Showing 30001 words to 33000 words out of 40625 words

Chapter 11 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

374







A hankali Bashir ya ɗago kansa daga cikin hannayensa, idonsa ya cika da hawaye, amma a ƙarƙashin su akwai wani sabon haske hasken da ya rasa shekaru da dama, hasken tunawa ya dafa kirjinsa, numfashinsa yana fita da sauri, kafin a hankali ya furta cikin murya mai rawa “Mommy… yau… yau na tuna komai. tabbas, nine Bashir.”
Mommy ta dafe ƙirji, Daddy ya ja numfashi da kyar, Sagir kuwa ya matso kusa, muryarsa cike da ruɗani “waye kai Bashir? wacece Noor da kake faɗa?”
Bashir ya lumshe ido, hawaye na zuba a hankali, yana jin kamar zuciyarsa tana sake rayuwa daga farkon ta ya ɗan murmusa da ciwo a fuskarsa, sannan ya ce:
“Sunana Bashir mahaifiyata ta haife ni cikin kurɓattaccen yanayi — ta mutu tana kuka, tana roƙon Allah ya kare ni daga zalunci na taso cikin wahala, cikin azaba, amma akwai wata rana… wata rana da ta sa rayuwata ta zama haske. ya ɗan yi shiru, numfashi na rawa, sannan ya ci gaba:
“Noor ce — yarinya ce da ta zama hasken rayuwata mun taso tare, mun yi alkawari na ce mata zan dawo garinta, na dawo da amana, saboda soyayyarmu ta yarinta ba ta gushe a raina ba.”
Ya share hawayensa, idonsa ya ƙara ƙyalli kamar wanda yake kallon nisan baya.
“Mallam Sambo… shi ne wanda ya raina mu, kuma shi ne mahaifinta. Shi ya sani yadda nake numfashi da wahala, yadda nake rayuwa da fatan wata rana zan dawo da cikakken ni.”




Shiru mai nauyi ya biyo bayan kalmomin sa. Mommy ta kasa magana, hawaye suka gangaro ta kumatunta Daddy ya dafa kafaɗarsa cikin taushi yana cewa:
“Bashir, tabbas ka zama ƙadangaren bakin tulu — duk wahalar da suka baka tun kafin ka zo duniya, duk ɓacin ran da ka sha, ga shi yau ka fito da haske. Allah ya baka rayuwa mai kyau, da kamala da nagarta. Amma… shin zaka iya tuno gida? kana tuna inda kake fitowa?”


Sagir, wanda har yanzu idonsa cike da hawaye ne, ya ƙarasa cikin rawar murya:
“Yallabai, motarmu ce ta buge shi shekaru da suka wuce a hanyar gaba da ƙauyen Rimi dake Kano mun ta nema — mun nemi danginsa har muka gaji. Likita ya ce brain dinsa ya samu rauni, jinin kansa yana ƙanƙancewa. Ya ce idan Allah ya yarda, lokaci zai gyara komai...”
ya juya yana kallon Bashir da murmushi mai cike da tausayawa:
“Yau lokaci ya yi, Bashir. Ka dawo da kanka da labarinka.”
cikin ɗakin aka ɗauki shiru — shiru mai daɗi, shiru mai cike da hawaye da godiya.
Mommy ta rusuna ta rungume ɗan nata, tana kuka da murmushi lokaci guda.
“Alhamdulillah… ka dawo Bashir… ka dawo daga duhu.”




Nan ya ɗago da jajayen idanu, muryarsa na rawa kamar mai jin sanyi cikin zafi ya ce:


“Tabbas zan gane hanyar daji, zan gane ƙauyenmu.”ya yi shiru na ɗan lokaci, yana kallonsu cikin mamaki da zafin zuciya, sannan ya ci gaba, muryarsa cike da raɗaɗi:


“Amma me yasa kuka riga ni da amana tsakaninku da Allah? me yasa kuka kai ni wannan matakin? Su waye ku a zahiri? Ku mutane ne ko kuwa wata jarabawace da aka aiko min da ita?”
Sai ya dafe kansa da hannayensa biyu, yana girgiza kai a hankali, hawaye na zuba kamar ruwan sama da bai da niyyar tsayawa.
Mommy ta zuba masa ido cikin tausayawa, Khady kuma ta matso da sannu tana ƙoƙarin riƙe hannunsa, amma ya ja hannunsa a hankali, yana cewa“Kada ki taɓa ni yanzu... ban gama fahimtar komai ba.” wannan yanayi ya ɗauki hankali gaba ɗaya, har iska ta ɗauki sassan ɗakin cikin shiru mai cike da nauyi.
Sagir ya matso da nutsuwa a fuskarsa, yana dubansa da idon da ke cike da tausayi, ya ce cikin murya mai laushi:
“Ka kwantar da hankalinka, dan’uwa… babu abin da ya faru da kai da ba Allah ya ƙaddara ba.”Muhsin ma ya gyara zama kusa da shi, yana ɗan lumshe ido kafin ya ce cikin natsuwa:
“Lokacin da muke tafiya da gudu muna shirin shigowa garin Kaduna, a lokacin ne muka buge ka da mota. Mun firgita sosai, hankalinmu ya tashi… muka yi ƙoƙarin taimaka maka. Mun kai ka asibiti, muka bayar da jininmu, da dukiyar mu, har sai da ka warke.”


Ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba da bayani:


“Mommy da kake gani ita ce mahaifiyarmu, Khady kuma ƙanwarmu ce. Daddy ne ya ɗauke ka tamkar ɗansa, suka ba ka kulawa fiye da yadda kai kanka ka taɓa tsammani. Aka saka ka makaranta, aka koya maka karatu mai zurfi, har ka kai matakin degree na biyu a fannin Political Science.”
Sagir ya ɗan murmusa cikin yanayi na alfahari, sannan ya ce:


“Yanzu kai mutum ne mai burin zama shugaba — Shugaban ƙasa! Wannan shi ne burinka, wannan shi ne abin da kake so ka cimma shin yanzu ka gane waye kai?”


Shiru ya rufe ɗakin, sai numfashinsa da ke fita a hankali ya durƙusa da hawaye a idanu, zuciyarsa cike da godiya da mamaki.


“Na tuna komai…” ya furta a hankali, yana duban Mommy da Daddy da sauran ’yan gidan.“Na gode da kuka bani rayuwa ta biyu.”
sai Daddy ya ɗan yi murmushi cikin natsuwa, yana cewa “Haba Bashir, yanzu ba lokacin kuka bane mu shirya, zamu tafi Kano.”
duk suka amince, fuskokinsu na cike da kwanciyar hankali da sabon fata.




Safe journey Bashir








###################
Ana haka, uncle ɗinsa, wato ƙanin baban sa, ya iso cikin ɗakin horo cikin hanzari, idonsa cike da damuwa da fargaba. Sai Umme ta tsaya a gefensa, ta bayyana masa halin da ake ciki: yadda Rayyan ke cikin ɗakin horo ana azabtar da shi, kuma yadda jinin sa ke zuba saboda sun yi tsammanin zai ɗauki kuɗi mai yawa.
Da wannan bayanin, uncle ɗin ya miƙa hannu, ya ce da ƙarfi:
“Haba, Daddyn Rayyan, kana kallo ne? Ana azabtar da ɗan ka saboda jini da kudi? Ashe menene a zuciyar su? Shin basa ganin cewa babu yadda zai iya ɗauke kuɗin nan? Kowa ya san Abdul ne kadai zai iya kwashe ma kuɗi. Wannan ya ishe!”
Da wannan, ya ɗauki matakin da zai ceci ɗansa. Ya yi saurin buɗe ƙofa, ya shiga ɗakin da zafi da duhun horon ya cika, ya ɗaga Rayyan cikin kulawa, yana yi masa kwantar da hankali:
“Rayyan ɗana, yanzu ka tsaya. Zan kai ka Dubai zaka samu tsaro, za ka zauna lafiya, kuma za ka cigaba da karatunka a can. Anan ba za ka ƙara jin tsoro ba, ba za ka ƙara wahala ba ,tun bayan mutuwar ka mahaifiyar ka nake so na ɗauke amman Daddyn ka ya hana , kasani yau babo wanda ya isa ya rabani da ɗaukar ka ”






Rayyan, cikin shiru da mamaki, ya ji zuciyarsa ta ɗan sassauta. Duk da tsoron da ya sha, ganin uncle ɗinsa da kulawa, da cewa zai samu tsaro da ilimi a Dubai, ya sa ya fara murmushi a hankali, yana jin cewa Allah ya shirya masa hanyar kuɓuta da rayuwa mai kyau.






Bayan uncle ɗinsa ya ɗauke shi, Rayyan ya shiga mota cikin sauƙi, duk da cewa zuciyarsa cike da haɗuwa da tsoro da fargaba. Safiyar nan, motar ta fice daga gidan horon, kuma ya ga duhu da zafi suna rabuwa da nesa da su, kamar duhu da azaba sun tsaya a baya, suna kallon yadda yake barin su.


A hanya, uncle ɗin ya rike hannunsa, yana masa kwantar da hankali:
“Rayyan ɗana, komai da suka yi maka an bar shi a baya. Yanzu za ka fara sabon rayuwa. Za ka samu tsaro, karatu, da damar da ba ka taɓa tunanin samu ba.”






Jirgin sama ya ɗauki su daga filin saukar jirgi na Kano zuwa Dubai. Rayyan yana kallon birnin daga sama, hasken dare da taurari sun yi kamar suna yi masa maraba. Duk fargabar da ya sha a baya ta fara raguwa, zuciyarsa ta ɗan sassauta.


Da suka sauka, aka karɓe su a tashar jirgin da motoci masu tsaro suka zo, suna ɗaukar su zuwa wani hotel mai tsada. A can, Rayyan ya fara fahimtar cewa duniya tana iya canzawa daga mugunta zuwa tsaro, kuma akwai damar da Allah ya tanadar masa cikin gidan su ɗin, ya zauna yana kallon birnin da tsawo, zuciyarsa cike da sabuwar fata:
“Zan yi karatu mai kyau zan zama mutum mai nagarta kuma ba zan taɓa bari mugun zuciya ta dinga rike ni ba.”






A nan ne ya fara sabon babin rayuwa, cike da karatu, tsaro, da damar da zai iya amfani da shi wajen gyara rayuwar kansa da ta waɗanda yake ƙauna. Kuma kowanne dare, kafin ya kwanta, yana tuna duk darasin da ya koya daga wahalarsa a gida — da ƙoƙarin fita daga mugun hali zuwa sabuwar fata.






Rayyan ya iso gidan uncle ɗinsa, wanda shi ne ƙanin mahaifinsa, mutum mai arziki sosai a birnin Dubai. Gidan cike yake da kyakkyawan kayan ado, fitilun zinariya, da kayan alatu — komai na nuna tsari da daraja. A gefen gidan, Raizah, yarinya ɗaya tilo, tana wasa cikin lambu mai tsabta da ciyayi kore-kore, tana dariya mai kayatarwa.


Uncle ɗin ya rungume Rayyan yana cewa “Yaron nan, yanzu rayuwarka zata canza. Ka gama wahala, yanzu lokaci ne ka ji daɗin abin da Allah Ya tanada maka.”
an shirya masa ɗaki mai kyau, gado mai launin zinariya da auduga mai laushi, duk abin jin daɗi yana nan. Rayyan ya ɗan yi mamaki, zuciyarsa cike da farin ciki da rashin tabbas: ko da yake yana cikin gidan mai kuɗi, har yanzu akwai raɗaɗin baya da azabar da ya sha. Amma ganin Raizah na wasa a lambu, da murmushin uncle ɗinsa, sai zuciyarsa ta fara sassautawa.


A kowane dare, Rayyan zai zauna a dakin karatu mai fadi, yana ganin birnin Dubai daga taga. A can ne zai fara tsara yadda zai ci gaba da karatu da horo, kuma zai koyi darussa masu mahimmanci daga uncle ɗinsa:


yadda ake tafiyar da kasuwanci,yadda ake amfani da albarkatun kuɗi don taimaka wa mutane, yadda ake tsayawa da ƙarfi a rayuwa ba tare da barin azaba ta rushe zuciya ba




To be continued.....












Kasan matsayin ka a siyasa yanzu kana neman takarar zama Senator a Majalisar dokoki ta Kaduna State House of Assembly, kai ne kuma Speaker, kana ci gaba da karatu domin cika burinka na zama Gwamnan Kaduna State nan gaba kadan.


A yau, jirgin su Bashir, Daddy, Mommy, Sagir, Muhsin da Khady ya tashi daga Kaduna International Airport da ƙarfe takwas na safe, cikin lokaci kaɗan jirgin ya ɗaga sama cikin sanyi da natsuwa bayan awa ɗaya daidai, sun sauka lafiya a Mallam Aminu Kano International Airport.


Bashir tun a cikin jirgi ya kasa samun nutsuwa — zuciyarsa tana ta bugawa da sauri kamar ana buga gangar alhini da suka sauka, duk da Mommy tana ta masa nasiha da Sagir na ƙoƙarin kwantar masa da hankali, ya kasa zama a mota ko jiran lokaci.


Tuni aka shigo da motoci masu tsaro zuwa filin jirgin, ‘yan sanda da jami’an gwamnati suna nan suna jiran su, saboda tuni aka sanar da su manufar tafiyar. Ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi hanyar ƙauyen Rimi, inda komai zai bayyana.






Motoci suka rinka shigowa cikin ƙauyen Rimi a hankali, ƙura na tashi a sama tamkar hadari mai shirin sauka mutane suka fara fitowa daga gidajensu, kowa cikin mamaki da tambaya a fuskarsa.


“Lallai yau akwai wani abu!” cewar wani dattijo yana jingina da sandarsa, yana kallon jerin motocin gwamnati da ke shigowa cikin ƙauyen da ƙarar siren ɗin su ke cika iska. ƴan sanda suna gaba, suna gyara hanya cikin girmamawa, yayin da motar gwamnati ke bi a baya a cikin motar kuwa, Bashir ya zauna a gefe cikin nutsuwa da wani irin yanayi mai cike da tunani kallon da yake yiwa kowace kusurwa na ƙauyen tamkar yana neman wani ɓangare na rayuwarsa da ta ɓace shekaru da suka shuɗe.


A gefensa, Mommy ta dafa hannunsa a hankali, tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali “ka kwantar da zuciyarka, Bashir komai da ka rasa a baya, Allah zai mayar maka da shi cikin alheri.”ya jinjina kai kawai, ya kasa magana. Idanunsa sun cika da hawaye da bai so su zubo ba da suka shiga tsakiyar ƙauyen, yara suka fara bin motocin suna ta dariya da ihu. matasa suna tsaye suna ɗaukar hotuna, wasu kuma suna ta kallon wannan shigar da ba a taɓa gani ba a cikin ƙauyen.
Daga nesa, wani tsoho mai farin gemu ya fito daga ɗan ƙaramin gida yana rarrafe da sanda. Kallon motar farko yayi sosai kafin ya furta cikin murya mai rawar sanyi:
“Subhanallah... wannan kam irin wannan rana bata taɓa zo ƙauyen Rimi ba.” a wannan lokacin, Daddy ya ba da umarni, motoci suka tsaya. Ƴan sanda suka zagaye wajen, sannan aka buɗe ƙofar motar da Bashir yake ciki.
yana sauka, iska mai sanyi ta buga masa a fuska, zuciyarsa ta fara bugu da ƙarfi. Kallon ƙauyen yayi da idanu masu ɗauke da hawaye ganuwar ƙasa, bishiyoyi, da ƙofar tsohon gida da ya fara gane ta a hankali.


Mommy ta fita a hankali tana kallon yadda kowa ke rufe baki cikin mamaki. Sai dai Bashir ya tsaya cak, idonsa ya tsaya a kan wani dattijo da yake kusa da wani tsohon gida —
murya ce ta fito daga bakinsa cikin rawar murya:" Babaa"


Dukkan su suka kalli inda yake kallo. Dattijon ya tsaya shiru, yana ƙoƙarin gane muryar. Sai da ya kalli Bashir sosai kafin ya furta da hawaye suna gangarowa “Kai… kai ne Bashir ɗana?!” a hankali suka nufi juna, duniya ta yi musu kamar ta tsaya cak
“Baba… kai ne?”
Dattijon ya ɗago a hankali, idonsa ya tsaya kan Bashir — kyakkyawan saurayi cikin kaya masu tsada, takalminsa ƙirar Louis Vuitton, ƙamshin turarensa yana ratsawa har cikin hancinsa sai Bashir ya matsa dafff, ya durƙusa a gabansa, ya dafa kafaɗarsa cikin rawar hannu da hawaye “Baba… kaine ka dawo haka? me ya sameka? me yasa rayuwa ta juyar da kai haka?”






Kamar a mafarki, Mallam Audu ya tsaya kallonsa da ido mai girgiza, kamar yana son musanta abin da ke gabansa. Sai dai lokacin da ya ji muryar Bashir — muryar da take kama da ta yaron da ya kore daga gida shekaru da suka shuɗe, muryar da ta yi masa barazana da zafin tarihi — sai numfashinsa ya tsaya.


Sandar da yake riƙe da ita ta sulale daga hannunsa ta faɗi ƙasa da ƙarar wargasss!
Idonsa ya faɗa da tsoro da girgiza, jikinsa yana rawa sai ya ja baya da ƙyar yana ƙoƙarin fitar da kalma “Wannan... wannan muryar… ba zai yiwu ba…”Hawaye suka gangaro daga idon Bashir, yana dubansa cikin tausayi da ƙauna:
“Baba... ni ne… Bashir ɗanka ne… wanda ka kori da hannunka...”


Kamar wanda aka jefa cikin wutar zafi, Mallam Audu ya dafe kirji yana kakkarwa. Wani irin zafi ne ya mamaye zuciyarsa — zafin nadama, zafin tarihin da ya shafe shekaru yana ƙoƙarin mantawa da shi.
Sai kawai ya furta da murya mai rawa, kafin idonsa su cika da hawayen da ba su da ƙarewa “Yaron da… na kora kamar kare Allahu Akbar!”


Sai ya zube ƙasa, sandar sa ta narke a gefe, ƙauyen ya ɗauki ihu.
Mommy ta ruga da gudu ta riƙe Bashir, Khady ta kame bakinta da kuka, yayin da Daddy ya tsaya a gefe yana kallon abin da ya faru kamar a fim Bashir ya durƙusa da kuka, yana dafa tsohon da ya faɗi “Baba, ka tashi..."


Sai dai Mallam Audu ya riga ya sulale cikin rashin kuzari, idonsa a buɗe, yana kallon sama kamar yana neman gafarar da bai samu ba shekaru da suka shuɗe…


""""""$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$"""""""






Rayyan ya shiga gidan uncle ɗinsa, zuciyarsa cike da mamaki da ɗan tsoro. Falo ya yi girma fiye da tunaninsa; labulen zinariya suna shafa ƙasa, fitilu masu haske kamar tauraruwa na sheƙaɗa kowane kusurwa. A gefe, Raizah, yarinya tilo mai shekaru goma sha ɗaya, tana wasa cikin lambu mai ciyayi kore-kore, murmushi a fuskarta yana kama da haske mai ɗaukar ido. Uncle ɗinsa ya rungume shi da hannu mai ƙarfi, ƙamshi na turare mai daɗi ya lullube dakin, yana cewa:
“Yaron nan, yanzu rayuwarka zata sauya. Ka gama wahala, yanzu lokaci ne ka fara jin daɗin abin da Allah Ya tanada maka.”
Rayyan ya ji wani ƙarfi na natsuwa ya lullube zuciyarsa, amma har yanzu fargaba da mamaki na cikin sa. Duk da alatu da kayan alatu, zuciyarsa tana tuna wahalar baya. Amma ganin Raizah, murmushi a fuskarta, da yadda take kallon sa da ƙauna, sai wani ɗan shauqi mai sanyi ya shiga zuciyarsa.


An shirya masa ɗaki mai fadi, gado mai laushi da auduga mai tsabta, taga tana kallon birnin Dubai mai haske da dare. Kowane dare zai zauna a dakin karatu, yana tunanin yadda zai fara karatu cikin ƙwarewa da natsuwa, da yadda zai zama mutum mai ƙarfi da hikima a rayuwa.


Raizah ta zama wani ɓangare na sabuwar rayuwarsa. Kallo daya kawai daga gare ta, sai zuciyarsa ta tsinke da wani irin jin daɗi, kamar ya dawo gida bayan dogon lokaci. Amma duk da sabuwar rayuwa, Rayyan bai manta da azabar baya ba — waɗanda yanzu za su zama ƙarfi da himma a sabon fara rayuwarsa.
A hankali, murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya faɗi:
“Wannan shi ne farkon rayuwata. Zuciyata zata shigo cikin sabuwar duniya, kuma babu wanda zai iya tsayar da ni.”








Rayyan ya juya kallon Raizah, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Kyakkyawar fuskar ta, idanuwanta masu sheƙaƙe, da murmushinta mai laushi sun lullube zuciyarsa cikin wani irin shaukin da bai taɓa ji ba.
Raizah kuwa, tana kallon shi da ƙauna da fahimtar juna, ta ji wani ɗanɗano na soyayya mai laushi a zuciyarta, kamar ranar farko da duniya ta bayyana mata da haske. A hankali ta matso kusa da shi, hannayenta sun haɗu da na Rayyan, kuma kallo ya zama kamar harafin zuciya da ke bayyana komai da ba a faɗa ba.


Rayyan ya ɗan ja numfashi, ya ji dumin Raizah yana shiga zuciyarsa. A hankali ya ƙara matsawa, har idanun su suka haɗu, sai zuciyoyinsu suka yi magana fiye da dukkan kalmomi. A wannan lokaci, duk abin da ya faru a baya — wahala, azaba, rashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login