Showing 27001 words to 30000 words out of 40625 words

Chapter 10 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

378

ya kara ɓatsarwa, wasu suka yi ihu, wasu suka yi dariya, yayin da zuciyar Ramcy ta karye ƙalubale.



ICU


Muhsin ya zauna a ƙasa, ya rufe kansa da hannu biyu, zuciyarsa cike da godiya da fargaba. Wani irin sanyi ne ke ratsa zuciyarsa kamar iska mai ɗauke da hawaye. A can nesa, ƙarar motoci da hayaniyar birni suna dawowa, amma a nan cikin ICU, shiru ya mamaye ko’ina shiru mai nauyi, wanda ke ɗauke da fatan rayuwa da ƙaunar wanda ake jiran ya buɗe idonsa lokaci ya ja, hasken rana ya ragu, har awa biyu suka shige kamar shekaru biyu. Sai kawai likita ya fito da sauri, idonsa cike da damuwa.
“Jininsa ya ƙare! muna buƙatar jini nan da nan irin jinin B-negative!”cikin ɗan rikici da firgici, kalmarsa ta bazu a zuciyar Muhsin da sauran dangi. B-negative! — irin jini da ba kasafai ake samu ba Saqir, wanda tun da farko ke tsaye a gefe, ya dafa kirjinsa da sauri “Dokta… gwada da Ni ne irin wannan jini nake da shi.”


An kalle shi da mamaki, likita ya ɗauki samfurin jinin nasa da gaggawa. Ɗan lokaci kaɗan ya shige, sai ya dawo da murmushi mai ɗauke da alamar ceto.
“Alhamdulillah… ya dace. Jinin Saqir ne daidai da nasa.”An kwantar da Saqir, suka haɗa layin jini zuwa jikin Bashir. Jinin ya fara gudana cikin natsuwa kamar tafkin bege.
Lokaci ya shude, ranaku bakwai suka wuce kamar mafarki. Ranar da rana ta farka da haske mai sanyi, Saqir da Muhsin suka zo cikin shiga mai kyau — riga da wando masu kamshi, fuskokinsu cike da murmushi da fatan alheri.


A bakin gadon da Bashir ke kwance, wata kyakkyawar mata ce zaune, idanunta a kumbure saboda kuka da rashin barci. A gefe kuma mijinta ya dafa kafaɗarta yana lallashinta da murmushi mai sa zuciya nutsuwa.


Shiru ya ratsa dakin. Na’urorin ICU suna ta ƙara da wani irin sauti mai sanyi.
Sai kuma… hankali ya karkata gaba ɗaya zuwa kan Bashir.


Ƙananan motsi ya bayyana a fuskarsa. Fuskarsa ta yi ɗan rawa, idanunsa suka motsa a hankali — sannan a hankali sosai, kamar wanda ya dawo daga duniyar mafarki, Bashir ya fara buɗe idonsa…


Ƙamshin magani da sanyin dakin ICU ne suka lullube dakin. Na’urori suna ta ƙara da sautukan su, kamar shaidar cewa rai da mutuwa suna ta jayayya a cikin wannan wuri.


Sai kawai Bashir ya motsa hannun sa ya ɗan yi rawa, idanunsa suka motsa a hankali kamar wanda ke son ya buɗe ko kuma yana gudun abin da zai gani.
Likita da ke tsaye ya matsa kusa, Saqir da Muhsin suka kame numfashi, zuciyoyinsu na bugawa da sauri a hankali… idonsa suka buɗe. Haske ya daki idanunsa, sai ya rintse su na ɗan lokaci kafin ya sake buɗewa gaba ɗaya.
Idanunsa suka hau yawo a hankali cikin dakin kallon mamaki, kallon tuhuma, da ɗan girgiza kai kamar wanda ke cikin mafarki.


Likita ya matsa kusa da gadon, yana kiran sunansa cikin sanyin murya:
“Bashir… Bashir, ka ji ni?”ya zuba masa ido, ba tare da ya motsa ba. Saqir da Muhsin suka matsa kusa, zuciyoyinsu suka yi nauyi.
Muhsin ya kama hannunsa cikin rawar murya:
“Bashir"
Bashir ya ɗago kai kadan, ya kalli su, sai ya furta cikin rauni da rawar murya:
“Ni… ni wa nake? Sunana waye?”
Kamar iska ta busa cikin dakin, kowa ya tsaya cak. Saqir ya kalli likitan da mamaki da tsoro suka gauraya a fuskarsa. Likita ya sauke numfashi mai nauyi, ya furzar da iska daga bakin sa yana girgiza kai.


“Na san hakan zata iya faruwa…” ya ce a hankali, yana duban su duka. “Ya bugu sosai a kansa lokacin hatsarin, jini ya zuba da yawa. Wannan ne yasa memory ɗinsa ta samu matsala. Ya manta da kowa, da komai — har da kansa.”
Dakin ya dauki shiru. Zuciyar Muhsin ta buga da ƙarfi, hawaye suka fara taruwa a idonsa.
Likita ya dafa kafaɗar saqir cikin tausayawa ya ƙara da cewa:


“Yanzu hakkin kulawa da shi ya rataya akan wuyanku. Zai iya zama kamar jariri, yana bukatar a koya masa komai daga farko. Ku shirya… tafiya ce mai tsawo.”


Sai ya juya ya fita a hankali, yana barin su cikin dakin da ya cika da shiru — shiru mai nauyin tambayoyi da hawaye.


Saqir ya zuba wa Bashir ido, ya kama hannunsa a hankali, zuciyarsa cike da raɗaɗi da alkawari a hankali ya furta cikin zuciyarsa:
“Ko ka manta da duniya Bashir, ni ba zan manta da kai cewa mune sillar shigar ka wanan yanayi na…”




BAYAN WANI LOKACI KAƊAN...


Shaquwa mai zurfi ta shiga tsakanin Noor da Suhail duk inda ka ga ɗaya, to ka tabbata ɗayan yana kusa. Suhail ya saba da kallon ta tana dariya, yadda take tura gashinta gefe ɗaya idan iska ta ɗauke shi, yadda take girmama shi da kulawa irin ta zuciya mai tausayawa.


A gefe guda Noor ta saba da kiran sa “Suhayl” cikin muryar da take fita da salo mai taushi, kamar kiran da yake ta da ƙauna daga wani ɓangaren zuciya da ba ta san yana akwai ba.


Idan suna aikin gona, Noor ce ke kai masa ruwa. Idan suna hutu, shi ne ke lallaba ta da faɗin,
“Ke dai kin zama kamar hasken safe ko rana bata fito sai na ganki.” zuciyarta kan buga, tana juyar da kai tana murmushi:
“Wannan magana taka ka bari, ba komai bane face wasa.”ya ce cikin murya mai natsuwa:
“Wani wasa ne da yake fito daga zuciyar da ba ta iya ɓoye gaskiya.”
haka shaquwar su ta zurfafa har ta kai ga Noor ta daina jin nauyin zama kusa da shi. duk inda suka je, sai a ce “su biyu nan sun zama kamar ruwa da kankara, ba su rabuwa.”


A ƙauye kuwa, magana ta zama abin ci da sha.
Wasu suna faɗa da murmushi, wasu kuma da haushi “wai Noor wacce ta taɓa yin rantsuwa da sunan Allah cewa zata jira Bashir… yanzu ga ta da sabon saurayi.”maganar ta yawaita har ta kai ga iyayenta, zuciyarsu ta yi nauyi da damuwa.
Amma Noor ba ta da ikon tsayar da abin da yake girma a zuciyarta — wani abu mai kama da tausayawa amma yana sauyawa zuwa so cikin sannu, cikin sirri, kamar yadda iska ke sauka a dare ba tare da sauti ba.


Wani dare tana zaune a bakin tagar ɗaki, tana kallon taurari. Sai ta furta da sanyi a cikin ranta:
“Bashir... ka bar ni cikin duhu da alƙawura. Amma wannan zuciya ta... tana neman wani haske ne daga inda ba ta zata ba.”hawayenta ya sauka a hankali, ta shafi kumatunta tana lumshe ido amma a zuciyar Suhail, soyayyar da ke ci kamar wuta ta gama cinye shirin komawa baya.


A wannan lokaci, kowa a ƙauye ya yarda Noor ta manta da amana, ta manta da Bashir.
Sai dai a zuciyarta, akwai sirrin da ita kaɗai ta sani — soyayya ce mai rikitarwa, tsakanin amanar da ta bari da zuciyar da ta fara jin wani sabon sauti.








* What will happened in the next…










✨🌟 KAƊANGAREN BAKIN TULU 💥✨
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)







GARGAƊI


Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba ,
********

PART TWO
PAGE 24/25








BAYAN WASU SHEKARU


Firgit ya farka daga nannauyan baccin da ya ɗauke shi kamar wanda aka nutsar cikin duhu numfashinsa ya yi nauyi, idonsa ya buɗe a hankali kamar wanda ke komawa duniya daga wani wuri mai nisa cikin muryar da ta rikice, sai ya fara maimaita addu’a:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”


Kalmar ta tsaya a kan laɓɓansa, tana fita a hankali, tana haɗuwa da rawar jiki da firgici. gumi mai sanyi ya bayyana a goshinsa, yana gangarowa bisa kyakkyawar fuskarsa wadda ta haɗu da tsananin kamala da kwarjini.


Yana daurewa, amma fargabar mafarkin da ya farka daga gareta ta kasa barin zuciyarsa ta zauna a hankali ya dafa kansa, hannayensa masu tsawo da haske suka motsa a hankali kamar yana neman kwanciyar hankali daga cikin jikinsa.


Sai ya sauke ƙafafunsa — dogaye, masu santsi — daga kan gadon farin zanen da ya lullube shi. Gashin kansa mai laushi ya kwanta luff-luff a kan fatar kansa mai haske, yana ƙara masa wani irin kyau da natsuwa da ba a iya fassara wa.


Ya jingina da katangar gefen gado, yana sauke numfashi a hankali, yana ƙoƙarin tuna... amma babu komai. Abin da ya rage a cikin zuciyarsa shi ne wani abu mai nauyi — tsoro, da tambaya, da shiru mai cike da asiri.





Hannuwansa biyu ya saka cikin gashin kansa, yana ja da su a hankali kamar mai son tabbatarwa da kansa cewa yana cikin duniya. Doguwar ajiyar zuciya ya saki, sautin numfashin sa ya gauraya da shiru mai nauyi.


A wannan karon, mafarkin da yake masa kamar rigar jikinsa yau ya sauya salo — domin komai ya dawo masa bayan dogon lokaci na duhu da rashin sanin kansa, yau ya fara tuna komai yau ne Bashir ya dawo cikakken mutum.


Siraran hawaye masu dumi suka fara gangarowa a fuskar sa, suna haɗuwa da ɗan murmushin da bai cika ba — murmushin wanda yake tsakanin farin ciki da firgici.


Sai kawai aka ji ƙarar ƙofar da aka turo da sallama, cikin taushi da nutsuwa.
Wata yarinya ce ta shigo — kyakkyawa, tsaf cikin doguwar abaya mai kamshi, mayafi mai ɗan haske a kanta zubin ta na nuna tarbiyya da asalin gida mai natsuwa.


Da farko ta tsaya cak, idonta a kansa, ta ɗan firgita ganin yadda yake zaune cikin ruɗani da hawaye da sauri ta matsa kusa da shi tana faɗin “Yayah Bashir, lafiya kuwa? Me yasa kake kuka?”






Muryarta mai sanyi da taushi ta dawo da shi daga zurfin tunanin da ya nuts ahankali ya kalle ta, idonsa cike da mamaki, da tambaya, da tsoron gaskiyar da ta dawo masa.


Ta sunkuya, ta tattara light breakfast ɗin da ta ajiye a kusa da gadon — faranti mai ƙunshe da toast, omelet mai cike da kayan lambu, da kofin warm milk wanda kamshinsa ke tashi cikin ɗakin ta juya a hankali, tana kiran:
“Mommy! Daddy! Ya Bashir ya farka!”






Muryarta ta ɗan sarƙe, tana haɗuwa da rawar jiki da jin daɗin mamaki ta jinjina kai, tana kallon Bashir da idanun da ke cike da tambaya da bakin ciki lokaci guda.
“Yaya na kuka Mommy, wallahi yana kuka!”
muryar Khady ta tsinke cikin dakin da ɗan rawar jiki, tana magana cikin hanzari da tsoron abin da ta gani. Idonta ya kaɗa da hawaye, zuciyarta ta buga da sauri kamar zata fito daga kirjinta.


Mommy, wacce take a falo tare da Daddy, ta ɗago da mamaki da hanzari ta miƙe tana cewa cikin murya mai daure da fargaba “Khady, ki yi shiru mana! kwantar da hankalinki... let’s go and see him.”






Bata ma gama kalmar ba sai ta kama hannun yarinyar, suka nufi ƙofar ɗakin Bashir cikin tsoro da fatan alheri cikin wannan ɗan lokaci ne Sagir da Muhsin ya biyo bayansu, yana riƙe da hankici, fuskarsa cike da damuwa da mamaki.


Suna shiga dakin, sai kallo ɗaya ya wadatar.
Bashir na zaune turƙus a ƙasa, gaban gadonsa, hannayensa biyu sun dafe fuska, ƙirjinsa yana motsi da numfashin kuka.


Kamar ƙaramin yaro da aka wayi gari da tsoron mafarki, yana rawar murya yana maimaita addu’a, hawayensa na bin gefen kumatunsa har zuwa gemu.


Mommy ta tsaya cak a ƙofar, zuciyarta ta buga, hawaye suka cika idonta kafin kalma ta fito.
Daddy kuwa ya kasa motsi, yana kallon ɗan nasa da wata irin shiru mai nauyi — shiru mai cike da tambaya, mamaki, da godiyar Allah.


Sagir ya matso a hankali, muryarsa ta yi rauni:
“Bash... Bashir?”






Amma Bashir bai amsa ba — sai ma ƙara saka hannuwansa cikin gashin kansa, yana jan numfashi mai nauyi kamar wanda yake ƙoƙarin farfaɗowa daga tarihin da ya daɗe yana mafarki daga gare shi, gashi yau Allah ya..






#####
DUBAI
A hankali ta shafa kansa, ƙafafun hannunta sun rungume jikin sa da kulawa mai laushi. Nan ya firgita, zuciyarsa na buga da sauri kamar zata fashe.


“Haba Habibty, wallahi na tsoro ta…” cewar Rayyan, murya cikin kaɗan da rashin tabbaci.


Harara ta buga mai kai, idanunta suna cike da tausayi da damuwa. “Don Allah, Kaye… auren ma ba zaka daina wannan tsoron ba ko?”


Cikin murmushi mai cike da baƙin ciki, ya dawo da hankali a hankali. Murmushin sa ya yi sanyi, cike da wani irin nauyi da ya sha wahala, ya furta, “Habibty … kinan… rayuwa tamkar bani da uba, na azabtu a gidan mahaifina. Wallahi, bazan manta watarana da aka min sharrin sata ba ranar da tafe kowacce rana wahala a guna…”


Ya tsaya, ido na kallon ƙasa, zuciyarsa cike da tsoro da fargaba, amma a lokaci guda, akwai wata ƙaramar haske na farin ciki da ke bayyana a gefen fuskar sa — saboda yanzu, a ƙarƙashin kulawar Rayyan, ya fara jin cewa akwai wani wuri mai aminci a rayuwarsa.




A cikin murya mai rauni, Rayyan ya faɗi, yana kallon matarsa da idanuwa cike da zafi labarin da ya sha kamar wuta a zuciyarsa.


“Sun kawo wani tsohon soja Iri — mutum mai fuska kamar dutse, hannunsa kamar sanda. Sun daure ni a bayan hannu, aka rufe ni a ɗaki mai duhu; babu rana, babu iska, babu ruwa, babu abinci. Rana da dare duk sun tsaya a wuri ɗaya — zafi ya mamaye wajen kamar an jefa ni cikin ƙarfe mai ɗumi, tsawon kwanaki ukku ina azabtuwa


A can ne suka fara ‘horon’ — ba horo na ilimi ba, horon azaba. Sun kunna mini fargaba, suka nuna mini wani abu a matsayin ‘shaidar wuta’ — alamun azaba da nufin tsorata ni. Idona ya yi jaƙeƙe, zuciyata na bugawa kamar kararrawa, a duk lokacin sai na ji ƙamshin hayaki na bakin zuciya.


Hawayen suka fara cika idona; a lokacin Iro ya ƙi tausayi — ya shafa hawayen da hannunsa mai ƙarfi, amma shafinsa ba tausayi bace, sai tambaya mai sanyi: ‘Tabbas ka sha azaba Hayyaty amma me ya ƙubutta da kai a wancan ranar?’


ya sauke ajiyar zuciya, ya amsa cikin murya mai ƙasa, Muryar da na rawa: ‘Na ƙubutta... saboda ba ni da wata hanya tsoro ne ya ja ni, rashin gida ne, da rashin abin dogaro. Amma ba azabar ta zama banza ba; na rike abin da aka bani, na ɓoye amanar da zata ceci wasu.’


A duk lokacin da na tuna, numfashina na faɗuwa da sauri; amma a zuciyata akwai ƙanƙanin haske — sanin cewa duk wannan azaba ba ta ɓace ba, tana da lokaci tsanani baya tabbata haka daɗi baya dawwama ”




A jiyar zuciya na sauke, hawayen na zube kamar ruwan damina — a hankali, numfashin na ya fara rikewa cikin ƙarfi da kuka. Duk da haka, a tsakiyar ƙunci da azaba, sai wani abu ya zo min kamar labari mai dumi a kunne: murya — murya mai ƙamshi na gida, mai cike da tausayawa.


“Yaro na… ka natsu, ka daina kuka,” muriyar ta zo a hankali kamar ta fito daga cikin inuwa. Rayyan ya ɗaga kansa da sauri, idanunsa sunɗan yi jaƙeƙe. Bai yi shakka ba — muriyar mahaifiyarsa ce; ta fito masa fili a zuciya kamar ido yake gani.


A lokacin, sai na tuna da zanruttukannhikima da ƙawata Suwaiba kimin “Ka kasance ƙarfin zuciya, ka jingina da addu’a, kada ka bari tsoro ya mallake ka.” Wannan ƙaramar muryar ce ta sa zuciyarsa ta ɗan natsu.


Ya ɗan yi dariƙa, ya share hawayensa da bayansa na hannu, ya ce cikin rawar murya mai rauni:
“Mom… na tsoro… na sha azaba…”


Muryar mahaifiyarsa ta ƙara taushi, tana ƙoƙarin mika masa kwanciyar hankali:
“Na sani, ɗana. Amma ka ji daɗi — kai ba kaɗai bane. Mun zo tare da kai ka rike wannan ƙarfin zuciyar, mu za mu tafi tare muka samo mafita kada ka manta, hayaniyar duniya ba za ta wuce ba — amma girmanka da kirki zai zauna.”


A hankali, Rayyan ya sami ƙaramin natsuwa. Kukan sa ya ragu, numfashinsa ya koma daidaito yana kallon matarsa da idanu masu ƙara laushi, ya ɗauki hannunta, ya matsa kusa da ita da ƙanƙantar murya:
“Na gode, kin zo min a daidai lokacin da na fi buƙata.”


Ta rungume shi da ƙarfi, kamar tana ƙoƙarin ja masa duka danƙon duniya. suna kallon yadda ƙauna take warkar da raunuka.


To be continued.............





✨🌟 KAƊANGAREN BAKIN TULU 💥✨
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)







GARGAƊI


Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba ,
********

PART TWO
PAGE 26/27



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login