Showing 33001 words to 36000 words out of 40625 words
Chapter 12 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt
tsaro — ya zama kamar gajeren mafarki ne kawai, saboda yanzu akwai wannan haske na soyayya da ke ɗaukar su gaba.
Raizah ta ɗan murmusa, ta faɗi cikin muryar sanyi mai shauki “Rayyan… yanzu babu wani abu da zai iya raba mu.”
Rayyan kuwa ya rungume ta da ƙarfi, yana jin zafin zuciyarsa da farin ciki a lokaci guda. Wannan shine farkon labarin soyayya da shauki tsakanin su, inda duk wata tsoro ta baya ta narke a cikin wannan sabon haske ..
“Kasan fa, Daddy, na jirar mu zamu tafi airport yanzu. Dole muyi wani wankan jarabar kananan,” Raizah ta ce da dariya, idanuwanta cike da walwala da shauki Rayyan kuwa ya murmusa, ya janyo ta a hankali zuwa jikinsa, yana jin zafi mai laushi a zuciyarsa “To, menene, baby? Kinsan fa idan kina tare dani, mantawa nake da kaina,” ya ƙara cewa yana kunce mata tawol cikin shauki...
A wannan lokaci wayarsa ta dakkar tar, sai ya ɗaga hannunsa yana murmushi.
“Hello… ehh, Uncle,” ya ce cikin sautin nutsuwa, sannan ya gyara muryarsa:
“By 11 jirgin mu zai tashi, 10:30 me kukiye baku zo airport ba?”
?????????????????
Zuwa ina
to be continued.
An shigo da Mallam Audu cikin gidan a hankali; an ja shi har zuwa zauren inda Baaba ke zaune. Ta jingine bakinta, yawu na zubo da wari mai ƙarfi; a ƙirjinta sai ƙudaje suke bayyana kamar sun fara samun nama — alamar cewa ciwon ya dade kuma ya tsananta.
Ta zauna tana sauraro, idonta a buɗe amma babu yadda za ta iya magana; hawaye na zuba a gefen idanunta kamar ruwan sama. Bashir ya tsaya a gabanta, zuciyarsa cike da nauyi, ba shi da magana; Mommy da Khady suka tsaya a baya, sun dan natsu, sun yi nesa da ita domin gudun ɗaukar cuta gidan ya yi sanyi, shiru na nauyi yana zaune a ko’ina, kowa na kallon Baaba cikin tausayi, yayin da ta ci gaba da sauraron maganganun da ke zagaye da ita, hawaye na zubowa a ƙusuranta.
Chan Mallam Audu dake kallon Mommy, ko ƙiftawar ido bai yi ba.
Babo yace da murya mai sanyi amma cike da iko:“Duk ku zauna… Bashir, tabbas kaine ƙadagaren bakin tulu!”
Wannan kalma ta kada zuciyar kowa dake wurin. Shi ne abinda koyaushe Mallam Sambo ke faɗa — amma yau ne aka tabbatar da ita a fili. Ashe wannan rana ce da za ta tona sirrin shekaru masu tsawo.
Wani shiru mai nauyi ya biyo bayan kalmar.
Sai wata kyakkyawar yarinya ta matso daga bayan jama’a — ƴar shekara goma, idanunta kamar taurari amma cike da tsoro da mamaki.
“Zo nan, ke zauna anan NOOR ,”
in ji Mallam Audu yana nuna mata kujera kusa da shi Ya juyo yana kallon Mommy da Bashir, sannan ya ɗan gyara zama.
“Yau zan faɗi labarin da nasan cewa hakkin wannan labarin shi ne dalilin da yasa har yau ban mutu ba…
Ina ganin rayuwa kalla-kalla, saboda wannan sirri da ke cikin zuciyata.”
Mallam Audu ya dafe ƙirjinsa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfin da ya wuce na mutum mai rai. Idanunsa sun cika da hawaye, muryarsa ta yi sanyi amma tana ɓoyar da zafin da shekaru suka tara a ciki ya ɗan kalli Bashir, sannan ya sauke numfashi mai nauyi.
“Bashir… ka saurare ni da kyau, saboda abinda zan faɗa maka yau shi ne abin da nake jira shekaru da dama in faɗa kafin in mutu.
Mamanka, sunanta Ummu Kulsum — mace ce da Allah Ya halitta da ƙima da haƙuri Lokacin da ta zo ƙauyen nan, mutane suka ce ‘yar gudun hijira ce, suka ce ta fito daga arewacin kasar nan saboda yaƙi amma gaskiyar magana ita ce — ta zo ne da wani tsohon makaho, wanda ya ɗauke ta tamkar ‘ya. Mutane suka raina su, suka ɗauka ba su da galihu.
Ni kuma… ni ne bala’in rayuwarta.”
Ya lumshe ido, hawayen da ya dade yana riƙewa suka sauko kamar ruwan sama.
“Na aure ta saboda son zuciya, saboda kishi da ƙeta amma ban aure ta saboda Allah bana zama azzalumi. Na hana ta dariya, na hana ta kwanciyar hankali.
Duk sautin muryarta yana tuna min da hasken da ban taba samu ba.
Na mata duka a bakin murhu, na wulaƙanta ta har ta gaji da numfashi.
Wata rana cikin fushin da ya makantar da zuciyata, na zuba mata ruwan talken towo mai zafi a lokacin ruwan sama.
Ta faɗi, ta mutu a gabana.”
Ya durƙusa yana kuka kamar ƙaramin yaro.
jin irin rawar muryarsa yasa kowa a wajen ya kasa motsi “Tun daga wannan rana, zuciyata ta zama kamar wuta. Amma kafin ta mutu, ta bar kadangare a gidan nan — shi ne kai, Bashir.
Duk da ban san ka ba, ban san lokacin da aka ɗauke ka ba, amma kullum ina jin zuciyata tana tsanar ka, tana tsoran ka, tana son ka lokaci ɗaya ashe wannan yana nufin kai ɗan mamanka ne, kai ne amanar da na watsar.”
Ya share hawayensa da hannun da ke rawa, yana kallon Bashir da idon nadama.
“Rashin addini ya rufe ni, giya ta zama abokiyata, mata suka zama abincina, har na manta da mutuncin rayuwa.
Amma yau na fahimci cewa Allah bai manta da ni ba, saboda har yanzu ina numfashi don in furta wannan gaskiya.”
Sai ya ɗaga kansa sama, yana girgiza kai kamar mai kuka cikin addu’a.
“Ka yafe min, Bashir.
Ka yafe min don mamanka.
Ka yafe min don Allah.
Ka yafe min domin wannan rai da ban cancanci in rayu ba.”
Shiru ya cika wajen, kamar iska ta tsaya.
Sai muryar sa ta katse natsuwar wajen cikin sanyin murya “Bayan mutuwar Malam Sambo, Noor ta ƙi aure kullum maganarta ɗaya ce — ‘zaka dawo kayi alƙawari…’Amma babu labari, babu wasiƙa.Har ƙauyukka ta bi tana nemanka, wancan lokacin.” Mallam ya share hawaye sa, ta ci gaba cikin murya mai motsa zuciya “Lokaci ya ja, ta girma .
Kawayenta sunyi aure, ta ƙi kula da kowa.
Sai wani yaro ya bayyana daga daji — yaro mai kallo kamar aljani, amma idanunsa suna cike da haske da hikima Sunan sa Suhayl.
Shi ne ya kawo mana haske da ilimin sa na Addini Haske da har yanzu ba mu gane ko daga ina yake ba.”
Mallam Audu ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa kukan da ke fitowa daga zuciyarsa bai da sauti, amma ya cika ɗakin da nauyin nadama.
Zuwan Suhayl ya zama tamkar sabon safiya ga ƙauyen un daga lokacin da ya shigo, murmushi ya fara komawa a fuskokin mutane, kuma Noor ta zama kamar sabuwar fure a cikin daji.
Idanunta suna haskawa da farin ciki, zuciyarta ta cika da nutsuwa kamar ta sami abin da take nema shekaru Lokaci bai jima ba, yayan ta ya aurar da ita ga Suhayl, cikin kalmar da ta ce:
“Bangaji da jiran wanda bazai dawo ba ,amman bazan manta da cewa inason Bashir da har abada ba ”
Amma, kaddara ta fi ƙarfin burin ɗan adam.
Noor ta rasu cikin imani, ta koma ga Mahalicci tana riƙe da sunan wanda ta kasa mantawa da shi — Bashir.
Har zuwa mintin ƙarshe na rayuwarta, kalmarta ɗaya ce:
“Zai dawo... zai dawo ne...”
Ta haifi ɗa mace guda ɗaya, mai kamannin ta da kyawunta, mai nutsuwa kamar mahaifiyar ka ta sakawa yarinyar sunan mamanka — Ummu Kulsum,amma kowa a ƙauyen yana kiranta da suna ɗaya kawai: Noor — domin kamar hasken mahaifiyarta take.
Mallam Audu ya ɗan numfasa, yana kallo cikin idon Bashir,muryarsa ta yi sanyi kamar ana furta sirrin da rai ke so ya ɓoye.
“Ga yarinyar nan a gabanka, ita ce amanar da Noor ta bar maka kuma ita ce ‘yar Noor.
Ka sani, tunda Noor ta haifi wannan yarinya, Suhayl ya bar ƙauyen nan..
Ya ce zai dawo, amma har yau bai sake komawa gun yarinyar sa ba,
shekaru na tafiya, lokaci yana shanye mutane, amma har yanzu ana jira.”Ya ɗago da idanu, yana kallon sama kamar yana magana da wata ƙaƙƙarfan zuciya da ta daɗe tana ƙuna.
“Wannan shi ne abinda nake so ka sani, Bashir Amma har yanzu akwai wasu abubuwa da na ajiye, ajiyar mahaifiyarka, da kuma ajiyar Noor tana da imani cewa wata rana,
kai ne zaka dawo gida ka karɓi amanar nan da hannunka.”
Ya yi shiru, ya kalli Noor ƙarama wacce ke tsaye a gefe, idonta yana cike da hawaye amma tana murmushi, kamar zuciyarta ta gane cewa labarin da aka ɗauki shekaru ana jira ya kai ƙarshe.
##$$$$$$$$$$$$$$$#####
A gurguje suka shiga wanka, ruwa mai ɗumi yana zuba musu jin daɗin jiki. Sun shirya cikin abaya irin ta alfarma, mai launin koren zinariya da ja mai haske, an yi ado da ƙyallen ƙasa mai tsada, turare mai ƙamshi na musamman wanda har kewayen gidan ya cika da shi. Hannuwansu da wuya an yi musu ado da ƙaramin zinariya da lu’u-lu’u, fuskar su kuma tana haskakawa da hasken soyayya da farin ciki.
Da sauri suka fito daga gidan, Raizah ta ɗauki kakar akwati guda ɗaya mai daraja, Rayyan kuma ya lumshe ido yana jin dumin zuciyarsa. Sun shiga mota, direban ya danna gaba, ba tare da bata lokaci ba suka tashi kai tsaye airport na Dubai.
A cikin mota, hasken safe ya cika su da kwarin gwiwa, zuciyoyin su cike da bege da shauki. Duk wani damuwa ya narke, yanzu rayuwa ta fara musu sabon babi mai cike da walwala da alfarma.
Daddy ya yi murmushi, ido cike da fahimta, ya ce “Daddy, mun makara ne… we are sorry.”
Rayyan da Raizah suka yi ƙanƙantar murmushi, suna jin sauƙin zuciya saboda Daddy ya fahimce su nan suka shiga jirgi, kowanne na ɗauke da raƙuman tunani da shauki, yayin da jirgin ke tashi daga Dubai zuwa Nigeria, Abuja.
A cikin jirgin, kowane fuska na cike da tsammani da bege, Raizah na kallon Rayyan da wani ɗan murmushi mai taɓa zuciya, yayin da Rayyan yake duba fuskar Raizah cikin shauki. Yanayi na cike da ɗan tsoro amma kuma natsuwa....
A hankali Mallam Audu ya miƙa sandar hannunsa ga Bashir, idanunsa suka kada da hawaye.Bashir kuwa yana kallo little Noor, wacce ta riƙe hannun Mommy tana shiru, kamar zuciyarta na fahimtar nauyin da ke faruwa Duk suka tsaya cikin natsuwa, ƙarar hucin iska kawai ake ji sai Mallam Audu ya zaro wata tsohuwar tsunma daga ƙarƙashin katifa.
Tsumar ta yi duhu saboda tsawon lokaci, amma ana buɗewa sai kamshin turaren da ya tsufa ya cika ɗakin “Wannan ajiyar mamanka ce,”ya ce da muryar da ke rawa.
“Wannan ganye da wannan leda... da takaddar Noor — ita ta ce in ba shi idan ya dawo... idan Kadangaren Bakin Tulu ya dawo gida.”
Bashir ya karɓa da hannunsa, zuciyarsa na tsinkewa kamar ana sare masa numfashi.
Ya buɗe tsumma ɗaya bayan ɗaya…
Sai zoben zinare ya bayyana — zoben da aka rubuta ƙarami a ciki “ Ummukulchum.”
sai kuma hoto guda biyu da aka haɗa cikin takarda mai launin rawaya saboda tsufa.
Ya ɗaga hoton farko...
Sai Mommy ta sake numfashi da ƙarfi, Daddy ya tsaya cak, Sagir da Muhsin suka kalli juna, idanunsu suka cika da tsoro.
“Innalillahi...” kawai aka ji ana furtawa a hankali.
Bashir yana kallon hoton — idonsa ya faɗa, jikin sa ya ɗauki rawa “Wannan... wannan kuwa...?”
Sai kawai ledar ta zame daga hannunsa ta faɗi ƙasa, hoton na biyu ya zame daga ciki...
sai iska ta kaɗa shi a hankali zuwa ƙasan ƙafarsa ya durƙusa yana ɗauka, idanunsa na rawa kamar mai jin kiran da ya ɓace shekaru aru-aru........
A take Mommy ta firgita, hannunta ya saki wayar da ke riƙe da ita, jiki ya yanke mata — ta fadi ƙasa “Mommy!!”
Khady ta kurma ihu tana rarrafe zuwa gare ta, Daddy ya durƙusa yana riƙe ta da rawar hannaye, Bashir kuwa ya tsaya tamkar an soke shi da wuka a ƙirji.
A zuba mata ruwa cikin tashin hankali, sai ta ɗan motsa, ta buɗe idanu cikin hawaye masu zafi.
A hankali ta miƙa hannu ta karɓi hoton daga hannun Bashir, ta dade tana kallonsa kamar wacce ke tafiya cikin wani lokaci daban.
Hawayenta suka zubo a hankali, suna sauka bisa fuskarta kamar ruwan sama mai ɗumi.
Idanunta suka yi haske kamar tauraruwa daga sama, zuciyarta ta kasa ɗaukar nauyin abin da take gani ta furta cikin murya mai sanyi, tana shafa hoton da yatsunta “Subhanallah... wannan hoton... wannan fuskar... ita ce... ita ce Ummu Kulsum.”
A take aka tsaya shiru — iska kawai ake ji tana kaɗawa ta taga.
FLASHBACK 🌙
Bakin dare ne — dare mai tsanani da duhu, kamar sararin samaniya ya ɗaure da damuwa.
Iskar sanyi na busowa a hankali tana rawar da labulen window ɗin da ke gefe.
A cikin ɗaki kuwa, ana iya jin ƙarar ƙaramar fitila mai launin zinariya tana ɗaukar ido da walƙiya mai sanyi.
Ɗakin kuwa cike yake da ƙamshi da tsafta. Katifar gadon farin zane ce, an shimfiɗa ta cikin tsari kamar ɗakin ‘ya mace mai kula da kai.
A kan gadon, yara biyu ne kwance — ba ƙananan yara ba, ɗaya ‘yar shekara ashirin (20) ce, ɗaya kuma tana da shekara goma sha biyar (15) Dukansu cikin kayan bacci ne masu launin ruwan hoda da fari, fuskar su cike da natsuwa da kwanciyar hankali.
‘Yar babba tana kwance da littafi a gefenta, alamar ta dade tana karantawa kafin bacci ya ɗauke ta Kanwarta kuwa ta rungume teddy bear tana baccin zuciya kamar wata ƙarama da bata san komai ba game da abin da ke shirin faruwa.
A hankali wata ta sauko ta haska gefen gadon, hasken nata yana bugawa kai tsaye kan fuskokin su — haske mai kama da annuri.
Wani abu mai nauyi a sararin dare, kamar iska ta ɗauke numfashi na wani abu da ke shirin ɓullo wa cikin rayuwarsuDaren da zai zama farkon wata sabuwar rayuwa.
Sautin bindiga ya fashe cikin dakin malam, ya girgiza duk gidan. Ummu Kulsum ta tashi cikin tsoro, ta kame hannun Maryam, amma kafin su yi wani abu, an ja su cikin sauri — sai dai yaran sun riga sun ɓuya a wajen babban parlour, a bayan wani ɗaki mai zurfi; suna tsare numfashi, idonsu na zurfi suna kalle abinda ke faruwa kamar an dake musu duniya.
Mutanen baki sun faɗo cikin gidan kamar hadari; sun shiga cikin sauri, suna nufi babban tebur. Sun rufe kofa da sauri, suka tilasta iyayen su zauna a wajen parlour, an murƙushe su a wani wuri domin kada su iya motsi — amma yaran suna tsaye ɓoye, suna ganin komai cikin firgigiya da azaba.
Shugaban waɗannan bakaken ya buɗe jakar fata ya zaro wasu takardu. Ya juya ya kalli mahaifin gidan da muryar ƙarfin zuciya:
“Ko ka kawo mana files ɗin? Ka sani — ko da ba mu samu ba, za mu iya ƙaddamar da hukuncin nan — mu kashe iyalanka a nan.”
Kalmar ta fadi kamar wuta a cikin dakin. Ummu Kulsum ta yi ƙoƙarin tsawata, amma an hana ta magana; hawaye sun toshe mata makogwaro. Maryam ta rufe bakin ta da hannunta, zuciyarta na buga kamar za ta fashe.
A ɓoye, Ummu Kulsum da Maryam suka matso kusa da juna, hannayensu na rike da tsananin tsoro. Sun ji dukkan kalmomin, sun ga fuskar mugunta a bakin waɗanda suka shigo — fuskar da ba za su taɓa manta ba.
A gefen duniya kuma sun yi maganganu game da Alhaji Abubakar Imam — shahararren ɗan kasuwa, tsohon gwamna sau biyu, an yi masa fashi da darar miliyoyi a sansanin gidansa a unguwa mai tsada. Amma a nan, abinda ke zamewa shi ne tambaya: menene a cikin waɗannan files? Kuma shin waɗannan masu fashi suna neman su ne, ko suna amfani da takardun ne don yin barazana?
Dakin ya nutse da shiru, sai kawai ƙarar zuciyar yaran da ke ɓoye — numfashinsu na rawa, idanunsu na cike da girgiza. Sannan shugaban ya yi murmushi mai sanyi, ya sake duba takardun kamar wanda zai yi hukunci.
Sautin bindiga ya fashe cikin dakin kamar guguwa — ya tashe su daga bacci, ya katse duk wani natsuwa.
Ummu Kulsum ta ja kanwarta Maryam cikin ƙirjinta kamar zata ɓoye ta gaba ɗaya; idanunta sun cika da tsoro, muryarsu na yin ihu suna kiran “Mom! Dad!” cikin rawar murya da firgici.
Ba da jimawa ba sai wasu mutane cikin bakaken kaya suka bullo cikin ƙofar gidan, fuskar su ƙara duhu a karkashin hulun fata. Sun zo da bindigogi a hannu, suna yawo kamar waɗanda ba su zo neman wasa ba. Wani babban mutum ne yake gaba — murya mai sanyi, ido kamar ƙanƙarar dutse. Ba su tsaya ba; cikin sauri suka kewaye babban parlour.
A baya, a ɓoye, Ummu Kulsum da Maryam sun buya cikin ɓangaren da aka ɓoye — suna matsa juna, numfashinsu ya rage, idonsu na duba komai cikin tsoro. Sun ga yadda aka tilasta iyayensu su zauna, an murɗe su a gefe; sun ga yadda mugun nufi ya mamaye gidan.
Shugaban ’yan bakin ya ɗago jakar fata, ya buɗe ta da hannu mai kauri. Ya ja takardu, ya nufi mahaifin gidan da talabijin-like stare, ya furta a hankali da murya mai ɓaci:
“Ka kawo waɗannan files — ko mu kashe iyalanka a nan.”
A gefe guda kuma, suna magana da murya ta ƙasa kamar suna tunanin wani abu mafi girma: labarin Alhaji Abubakar Imam — shahararren attajiri da tsohon gwamna wanda aka ajiye masa asiri, wanda ma an sace masa daruruwan miliyoyi a gandun sa na Kano. Amma a nan, a tsakiyar wannan gida, tambayar ita ce: menene waɗannan files ɗin? Shin sun shafi wannan sunan babban mutum ne, ko kuwa wani abu ne da zai tarwatsa rayuka?
Dakin ya nutse da shiru mai nauyi, sai kawai ƙarar rawar tufafi da ƙasa ta zama kamar waƙar tsanani Ummu Kulsum da Maryam sun rike juna, idanunsu a bude, suna kallon waɗanda suka zo — ba su da abin yi amma tsinkayar cewa wannan dare zai canza musu komai.
Sautin bindiga ya tarwatsa dakin kamar guguwa; duhun dare ya cika da karar ihu. Ummu Kulsum ta riƙe ƙananan hannayenta, ta matso kusa da Maryam cikin rawar murya:
“Ki ɓoye, ki yi shiru… ki rike wannan.”
Da ƙarfi Maryam ta ɗauki takarda ta lulluɓe a cikin jakar da Daddy ta ya bata amanar da ba za a sake mika ba, Maryam ta jefar da kanwarta cikin ɓangaren da aka ɓoye, ta murɗe baki da hannu kamar wanda zuciyarsa ke ƙara bugawa , suka shigo — bakaken kaya, fuska ƙasar duhu, bindigogi