi yai masu alamar suyi shiru da bakinsu, nan fa kowan nan su Yaja baki yai shiru, Lamarin ya ɗaure mashi kai, don bai fahimci me ta ke yi ma danish din ba, yadai ga tayi mashi rumfa da sumar kanta, Cikin sanɗa yaje gaban gadon Ya daddage Ya damƙo gashinta kanta.
"Ki ji tsoron Allah Jari, Faɗa min kike Aikata ma bawan Allahn nan" fuskar shi ɗauke da murmushi yayi maganar yana bin ta da kallon tuhuma, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi Ni ba ƴar iska bace, ba abun da kake tunani bane, Ka tambaye su ka ji" ta faɗa tare da ɗago da kanta a lokacin ya sakar mata gashin kanta, duk tabi ta ruɗe, gani ta ke yi kamar kallon ƴar iska yake yi mata, tun akan abun da Ya faru ɗazu da suka kama ta a ɗakin Danish ta cire mashi ma6allin gaban rigarshi, shiyasa take fargaban kada ace kallon yar iska yake yi mata.
Sunnar da kanta ƙasa tayi, fuskarta a tur6une babu annuri, sai faman ƙyafkyafta idanunta take Yi
"Ƴan uwan Jari, ku fada min me take aikatawa tunda ita bazata fadamin gaskiya ba" Ya fada Yana nuna su Sajeed Da hannun shi
Har suna hada baki wurin maimaita sunan JARI,
da shagwa6a66iyar Murya Jemimah tace"Unaisa ɗin mu ce Jari"
Big guy yace"Yeah, Ita nake nufi, ko bakusan cewa ita ɗin Jari bace"? Da mamaki suka girgiza mashi kai gami da tambayarshi ma'anar jari.
"Shi Jari wani abu ne da idan ka sanya shi zaka samu riba, yar uwarku jari ce gare mu baki ɗaya, tun da muna ƙaruwa da ita, kamar dai yanzu da take koya mana wani baƙon abu...." tunkan ya ƙare maganar Unaisah tai saurin furta"wlh bani na faraba ai, Naufal ne Ya fara Yi mashi kiss, kowa yayi nice ma ta ƙarshe, Kuma ni bama kiss nake mashi ba, Falaƙi da nasi nake karanta mashi..." a shagwa6e ta ƙare maganar.
Dariya suka saki gaba ɗayansu, bayan sun lafa, Big guy yace Ku tashi muje in rakaku ɗakunan ku, Dare Yayi sosai, Yakamata kuna bacci da wuri saboda karatun asubahi da ake koya maku" amsa mashi su ka yi da toh, yakai hannu ya ɗauki Jemimah, kafin su bar ɗakin saida Kowan nan su yayi mashi addu'a suka tottofe mashi jikinshi, har sun fita Unaisah ta dawo ɗakin da gudu ta lullu6e garkuwa