Showing 21001 words to 24000 words out of 40625 words

Chapter 8 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

376

yi nisa, fitilun masarautar suna kyalli tamkar taurari, amma a cikin ɗaki mai ɗauke da ƙanshin turaren wuta, Hajiya Binta ta naɗe jikinta da farin lulluɓi tana barci. Sai dai barcin ya koma azaba.


A mafarkin da take ciki, ta ga yaro mai shekara kusan goma sha biyar hannunsa rike da makami mai zafi, yana ta ƙoƙarin shanƙo ta da shi. Idonsa jajir kamar wuta, muryarsa ta daki kunnenta “Zan dawo! zuciyar ki za ta tsage da azabar gaskiya!”
tayi ƙoƙarin gudu cikin mafarki, amma ƙafafunta sun makale a cikin ƙasa mai jini. Gidan sarauta ya koma wuta, kuma daga saman wutar ta hango fuskar mace da aka taɓa sani…


Hajiya Hafsah.
Wacce ta kasance tsohuwar kishiyarta, wadda aka zarge ta da ɗauke ciki namiji shekaru da suka shuɗe, amma aka kashe ta da makirci don kar ta haifi ɗan gado. Fuskar Hafsah ta bayyana cikin hayaki tana dariya mai ban tsoro, ta na kallon Binta da ido biyu masu cin rai “Binta! kin yi zalunci! Kin ɗauke rayuwata, amma ba zaki iya hana zuriyata dawowa ba. Jinin jaririn da aka kashe zai dawo ne da ƙarfin sarauta!”






Cikin tsananin tsoro, Hajiya Binta ta yi ihu — sai ta farke da gumi ya jika lulluɓinta. Numfashinta ya yi nauyi kamar wanda aka tsere da shi. Ta ɗaga kanta sama tana hawaye, zuciyarta cike da rawar jiki anan take, ta hango cikin ɗakinta Hajiya Maryam, wacce ta shigo da sauri da riga mai duhu. Fuskar Maryam ta sha bamban: daɗin rai da makirci suka gauraye, idanunta sun yi ƙyalli.
“Lafiya, Hajiya? Kin yi ihu kamar wacce aka kunna da wuta.”


Hajiya Binta ta farka daga mummunar mafarki da ta ƙona mata zuciya. Numfashinta na fita da sauri, zufa na zuba kamar an tsoma ta cikin ruwan zafi, ta kasa ɓoye firgicinta “na ga Hafsah…! na ga jinin da muka ɓoye yana dawowa! wataƙila cikin nan nata zai kawo abin da zai ruɗe mu…”
Maryam ta yi dariya mai taurin zuciya, ta matsa kusa da ita tana shafo fuskarta da yatsa: “Ke dai ki daina damuwa mun riga mun mallaki sarauta. Duk wanda ya tsaya mana a gaba, sai mu sarrafa shi da dabararmu.”
Hajiya Binta ta girgiza kai, hawaye na sauka:
“Amma mafarkin nan ba alheri ba ne, Maryam Ina jin kamar masarautar nan za ta shiga bala’i.”
Maryam ta kaɗa hannu da izza, ta miƙe tsaye:
“Bala’i kuwa sai dai idan mu ne muka ƙirƙira shi, kuma mu ke tafiyar da shi. Ki kwanta ki huta, Binta. Rana ta gabbas ke fitowa ba kuɗi ba kuma yauwa ce ta gari ba ta bari kishiya ta ɗauki matsayi.”






Ta fice daga ɗakin da ƙafar ta ta buga ƙasa tamkar aljana. Hajiya Binta ta ci gaba da kuka cikin zuciyarta, tana rike cikinta da hannaye biyu awaje kuwa, iska ta taso daga gefen masarauta, tsuntsaye suka tashi sama suna yi kamar ƙararrawa. Wani fari na wata ya kakkarya cikin duhu, ya haska bangon fada.


Sai wata murya daga zuciyar dare ta faɗo cikin kunnenta:
“Wanda aka kashe ba ya mutu… Jinin gaskiya zai taso daga ƙasa kamar Kaɗangare.”


*******************


Gidan Sarautar Zazzau Alqamar 🌙👑


Masarautar da aka kafa tun ƙarni na da, tana alfahari da tambarinta na “Zanen Wutar Alqamar” – wato wata cike da walƙiya da wuta a jikinsa, wanda ke nuna cewa hasken su ba ya gushewa ko da aka rufe rana. Wannan tambari ana ƙulla shi a kirjin duk wani ɗan sarauta, musamman maza da ake kallo a matsayin garkuwa.


A wannan masarauta aka haifi Prince Idris, wanda aka fi kira Idrisul Kawthar, mai ɗimbin kwarjini a idon jama’a. Shi kaɗai ne ɗa namiji da ya rage a gidan sarautar bayan shekaru na asara da makircin mata da kishiyoyi. A idanun duniya, shi ne madubin masarauta.


Wannan tunanin ya fi mata duka wani bala’i. Cikin firgici ta kira mai gadin ɗaki:
"Ku kira min Idris! Prince Idris yanzu-yanzu ya zo wurina!" cewar Hajiya Binta .
Shigowar Prince Idris


Sai ga shi ya shigo da ƙamshi da ƙarsashi. Dogo, kyakkyawa, farin kaya ya lullube shi, tambarin Wutar Alqamar na kyalli a ƙirjinsa.
Ya kalli mahaifiyarsa cikin damuwa:
"Ummah, me ya same ki haka? kin kira ni cikin tashin hankali…"


Hajiya Binta ta yi shiru tana huci, daga bisani ta ce da rawar murya:
"Idris, al’amura sun fara dawowa garemu. Na hango Hafsah, wacce muka binne tare da asirinmu. Tana dawowa cikin mafarkina, tana riƙe da ɗa namiji! Wannan alama ce cewa zaluncin baya zai dawo ya tarwatsa masarautar mu… Idris! Kai kaɗai ne hasken da ya rage a wannan gida. Kada ka bari wuta ta cinye mu."





Idris ya yi dariya mai ƙanƙanar sanyi, fuskar sa ta kwantar da murya kamar wanda yă san ransa babu matuƙar damuwa. Ya ɗaga hannu ya gyara rawanin ajalin da ke ƙirjinsa — tambarin Wutar Alqamar ya walƙace ƙasa da rana.


“Mom,” ya ce cikin sassanyar muryar da ba ta da tausayi, “mafarki ƙarya ne, mafarki ya kan rarrashi zuciya. Kina ƙoƙarin hana mini natsuwa. Ki kwantar da hankalinki — ba za mu sake barin waɗansu su kawo mana matsala ba. Ki faɗa mini, wacece Hafsah game da mu? Ashe kin yi bacci da tunanin haɗari ne?”


Ya matsa gabansa ya yi murmushi mai ɗaci. “Ki tuna dai, yayin da muke zaune cikin ƙarfi, mun shirya komai.” Ya sauke murya zuwa ƙasa kamar maganar asiri. “Mun kai ta kogi a dajin nan, an harbe ta sau biyu — ban manta ba. Mun buɗe ƙofa ga barazanar gado, amma mun rufe ta da ƙarfi. Ba wanda zai iya tayar da ita yanzu.”


Hajiya Binta ta fasa numfashi, kyallin mafarkin ya riƙe mata tunani. Idanunta sun cika da damuwa, amma da fargaba ta gaɗa baki ta yi ƙoƙarin ƙara haske a murya. “Idris… Allah ya sa mu yi gaskiya. Wannan mafarki… ya na nuna mana wani abu — kamar faɗakarwa. Ka ji muryar ta ce ‘jinin da aka kashe zai dawo’… Me idan akwai gaskiya a cikin wannan mafarki?”


Idris ya matso kai ya kusance ta da sauri, idonsa sun yi ƙyalli. “Mom, ki ɗauki hankali. Ba mu da lokaci na hira da jarabar mafarki. Mun riga mun yi abin da ya dace. Duniya za ta zauna, kuma mu za mu ci gaba. Ki rufe bakinki ki huta — zan tsara komai.”


Sai ya juya ya nufi ƙofar zaure, ƙafar sa ta doke ƙasa da sautin hukunci. Amma kafin ya fita, ya juya ya ƙara faɗa:
“Ki sani, idan har wani yaro zai fito daga cikin ikilisiyar da kuka ɓoye, to zan yi masa abinda ya dace domin kare madafun iko na. Wannan gida ba fili bane na tausayi.”


Hajiya Binta ta zauna gaba ɗaya cikin tsananin firgici, zuciyarta na bhaƙa. A waje, iska ta yi ƙarfi, tsuntsaye sun yi kauri, kuma wani ƙaho mai nisa ya bushe kamar sanarwar wani abu mai zuwa.
— Zarah, ungozoma — na tsaye a bakin ƙofa, idonta na rikitattu. Ta kalle su da idanun da suka san sirri da yawa, sai ta motsa jikinta ta yi shiru. A zuciyarta ta san cewa mafarkin Hajiya Binta ba zai zama abin banza ba — akwai wata ƙasa ta gaskiya da za ta so ta rufe.


Kai a kai labarin ya tsaya, murya na ƙasa ta faɗi cikin duhu:
“Wutar Alqamar ba ta faɗi fage da sauƙi. Wani abu mai tsarki zai fito daga cikin ruwan da kuka ɓoye…”


*********
SUHAYL – Kaɗangaren Tsibiri
Bayan wani lokaci mai tsawo da Suhayl ya ɗauka yana tafiya ta gabashi ba tare da guzuri ko tsoro ba ya kwana a daji yaci ganye yayi sutura da ganye da ya samu, a chan ƙifin hanyar bishiyoyi da ya dosa nan ya fara jin hayaniya ta mutane da dabbobi da bai saba jin su ba , cikin hanzarin ya ƙara kaimi burin sa bai wuce samun abinci ba , yana isowa bai ankara ba yana ganin wasu halittu na mutane da sutura ta jikin su..



Da zarar ƙauyen suka taru a kansa, idanunsu suka fara yawo a jikin Suhayl. Ba rigar mutane yake sanye da ita ba, sai sunaye da ganyaye da ya zagaye jikinsa, tamkar wani ɗan tsibirin almara.
Nan da nan yara suka fara tsokana da ihu:
“Wayyo, ga ɗan tsibiri! Ga mai ganye , "Sauran manya kuma suka tsaya suna yi masa sambatu, wasu dariya, wasu kuma tamkar suna jin tsoro. Suhayl kuwa sai zuciyarsa ta buga da ƙarfi, tsoro ya kama shi, jikinsa ya fara rawa. Wannan shi ne karo na farko da ya hango irin wannan taro na mutane, kuma bai san ko da gaske su ’yan adam ne ba.


Amma kafin ya iya cewa komai, gawata kyakkyawar yarinya ta bayyana daga gefe. Fuskar ta cike da walwala, kyawunta ya tsaya tamkar hasken alfijir. Ta yi dariya mai taushi, ta rufe shi da mayafin da ke jikinta don ya daina jin kunya.


Yaran suka yi shiru suna kallon ikon Allah. Ita kuma cikin nutsuwa ta ce:


“Suna na NOOR… kai fa?”


What the F****k


Mujeeee zuwa










*****


BASHIR
Motar na gudu kamar za ta tashi sama, ƙurar hanya ta mamaye musu baya. Sagir ya riƙe hannun Bashir da jini ke fita ba ƙaƙautawa, yana toshe gurin da ya fi zubarwa da riga. Muhsin kuwa ya riƙe sitiyari da duk ƙarfin zuciyarsa, yana tsalle da hanzari a kan ramuka da gangaren hanya.


“Ka tsare shi kada ya mutu min, Sagir! Kada ka bari ya mutu kafin mu kai Kaduna!” Muhsin ya huro, idonsa na zubar da hawaye amma yana ƙoƙarin boyewa.


“Wallahi jinin nan ya fi ƙarfin rigata! Ya zuba sosai!” Sagir ya yi ihu, yana tura riga a wurin raunin. Idonsa ya koma ja, zuciyarsa na bugawa kamar ana dukan ganga.


Motar ta nufi Kaduna cikin saurin da babu tunani, ƙarar horn na ta fasa iska. Har suka shiga cikin birnin Kaduna, mutane suna kallonsu cikin mamaki.


Da suka ƙaraso bakin wani asibiti mai taken “Garkuwa Specialist Hospital Kaduna”, Muhsin ya yi tsayawar gaggawa har tayoyi suka yi ƙara. Nan take ya fito da gudu tare da Sagir suka ɗaga Bashir da aka kusa tsinke masa rai.


“Help! Help! Doctor! Yana mutuwa ne! Please ku taimaka min!” Muhsin ya fasa ihu da harshen Turanci da Hausa a haɗe.


Cikin hanzari ma’aikatan asibiti suka fito da gadon turawa. Suka kwashe Bashir, jini na riga musu hannaye da kaya. Nurse ɗaya ta danna wayar gaggawa tana kira “Emergency theatre! Prepare for surgery! yaron nan zai mutu idan aka bari haka!”


Sai suka zuba gudu da shi zuwa ɗakin tiyata. Likitoci biyu suka shigo da sauri cikin farin kaya, ɗaya daga cikinsu ya yi magana da ƙarfi:


“Ku cire masa kaya nan take! Ku danna drip ɗin gaggawa, ku kawo oxygen!”
Sagir ya tsaya a bakin ƙofa, zuciyarsa na tsalle-tsalle, jikinsa na rawa. Muhsin ya rungume kansa da hannu biyu yana maimaita:
“Ya Allah, ka tsare shi… kada ya mutu a hannuna… Allah ka ba shi rai…”


Cikin mintuna aka fara ƙarar kayan tiyata — scissors, scalpel, clamps — an rufe ƙofar operation room. Nurse ɗin ta tsaya a bakin ƙofa ta ce musu:


“Ku jira a waje. Ko da nawa ne, sai an yi masa treatment. Amma ku sani… rayuwarsa tana hannun Allah yanzu.”


Sagir ya ji jikinsa ya saki, ya durƙusa ƙasa da hawaye. Muhsin kuwa ya jingina da bango yana kallon ƙofar da aka rufe, zuciyarsa cike da tashin hankali.


Sai suka fara kiran sunan Allah a bakunan su duka biyu, saboda rayuwar Bashir yanzu ta rataya a tsakanin numfashi guda da mutuwa.




Labari na tafiya


Something big is ........ g


Narnah ƙanwar soja ✍️ ✍️ ✍️






🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t


GARGAƊI


Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba ,
********

بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️



PAGE 18 / 19
08101235739



Bishiyar Ƙauyen Rimi


Suhayl ya zauna a ƙasan bishiyar, idonsa na kallon ƙasan ƙasa tamkar yana jin tsoron kallon fuskarta. Amma sautin muryarta ya tsinke shi tamkar iska mai sanyi da ta ratsa zuciya.


“Noor… sunan ki Noor? Kin ce a nan aka haife ki, Mallam Sambo shine mahaifinki, Allah ya mai rahma…” sai ta kalle shi a hankali, tana ɗan murmushi da ƙarfin hali:
“Eh, haka ne. Amma kai fa? waye kai da baka da kamanni irin namu? kamar baka saba ganin bil’adama ba me sunanka?”


Shiru ya biyo baya. Kukan tsuntsaye ne kawai ke cika sararin bishiyar. Suhayl ya ɗaga kai a hankali, idanunsa manya suna ɗauke da wani irin sirri.


“Ni… suna na Suhayl ban taɓa sanin gida ba, ban san uban da ya haife ni ba, ban san uwa ba. na taso ne a cikin daji, da namun daji, da ruwa. Tsohuwa ce ta rene ni, ita ce ta rasu ta barni da wannan zoben…”
Ya zaro zoben daga hannun sa ya nuna mata yana rawar hannu.
“Ta ce idan nabi zoben zai kai ne ga makomata.” Noor ta kalle shi da mamaki, zuciyarta ta buga. Kamar ba a duniya yake ba. Ta sauke ajiyar zuciya tana ɗan girgiza kai.
“Subhanallah… toh, Suhayl, wannan ƙauye ne. A nan mutane suke rayuwa, wasu da wahala, wasu da farin ciki. Idan ka yarda, zan nuna maka hanyar gida. Amma ina tsoron yayana idan ya dawo daga gona, saboda shi ba ya son baƙi.”
Suhayl ya runtse idanu, yana jin muryarta kamar wacce ta kira shi tun shekaru masu yawa. Ya ɗaga kai ya ce a hankali:
“Noor… zan iya zama kusa dake? Ko da a ƙarƙashin bishiyar nan kawai…”


-


Suhail da Noor suka ci gaba da tafiya a cikin hanyar ƙauyen, cike da nutsuwa. Hira suke yi tana ta ba shi labarin soyayyarta da Bashir, irin alƙawarin da suka sha yi lokacin ƙuruciyarsu. Muryarta ta yi rauni, tana haɗa dariya da hawaye.
Sai Suhail ya kalleta cikin mamaki ya ce: “Mene ne soyayya, Noor? na ji ki kina ta maganarta kamar wani abu ne mai ƙarfi.”


Noor ta tsaya cak, ta dubeshi da ido cikin rashin tsoro, ta fashe da dariya tana girgiza kanta.


“Kai fa ba ka san komai ba! ashe ba ka taɓa ji ba? Soyayya ita ce abin da ke sa mutum ya yi dariya da hawaye lokaci guda, itacce mai sa kamanta da mugun hali ,ko wulakanci tsakanin ka da abin sonka , ittace garkuwa zuciya mai sanya tsinkewar zuciya a bazara da da damina da rani , ittace Allah ya fasa a zuciyoyyin mutum biyu , ita soyayya gaskiya ce mai yinta baya mantatta ko daɗin ta ko azabar ta , Ita ce abin da ya haɗa ni da Bashir har yanzu, ko da ya barni, har yanzu ina jin shi a zuciyata. Amma kai sai ka ce jaririn da bai taɓa dandana rayuwa ba.”


Suhail ya yi murmushi ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce:


“To idan haka ne, za ki koya min? ko kuwa sai dai ki ci gaba da dariya?”Noor ta sake dariya, ta share hawayen da ke gefen idanunta.


“Kai kaɗai ne ka san yadda zaka koya wa kanka. Ni fa yanzu kawai bari mu tafi gida, Yaya ya hana ni yin yawo nesa da gida.”


Ta juya cikin ɗan tsoro da fargaba, zuciyarta tana harbawa saboda ta manta kanta har ta tsaya da shi a ƙarƙashin bishiyar da suke zama. Suhail ya yi mata rakiya yana jin daɗin yadda hirar ta ɗebe masa kewa, shi ma yana jin kamar ya shiga wani sabon yanayi da bai saba da shi ba.


Sannu a hankali suka nufi gidan Noor, tana ɗan dubansa lokaci zuwa lokaci da mamakin wannan sabon bawan Allah da ya shiga rayuwarta a ba zata.




Suka iso harabar gidan Noor, da sallama ta shigar da shi. Amma kafin su zauna, yayan Noor ya fito daga cikin gida, ya tsaya yana kallon Suhail da mugun ido.


“Noor, wa ya kawo wannan ɗan dajin nan gida? Ba zan lamunci zaman sa a cikin gidana ba.”Noor ta yi shiru, zuciyarta na bugawa da sauri. Ta kalli Suhail, sai ta dubi yayanta cikin tausasawa ta ce:
“Yaya, don Allah ka sassauta. Ni ne na kawo shi saboda tausayi. Ka duba fa, mutum ne mai kamanni, bai cancanci a ce a kore shi kamar dabba ba.”Yayan ya girgiza kai, ya ce:


“Kin ga irin kamanninsa? gashi da ba a aske ba, mutane ma suna gudunsa. Kina so ace an haɗa ki da irin wannan?”
Noor ta yi murmushi mai cike da tausayawa, ta nuna masa gashin jikinsa mai yawa:


“Wallahi Yaya, gashin jikinsa kaɗai ya isa mutane su yi tunanin ko mahaukaci ne ya fito. Amma idan aka kula da shi, aka tsaftace shi, za ka ga asalin kyakkyawan saurayin da ke cikinsa.”Sannan ta dubi Suhail da idanu masu nuna tausayawa:


“Ka bari nan gaba kadan zan samo maka abin aski. Lokacin nan sai na cire maka wannan gashi, ka ga yadda mutane ba za su ƙara gudunka ba.”
Daga nan, ta juya cikin sauri, ta shige gida, zuciyarta na tsalle-tsalle da mamaki da kuma wani irin nauyin tausayi da ta ɗauka akansa.


Suhail kuwa ya tsaya a bakin ƙofar gida, ya rasa ko ya shiga ya tsaya ko ya koma, amma abin da ya tabbata shi ne kalmomin Noor sun ratsa zuciyarsa fiye da yadda ya taɓa zato.




Bayan kwana biyu, labari ya bazu kamar wutar daji a cikin ƙauyen Rimi. Kowa ya san cewa wani ɗan daji mai suna Suhayl ya bayyana, kuma ana ta danganta shi da kyakkyawar yarinya Noor.Matan gari suka fara gulma:


“Ai ku ji abinda ke faruwa! Noor ta samu sabon saurayi, shi ya sa take taƙi amincewa da kowa a ƙauyen nan. Tana cewa wai tana jiran Bashir, ashe ƙarya ne.”Wani dattijo ya ce da raini:


“Haba! To ba don ta haɗu da wannan ɗan dajin mai kama da mutum ba ne sai yanzu take dariyar aure? Ashe alkawarin ta da Bashir babu gaskiya.”


Wasu kuma suka ɗora da munafurci:


“Kunga kuwa? Ai idan aka ce mace ta yi nisa da soyayya sai ta manta alkawarin da ta yi. To Noor ta manta Bashir saboda wannan sabon saurayi kyakkyawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login