Showing 9001 words to 12000 words out of 40625 words

Chapter 4 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

375


*Gaskiyar labari mai haɗa farin ciki, baƙin ciki, soyayya, tausayi, da haƙuri.*








7. *Ruhi Biyu*
*(Labarin da ya kasance a matsayin ban tsoro da fargabar ruhi ?)*










8. * Hanyar Ruwa*


( Fyaɗe da cin zarafin yara mata )








9* Ahlin Laashkar*


(, Hargitsin sarauta da jarumta na yara mata ).








10* Princess Rahilat *


( Adventure story da ya shiga gidan masarautar na gargajiya salon mulki da bajinta ).





11* MAI CIKI CE ,*


( Nishaɗi salo na musamman ma masoya tare da rikicin masu rikicin)








12* Zaɓin zuciya*


( Soyayya, tausayi , mai karya zuciya ).







13 * Madobin ido *


( Just romance and drama , ga masu lesbian da kwaɗayin duniya).



14* KAƊANGAREN BAKIN TULU*


( Labari na musamman wanda aka fara shi yanzu ).



08101235739


NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️














🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t


بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️



PAGE 8


300 only


08101235739









KANO (ƘAUYEN RIMI)


BAYAN WANI LOKACI


...Suratul Mulk...


Bashir na durƙushe gefen rijiya, hannunsa cikin ruwa, yana wanke kayayyaki. Muryarsa ta mamaye sararin ƙauyen, yana maimaita ayoyin Suratul Mulk da nutsuwa irin wadda take saka zuciya ta lafa. A hankali kukan saƙa ya shiga cikin karatun—ba kuka na rauni ba, kuka ne na wanda ya haɗiye damuwa da fata ɗaya: samun rahamar Ubangiji.


Kamar wanda aka ɗora masa nauyin duniya, bai ma ji motsin da ke bayan sa ba har sai da wata murya mai cike da ƙiyayya ta katse shi:


> “Wai kai! Wani irin mahaukacin yaro ne? Wawa ɗan iska! Mu za ka ishe mu da shegen muryarka? Ina bacci kana damuna da karatu? Wa zaka gaya wa cewa kai mai karatu ne?”






Ba tare da ta tsaya ba, sai ta bugo shi da dundun a baya. Bashir ya saba da duka tun yana ƙarami—mai zafi da mara zafi—don haka ya ce cikin ladabi:
“Yi haƙuri, Baaba. Ban sani ba kina bacci.”






Bai ɗaga kansa ba, ya ci gaba da karatu a hankali. Amma sai warash!—sandarta ta sauka a bayansa.
“Don uwarka na hakanaka karatun ne zaka yi?!”






Zafin ya ratsa jikinsa ya kai har kwakwalwarsa. A wannan lokacin ya ɗago, idanuwansa jajjir, amma kyawunsu ya fi duka fuskar sa. Idanunsa farare, tamkar an hura haske a cikinsu, sai ƙasan idanun da yake baƙi kamar an zana masa kwalliya da ƙyalli.
Baaba ta ce da tsaki “Shegen idonka nan da kake kallo na dashi... wata rana sai na zubar maka dasu.”






Bashir ya yi murmushi kaɗan—murmushin da ke da ɗan ɗaci. Duk da rashin ƙiba, yana da wani ƙefin da baya iya ɓoye. Abin mamaki, duk lokacin da Baaba ta kalli idanunsa, sai ta kawar da nata cikin hanzari, kamar tana gudun wani abu da take ji a zuciya.
“Allah, ka ba ni mafita,” Bashir ya furta a ransa, yana ɗaure kayan mata da yake wankewa.






A nan ne Inna Uwaliya ta fito daga ɗaki, tana tura baki, duk haƙoranta sun zube. Tana riƙe da sanda a hannunta tana mai magana da muryar da take cike da hukunci: “Bashir! Bashir!! Bashir!!!”Da sauri ya amsa, cikin ladabi “Na’am, Inna, gani nan zuwa.”
yana rarrafe ya durƙusa a gabanta “Gani, Inna. Kina da wani aiki ne?” kamar wanda ke tsoron kallonta, ya tsaya shiru yana sauraren abin da zata ce a dai dai lokacin da ya gama tambayarta,
"Ko kina da wani aiki ne da zan yi miki?"


Ta kalle shi da wani irin murmushi mara annuri, sannan ta ce:
"Ka tafi bakin rafi ka gama wankinka. Kuma daga yau na sa maka doka — kar ka ƙara mana wanki a gida duk abin da ka ke yi, ka yi shi a bakin rafi."


Kalmomin sun zame masa ƙamshi mai ɗaci. bai iya cewa uffan ba, ya kama hanyar fita sai hawaye suka fara taruwa a idanunsa, zuciyarsa na cike da wani nauyi da shi kaɗai ya san yawan sa.
Maganganunta sun buga masa zuciya kamar wuka. Kafin ya samu damar cewa komai, ta juya ta bar shi, ta bar masa ƙura da ƙuncin rai.


Ya tattara rigunan da ya gama wanke, ya ajiye a gefe, ya kama hanyar bakin rafi. Kowane mataki da yake ɗauka yana jin zuciyarsa na nauyi.
Ya kwashe kayan kafarsa, ya ɗora a kafaɗa. Hanya mai nisa, mai sanyi amma a gare shi ta zama hanyar azaba. Yana tafiya yana sheshsheƙar kuka, yana maimaita a ransa:
"Wai Mama na... me yasa kika mutu kika bar ni? ne yasa kika tafi kika bar ni cikin wannan duniya babu wanda zai rufa min asiri?"


A cikin wannan tafiya, kowace ƙafa da ya ɗaga kamar ta ɗauke wani ɓangare na ƙarfinsa, amma zuciyarsa tana ƙara nutsewa cikin wani daki mai duhu — dakin rashin uwa.










Hawayen ba su jira ya isa wurin rafi ba — suka gangaro daga idanunsa cikin sauƙi, suka haɗu da ƙura a fuskarsa ya zauna a bakin rafi, yana jin ƙarar ruwan da yake gudu tamkar yana yi masa waƙar baƙin ciki.


Sai ya furta cikin murya mai rauni, wadda da kyar za a ji:
"Wai Mama na… me yasa kika mutu kika bar ni? Waye yanzu zai rike ni kamar yadda zaki rigi ne ?Waye zai yi min dariya idan nayi kuskure? Mama… yaushe zan sake ganinki?"






Kamar wani yaro ƙanana da aka tsinci a cikin duniyar da babu tausayawa, ya runtse idonsa yana jin sanyi na ruwan rafi a hannunsa, amma zafin rashi a zuciyarsa ya fi kowanne sanyi ƙonewa.




A haka ya ci gaba da tafiya, zuciyarsa cike da raɗaɗin zafin rashin uwa, hawaye na zubo masa kamar ruwan sama. Kamar dai duniyar gaba ɗaya ta ɗauke masa ƙauna ta maye gurbin ta da shiru da kunci.


Kwatsam, ba tare da ya lura ba, ƙafarsa ta bugu da wani abu — ashe ƙafar mutum ce! A cikin ɗan kankanin lokaci jikinsa ya yi sanyi, ƙafafunsa suka yi laushi kamar za su saki, ya fara faɗuwa ƙasa a hankali, “laauuuu…”


Kafin ya kai ƙasa, sai kawai ya ji an ɗan tsinke iska a bayan sa — wifff! — wata hannu ta kama rigarsa ta baya da ƙarfin da bai zata ba. Kamun ya tsaya masa tamkar an dasa shi a wurin, zuciyarsa na bugawa da sauri.


Ya tsaya cak, idonsa ya lumshe, zuciyarsa ta fara tunanin ko wannan shi ne farkon wani sabon labari… ko kuma wata sabuwar ƙaddara.


*****************************
ABUJA


Fitsari ne ya kuɓuce masa ba tare da ya ankara ba, sai ka ji zulllll yana zuba a ƙasa, yana ƙara tsananta kunya da raunin da ke cike da zuciyarsa. Kafin ya iya share hawayen da suka gangaro masa, wata jabbar bulala ta tsinke a bayansa, ta shigar masa da zafi mai tsanani har sai da ya yi wani irin tsalle ya sulale ƙasa kamar ruwan kankara da aka zuba wa wuta.


A can ƙasa yake kwance yana rawar zafi, hawaye suna cika idonsa, yana kallon sama da idanu masu taɓarɓarewa. Wannan yaron — kyakkyawan yaro ne, fari sol kamar hasken alfijir, fuska mai santsi wadda da ta dace ta kasance cikin farin ciki da kulawar uwa. amma yau, babu mai rungumar shi, babu mai share masa hawaye — sai duka da zagi da zafi.


Hawaye suka ci gaba da zuba kamar ruwan damina, zuciyarsa na amsa masa tambaya ɗaya: “Wai Mama na… me yasa kika mutu kika bar ni a cikin wannan rayuwa…?”
Fitsari ne ya kwance masa bai sani ba, sai zulllll… fitsari yana tsalle kwaɗo kamar ruwan sama daga bututun da ya fashe.
Kafin ya ankara, wani jabgiggin bulalla ta tsula masa a baya — ƙarar ta cika kunne, jininta ya cunkushe, ƙashin bayansa ya amsa.
A zabure ya runtse idanu, ya furzar da numfashi mai zafi, amma kafin ya sami damar tsayawa, gwiwowinsa suka yi rauni suka sulale ƙasa.


Rayyan kyakkyawan yaro ne fari sol, fuskarsa tana da ɗan zagaye da ke sa idanunsa su fito fili, manya kuma masu sheƙin ƙwalla.
Hawaye suka haɗu da zufa a kumatunsa, suna bin fuskarsa kamar zaren lu’ulu’u.
Bakin sa ya ɗan buɗe yana neman iska, amma muryarsa ta kulle cikin kirji, sai kawai jijiyoyin wuyansa suka fito saboda tsananin zafin bulallar da ta ratsa har ƙirjinsa.




BORNO


🌙 Suhyayl
A tsakiyar dajin Borno, a bakin wani babban kogi mai kaurin iska da hayaniyar tsuntsaye, can nesa daga birnin da jama’a ke cike, akwai wani ƙaramar tsibiri. Tsibiri ce da namun daji ke yawo, kuma baƙon dan adam idan ya shigo, sai ya fuskanci ko dai rahama ko hallaka.


A gefen wani dutse mai kaifi, yaro ne ke durƙushe — ba wanda ya isa ya ga fuskar sa ya manta da ita. Fatar jikinsa ta launin chocolate mai sheƙi, idanunsa manya, suna kaɗaɗe da hawaye amma yanayin fuskarsa ya nuna tamkar mai ɗauke da shekaru na wahala.


A gabansa tsohuwa ce ta kwanta tana shirin barin duniya, hannunta yana rawar sanyi. Sai ta ce da shi cikin muryar da take dushewa:


"Suhyayl... anan ne mahaifiyarka ta zo ta haife ka. Ka sani, yanzu zan bar ka, amma ka ɗauki wannan zobe... Zoben mahaifiyarka ne. Idan ka shiga birni, ka zama ɗan jarida mai gaskiya. Wannan ce wasiyyata… ka rayu da kalmar shahada."






Kafin ya iya cewa komai, numfashinta ya tsaya.


Suhyayl ya kalli gawar, hawaye na zubo masa tamkar ruwan sama. Ya rik'e hannunta yana girgiza shi:
"Waiyooo Mama na! Me yasa aka kashe ki, ban mutu ba? Ina zan tafi yanzu?"






Kukan ya ratsa dajin, ya sa tsuntsaye suka tashi. sai zuciyarsa ta lulluɓe da tausayin wannan ƙaramin yaro mai asalin gaskiya amma rayuwa ta fara gwada shi tun yana ɗan ƙarami.


Narnah ƙanwar soja ✍️✍️














🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t


بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️



PAGE 9
300 only


08101235739















KANO – ƘAUYEN RIMI


Bashir ya tsaya cak kamar mutum da aka zuba a cikin hoda. Idonsa ya rufe na ‘yan daƙiƙu, zuciyarsa ta buga da sauri kamar ta ji wani sabon saƙo daga sama. A zuciyarsa yana tambayar kansa, "Shin wannan ne farkon wani sabon labari? Ko wata sabuwar ƙaddara ce da zata canja rayuwata?"


Kafin ma ya gama wannan tunanin, sai ga Haule — yarinyar da kowa a ƙauyen ya sani da halin tsiya — ta tintsire da dariyar mugunta, tana riƙe ciki kamar mai jin daɗin cin nasara. “Kai! Allah ya kama ka,” ta furta da murya mai ɗauke da jin daɗi.


A gefensa, ƙawayen Haule suka zagaye shi kamar ‘yan kallo a wasa, suka zura masa ido suna jiran ganin abin da zai faru. Amma kafin su kai ga wani abu, sai Noor ta taso daga bayan su kamar iska, ta riƙe Hannun Bashir da ƙarfi tana janye shi baya, tana kare shi daga zagayen Haule.


Numfashi ya ja dogo, yana mai jin ƙamshin turaren wankan sabulu daga jikin Noor — abin da ya sa zuciyarsa ta buga karo na biyu.
Haule kuwa ta harare Noor, idonta cike da fushi da ƙyashi.
“Wai ke Noor, ina ruwanki? Ai wannan ɗan uwana ne, . Ki daina shishigi cikin lamarin gida, kin ji ko?”
Noor ta tsaya tana kallon Haule, ta na shiru amma idonta na nuna ba zata ja da baya ba.
Sai Haule ta ja zanin rigarta da ƙarfi kamar zata kama yaƙi. Amma kafin ta isa kusa, Bashir ya ja hannun Noor a hankali yana nuna mata ta yi shiru.


A zuciyar Haule kuwa, ba ta buƙatar jin wani hujja. Ta yi ƙaramar tsalle, ta koma cikin ƙawayenta tana ƙwala musu kira, “Ku tashi mu tafi! Wallahi sai na gaya wa Baaba yau. Zan faɗa masa duk abinda na gani. Sai yaga irin ‘yar banzar da kuke yi a hanya!”


Suka tafi suna gudu, suna shewa kamar ‘yan tsuntsu masu cin abinci, suna ɗaga ƙafafunsu da ƙura ke tashi.


Bashir ya tsaya yana kallon bayan su har suka ɓace a ƙofar rafi. Ya girgiza kai da ƙaramin murmushi mai ɗauke da takaici.




Noor kuwa ta turo baki kamar wacce aka ci amanarta. “Ai ka kyale ta ne kawai, ka san halinta fa? Gobe sai ta je ta ƙara daɗa labari har ta mayar ka ka ci amanar gidan ku.”


Bashir ya yi dariyar ƙasa-ƙasa, yana kallonta da ido mai cike da annuri. “To Noor, me kike so in yi? In yi mata dukan tsiya a gaban ƙauyen?”


Noor ta murɗa zanin rigarta tana hararar sa. “Eh, ai da ka yi mata raddi ne ko ka ja mata kunne. Ba ta da kyau ka bar ta ta raina ka haka don kawai tana ƙamwar ka kuma ɗiyar Baaba.”


“Kin dai san Haule,” ya ce yana ja da baya, “idan ka yi mata raddi, gobe sai ta kawo maka gaba ɗaya ƙungiyar ‘yan ƙauye.”


Noor ta yi dariyar ƙasa-ƙasa itama, tana jin wani abu mai daɗi a zuciyarta — domin da alama Bashir ya fi damuwa da haɗa kai da ita fiye da komai.


WANI LOKACIN
Bakin Rafin Ƙauyen Rimi


Iskar safiya tana kadawa a hankali, tana ɗauke da ƙamshin ruwan rafi da aka haɗa da wari na sabulun wanki. Rana ta fara hango ƙasa, ta haska ruwa mai sheƙi kamar gwal da aka jika.


Bashir yana tafiya a hankali, yana rike da ƙaramin bokitin kayan wanki, kafafunsa suna tsoma a ƙasa mai laushi. Idonsa ya yi nauyi da tunanin yau ma an ɗora masa aiki kamar kullum.


Sai kawai ya ji muryar Noor daga bayan sa, mai taushi kamar sanyi a zuciya.
“Ka tsaya ka jira ni mana.”


Ya waiwaya. Noor ce ke tahowa, tana riƙe da zanin jikinta da hannunta guda, ɗayan kuma ɗauke da ƙaramin kasko da aka cika da kayan wanki. A fuskarta akwai murmushin rarrashi, kamar ta san zuciyarsa na cike da kunci.


Bashir ya tsaya yana jiranta. Suna haduwa, sai ta ɗan yi masa dariya.
“Bashir, ka sake, ai wankan ba laifi bane. Idan kana tare da ni, sai ya zama kamar wasa.”


Ya kasa ɗaga ido sosai, amma a zuciyarsa ya san gaskiya take. Duk da cewa shekaru kaɗan gare shi, akwai wani irin natsuwa da yake samu idan Noor tana kusa da shi — kamar iska mai sanyi bayan ruwan sama.


Suka isa bakin rafi. Ruwa yana kadawa a hankali, yana tafka ƙaramin amo da ke haɗuwa da ƙarar tsuntsaye masu shela a kan bishiyoyin kusa. Noor ta zauna kan wani dutsen da ya yi fadi, ta saka hannayenta cikin ruwa, tana ji kamar tana wanke damuwar zuciyarta ma.


Ta fara zuba kayan cikin rafi, tana murza su a hankali. “Ka daina damuwa Bashir, wallahi rayuwa haka take. Amma kai fa zaka ga rana mai kyau a gaba. Kar ka bari Baaba ko su Haule da su Inaa da Baba su bata maka zuciya.”


Bashir ya zuba mata ido na dan lokaci, yana jin cewa kalamanta suna shiga shi fiye da yadda zata iya zato.


Noor " ina cikin bachi jiya bayan magana dukkan aikin da aka ɗauramin ina cikin bachi a tsakiyar dare Baba ya dawo gida ya hau kaina da dukka cewa tun da aka haifi ne rayuwar sa ta lallace ko kuma tunda ya haɗu da uwata da ƙyar maƙobta suka shigo da Mallam Sambo mahaifin ke sune suka ceto rayuwa ta duk sanda Baba yasha giya ya dawo gida sai ya zuba min rashin mutunci da zanyi hawaye ..





Matsowa kusa dashi taye ta dafa kafaɗar da saiga hawaye a idon ta ya cigaba da cewa " ba dukkan Baba nake tsoron ba bana don yana zagin mahaifiyata shin me Mama na taye meye lafinta haka zan chigaba da rayuwa ga aiki gida ga gona , ga duka ga zagi na fara gazawa Noor zuciya ta kamar zata buga duba fa ne fa satar hanya nakiye nake zuwa makaranta Allo da litattafai kuma duk sanadin ke ne , kicce mai rufamin asiri ta hanyar zuwa kina taya ne wahalar .... Dole na kasance cikin yanayi mara mesaltuwa .
“Haule fa… ko a mafarki sai ta tsokane n Amma ke… ke ce kaɗai kike sa in manta da komai, duk lokacin da muke tare sai in rasa dalilin ɓacin raina ”


Noor ta yi dariya ta ƙanƙance ido, tana ɗan zuba masa ruwa da hannunta. “To sai ka yi min alƙawari, idan na girma ka zama gwarzon da zan rika alfahari da shi.”


Ya yi murmushi mai sanyi, sannan ya ɗaga kai yana kallon ruwan da yake gudana kamar yana dauke da sakon wani nesa. “Na yi miki alƙawari.”


Iska ta busa ganyen bishiya sama da su, wani ya faɗo cikin rafi ya yi yawo. Wannan ƙaramin lokaci, duk wani bakin ciki ya ragu — domin a gaban Noor, Bashir ya samu kwanciyar hankali fiye da kowane wuri a duniya.






Bayan sun gama wankin kayayyakin da aka dibo daga rafin, Noor ta ɗaga leɓenta tana hura numfashi cikin gajiya.
"Wallahi Bashir, yau kam hannuna ya gama karyewa," ta ce tana zuba ƙaramar dariya.


Bashir ya ɗaga kai yana kallonta da murmushi mai cike da tsokana "ke ai ke da laifi. Idan kin rage gulma da surutu da tuni mun gama tun dazu," ya ce yana miƙe don ɗora bokitin ƙarshe a gefe.


Sun ɗaga kayan suka nufi inda suke shanya su kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login