Showing 1 words to 3000 words out of 40625 words

Chapter 1 - KADANGAREN BAKIN TULU COMPLETE BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

24 Oct 2025

365

https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC










YouTube channel domin samun littattafai na Hausa don't forget please like and subscribe , Thank you.
https://youtu.be/6-Jrkc2kmmE






FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI


08101235739
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️




PAGE ONE


Ƙarar ruwan sama ya ƙara karfi. Gajimare sun cika sararin gidan, kamar sama na kukan wata muguwar saƙo da duniya ta ƙi karɓa ana iya jin ƙaramin igiyar ruwan da ke gangarowa ta sama — amma abin da yafi damun mutum ba ruwan sama bane — azaba ce, da kuma ɓacin rai da ake sakawa a matsayin “tarbiyya.”


KALTUME ta durƙusa gindin murhu, hannu na famar busa wuta, idanunta cike da hawayen da basu da alaƙa da ƙanshin hayaki. Ita da kanta ba ta san me ya fi nauyi ba: yunwar da ke jikinta ko ciwon zuciyar da ke cike da ƙiyayya busa wutar takiye bakin ta da hannun ta iya ƙarfin da Allah ya bata ganin lokacin dawowar Malam ya kawo kai ga talken towo akan wuta ga rashin isasshen wutar .




Ƙara hura iskar bakinta taye akasar murhur a banza, kanta ta ƙara ɗagowa sama, ganin gagarumin haɗarin yana ƙara haɓɓaka. Take hawaye suka malallo kan kyakkyawar fuskar nata, ƙara durƙusawa taye da gaske, ganin ta ƙara himma gun zuga wutar ittacen, ko zai kammala kafin Mallam Audu ya dawo daga gona...


Dariya da shewa daga bayanta, a hankali Kaltume ta juyo tana ganin Baaba dake tsaye da buta zuwa bayingida ( toilet ) ta ƙara da cewa, "Ye dai mugani, ko tusa zai hura wuta?" Ta shiga ƙaramin bayangida dake maƙale a barandar da ake kewo akuya — ko nace akuyoyyin gidan.


Kaltume ba ta tsaya binta da kallo ba, ta ci gaba da duba wutar girken ta, har lokacin da Baaba ta fito tana ɗaga butar sama da niyyar ta watsa mata ruwa a murhur da take famar ganin yana aiki. Aikuwa, taye nasarar, zuba mata ruwan taye ya watse akan ittacen.


Kaltume ba ta san lokacin da ta runtuma ihu mai kama da kuka ba, ganin wutar ta mutu murguz, kamar ba ta ye wahalar awwani a ƙasar ittacen ba kafin ta buɗe baki taye magana, sai ga ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya nan da nan. Hawayen da ruwan suka mamaye fuskar ta cikin azaba.
Ta fara ƙoƙarin mikewa daga durgushen, sai dai kash guiwarta bai amince ba, sakamakon wane azaba da ƙafar take mata tumbin nata ta ƙara himma gun tashi, ga talken masarar yana huce, gaba ɗaya ruwan sama ya shigi ciki, ya zama kunu sai zubewa yakiye inda Baaba ta barta tana dariyar mugunta.




Ba zato ko tsammani Kaltume ta tsinci kanta a mugun yanayi, ihu kawai ta yi, tana neman taimako "Har yanzu bakiye hankali ba! Ashe mahaukaciyar! Ina ce ke abincin nawa ke zuba a ƙasa? Wawiya karuwar banza!"


Yana duka, yana ihu da surutu a ihun neman ceto, duk suka fito daga dakunan su ba wanda ya je balle ya karɓe ta daga azabtar da yake mata.


"Kaltume, nasha wahalar noma, na kawo abinci ki ci! kiye kashi shine za ki min asarar tukunya gida!"yar da sandar hannunsa yayi, ya ɗauko tukunyar, ya kwara mata a jikin ta.


Inda taye sauri kifewa domin ta kare cikin ta daga azabar wuta, duk da cewa ruwan sama yasa ya huce, amma har yanzu akai bala’e zafi wanda yayi sillar tarwatsewar dukkan jiyoyin jikinta. Ihu ta buga don wani bakin azabar da ya shiga sassan jikinta...












Kamar yadda zai dinga karɓan tuwo daga tulu, haka ya ɗauki sanda ya dinga zuba mata da sukar magana "Wawiya! Ashe ke har yanzu baki yi hankali ba! Abinci nawa kike zubarwa wai ke wacce irin sakaryar ce mata hankali da gumi na kike wasa don ubanki ?"






Inna ce ta ga abun ya wuce misali, ganin azaba da wuta, da sauri ta baro nata guntun ɗakin taɓon ta iso tana faman janye sa da cewa:
"Kai Audu, zakaye kisan kai! Shikkinan ka kashe ta!"


Ganin lallai Kaltume bata numfashi sai yanzu ya lura da mugun ɓarna da yakiye, ganin fatar jikinta na suɓukewa daga ruɓaɓɓon kayan ta...


"Ke Ma’u tahu nan!" ta faɗi tana kallon Baaba da take zabga murmushinta hankali kwance.


"Allah yasa shegiyar ta mutu na huta da ganin baƙinciki."










Wutar murhun da ya dade yana so ya hura ya hana fitowa daga hanyar jikin sa. Kaltume ba ta da iko — jikinta ya saki. Amma zuciyarta tana kuka, tana kuka da Allah... "Ka bar ɗana ya rayu kayi masa jagora... ka sa kada ya zama kamar ni wallahi bada niyya na aikata ba ."
zuba mata ido a makance ihu ta buga " Nashiga Ukku uwata na tuba Allah ka gafarta min , cikin ihun azaba ta yanke. numfashi rayuwa ta ɗauke babu kukan da ya isa ya hana mutuwa.
Babu idon da ya isa ya ɗaga murya kowa shiru Sai ihu.
Ihu daga ciki... ihu daga sabuwar rai da ke ƙoƙarin shigowa duniya...Kai Audu, kamata muyi ɗaki da ita, suna ƙoƙarin ɗaukar ta, sai ga kan jariri na ƙoƙarin fitowa daga cikin mahaifiyar sa da sauri suka ƙarasa da ita ciki. Duk sun yi cirko-cirko suna ganin haihuwar Kaltume da bata numfashi, amma ga yunkurin haihuwa.


Tun suna ƙoƙarin tayar da ita, amma Kaltume rai yayi halin sa ba alamar numfashi a jikin ta. Inna ce ta fita zuwa maƙobtan su har ruwan sama ya ɗauke, ba alamar fitowar yaro ga kai ya maƙale.


Ganin ba kowa a ɗakin, Baaba ta juya gabas da yamma, hannu tasa ta tura kan yaro da ƙarfin tsiya masifa don ya kuma cikin mahaifiyar sa dake kwance a matsayin gawa mai tururren wutar talken tuwo...


Cikin hanzari, Inna ta shigo da maƙobtan su ihu Sallame ta tsala:


"Kaltume ta mutu, waiyoo! Allah na mutu, na lallace, shikkinan sun kashe ta, sun yi kisan kai!"


Haka ta fita bakin zauren gidan tana tsalalla ihu da wanda suka hallara da masu hallara abin da ya ɗaurewa Inna kai. Ganin yaron ya kuma ciki da kallon tuhuma, ta nufi Baaba da sauri ta antayo idon ta waje:


"Na rantse miki Inna, ban yi komai ba. Asali ma na fita don ina tsoron gawa..."


Inna ce ta fito daga sunkuye tana hango tillon ɗanta Audu da ya zabga uban tugumi cikin tsoro da fargabar abin da zai iya faruwa a gaba. Da sauri ya matso kusa da Inna:


"Ina fatan bata mutu ba..."


Cikin murya mai amo da ƙaraji daga bayan sa:


Is just a beginning











gaisuwa ta musamman ga Sister Ummi Nagode sosai Allah ya saka da alheri Allah ya biya da gidan Aljanna , Allah ya sauke ke lafiya ,


HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA
Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. Ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya...**


Itta baiwa daga Allah ce, Ubangiji ke bada itta ga wanda ya so. Duk wanda aka ba wa itta, sai ya sarrafa ta yadda ya ƙi so: wani ta jawo masa arziki, wani kuma ta janyo masa ɗaukaka da masoya masu girma da daraja...






PAGE 1
Paid book 300 only , posting daga Monday zuwa Friday in Sha Allah
08101235739
FREE PAGE





NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️







https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC?mode=ac_t









YouTube channel domin samun littattafai na Hausa don't forget please like and subscribe , Thank you.
https://youtu.be/6-Jrkc2kmmE






FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI


08101235739
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️








PAGE 2


“You are under arrest, Audu Dogoro!”


Juyowa yayi a tsoraci, jin yaren Turawa ta ki hanjin cikin sa suka murɗa, zubewa yayi a ƙasan. Ɗan sandan yafara bigima da rantse-rantse...




Cikin firgici da tashin hankali wasu ƙoƴaƴyun 'yan sanda suka shigo gidan, sun zo bisa kiran gaggawa da maƙwabcin su Mallam Sambo ya yi, wanda tun farko yake leƙen halin da ake ciki daga katagangarsa


Ganin halin da Kaltume ke ciki da kuma faɗuwar jikin Mallam Audu a kasa yana birgima cikin ruwa da ƙasa yasa ɗayan 'yan sandan ya ɗaga murya cikin ƙarfi:


“Nobody moves! kai, Malam Audu Dogaro, ka tashi mu tafi!”


Audu, cikin fargaba da rawar baki, ya fara birgima yana cewa:
“Don Allah malam 'dan sanda kuyi hakuri! Wallahi ba ni na kashe ta ba! Allah na sani, wallahi ba da gangan ba! Tukunyar ce kawai ta zube... ni dai ban kashe ta ba!”






Cikin ƙarya da ruɗu ya fara zubo rantsuwa, yana yunƙurin kare kansa daga halin da ya jefa kansa ciki. Ya koma yana yi wa kansa kuka, yana nannade hannayensa yana roƙon gafara.


Maƙobtan sun cika harabar gidan, wasu suna hawaye, wasu suna siffanta ta da kalmomin alhini. Mallam Sambo kuwa ya kura masa ido yana huci kamar wuta , anan wasu ke furta mugayen abubuwan da yake wa Kaltume
“Wannan fa ba da wasa bane,” inji ɗaya daga cikin 'yan sandan cikin takaici. “A jikin mace da ciki kayi haka? Wannan fa laifi ne mai girma, kisan kai da yunkurin kashe jariri!”






Baaba kuwa tana gefe, tana ƙoƙarin ɓoye dariyar mugunta a fuska. Amma Inna ta kura mata ido tana tafe da gumi, tana ayyana yanda komai zai ƙare.


Sai kawai aka ɗaure Mallam Audu da ankwa, aka ja shi zuwa motar 'yan sanda cikin sarkakiya. Mutane na zagin sa, wasu kuma suna kallon shi da tausayi, amma da yawa daga cikin su sun fi yarda cewa akwai wani abu a ciki – ba rashin sa'a kawai ba ne.




Baaba ta tsaya cak! Idanunta sun kafeshi ana ja da shi cikin ankwa, zuciyarta na huci kamar wuta da aka watsawa fetur.
“Wayyo Audu! Audu na! Me kuka masa?! Wannan ba gaskiya bane wallahi! Ba zai iya kashe mace ba! Wayyo duniya ta bani!”






Ta kwalla ƙara, ta zube a ƙasa ta dafe kai, numfashinta na hauhawa. Idanunta suka cika da hawaye, amma zuciyarta cike take da rudani da wata irin firgici da ba ta taɓa ji ba.


Cikin wannan rikicin, sai kawai Inna ta rikice. Ta lumshe ido, jikin ta ya yi sanyi kamar daskararre.
“Subhanallah!”
Ta faɗi a ƙasa tamkar sanda aka sare itace. Kamar ba rai a jikinta. Hankalin kowa ya tashi! Maƙobtan suka nufo da gudu.
“Ku kawo ruwa! Ku ɗaga kafafunta!”
“Ina mai zare mata mayafi? Tana numfashi?”
Wani dattijo ya sa hannu a ƙirjinta yana duba bugun zuciyarta.
“Alhamdulillah tana numfashi... amma zuciyarta na bugawa kamar ana kara mata wuta.”






Wasu suka ce a kaita asibiti, wasu kuma suka tsaya suna ambato. Maƙobtan sun firgita, gidansu Audu ya koma gidan tashin hankali. Yara suna kuka, mata suna salati, maza kuma sun rude.


Wani dattijo daga cikin su ya tsaya yana kallon su yana girgiza kai:
“Wannan fa ba ƙaramin al’amari bane. Gidan nan ya haukace. Wannan ba ƙaramin sharrin aure bane , ina gawar Kaltume a Kaita asibitin ƙauye ko za'a samu damar ceton yaron cikin ta cewar wani ɗam cooper ”










Kamar hadari su Inna da Baaba suka runtuma da ƙafa suna bin Malam Sambo da wanan cooper min , sai maƙobta su ka biyo su da hawaye da addu’a. Har wasu daga cikin matan ƙauyen suka ɗauki jariran su, suna kuka da sambatu.


Asibitin ƙauyen—wani tsohon gini ne da GOVNATI ta manta da shi. Bangon sa ya faɗi gefe, ɗakin haihuwa kuwa yana da bargo na tantanin sauro a maimakon labule. Kujerun dakin jiran gwaji duk sun karya, sai murɗaƙƙen jini a kafet da iska mai wari. Duk da haka, shi ne asibitin da suke da shi.


A nan Malam Sambo ya shigo da babur ɗinsa, yana ihu:
“Ku taimaka! Ku ceci ta! zai mutu! Jariri yana fitowa!”
Wata nurse – mai dogon hanci da rashin jinkai – ta fito da leda a hannu, ta dubi Kaltume daga gefe:
“Kai... ashe wannan ce?! Waye ya ce a haifi a gida? Ta yi rajista kuwa?”






Malam Sambo na haki kamar wanda zai faɗi:
“Bani da rajista! Ku karɓe ta da gaggawa... wallahi ta mutu Amman yaron na motsi !”






Sai wani dattijo malamin lafiya ya fito daga wani daki, yana watsa idanu da kausasa murya: “Mun gaji da wannan halin! Duk da gwamnati bata ba mu albashi ba, har yanzu ku zo da matan ku cikin jini, babu kati, babu kudi, babu rajista. Ku na so mu yi aiki da soyayya ne?!”


Inna ta faɗi a ƙasa tana kuka:
“Don Allah... mu talakawa ne. Katin ba mu da shi, amma ku taimaka. Ku ceci 'yata da jaririnta. Ta riga ta shure... amma ba a gama ba...”
Nurse ɗin ta girgiza kai tana faɗa:
“Wani likita ba zai taɓa tabawa ba idan ba katin haihuwa. Ko a ƙarƙashin bishiya ne aka haife ta. Wannan ba matsalar mu bace.”






Yayin da su ke ta masifa, wata karamar ma’aikaciyar asibiti – mai sauƙin hali – ta leƙo, ta ga halin da Kaltume ke ciki. Sai ta fasa tsawa:
“Koma menene, wannan jariri yana cikin rai! Idan kuka bari ya mutu, kun kashe shi da gangan! Bari in kira Likita Bashir. Wallahi, na shiga tsakani.”
Ta nufi ɗaki da gudu.


Yanzu dakin asibitin cike da mutane ne. Muryoyi sun rikice. Wasu na kuka, wasu na masifa. Malam Sambo yana zamewa daga jini, ya tsaya a gefe yana zubar da zufa.


Rayuka biyu ne ke rataye da ƙaramin zaren kulawa da imani.


haka wanan cooper ya shiga cikin office nin ya bashi dubu biyar da ban haƙuri domin a ceto wanan abinda yake cikin matar nan...


Is just a beginning



🦎KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎
PAGE 1
Paid book 300 only , posting daga Monday zuwa Friday in Sha Allah
08101235739
FREE PAGE





NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️












🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎
BY


NARNAH ƘANWAR SOJA








https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t








FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI


08101235739
بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️




PAGE THREE











*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️













Likita Bashir ya fito da hanzari cikin ɗamarwa, yana ta girgiza kai kamar zuciyarsa ta ƙi amincewa da abin da idonsa ke gani.
“Ina marar lafiyar take?!” ya faɗa da ƙarfin da ya ɗauki hankalin duka cikin asibitin.






Nurse ɗin da ta kira shi ta nuna wata ƙaramar ƙofa, jikinta na rawa da ɗuwatsu a ido.
" can ne, Doctor... jini ne ke ta zuba kamar an buɗe rijiya...!”ba tare da wata tattaunawa ba, sai ya ɗaga hannunsa cikin hanzari, ya umarce su da su ɗauke mata da ake fama da ita zuwa ɗaya daga cikin tsofaffin ɗakunan haihuwa ɗakin nan cike yake da wari, gadon da ke cikinsa na daure da wayoyi, ya ruɓe, ruwan rijiya yana cicciko daga gefe, yana gauraye da jinin da bai daina fita ba.


An shimfiɗa Kaltume hannayenta duk sun kumbura fuskarta fara ta kumbura kamar wacce aka ƙwace rai. Idanunta a rufe, bakinta bude kadan kamar mai neman taimako daga sama nurse biyu suka kama ƙafafunta da gaggawa suka buɗe su, yayin da Likita Bashir ya zura safar hannu, zuciyarsa cike da damuwa “mu ceci jariri... sai mu ceci wanda ba shi da laifi!” ya faɗa da huci, yana kai hannunsa cikin mahaifar Kaltume.






Sai yaron ya fara motsawa, yana kokarin fitowa daga duniyar duhu amma jinin—jinin nan yana zuba kamar an karya madatsar ruwa nurse ɗaya ta tsayar da numfashinta, tana kallo da hawaye a idonta.
“Tayi mutuwa,” wata daga cikinsu ta faɗa cikin sanyin murya mai tsanani “tayi mutuwa tun kafin a zo...”






A ƙasan gadon, jini ya wuce ƙafa. Ya gauraye da ƙura, ya kumbura kamar ruwan sama da ba’a dafa ba jikinta na laushi, ba numfashi, ba motsi qmma cikin cikinta, ga rayuwa na ƙoƙarin fito da kukan farko.
“Dokta, za a iya ceto yaron?” nurse ɗaya ta tambaya, murya na karkarwa.






Likita Bashir ya runtse idanu, ya kalli gadon da bai dace da ɗan Adam ba ya kalli Kaltume, wannan marainiyar Allah da aka saki kamar dabba a kasuwa. Sai ya ce da zuciyar da take dukan azabar gaskiya
“Zan yi iya bakin ƙoƙarina amma wannan ba haihuwa bace wannan ƙasa azaba ce, wannan haihuwa kuka ce!”






Yayi ƙwace, ya jawo jaririn da ƙarfi hannunsa yana rawa, numfashinsa yana tashi da sauri. daga nesa, aka ji kukan wani yaro mai raɗaɗi, mai rauni, mai kukan ban kwana da duniyar da bai iso ba tukuna kukansa ya sare dakin gaba ɗaya dukkansu suka tsaya cak, da hawaye, da kaɗuwa, wannan yaro ba kawai ya zo duniya ba ne... ya zo ne da ihu, da baƙin ciki, da jini mai ɗumi, ya zo ne da alhini mai nauyin dutsen dutse.


Inna ta durƙusa a ƙasa ta aza hannu a kai. wannan ba haihuwa bace – wani sabon babi ne a cikin littafin ƙaddara.


Sai wani mutum – dogo, siriri, farin fata – ya faɗo cikin ɗakin da sauri. Likita ne, amma bakinsa kamar ya cika da al’ada ya karɓi yaron yana jijjigashi, yana kallo kamar yana karanta labarinsa ta fuska yron ya yi ihu... amma bai tsagaita ba kamar yana faɗin "ni ne wanda aka kore daga jinƙai, na fito daga cikin azaba... ni ne wanda duniya ba ta shirya karɓa ba..."






Mutumin nan ya karɓi jaririn daga hannun likitan, hawaye na zubo masa “wannan yaro ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login