Showing 39001 words to 42000 words out of 56271 words
Chapter 14 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt
hau amma sai taga Ya nufi elevator, Zaro idanu tayi ganin inda zasu shiga, tunda take arayuwarta bata ta6a hawa elevator ba sai yau, wani irin daɗi take ji, musamman da suka shiga daga ciki, tayi sama da su A hankali ta sauke su a second floor, kofar ta zuge, fitowa yai daga ciki da sauri tabi bayanshi, abakin kofar ɗakin nan data ta6a zuwa kwanaki taga wani mutun Yana motsa jiki nan yakaita nan take ta gane cewa shine ɗakin kuma mutumin da tagani shine chief dinsu.
Abakin door room din suka dakata da yin tafiyar,
"Ƙofar tana da password, ba zaki Iya shiga ciki ba tare da kin sanya password din taba, sai kuma idan shine ya baki iznin shiga" ɗaga mashi kai tayi alamar toh.
"Amma yanzu babu security din ƙofar zaki iya shiga, sai dai ki kula please banda 6arna" dariya tayi tana fadin"6arna kuma sai kace wata ƙaramar Yarinyar"
"Nasan ki da ƙiriniya, shiyasa na faɗi hakan"
Yamutsa mashi fuska tayi batare da tace komai ba, Ya buɗe mata ɗakin Yace ta shiga ta fara aikin idan ta kammala yana s falo Yana jiran ta" amsa mashi tayi da toh, sai da taga Ya bar part din tukunna tayi sallama ta shiga daga ciki.
Kamar yau ta fara ganin dakin, dama time din farko data fara shiga bata samu damar ƙare mashi kallo ba, har mamaki takeyi idan ta tuna mai rai ne ke rayuwa a dakin, Kamar baza'a mutu ba, komai ka kalla mai tsadane da inganci furniture din dakin har daukar ido suke yi idan ka kalle su, tsabar haɗuwarsu.
Ga wani sanyin A.c mai haɗe da ƙamshin room freshner har cikin hancinta take shaƙar shi.
A ƙalla ta 6ata tsawon mintuna, kafin ta soma tambayar kanta, meya kawo ta dakin? Don ita bata ga abun da zata gyaraba, babu datti ko kaɗan komai a gyare yake kamar yau aka fara amfani da ɗakin, har ƙwara bedsheet dinsa Ya tattare alamar anyi amfani da shi.
Ɗaura idanunta tayi akan Toilet dinsa, daga inda take tana kallon komai dake aciki ta jikin glass din bangon , atsaftace yake komai na cikinsa fari ne ƙal.
Ruƙe qugu tayi da hannu aranta tana fadin"Ikon Allah, To ni meye amfanin zuwana part dinsa? Me ake so nayi! Bayan babu wani abu da zan gyara, ni wannan dakin ma in nawane ai say yayi sati kafin in gyara shi"
Ta jima atsaye ba tare da ta ta6uka komai ba, tunawa da big guy dake jiranta a falo, ne yasa tayi saurin nufar gadon chief, Ta soma gyara shi, bayan ta gama ta koma tana jera mashi turarurrukansa da body lotions dinsa da yayi amfani da su da safe, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama gyara ko'ina na part dinsa..
Fitowa tayi daga part dinsa ta sauko down, Babu kowa A falon, Ƴan uwanta duka suna a bedrooms dinsu.
"Kin gama gyaran"? a hanzarce Ta juya Baya jin muryarsa, Big guy ne ya nufe ta hannun shi ruƙe da haɗaɗden wooden tray madaidaici daga saman lafiyayyan breakfast ne.
"Na gama,"
"Madallah sannu da ƙoƙari" tace mashi yawwa,
"Yanzu ki biyo bayana muje dakin, inaso na gwada maki yadda za ki yi serving din shi abincin" amsa mashi tayi da toh,
Sai da ya fara tafiya tukunna tabi bayanshi, har suka haura second floor, bayan sun shiga ɗakin ya ɗaura tray din kan wani ƙayataccen table, kafin ya dube ta yana fadin"kin yi ƙoƙari Jari, haka kika Iya gyaran ɗaki"? Murmushi tasaki jin ya yabe ta, aranta tace dama can a gyare yake.
Batare da 6ata lokaci ba, ya soma kwatanta mata yadda zata gaishe da chief da kuma yadda zata tambaye shi me yake buƙata ta zuba mashi, hada yadda zata zuba mashi abincin duk sai da ya koya mata, ya yaba da hankalin ta shiyasa bai kawo ma ranshi cewa zata yi mashi kwa6a ba.
"Zan tafi Jari, please Kada ki bani kunya, Kiyi komai awanyance, Inaso Chief ɗinmu Ya yaba dake" ya faɗa yana kallonta,
"In sha Allah, zanyi ƙoƙari"
"Good Girl"
Juyawa yayi da sauri Ya nufi ƙofar fucewa daga falon, tsaye tayi tana yanke shawara da zuciyarta.
Maimakon tayi abunda yace mata, sai ta Fito cikin sanɗa kamar 6arauniya tana ƴan waige waige ganin babu big guy ne yasa ta saki jiki, da sauri ta sauko down stairs ta nufi bedroom ɗin su, tunkafin ta shiga ta soma kwalawa Batool kira.
Batool dake a zaune kan mirror chair, har tayi wanka ta sanya Pakistan ajikinta, Riga da wando, launin blue sky, ta sauko da sumar kanta har tsakiyar bayanta masha Allah.
Jin kiran da Unaisah take ƙwala matane yasa tayi saurin miƙewa tare da juyawa tana kallonta da mamakin ganin yadda take haƙi
"Lafiya"?
"Toilet zan shiga sister, uziri gare ni, gashi big guy ya sanya ni yin aiki a part din Chief dinsu, Dan Allah ki taimaka ke ki yi aikin" tana magana haɗi da dafe cikinta.
Adabarbarce Batool tace"to ai ni bansan dakin shi ba, sai dai ki nuna min"
"Muje in nuna maki" ta faɗi tare da yin saurin zuwa gaban closet din kayansu ta ɗauko mata mayafin pakistan dinta, sai da tayi mata rolling din shi tukunna ta Ruƙo Hannunta.
Gaba tayi Batool tabi bayanta suka shiga elevator, su batool basa banbana sai bin elevator din take Yi da kallo
"Sister menene wannan?
"Sunanta Elevator, Na'ura ce dake ɗaukar mutun daga sama takai shi ƙasa ko daga ƙasa takai shi sama, tafi sauƙi akan bene, Kin ga shi yana gajiyar da mutun amma ita wannan tsaye kawai zakiyi tayi sama dake, bari na gwada maki yadda zakiyi amfani da buttons dinta, Nima a wurin big guy na gani da muka shiga atare" A tsanake tayi mata bayanin yadda zata Yi amfani da ita.
Murmushi Batool tasaki"meyasa baki ta6a nuna min ba? Ai da bazan ƙara hawa bene ba, duk in zanje dakin aunty ummi kona Danish, sai dai in hau elevator"
Unaisah tace"indai wannan ce har sai kin gaji da ita, don daga yau kece zaki dinga zuwa gyara ma chief dakinsa sannan ki kai mashi abinci"
A matuƙar ruɗe Batool ta furta"Ni kuma"? Ta faɗa tana zare idanuwanta.
"Ƙwarai kuwa, big guy yace ta wannan hanyarce kadai zamu Iya biyanshi abunda yayi mana, wato mu dinga kyautata mashi..... " cikin kwantar da murya tayi ma batool bayani.
Fuskar Batool da fara'a tace"indai wannan ne babu damuwa, zan dinga kai mashi abincin in gyara mashi ɗaki kullum in sha Allah"
Murmushin gefen fuska Unaisah ta saki, Aranta taji daɗin amincewar da Batool tayi, Dama da biyu tayi hakan, saboda batason tana kusanta kanta da wani Namiji, ta san halin mutuminta sarai, duk ranar da Allah ya farfaɗo da shi ya risƙeta a ɗakin chief tabbas komai zai Iya faruwa.
Fitowa su ka yi daga elevator din, A bakin ƙofar ɗakin nashi, Unaisah ta sanya hannu ta buɗe, suka shiga daga ciki, tun da Batool ta daura idanuwanta akan haɗuwar ɗakin nan fa tabi ta ruɗe ta rikice kamar wuyanta zai balle saboda yadda take ƴan leƙe leƙe, tambayoyin tadinga jefa ma unaisah menene wannan? Ya ake amfani da shi.
"Kinga kiyi abunda ya kawo ki, a sannu zanyi maki bayanin komai, Yanzu dai zan tafi in barki, ai na fada maki toilet zan shiga, ki natsu ki saurare ni kada ki yi mashi kwa6a, mutunne mai son mace mai tsafta da natsuwa, nasan duk kina da wannan, dan Allah kada ki bani kunya my sister,"
"In sha Allah"
"Yawwa My baby Girl, Idan chief din Ya shigo cikin girmamawa zaki gaishe da shi, kina ji na ko"? Ɗaga mata kai tayi alamar eh, taci gaba da koya mata komai dangane da yarda zata yi serving din shi.
Daga bisani tace"toh, Sister ni zan tafi, ki yi zamanki ki sha A.c kafin chief Ya ƙaraso" tana fadin hakan tayi saurin fuce wa daga dakin.
Batool ta samu abun kallo, haka ta dinga ƴan leƙe leƙe tana yi mashi yawo a ɗakin shi.
Bayan Unaisah ta sauko down stairs bedroom dinsu ta koma, fuskarta ɗauke da murmushi, har ta ƙagara Batool ta kammala aikin ta dawo don taji meye faru bayan chief Ya shiga ɗakin? Abu ɗaya take zullumi kada Batool tayi mashi kwa6a.
Tunani ta soma yi mai yakamata tayi yanzu? Ɗazu dai da asuba sunyi karatun alƙur'anin da ake koya masu da wasu littattafan addini, sannan sunyi breakfast dinsu, shiyasa sauran duk basu fito daga ɗakin su ba, saboda baccin da bai ishe su ba.
Lokaci ɗaya ta tuna da i phone ɗinta, Jiki na rawa ta nufi bedroom din su, tana shiga ta nufi inda ta ajiye ta, ta ɗauko wayar tare da backpack ɗin Unaiza.
Saman gadonsu ta haye, ta sanya hannu ta zuge zip din jakar ta soma ƙoƙarin lalubo sim din, sam ta manta inda boss man ya sanya mata shi, ranta ne ya bata cewar ta bincika littattafan dake abackpack din wata'ƙil a tsakiyarsu ya zura sim din.
Nan take ta zazzago da Textbooks din Ciki, tare da Diary din Unaiza, buɗe su ta dinga yi tana neman sim din har tazo kan Diary din Shafin farko data buɗe hoton Unaizah ne, Lokaci ɗaya jikinta yayi wani irin sanyi ganin fuskarta, tayi kyau a hoton kamar ka kira sunanta ta amsa maka.
Tunda ta ƙurama hoton ido ko ƙyaftawa batayi ba, A hankali ta daura hannu tana shafa fuskarta, yayin da idanuwanta su ka cicciko tab da ƙwalla.
Taso ace zata Iya karanta labarinta data rubuta a diary din sai dai raunin zuciyarta bazai barta ta Iya karantawa ba, A hankali Ta furta"I love You so much our lovely sister, Allah yaji ƙanki"
Tana ƙoƙarin rufe diary ɗin, Ba zato ba tsammani, Sajeed Ya faɗo dakin sam babu sutura a jikin shi sai ɗan gajeran wando, sumar kanshi ta yamutse kamar yadda fuskarshi take a yamutse babu annuri babu walwala ko sallama baiyi mata ba, Ita kanta data kalle shi sai da gabanta ya faɗi ganin yadda ya faɗo mata ɗaki da short.
Muryarta na rawa ta furta"Sa... jeeed!? Lafiya ka shigo min daki babu sallama meke damunka!? ta jefa mashi tambayar tana kallon shi, babu alamun zai amsa mata har saida ya haye kan gadonta Ya zauna Yana fuskantar ta, la66ansa Na rawa Ya furta" I had a dream..." Ya faɗa yana ƙoƙarin tattara natsuwarshi
A matuƙar ƙagare tace"Wani irin Mafarki kayi ne daya rikitar dakai haka"
Ruƙo hannunta yayi acikin nashi ya matsa shi kafin cikin sanyin murya ya furta.
"TWIN SISTER ƊINA!!" Rass Taji gabanta yayi mugun faɗuwa tunkafin ma taji ƙarashen zancen.
"Sister tun bayan da muka baro prison muka tsinci kanmu a Daji, kafin Allah ya kawo mana ɗauki muka bar dajin Zuwa america, ban ta6a yin mafarki da ita ba, tamkar ma namanta da itane don ko tunaninta bana yi, amma Yau bayan mun kammala Yin breakfast, dama bacci bai isheni ba, na koma ɗakin na kwanta cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ni, kwatsam nayi mummunan mafarkin duk da kin ta6a fadamin babu kyau mutun yayi bad dream ya faɗa ma wani amma wannan mafarkin kamar wani tuni ne da Allah yake yi min akan Ƴar uwata da kuma sauran yaran da ake azabtar da rayuwarsu a gidan kurkukun ƙaddara....... " a yayin da yake yin maganar hawaye tuni sun wanke fuskarshi, Jikin unaisah sai tsume yake yi
"Ina sauraronka, ka faɗamin me ka gani a cikin mafarkin naka"?
"Naga abun da ya fi ƙarfin idanuwana, saboda bala'e kukan da nikeyi acikin mafarkin har a zahiri sautin shi yake fita batare da sanina ba, har sai da naufal ya farkar dani daga baccin ya ke faɗa min.... " shiru ya ɗanyi na wani lokaci suna kallon juna idanunsu azazzare yayin da bugun zuciyarsu ke hauhawa.
"A Cikin mafarkin da nayi, naga sister dina GABRIELLA, tare da wasu Yara sanye cikin jajayen uniform kalar namu, ko'ina na jikinsu Jiƙe Yake da Jini, Hannayensu da ƙafafuwansu a daure suke da igiyoyi, hatta bakunansu an toshe su da jan ƙyalle, na dinga ihu ina kiran sunanta, bata iya yi min magana sai dai hawayen jinin da ke fita acikin idanuwanta.... Sister bansan ya zanyi ba, Ni da farko na fidda rai da ita amma a yanzu inason ganinta inason nasan awani hali take aciki, tana araye kota mutu? Duk da bana kawowa raina cewa bata arai.... " daƙyar Ya ƙare maganar wani irin kukane yaci ƙarfinsa, da sauri ya kifa kanshi saman kafaɗar Unaisah, Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa har yanzu ba su yi wani yunƙuri na ruguza kurkukun ƙaddara ba, tabbas sunyi ganganci saboda kowani ɗaƙiƙa ɗaya da suka 6ata barazana ce arayuwar sauran yaran dake a Prison.
A hankali ta daura hannunta saman bayanshi, Cikin sanyin murya tace"bansan ma me zance ba, ni kaina na girgiza da jin mafarkin da kayi, amma abin da nakeso in tuna maka mafarki ba gaskiya bane, ba lallai bane abunda ka gani ya zamana gaskiya, zaiyi wuya... " lallashin shi taci gaba dayi, Jikinshi duk ya saki babu kuzari kamar wanda yayi ciwo, hada zazza6i ke kokarin kama shi.
ɗago da kanshi tayi daga kan kafaɗarta ta talla6o fuskarshi da hannayenta biyu, dakyar yake iya buɗe runannun idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur da su.
"Dan Allah, ka daina kuka, bana son ganin ɗan uwana a wani hali na damuwa, bana jin daɗi"
Muryarshi na rawa yace"sister, ba zaki gane ba ni kadai nasan abunda nake ji, wannan mafarkin ina jin shi dagaske ba wasa ba, ni dai kawai ki shirya mana abunda ya kamata muyi"
Shiru tayi tana tunani aranta na tsawon mintuna batare da ta kau da idonta daga nashi ba tace"Sajeed, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah komai yakusa zuwa ƙarshe, Yunƙurin da zamuyi zai zamanto TAKUN ƘARSHE a tafiyar mu, A yanzu ba za mu Iya yin komai ba in har Danish bai samu Lafiya ba, Shine jagoranmu kuma garkuwarmu, su kansu mutanan dake kula damu burinsu Danish Ya farfaɗo daga muguwar kasalar da yake fama da ita...."
"Har yanzu bangane me kike nufi ba, shin mu ba zamu Iya tona masu asiri bane? Sai Danish"?
"Wani asiri Zamu Tona masu? Bayan sun riga da sunsan komai dangane da rayuwarmu!!" A firgice Sajeed Yake dubanta da alamun mamaki Ya furta"ke kika faɗa masu"?
Girgiza mashi kai tayi"a'a bani na faɗa masu ba, amma ina da tabbacin sunsan komai, kuma akwai shirin da suke Yi shiyasa suke buƙatar Danish.
Fuskarshi da alamun ruɗanin kalamanta yake kallonta.
Fahimtar hakan yasa tace mashi zan yi maka bayanin komai, Amma Ba yanzu ba, Ni dai burina ka kwantar da hankalinka, Sister dinmu kuma zamu cigaba dayi mata addu'a, Har zuwa lokacin da zamu ɗauko ta"
Kwantar mashi da hankali taci gaba dayi har saida taga Ya samu nutsuwa tukunna tace
"Ka ta shi ka shiga toilet ka wanko fuskarka duk ta 6aci da hawaye" in a cool voice Ya amsa mata da toh, Ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet din ɗakin su Ya shiga ciki.
Har saida taga Ya maida ƙofa Ya rufe sannan Ta kau da idonta, cigaba da neman sim din tayi, sai da ta tarwatsa littattafan A ƙarshe ta gano shi cikin ƙaramin aljihun backpack din, Ajiyar zuciya ta sauke, kafin Ta dauki wayar ta sanya sim din, power button ta danna nan take screen din wayar yayi haske.
Contact ta shiga anan taga phone numbers waɗanda dr laura ta yi mata saving akan waya, Murmushi tasaki tana tunanin wani time yakamata ta kirata awaya su gaisa"? Kafin Ta yanke shawara, Sajeed Ya fito daga Toilet fuskarshi da lemar ruwa ya nufe ta idanunsa akan wayar hannunta, tun kafin yayi magana ta dago da wayar tana nuna mashi tace"Ka tuna wannan wayar"? fuskarshi babu walwala yace"Na tuna, Itace Dr Laura ta america ta baki ko" daga mashi kai tayi"ina fata kanka baiyi maka ciwo"?
Cikin kulawa tayi mashi maganar, zama yayi daga gefen gadon kafin yace"yana yi min amma da sauƙi,"
"Ko in kar6o maka magani"? Girgiza mata kai yayi alamar a'a"basai nasha ba zanji sauƙi in sha Allah"
Diary din dake ajiye gefenta yakai hannu ya ɗauka, har zai buɗe shi tayi saurin fisge shi, Tamkar walkiya wasu hotuna guda biyu ƙananu suka faɗo daga cikin diary din babu wanda Ya lura da su a tsakaninsu har hotunan suka sulale kan floor.
"Bazan bari ka bude shi ba, saboda Zai Iya fama maka raunin dake a zuciyarka," ta faɗa tare da tattara textbooks din da sauran kayan da ta fiddo daga jakar ta mayar da su ciki.
Miƙa mata hannu yayi"tun da kin hanani ganin diary din, Bani wayar Hannunki," babu musu ta miƙa mashi.
Danna danne ya soma yi duk tana kallon shi.
"Unaisah, kinsan wani abu"? Da sauri tace A'a
"Ina ji araina na ta6a ruƙe waya, Kalar wannan, Kamar Mommyna ne ta siya mana nida twin sister dina"
Waro Idanu waje tayi jin abunda yace, Da mamaki tace"Sajeed, Zaka Iya tuna wani abu dangane da rayuwarka? Naji kana fadin ka ta6a ruƙe waya kalar wannan mai tsada"?
Jinjina mata kai yayi"bakomai zan Iya tunawa ba, Yanzu ne naji abun Yanayi min yawo akaina, Amma tabbas nima na ta6a mallakar I phone nawa nakaina hada Laptop, Sannan mahaifiyarmu Farace daddynmu kuma kalar skin dinmu gare shi chocolate colour......" tunda yafara magana Take binshi da kallon mamaki da al'ajabin ta yadda akai har ya fara tuna wani abu dangane da rayuwarshi, bayan ta ta6a tambayar shi a lokacin suna a prison yace mata bazai iya tunawa ba, wata'kil Allah ne Ya nufa sihirin da matsafan suka yi mashi zai warware shiyasa yafara tunanowa,