Showing 6001 words to 9000 words out of 56271 words

Chapter 3 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt

23 Nov 2024

3610

Chief Owais ne Yake nufo su cikin shiga ta tsadaddun suit launin ash colour, wani irin sanyayyan ƙamshin turarene ke fita daga jikinsa, tunkafin Ya ƙarasa garesu idanuwanshi suka sauka akan hannayen prime minister dake a ruƙe dana Garkuwa, walking gently ya nufi bakin gadon ya ɗan dakata da yin tafiya, miƙewa Boss yayi tare da sarah mashi.


"Uncle am ready, yakamata mu tafi suna jiran mu, tun ɗazu suke kira awaya" tamkar baisan furta maganar yayi ta.


Shiru babu alamun prime minister zai amsa mashi.


Boss man ne yace"Sir, wani abu ne ya faru wanda ya ɗaure mana kai, yanzun nan kafin ka shigo Danish Ya damƙi hannun prime minister Ya ruƙe shi sosai, ina da tabbacin shine dalilin dayasa ya shiga yanayin nan"


Ɗage girarsa yai alamar yaɗanyi mamaki kafin ya furta"Okey, kayi mashi magana ta yadda zai ji ka"


Boss ya amsa da toh, sannan ya je daga gefen prime minister yadan russina tare da cewa"Yalla6ai, Chief Ya shigo Yana son yin magana dakai"
Tamakar bazai ɗago ba, A ƙalla sai da ya ƙara mintuna biyar cuf tukunna A hankali Ya dago da fararen idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur da su tamkar mai fama da ciwon ido.


Zagayowa chief yayi ta 6angaren da prime minister yake a zaune Ya tsaya yana duban fuskarshi.


'Uncle are you okey," ya tambayane ganin yadda idanuwanshi suka yi ja.


Can ƙasan maƙoshi sound din muryarshi ke fita"Owais, kaga yadda ya ruƙe min hannuna? meaning, he feels what I feel about him."


"Uncle, don't let that bother you, zamu dawo ne anjima sai ka ƙara duba shi.


Jinjina mashi kai yai ba tare daya furta komai ba, shi kanshi chief yana mai al'ajabin ƙaunar da Uncle Hateem ya ke ma Danish.



Ganin yaƙi sakin hannun Danish, yasa shi sake furta"uncle, we ave to go" Magana chief yakeyi mashi amma gaba ɗaya hankalinshi na akan danish, ganin babu alamun zai motsa yasa chief, ruƙo hannunshi cikin kulawa yai mashi alamar ya tashi su tafi, yunƙura prime minister yayi da niyar ya miƙe daga saman gadon sai dai wani iko na Allah Danish Yaƙi bari ya raba hannun shi da nashi.


Muryar mai girma Hateem na rawa ya furta"My son, Yaron nan Yaƙi sakin hannuna, baison in tafi nabar shi"


"Uncle, kada hakan ya dame ka" chief ya faɗa, tare dakai hannu ya damƙi hanun danish daƙyar ya 6an6areshi daga ruƙon da yayi ma hannun hateem, shatun akaifun danish har saman fatar hannun prime minister, wurin yayi ja.
Hakan ya sosa ran Chief Owais, baiji daɗin yakushin da Danish yayi mashi ba, shi kuwa Hateem ko kaɗan baiji zafi ba, baima lura da yakushin ba.


Chief da boss ne suka kwantar da Danish, tare da lullu6a mashi bargo har saman ƙirjinshi, kafin suka bar ɗakin, bawan Allah prime minister yana tafiya yana waiwayon ɗakin, gani yake kamar idan ya tafi bazai ƙara ganin shi ba.


__________________________✍️


BARI MU ƊAN KOMA BAYA MUJI MEKE FARUWA A 6ANGAREN SU ARMY BOY DA TIGER.


Bayan Gari Ya waye suna akwance Saman Sofa, sun saki baki da hanci suna sharar bacci, ba zato ba tsammani Muryar Khadeeja ta farkar da su, Daga can saman bene ta kware murya da ƙarfi tana fadin"Wayyo Allah, Mayu sun kwanar mana agidanmu, wai ku ba zaku tafi gidan ubanku ba" A firgice Suka farka suna faman mutsustsuke idanuwansu, kafin suka kalle ta, a lokacin harta nufi bene tana saukowa down, Sumar kanta a hargitse babu kayan mutunci a jikinta Rigar baccin jiyace bata cire ta ba, dai dai gwiwarta rigar ta tsaya mata, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, ta dambara janbaki saman la66anta har kan kumatunta, ga wani man baki data shafa sai ƙyalli yake yi.


Kallon juna su ka yi fuskarsu babu walwala, Army boy yace"Allah ya wadaran naka Ya lalace wannan masifaffiyar yarinyar Allah Yayi mana maganinta, saboda jaraba baccin ma bazata bari mu ƙarasa shi cikin dadin rai ba, Ni dai harga Allah an takura min, yakamata sir ya bamu iznin komawa gida"


Takaici Ya hana Tiger cewa komai, Jira yake kawai Ta ƙaraso Yaji me zatace masu
Da gudu ƴan uwanta suka fito daga ɗakunansu, suka biyo bayanta,


A tsakankanin sofas din khadeeja ta dakata da yin tafiyar tana jifarsu da matsiyacin Kallo Tace"mayu masu cinye ma mutane abincinsu, Yanzu sai ku girka mana abunda zamu ci" zaro ido su ka yi suna kallonta.


Mamaki take basu, A iya sanin su dayawa mata suna jin shakkar sojoji amma ita wannan mai kunnan zoman babu alamun tsoronsu a fuskarta.


Tsawa Army boy Ya daka mata"ke karki kuskura ki ƙara kiran mu da sunan mayu idan ba haka ba zan harbe ki da bindiga" maimakon taji tsoron maganarshi saita galla mashi harara tana fadin"Ai wallahi sai kun girka mana abun da zamu ci, tunda kuka cinye mana sauran abincinmu na jiya"


Dafa kafadarta hawwa tayi"dan Allah ki ƙyalesu, Ki zo mu koma ɗaki, ki yi wanka ki canza kayan jikinki," murguɗa mata baki tayi"ni babu inda zanje, wallahi sai sun girka mana abincin da zamu ci, saboda Yunwa nake ji"


Girgiza kai sojojin sukayi suna kallonta kafin suka kalli sauran ƴan uwan nata,
"Jiya bamu samu damar Yin magana daku ba, muna fata kun tashi lafiya"
Atare suka hada baki wurin amsa masu da lafiyalou"
Tiger Yace"Ku fada mana sunayenku muna son ji"


Namijin cikinsu ne Ya fara Yin magana.


"ni sunana MUBEEN" Jinjina kai tiger yayi"Ke fa" Ya nuna Macan dake a gefenshi, Fara ce sol tana da kumatu da ƴar kiba
"RUBINA"
"Suna mai daɗi, Kefa mai idanuwan ƴan chaina, ya fada da zolaya yana nuna ta gefen rubina
"YASMIN SUNANA"
"Good Girl, and You " Da ido Ya nuna Ƴan matan dake ruke da hannun junansu ɗaya Doguwa ɗaya madaidaiciya
"Ni sunana Hibba ita kuma Sarah"
"Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, Allah yayi ma rayuwarku albarka" amsa mashi sukayi da ameen
Khadeeja masifaffiya tace"ƙwarama da baku tambaye ni sunana ba, don ba fada maku zanyi ba" murmushi suka saki ba tare da sunce mata ƙala ba.


Bubbuga ƙafafuwanta tayi"ni dai yunwa nake ji, ku tashi ku shiga kitchen ku girka mana abinci"
Army yace"bamu Iya girki ba, Ko kin ganmu da zannuwane ɗaure a ƙugunmu?
Harara ta watsa mashi
Tiger yace"Yar uwa khadeeja, baku da maiyi baku girkine a gidan"?
Hawwa ce ta bashi amsa da cewa"yayanmu salsabeel shine yake girka mana abinci"


Zaro ido Tiger yayi"kina nufin wannan ƙaton mutumin"?


Ɗaga mashi kai tayi alamar eh
Sarah tace"ba koda yaushe yake girka mana abinci ba, yaya omar yana kawo mana daga gidan su," sun gane wa take nufi, wato Big guy shi ne suke kira da Asalin sunan shi Umar.


Kallon agogo Army boy yai a lokacin ƙarfe goma sha biyu na safe.


"Da alama sun manta yau basu kawo maku abincin da wuri ba, Ya za'ai kenan"?


Da sauri Mubeen Yace'ai akwai yogurt da madara a frigde, hada bread a store, Idan muna jin yunwa kafin akawo mana abinci su muke ɗauka mu ci,"


Ran khadeeja Ya gama 6aci, Bubbuga ƙafafuwanta tayi hankalinsu ya dawo kanta, idanuwanta rufe ta soma zazzaga masu masifa tana fadin"ni wlh bazansha yogurt da bready ba, ai kune kuka cinye mana sauran abincinmu a kitchen, wlh idan baku je kun girma min abunda nakeso ba zan kira yaya Omar awaya in fada mashi kun ci mana abincin mu"
Aruɗe suka hada baki suna fadin"Me yai zafi, Kinji munce bazamu girka maki ba ne?


Nuna masu hanyar kitchen tayi da hannunta"ku tashi ku shiga ku dafa min abinci"


Agajiye suka miƙe tayi gaba suka bi bayanta sune har cikin kitchen.


Ƴan uwan dake a falo, saman sofa suka zauna, su kansu ba zasu Iya da rigimar khadeeja ba, Sara ce ta ɗauko masu Robobin madara, Ta miƙa ma kowan nan su, suka zauna suna sha
Daga falo suna jiyo sautin muryar khadeeja dake acikin kitchen.


"wainar kwai zaku soya min" ta fada tare da buɗe kofar store ta dauko masu egg container ta kawo masu shi akan Countertop ta daura shi.


Cikin kwantar da murya Tiger yace"khadeeja wannan kwan yayi maki yawa ina laifin a soya maki biyar" harara ta galla mashi"ai bani kadai zanci ba, hada Ƴan uwana suma suna jin yunwar" roba ta ɗauko masu inda zasu kaɗa kwan hada abun kaɗawar,
Kafin ta nufi freezer tana fadin"hada Chicken pepper soup zaku yi mana, Sannan Ku soya mana kifi mubeen yana son ci" Bin ta da kallo su ka yi baku nan su a buɗe kamar sakarkaru haka suka bi ta da kallo.


Kaji ta ɗauko Guda Uku Manya manya masu tsokoki ajikinsu ta ajiye masu


Tace"chicken peper soup zakuyi mana, akwai kayan miya da kayan ƙamshi duk zan ɗauko maku su" hankalinta kwance takeyi masu magana, har wani ƙyafkyafta masu idanu takeyi.


Daƙyar tiger ya iya bude baki yace"Yar uwa khadeeja, bakomai muka Iya girkawa ba, Kuma wannan abincin yayi yawa, ga kwai ga kuma kaji"?


Zum6ura mashi baki tayi"wanda yasa kuka cinye mana abincin mu na jiya," ta faɗa tare da juya masu baya ta nufi cikin store, gabansu har faɗuwa yake yi, Jim kaɗan ta dawo hannunta ruƙe da Manya manyan doyoyi guda uku ta ajiye masu aƙasa tana faman yin nishi tace"idan kun gama girka wadannan saiku fere doyar ku soya mana ita da kwai" Baki abuɗe suke sauraronta
Komawa cikin store tayi sai gata ta kuma dawowa hannunta ɗauke da ƙaramar roba, dankalin turawane acikinta
"Chips zaku soya mana da shi" ta ajiye robar, har ta juya zata koma Army boy yayi saurin shan gabanta, Muryarshi a tausashe Yace"khadeeja, Ya isa haka, wai ke meke damunki? Mu fa mazane ba mata ba, bamu Iya girki ba, Bindigogi muka Iya ruƙewa, taya zaki kwaso wannan uban kayan abincin kice mu girka maki"?


Fashe mashi tayi da kuka tana bubbuga ƙafa tace"wallahi idan baku girka ba saina fada ma Yaya omar kun cinye mana abinci, Kuma In ƙala maku sharrin kun ta6ani" Waro ido waje su kayi har saida gabansu Ya fadi jin abunda tace, Ita kanta da tayi maganar bada wata manufa ta furta ta ba.


Lallashinta suka soma yi"shikenan, Munji zamu girka maki, Yanzu ki koma falo ki zauna, ashagwa6e tace toh, kuma zan dinga leƙowa ina duba ku" amsa mata sukayi da toh
Bayan fitarta daga kitchen din tiger yace"Allahumma ajirni filmusibati wa aklikni khairan min ha, Yarinyar nan ba ƙaramar makira bace"
Army boy yace'ai duk laifinka ne, kaine jiya kasa na kwaso masu abincinsu da duk hakan bata faru ba, yanzu gashi ta daura mana wannan uban aikin"


"Idan laifina ne kaima hada laifinka ai, tunda atare muka cinye masu abincinsu"


Ran kowan nan su Ya 6aci, tamakar zasu rufe juna da bugu


"Faɗa ku ke yi ko"? Muryar Khadeeja ce ta fargar dasu, arude suka hada baki wurin fadin"A'a aunty, Muna yanke shawarane akan meya kamata mu fara girkawa"


Murmushi ta saki har dimple dinta Ya lotsa, Hannunta ɗaya ruƙe da Robar milk da take sha.


"Idan ma faɗa ku ke yi ku kuka sani, Nidai ina jiran abinci, kuma wallahi Kafin In shanye madarar nan ku gama min girki na, idan ba haka ba hmmmm kunsan sauran" Ta fada tare da juyawa ta fuce daga kitchen din.


Army ya ɗaura hannayenshi biyu saman kanshi"mun shiga uku, wannan wata irin bakar rana ce"?


Tiger yace"Ba surutu Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Mu fara mata girkin kada ta shanye madarar"


Tu6e rigunansu sukayi, Ya rage saura wandunan kakinsu a jikinsu, sham sun manta da bindigogin su da suka ajiye afalo.


Kamar mata haka suka fara aikace aikace, wanke nama, Fere doya, Gyaran cefane, da yankan kayan lambu suna haɗa uban gumi zufa ta ko'ina, da waya sukeyin amfani wurin yin browsing yadda akeyin chicken paper soup da sauran abunda basu Iyaba, duk bayan ƴan mintuna sai khadeeja ta leƙo kitchen don taga idan suna yin aikin yadda ya kamata, bayin Allah kamar ba sojoji ba, ta takura masu ta addabi rayuwarsu


Yayin da take zaune a falo cikin ƴan uwanta, Hawwa tace"khaeeja baki kyauta masu ba, dan Allah Ki yafe masu aikin yayi masu yawa"
Gatsina mata hanci tayi batare da ta tanka mata ba
Sarah taja guntun tsoki tana kallonta tace"kinji haushin rayuwarki, kuma wallahi saina fada ma Yaya Jazz abunda kika yi masu"
Banza tayi dasu tamkar bata ji me suke fadi ba,
Yasmin tace"please ku daina yi mata magana, Itama bayin kanta bane, Lalurace Yaya jazz fa yace mu runka hakuri da yar uwarmu"
Hibba tace"duk da haka halintane, Deeja tafiye rashin jin magana, bata da haƙuri, saina fada ma Yaya salsabeel"
Duk wanda yayi magana saita kalli la66ansa
Robar yogurt din dake a hannunta ta ajiye kan carpet, Ta yunƙura ta miƙe tana yin miƙa, duk suka bita da ido, bindigar da ta gani sakon kujera takai hannu ta dauka ta saita su da ita tana fadin"wallahi dukan ku sai kun mutu, banzaye kawai, Har ni zaku dinga yi ma faɗa"


Dariya suka saki gaba ɗayan su, saboda basu san meye amfanin bindigar ba.


Hawwa tace"dalla malama Ajiyeta a ƙasa, Kada ki lalata masu abunsu"


Harara ta watsa mata tana faman cije la66a tace"ta kanki zan fara hawwa Jiya Hada kulleni adaki don kada In futo waje, yau idan na kashe ki bazaki sake Yi min haka ba
Tana ƙare maganar ta daddage ta ruƙe bindigar dakyau, Tana ƙoƙarin harbawa, Mubeen yayi saurin Janyo Hawwa gefe daya, ba zato ba tsammani harsashin bindigar Ya harbi jikin kujarar inda Hawwa take zaune, Wani irin Hayaƙi ya fita Wurin da bullet din ya shiga nan take ya fashe.(😳)


Nan fa ido Ya raina fata, Gaba ɗayansu sun rude sun gigice, Amatuƙar firgice suka mimmiƙe tsaye suna faman zare idanuwansu
Dariya tasaki tana fadin"kunyi tunanin bansan yadda akeyin amfani da ita ba ko? To ai na ta6a ganin video a wayar Ya omar, wasu suna kakkashe mugaye da ita, ɗaya bayan ɗaya kuma zan kashe ku yanzun nan" Ta faɗa Tana saita su da ita, fashewa sukayi da kuka suna yi mata magiya, saboda rashin hankali Ta kara sakin wani harsashin kaitsaye ya sauka a tsakankanin ƙafafuwan Rubina, Baiwar Allah Kuka hada majina, sauƙin ma bai ta6a fatar ta ba.


Maza suna a kitchen suna girki, sun bar psycho afalo tana aiki, duk irin girman sautin harbin bindiga basu ji ba, Mubeen Ne ya watso da gudu Ya shigo kitchen din ya ɗaga murya Yace"ga khadeeja can ta daukar maku abunku tana harbin mu" gabansu ne yayi wani irin mugun faduwa, aguje suka fito daga kitchen din adai dai lokaci ta saita kan Sarah jikinta sai kerma yakeyi


Tsawa Tiger Ya daka Mata, da sauri Ta juyo da bindigar ta saitasu tana dariya tace"Ajalin ku ne ya fito daku daga kitchen, dama haushinku nake ji, Jiya kunkashe min jazz dina"
Hankalinsu idan yai dubu toh Ya tashi, Khadeeja ta saka su a tsaka Mai wuya, Ga girki sun baro a kitchen Ga wani tashin hankalin dayafi gigitasu
Dole suka zube kan gwiwowinsu muryoyin su na rawa suke yi mata magiya"dan Allah Anty khadeeja ki rufa mana asiri, wlh bamu kashe maki jazz dinki ba, Yana nan da ranshi, yaji sauƙi raunin jikinshi ya warke, Ki taimaki rayuwarmu ki ajiye bindigarnan aƙasa....." tamkar zasu fashe da kuka haka suka dinga roƙonta, zuciyarta kamar ta kafuran farko babu alamun sassauci tace
"Nafa san me nake Yi, baku isa ku raina min wayau ba, Idan dagaske Ya jazz bai mutu ba toh Yana ina"?
Fuska amarairaice Army boy yace"Yana asibiti, likitoci suna duba lafiyarshi,"
Ƙasa ƙasa da murya Tiger yai mashi raɗa"kai dole fa mu nemi mafita wallahi, Idan ba haka ba zata Iya kashe mu ko ta kashe ƴan uwanta tun da ba hankali gareta ba, ga kuma Abinci mun bari kan gass"


Army boy yace"to ya zamuyi! Ni wallahi komai ya kwance min,"
"Gulmata kukeyi koh"? Ta fada tana jifarsu da harara
Atare suka girgiza mata kai alamar eh, tace"idan ma gulmata kukeyi daga yau Idan na kashe ku bazaku sake yi ba"
"Ku lallashi yar uwarku, zata Iya ja mana bala'e daga mu har ku" Tiger ne yayi maganar Yana kallonsu Hawwa.


Duk wanda yayi yunkurin buɗe baki zai bata haƙuri da bindiga take saita shi,
Kwatsam Wayar Tiger Ta soma Yin ringing, adabarbarce ya zura hannu ya zarota daga aljihun wandonshi, duk sun rude, ganin sunan Major ya bayyana ne yasa hankalinsu Ya ɗan kwanta,
Picking call din yayi tare da kara wayar akunne
Ko sallamar major bai amsa ba, Ya furta"Jazz Ya Jikin Naka"? On the other hand Muryar Major da alamun mamaki yace"Jazz Kuma? Baka ga sunan wanda Ya kira ka bane"?
Tiger bai kula maganarshi ba yaci gaba da fadin"Kamar ka sani tun safe khadeeja take son Yin magana dakai, Ai saida na fada mata baka mutu ba lafiyarka ƙalou amma taki jin maganata"
Tun da ya ambaci sunan Jazz khadeeja ta jefar da bindigar kan carpet, ta nufe shi tana fadin"Bani shi muyi magana" jiki na 6ari Army yayi saurin Miƙewa ya damƙi ƙeyarta yana fadin"bashi bane don ubanki, Har mu zakija ma bala'e, masifaffiya kawai, Kin bi kin ƙuntata rayuwurmu kin hanamu sakat, wlh baki isa ba, Aɗaki zan kulle ki," kuka tadinga yi mashi tana zagin shi, ɗaukarta yayi ya nufi saman bene da ita, Daki ya shigar da ita ya kwantar saman gado, Ya fito da sauri yaja ƙofar Ya datse ta da mukullin daya gani ajikin ƙofar, Ajiyar zuciya ya sauke kafin Ya nufi falon, A lokacin Tiger Ya kammala yin wayar da major, Ya miƙe dasauri Yaje ya dauki bindigar ya hada da ɗayar da suka ajiye kan sofa, duka biyun Ya turasu karkashin dining table
Kallon sauran yaran su ka yi"ku koma ku zauna Yanzu zamu kawo maku abincin"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login