Showing 3001 words to 6000 words out of 40625 words

Chapter 2 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

368

da wasa aka haife shi ba wannan... wannan shi ne Kaɗangaren Bakin Tulu!”
“An barka ne, amma ba a barkar da murna ba. an kore ka, an fasa tulun da kake ciki, aka zubar da ruwan da ya kamata ya rike ka an zagaye ka da tsinuwa kafin ka ɗan sha iska. Amma Allah ya bar ka da numfashi!”






Ya fito da yaron zuwa harabar jama’a. Ya ɗaga shi sama kamar ya nuna duniya cewa: “Ko ba a so shi ba, ya zo ko ba a shirya masa ba, ya fito wannan yaron... wannan yaro shine jarumin da ba a nemansa ba amma dole duniya ta karɓe shi!”


Mallam Sambo – tsoho mai hangen nesa – ya karɓi jaririn da hannayen da suka girgiza.


“Yaro namiji ne! ya fito da ihu! ya fito da ƙarfi da baƙin cikin rasa mahaifiyarsa a cikin zafin haihuwa ya zama Kaɗangaren Bakin Tulu! Tabbas... wannan wata aya ce, aya mai cike da darasi!”


Yaron yana ta ihu, yana jijjiga hannu kamar yana faɗa da duniya da zarar ya shigo cikinta. jikinsa ƙururuwa ne, hannuwan sa kamar yana murɗa takobi ne cikin iska.


Cooper ɗin likita, wanda ke rike da yaron, ya rungume shi da ƙarfi kamar yana ƙoƙarin ba shi ƙarfin rayuwa da ɗumi hawaye na gangarowa daga gefen fuskarsa, yana kallo cikin idon jaririn kamar yana neman amsar wata tambaya da zuciyarsa ta kasa bayarwa shekaru da dama.
“An haife ka ne ba don ka zauna ba, Kaɗangare…” ya faɗa da siririyar murya. “An haife ka ne don ka girgiza tarihin waɗanda suka saba wulaƙanta marasa laifi.”






Yaron ya yi kukan da ya tsayar da kowa cikinsa. Yana kallon sararin sama da ido da ba ya ganin komai wata tsohuwa mai suna Inna Uwaliya, tsohuwar unguzoma ce ta kauye, ta durƙusa gefen gadon inda gawar Kaltume take kwance.


“Wannan haihuwa ce mai sako,” ta furta da bakin da ke rawar murya. “Wannan yaro... yaron da ba’a so ba ne amma baƙin tulu ya fasa kansa, ruwan da ke ciki ya fito da rana. Wannan yaron... zai ƙone da wuta, zai raba gaskiya da ƙarya!”
Likita Bashir ya matso ya lulluɓe gawar Kaltume da farar zani ya juya yana hawaye, ya kalli nurse ɗin da ke kusa da shi.
YACE




*********
ABUJA


Abuja — babban birni mai lulluɓe da kyalli, gine-gine masu ƙayatarwa, cike da gurbatacciyar iska mai ɗauke da kamshin arziki da sirri A cikin anguwar Asokoro, daga cikin jerin manyan gidajen gwamnati da jakadun kasashen waje, akwai wani gida wanda kallo ɗaya ka masa zaka san cewa kuɗi bai da daraja a ciki.


Wannan gida ba kawai na gida ba ne Gida ne da ke da murmushin wadata, zuciyar iko, da ƙahon sirrika shi ne gidan Ministan Lafiya: Alhaji Abba.


Gidan — mai matakai uku, rufinsa marmara ne na Turai, falonsa na ciki na cike da tagogi masu haske da tagulla, sai fitilun chandelier masu ƙyalli kamar rana cikin dar jikin bangon falon, hotuna ne na manyan mutane — shugabanni da ‘yan siyasa, da kuma wasu hotunan da ke ɓoye manyan al’amura da ke tafiya a bayan fage.


A cikin wannan gidan kuwa akwai mutane guda biyar da rayuwarsu daban take — kowanne da nasa salo, da burinsa, da nishadinsa:


1. Alhaji Abba – Ministan Lafiya; dattijo mai mulki, mai iya ɓoye dariya da fushi a lokaci guda kallo ɗaya ba zai nuna maka irin ƙarfin da ke cikin zuciyarsa ba Allah ya mallaka masa dukiya da baisan adaddin sa ba.




2. Hajiya Zulaihat – matarsa ta fari, wacce aka aura tun kafin ya samu minister mace mai kishi da son zuciya, tana rayuwa ne a cikin gida da duhu na siyasar mijinta.




3. Hajiya Maijidda – matarsa ta biyu, budurwa ce wacce aka aura bayan samun mulki. Kyakkyawa, mai juna biyu, tana rayuwa cikin jin daɗi da kewar wasu abubuwan da ba a faɗi.




4. Alhassan – ɗan’uwan Minista, wanda ke zama a gidan ba tare da aiki ba, amma yana cin arzikin gidan mai rainin hankali da shagube.




5. Khadija – 'yar gida, bai kai shekaru 20 ba. ba jini ba, amma tana cikin gidan saboda wata alaka da uwar gida. Kyakkyawa ce, amma tana rayuwa ne a cikin inuwa.






A yau, suna zaune a babban falo suna karin kumallo. Wajen cike da pancake, toast, coffee, zaƙi, da kusan komai daga Turai, amma kallon da ke tsakanin su yana ɗauke da abubuwan da ba a faɗa.


Rayuwa mai kayatarwa ce, amma kowa a ciki na ɗauke da wani sirri, wani fata, ko wani laifi da ba a bayyana ba kuma ko da yake suna zaman lafiya, wata rana... za su gamu da abinda zai girgiza tsarin su....








MUJEEE ZUWA WELCOME TO A NEW JOURNEY OF KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎












🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY


NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t




FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI
300 only
08101235739
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️



PAGE FOUR 4







*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)









PAGE FOUR 4



Asuba ta gabato da sanyi da ƙamshin ganyen lemongrass da aka yayyafa a falo domin dāƙile ƙamshin daddare. Amman cikin zuciyar Hajiya Maijidda — mace mai ciki — sanyi ba ya wanzuwa raɗaɗin cikinta da naƙuda yana tashi yana sauka kamar walƙiya a ɗakin da babu haske.


Ministan Lafiya, mijinta, yana can Lagos ya bar gida da jiya don taron kwamitin lafiya na ƙasa ba wanda ya ɗauka zai faru ba shi ba. A lokacin da ya tafi, naƙuda bata da alamar kusa.


Amma yau “Wayyo Allah... yallabaiii...!”
“Ciki... yana karkarwa... kamar ruwa mai tafasa...”
Sai gaban motar gida ya ɗan kaɗa – nurse ɗin da aka kira ya ta iso da ƙyar. Xulaihah, uwargida, ta tsaya a ƙofar falon manya, fuska ɗaure kamar wacce ta gaji da hakuri.
“Kada ki shige cikin gidan nan da ambulance. Wannan haihuwa ba zai bar wannan gida ba. In yaro ne ke ciki – sai ya mutu kafin ya sha iska.”
Ummi mai duba lafiyar gida, ta tsaya da hargowa.
“Hajiya, ai ciki ba a raina masa mutuwa! wannan ba adalci bane. Ko kina tunanin Allah zai zuba ido...?”
Zulaihah ta zuba mata harara mai zafi.
“Allah da muke kira shi ne na ba ni ɗa — ke kuma kina son a kwace shi daga wurina. Don an ce namiji yana ƙara daraja, da dukiya a gado sai ki ce sai an haife shi...?”






Gidansu Minista yana ɗauke da sirri an ce Idan mace ta haifi ɗa namiji a cikin gidan, tana samun cikon gida, gwal , iko da tabbaci a zamanta. Shi yasa Maijidda, da ta haifi mace ta farko kuma ta rasu, take fatan wannan ciki zai dawo mata da ƙima.


Amma Zulaihah — bayan sunan uwargida, tana da jinin namiji. Ɗanta, Majeed, yana shekaru goma sha biyar yan gidansu sun fi nuna masa kulawa, Minista ya fi yarda da shi.


Yanzu kuma... ana zargin cikin Maijidda zai iya zama ɗa namiji.




Zulaihah ta kira wasu daga cikin maidens nata, suka ɗauko wata ƙaramar sanda da ruwan zafi, suka ce:
“Muna iya ɗaukar ciki da taimakon zafi da matsa cikin hanji. Hakan ba saba wa doka bane — ba asibiti, ba 'yan jarida...”




Umme ta zazzaro ido.
“Hajiya! Wannan kisan kai ne fa!”


Sai Zulaihah ta ce cikin siririyar murya:
“To ki zabi — a haife da sunan ni ce uwargida kuma in koma gefe? Ko in kare gadona kafin su janye min kujera?”






Wata mai aiki, mai suna Latifah, ta durƙusa a ƙasan gado, tana share zufar Maijidda da kyakyawar kyalle.
“Wallahi idan wannan jariri na mace ne, zamu tuba — amma idan ɗa ne... ya kamata ki ɓoye shi. Ko in taya ki... mu gudu da shi.”


Maijidda ta ji kalmomin a cikin firgici, numfashinta na tsinke kamar mai jin karar mutuwa.




Kiran asuba na ta ƙoƙarin fasa duhun dare da salati, amma a cikin babban gidan Ministan Lafiya, wani irin duhu ya mamaye zuciyoyin da ke cikinsa fiye da na dare.


Hajiya Maijidda – mai ciki, tana kwance cikin zafin naƙuda, tana kiran Allah da numfashi mai sarkewa:
“Ya Allah... Na shiga tsanani... Ku taimake ni… ya Rabbi...”






Sai wata murya mai sanyi da duhu ta dawo da ita daga tunanin ceto:ma “Taimako ba ya nan. Ki haifi jaririnki — idan Allah ya so mace ne, zamu bar ki da rai. Idan namiji ne... toh, kiyi sallama da duniya da ke da yaron da zaki haifo .”






Tana ƙoƙarin tashi da kuka tana neman ƙofa, sai tayi ido hudu da Hajiya Zulaihat, uwargidan da ke kallonta da sanyi amma idanu cike da ƙiyayya.


A bayanta kuwa, ƴan aikin Xulaihah ce Hannun su na riƙe da ruwan zafi da abin nade kai. A gefe ɗaya kuma, Nurse Umme ta ke tsaye a jijjiga, amma da bindigar gwiwa a kanta!
“Ki motsa ki kira ambulance, ki gwada kaita asibiti — wallahi sai kin gane wannan cikin ya fi ki muhimmanci!”


Zulaiha ta faɗa cikin zafin kishi, tana wani mika ƙafafu kamar zakanya.
Nurse Umee ta fashe da kuka:
“Amma Hajiya... zafi take ji… ciwo! wataƙila ciki ne ke kusa fashewa! Wannan zubar da jini ba alama ce mai kyau ba tana da matsalar haihuwa !”
Zulaihat ta sake matsar da bindiga, ta ce:
“Ki tsaya mu gani duk wanda ya yi motsi sai dai a fitar da shi da gawa cikin nan zai haifu a nan mu gane ko Allah zai bar ni da sarkin gida ko wata ’yar gata ce zata kwace gareni.”






Maijidda tana kwance – hannunta yana ƙoƙarin shan numfashi, idonta sun yi jajir, jinin zufa da hawaye na gauraye da jini daga kasanta. “Ku taimake ni... don Allah... ku ce masa bana neman matsayi... bana neman gado... bana neman komai! Sai dai in haifi nawa!”






Amma kowacce murya da ta fito daga bakinta sai ta tashi ne a cikin dakin da zuciyoyi sun mutu da rahama.


Sai aka ji wata shigowa — yaron ƙarami Abdul-Majeed, ɗan Zulaihat, ya shigo da sanda yana kallon uwar Maijidda cikin jini. Ya ce: “Mommy Me yasa tana kuka haka?”






Zulaihat ta kalle shi, ta ɓoye bindigar hannun ta “Domin tana so ta kwace gidanmu ne, ta haifi ɗan da zai sa ku manta da kai. Amma Allah bai yadda ba. Ka tafi ɗakinka babo wanda zai ƙwace maka matsayin ka a gidan muddin ina numfashi , Nurse Ummee ta fashe da kuka, ta jefar da duk wata tsoro. Ta ce:
“Ni ba zan ƙare da rayuwa a haka ba wannan jaririn zai fito, in har ina numfashi!”
Amma kafin ta ƙarasa zuwa kusa da Maijidda
Zulaihat ta sauke yatsa kan bindiga!


TATT!
An ji ƙaramin harbi — ba kai tsaye ba, amma an harba kusa da ƙafarta.




“Wallahi zata sake haihuwa , yanzu ne! Cikin nan yana fitowa da yardar Allah!!”sai wani abu ya faru wanda ya gigita kowanne numfashi a dakin: Jinin haihuwa ya ɓarke!


Ya zubo kamar ruwan rijiya, ya ratsa zanin da ke ƙasan Maijidda, ya haɗu da gumi da zufa.
“Ku taimake ni... Allah... ku ce masa… ban mutu saboda soyayya ba… na mutu ne don na yarda da ƙaddara!”






Nurse Ummee ta fasa kuka sosai, ta zare hijabi ta nade hannunta
Sai wata murya mai ƙarfi ta bugo daga ƙasa cikin ƙirjin Maijidda: “Uhhh... uhhh... yaa Allahhhh!”
Sai kuma ƙaran kuka — kukan jariri!
Na farko, sai na biyu — amma ɗaya daga cikinsu yana cikin jini sosai.
Jariri biyu!
Namiji... da mace.


Zulaihat ta tsaya cak. Hannunta ya ɗauke da bindiga amma zuciyarta ta firgita.
“Me? ta haifi... biyu?!”
Nurse Ummee ta dube ta da kallo na tausayin banza:
“Ke kadai kika haifi ɗa. Amma wannan matar ta haifi kaɗangaren bakin tulu — biyu ne! Kuma duka suna numfashi.”


Zulaihat ta zube a kujera a daidai lokacin, an ji ƙarar buɗe ƙofa — motar asibiti ta iso daga ƙofar waje!


Amma kafin su isa — Maijidda ta kalli jariranta, ta fashe da ƙara mai sanyi. Sai ta ce da numfashi na ƙarshe:




Nurse Ummee ta daure gwiwa, ta jawo jarirai biyu, ta share musu fuska da jinin uwarsu.
Sai ta dora su a ƙirjin Maijidda da hannuwanta da ke rawa da sanyi.
“Ki riƙe su... sun riga sun fito Maijidda... ki sumbaci rayuwarki a cikin su.”
Maijidda ta kama su, ta rungume jariran da sauran ƙarfinta, sai ta fashe da kuka da dariya a lokaci guda. Idonta cike da hawaye, zuciyarta cike da azaba.
Ta ɗaga ɗan namijin da hannunta yana rawa, sai ta ce da karamin murya:
“Kai ne... kai ne Kaɗangaren Bakin Tulu... Na haife ka a gaban maƙiyanka... sun kashe ni, amma ba za su kashe kai ba! Zan mutu ba tare da jin daɗin uwa ba... amma zan bar musu KAƊANGARE...”






Ta kalli Nurse Ummee da murmushi, ta ce:
“Ke ce mataimakiyar Kaɗangare... karki bar su cutar da shi... karki bar su ce ba zai rayu ba...”
“Ke ce masa... bana son ya zama mara haƙuri da juriya sai dai idan zai warke da haƙuri TABBAS NA HAIFO IDON DUNIYA NA HAIFU KAƊANGAREN BAKIN TULU na haifu ka a gaban maƙiyan ka .”


Idanunta sun lumshe... jikinta yayi sanyi.


Sai Nurse Ummee ta fashe da kuka:
“Maijidda ta mutu... amma ta bar mana jarirai biyu — kaɗangaren bakin tulu. Daya zai yi sanyi kamar uwarsa… ɗaya zai ƙona... kamar yadda gidan nan ke ƙonewa yanzu...”
Sai dai kafin Ummee ta amsa, wata ƙara ta bugu!
TAW!!
Bindiga.


Jariran sun karye daga hannunta!
Nurse Ummee ta juyo da hanzari — Zulaihah ce, ta harbe iska ..
sai ta bindiga taye akan yaran dukkan biyu
kuwa ya tsaya chakk jikinsa ya saki. Tayi shiru amma kafin wani ya motsa, an ji karamin murya daga bakin kofar:
“Oyooo Daddy! Yaaa Daddy!!”
MAJEED ne, ƙaramin yaron gidan — ya shigo da dariya da nishadi.
Zulaihah ta rikice!
Ta jefa bindigar a bayan labule, sai ta ce cikin dukan zuciya:
“Duk wacce ta ce magana akan wannan... sai dai ta rasa rai! wallahi zan sa a kasheta kamar itama Maijidda!!”




Kafin kowa ya ƙarasa wani motsi — an ji ƙarar siren ambulance.
Minista ya shigo da ƙarfi da jami’an tsoro masu mara masa baya don su ji ƙarar abu yaran kuwa ihu sukiye wanda ya karaɗe dukkan gidan .


Kallon da yayi wa Zulaihah kamar ya fi kisa:
“Ina matata?! Ina Maijidda?!”
Ummee ta miƙa jariran biyu da hawaye, ta ce:
Ta haihu biyu ita kuma ta mutu cikin azaba
Minista ya ɗauki numfashi da ɓacin rai — sannan ya juya.
Abu ya canza. Rayuwa zata canza.






🥀 Idan Maijidda ta mutu — to da rayuwarta aka rubuta babin farko.


Kadangaren Bakin Tulu ya zo. Amma wa zai tsare shi daga guba, kiyayya da mugunta a gidan da aka haife shi?





Is just instructions har yanzu ba'a fara labarin ba mujee zuwa free page is going


Godiya mai tarin yawa ga masu mun fatan alheri Allah ya saka da dubbun alkaire daram daram tsakani na daku mujee zuwa KAƊANGAREN BAKIN TULU NA BIYU YA Bayyana a Birnin Abuja..




















🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY


NARNAH ƘANWAR SOJA





Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t






بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️



PAGE FIVE 5


300 only
FREE PAGE
08101235739




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)









PAGE FIVE 5



( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕).












TSIBIRI


Cikin duhun dare da sanyin iska, wata mata tana gudu cikin dajin yankin Maiduguri. Ƙafafunta cike da ƙura da jini, ciki kuma na ƙaton ciki yana girgiza tamkar zai fito kamar wacce ta ratsa azaba, tana ta rawar jiki tana duban baya lokaci-lokaci.


"Allah Ka kare ni da abin cikin nan… Allah ka cece mu daga hannun su…" ya faɗa da karamin murya yayin da hawaye suka haɗu da zufa a kumatunta.


A lokacin da ta iso gaban kogin Bula, sai ta tsaya ta shaƙi iska – tana ƙoƙarin cewa da kyar ta iso amma karar bindiga ta sake girgiza gabobinta. sai gashi TSAA!! an harbe ta a tsakiyar bayan ta , jinin ya ƙara zuba daga ƙafarta – amma bata tsaya ba, tana ƙoƙarin kare cikin cikinta.


Da wani kishi mai ban mamaki, sai kawai ta faɗa cikin kogin tsunduma, ruwa ya ɗauketa da sauri ya niste ta zuwa cikin duhu da ruwan kogin…




Ba da jimawa ba, motar jeep mai baƙin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login