Showing 6001 words to 9000 words out of 40625 words
Chapter 3 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt
gilashi ta tsaya a gefen dajin sai wasu mutane uku masu sanye da baƙin kaya, suka fito, fuskar su a rufe da baƙin mayafi suka tsaya a bakin kogin, ɗaya daga cikinsu ya kalli cikin kogin sannan ya ɗaga waya:
Yallaɓai mun kammala aikin mun kawar da ita da abin cikin ta ko gawar ta baza a tsinta ba."
sai suka koma motarsu suka bar wuri cikin gaggawa, yayin da kogin ke ci gaba da kwarara da sirrin da yake ɗauke da shi…
( Amma a cikin ruwan kogin akwai tsarkakken jariri wanda Allah ya tanada masa tsira zai rayu, ko da kuwa ba a san yadda ba tukuna. Wannan shine Kaɗangaren Sarauta – wanda ba ruwa, ba bindiga, ba makircin duniya zai iya hana sa bayyanar da ƙaddararsa. )
Tsssshhhhh...
Karar ruwan teku yana bugawa da ƙaƙƙarfan dutse a bakin wani tsibiri da ba a tasamma — babu kowa a kusa, sai tsuntsaye masu fari da baki suna shawagi sama, suna kururuwa tamkar suna shaida wani sirrin da duniya ba ta sani ba.
A can cikin kwarin kogin, wata mata mai ciki ta farka daga dogon suma, ta gaji, jiki ƙalau. sai ta buɗe idonta da ƙyar, tana kallon rana mai taɓa gashinta mai danshi jiki na rawa, ta fara motsi, tana jin zafin ciki da naƙuda.
A lokacin da numfashinta ke yin nauyi kamar zata shude, sai kawai aka fara hango tsohuwar mata mai farar kaya tana karasowa daga cikin ƙasar tsibirin. Fuskarta cike da natsuwa, kamar ba ta da tarihin duniya, kamar kuwa aljana ce ta bakin ruwa, annuri ya lullube ta.
Ta ƙarasa wajen matar da ke buƙatar taimako, ta durƙusa, ta ce da ita "ki zauna... kar ki tsorata. Allah na tare da ke. Lokacin haihuwa ya yi, kuma wannan ɗa ba zubin azzalumai bane — jarumin ƙasa ne da murya mai ƙarfi."
Cikin hanzari da tausayi, tsohuwar ta taimaka mata – sai aka ji kuka... kuka mai ƙarfi, wanda ya sa tsuntsaye suka firfito daga duk inda suka buya. Jaririn da aka haifa namiji ne – mai cikakken lafiya da farin fata, kamar haske a cikin duhu sai matar ta ɗaga shi sama – hawayen farin ciki a idonta, jikinta rawa, jini yana ƙara zuba daga kafarta, ta ce:
"Na haifu KAƊANGAREN BAKIN TULU! Ko ana so ko ba a so… watarana zaka tsaya cikin alfahari ka hana zalunci da murya ka."
"Ina fatan ka zama cikakken ɗan jarida – ka daga muryarka a gaban duniya da masarautar ku, har kogin ya rabe biyu daga ƙarfinka. Ka zama farin cikin masu shiru da mafitar masu rauni."
Sai ta lumshe ido, ta miƙa jaririn ga tsohuwar, sannan ta faɗi – numfashinta na ƙarshe. Ruwa ya tsaya kamar yana girmama jarumar da ta kawo ɗan ƙasa duniyarta.
Tsohuwar ta ɗaga sa sama cikin kururuwa ta tace na saka maka suna SUHAYL yakai bil adama ta shige da jaririn ciki tsibiri… ba a ƙara ganinta ba
🌊 KAƊANGAREN TSIBIRI / SARAUTA
Suna: Suhayl
Ma’ana: Tauraro mai haske daga cikin duhu
Halinsa: Rayuwarsa cike da asiri da wahala. An haife shi a bakin kogi, mahaifiyarsa ta faɗa ruwa bayan an harbe ta. Zai zama ɗan jarida mai zamewa murya ga marasa murya, kuma zai tunkari masarauta da kalmar gaskiya.
Shin ya kuke tunanin rayuwar sa zai kasance tsakanin aljannu da namun daji ..
shin burin mahaifiyar sa zai cika?
shin waye shi ?
me asalin labarin jinin sa ?
Ina muku barka da juma'a
08101235739
🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️
PAGE SIX
300 only
FREE PAGE
08101235739
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
PAGE SIX 6
( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕).
Happy birthday 🎉 to my lovely big brother Allah ya ƙara shekaru masu albarka da amfani more more money in ur bank account.. 25 august..
GARGAƊI
Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba ,
GAISUWA
Gaisuwa na musamman ga masoyyiya ta a bar alhafari ba sister Habiba Ubangiji na tare dake a dukkanin motsin ke da shirun ke..
KANO
A cikin ƙasar Kano, a gindin duwatsu masu launin toka, a bakin goggin da ke fitar da iska mai sa sanyi ta huci da dare, akwai ƙauye da lokaci ya ci—amma bai jefar da mutanensa ba.
Sunansa: Gidan Rini.
Ƙauyen da gwamnati ta manta da shi, da bishiyoyi suka maye gurbin gine-gine, da rijiya ce kaɗai ke zama asibiti, da masallaci ya zama gindin bishiya. A nan ne ake haifar rayuka da ake kawar da su kafin su futo duniya gaba ɗaya.
Mallam Sambo ya kura musu ido. Bai ce komai ba. Sai kawai ya rungumi jaririn da ƙarfi kamar yana kare masa duniyar da ta riga ta bijiro da masa da zafi.
Zan baka suna Bashir domin ka kasance mai bushara a wanan rayuwar muna godiya ga likita Bashir da ya fito dakai wanan duniyar da taimakon Ubangijin Halitta,, nan Baaaba ta juya da bakin ciki da takaice da sasaqesaqeen abinda zuciyar ta ke gayama ta akan wanan yaron da ta so kashewa tun a cikin mahaifiyar sa .
Nan Inna ma ta kama hanyar ta kai tsaye sai wani ruɓaɓen Police station nasu wanda bashi da bambanci da kasuwa mai ɗakunan mashaya da ƴan chacha da zuwan ta taga Audu zaune yana cin kurasa da ganin ta ya miƙi " Inna me ya faru a asibitin" hararra ta buga mai da cewa " ita wanchan ta mutu Amman ta bar yaro mai ban mamaki kamar ba kaine uban sa ba jajajjur dashi kamar uwar sa " nan wani mai uniform na ƴan sanda yazo yace Yaya mekekeso goron bakin ta ta zubar a kusa dashi " to Mallam ɗan sanda abinda aka saba shine yanzu ma ka gayyamin nawa zamu baka ka kashe wanan maganar dukkan ta kawai yayi Amman bai kashe ta ba lokacin ta ne yayi " girgiza kan sa yayi yasan hakan zai faru daman nan yaja tumbin sa da ya zaxzzago yana waige waige ya matsu kusa da kunnen ya " ke kawo dubu goma yanzu sai ku tafe gida " zaro ido taye waje Amman kaima ka fara shaye shaye ko to ko sata zanyi ai banga wanan uban kuɗin ba ". tsaki yaja " kedai anyi tsohuwar banza yaron ke yayi kissan kai zamu rufa masa asiri kicce wai bazaki iya ba to zan kira shugaban mu nawan nan qara mar hukuman....................kai malam dan sanda kai meya sa baka iya magana haka ba karufa min asiri duk inda zan shiga zan fita zan nemo maka dubu goma don ka sake min yarona don shi kadai na mallaka malam audu bawa ni bayan shi duk duniyan nan......................."
Cikin azama da gaggawa ta fita tana azama ta zazzago akuyar gidan su tayi wojen malam jauro har tintub be takeyi yi tana qwala kira hakan yasa Malam Jauro ya fito da ga bukkar bayan gida daga jin Salaman Inna yasan me ya kawo ta, " kai Jauro muyi ciniki nawa zaka seya haba innar audu ko gaisuwa babu abu ne na gaggawa ya tashi.............sai yace ya maganar gawan kultume an dawo da ita duk cikina na ciwo na dawo gida,? kaga Jauro ba wannan ya kawo ni ba na kawo maka akuyar sayarwa ne kaban dubu goma ko rance ne ka aramin ga akuyar nan " yace to Allah ya kyauta" ..................bai jima da shiga ba yafito da ɗan kuɗaɗen sa bayan ya rataya akuyar cikin tumakin sa
*************
A guje ta shigo police station in ko sallama babo takalmin ta a hannu sai dogon hali takiyin cikin azama Mallam ɗan sanda ya fara lashe baki ganin ta dawo da wuri don tabbas yau akwai dabkee a gidan sa .. tana bashi wanan kudin ya ɗirgasu tsafff sun cimma dubu goma nan aka fitar da Mallam Audu
Bayan dawowarsa gida a cikin damuwa da bakin cikim haihuwar Kaltume " akan wanan yaron aka rufe ne a police station don kutumar " ..... kafin ya gama sai ga sallama liman a kofar gida cewa a fito da gawar Kaltume domin a mata wanka da sutura akai ta makwancin ta haka ya kasance Mallam Sambo yayi jagora a inda aka nema Audu aka rasa shi mutane nata tsigume a ƙauye cewar matar sa ta mutu a sanadin sa kuma bai sallar gawar ta ba balle ya Kaita kabarin ta ..
🌾 KAƊANGAREN ƘAUYE
Suna: Bashir
Ma’ana: Mai bishara, mai kawo haske
Halinsa: Jarumi ne mai dogon juriya. Rayuwarsa cike da gwagwarmaya, amma yana da zuciyar son gaskiya da kare talaka.
Wanan kinan ..
ABUJA
Kallon da yayi wa Zulaihah kamar ya fi kisa:
“Ina matata?! Ina Maijidda?!”
Ummee ta miƙa jariran biyu da hawaye, ta ce:
Ta haihu biyu ita kuma ta mutu cikin azaba
Minista ya ɗauki numfashi da ɓacin rai — sannan ya juya.
Shigowar Zulaihahr cikin dakin ta ta rufe windows nata zuciyar ta sai bugawa yakiye akai akai ta daura hannun ta akan ta "Wayooo Allah na na mutu na lallace nayi kissar sauran ƙirris a kaine gidan Yari na shiga ukku ya zanyi " firgitt ta tashe ta buɗe wardrop nata nan ta zaro wani ƙaramin akwati ta fito da wani abu da aka zagaye da jan ƙyale tashi tsaye taye ta kashe hasken ɗakin gaba daya ta fito da wanan abun tama ɗagawa sama sai ga madubi ya bayyana a cikin sa nan ta ajiye yana kallon kudu ta shaffa da hannun ta guda biyu , akai ta fara wasu sambatu da ba'a ganewa kwatsam sai dakin ta fara girgiza kamar za'ayi ruwan sama " hhhhhhhhhhhhhhh wani murya mai amo da ƙaraji ya ƙauraye ɗakin da wani sautin mara daɗi. sauraro man madubin yayi duhu ita kanta ta tsira matukar gaske nan zufa ta fara kwatanta daga kanta har izuwa tafin kafuffunta .......
"Kinye saki kinye gaggawa kina bachi domin an haifo KAƊANGAREN BAKIN TULU alƙawarin Ubangiji ya cika tabbas bazaki iya komai ba " ya faɗa cikin sarƙaƙiyar Muryar sa mara sa daɗi.. cikin hawaye tana na shiga ukku na lallace me za ayi ka taimake ne banson Yaron nan ya rayu a doron duniya " dariya ya sake ƙyalƙyalewa dashi Yana cewa alƙalamin ya bushe KAƊANGAREN ya fitoo sai dai ita maccen zamu iya kashe ta kafin akaita asibitin Amman wanan yaron bamu isa mu taɓa shi ba " nan ta durgusa taye wani ihu mai bakin ciki yanzu ne za'ayi ka nunamin hanya kaine Ubangiji na ....
" Ka duba min kar asiri na ya tuno akaine gidan yari "..Babo wanda zai ye maganar mutuwar ta kowa zai manta da asalin mutuwar ta Amman da sharaɗin cewa dole watarana zamu tambayi ke ladar aikin mu cikin gaggawa tace ta yarda kafin ya saurarre abinda zaice nan ya Kuma da dariya ya ɓace ɓatttt
Isowar sa asibiti da yara biyu har na maccen ta mutu nan aka sata a kwali saiga hawaye a idon sa ya share ya ɗaga yaron yana mai cewa " nayi maka suna Rayyan Ubangiji Allah ya kare min kai a gaban ido na da bayan numfashi na Allah ya daukaka darajar ka ya sanya sallama a cikin zuciyar ka da juriya da haƙurin rayuwa da zaka fuskanta ina sonka domin Allah .kuma Allah ya jiƙan mahaifiyar ka RAYYAN
🌆 KAƊANGAREN BIRNI
Suna: Rayyan
Ma’ana: Kyakkyawa kuma mai albarka
Halinsa: Ya taso cikin duhun wulaƙanci da cin zarafin uwar sa, amma ya zama jarumi mai ɗokin kare 'yancin mata da yara. Hankali da ilimi ne makaman sa.
Narnah ƙanwar soja ✍️✍️✍️
🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
Follow my Wattsp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️
PAGE 7
300 only
FREE PAGE
08101235739
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
PAGE 7
( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕).
GARGAƊI
Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba ,
GAISUWA
Gaisuwa na musamman ga masoyyiya ta a bar alhafari na sister Habiba Ubangiji na tare dake a dukkanin motsin ke da shirun ke..
SUMMARY
🌾 KAƊANGAREN ƘAUYE
Suna: Bashir
Ma’ana: Mai bishara, mai kawo haske
Halinsa: Jarumi ne mai dogon juriya. Rayuwarsa cike da gwagwarmaya, amma yana da zuciyar son gaskiya da kare talaka.
Shine yaron da baban sa yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar sa ta hanyar duka da zuba mata ruwan talken towo sanan aka so a kashe she sai dai Allah ya nufa sai yazo duniya .
Shin ya rayuwar Bashir zai kasance a wanan ƙauyen da uƙubar cikin gidan su?
🌊 KAƊANGAREN TSIBIRI
Suna: Suhayl
Ma’ana: Tauraro mai haske daga cikin duhu
Halinsa: Rayuwarsa cike da asiri da wahala. An haife shi a bakin kogi, mahaifiyarsa ta faɗa ruwa bayan an harbe ta. Zai zama ɗan jarida mai zamewa murya ga marasa murya, kuma zai tunkari masarauta da kalmar gaskiya.
🌆 KAƊANGAREN BIRNI
Suna: Rayyan
Ma’ana: Kyakkyawa kuma mai albarka
Halinsa: Ya taso cikin duhun wulaƙanci da cin zarafin uwar sa, amma ya zama jarumi mai ɗokin kare 'yancin mata da yara. Hankali da ilimi ne makaman sa.
Ya rayuwar sa zata kasance a cikin gidan da Hajiya Zulaihah take zuba capacity?
Wanan ba dogon tunani ko nazari bane labarin ne na jarumai guda ukku wanda akaso a hallaka tun suna cikin mahaifiyar su sai dai sun zama KAƊANGAREN BAKIN TULU a barsu su lallata ruwan ciki . a kore su a fasa tulu
ko biyo ne ku chigaba da kasance wa da wanan ƙaramar marubuchiyar domin shiga cikin sabon chakwakiya da tunani mai zurfin gaske Amman wanan tafiya ta sauya salon domin wanan littafin anan zai dakata sai wanda suka biya 300 su ne zasu chigaba da samun update akan update ta private nasu . shin ka shirya ? ko kin shirya shiga cikin asalin labarin
08101235739
kai tsaye a wanan number amin magana
ina godiya mai tarin yawa
*Littattafan da Narnah Kanwar Soja ta rubuta:*
*✓ An kammala su:*
1. *Duhu Cikin Haske*
*Labari mai taɓa zuciya kan soyayya, iyali, da dangantaka.*
2. *Bayan Wata*
*Tarihin abokai da suka fuskanci ƙalubale a wata tafiya mai cike da ƙarfi da bege.*
3. *Farashin So*
*Gajeren labari na soyayya, ɓacin rai, da raɗaɗin zuciya.*
4. *Mijin Mage*
*Labarin soyayya da rikice-rikicen iyali wanda ke jan hankalin mai karatu.*
5. *Rayuwar Ummah*
*Labari mai taƙaitaccen bayani kan sadaukarwa, iyali, da juriyar rayuwa.*
6. *Biyayya Ga Uwa*