Showing 33001 words to 36000 words out of 72707 words
Chapter 12 - DUHU CIKIN HASKE BOOK COMPLETE BY KANWAR SOJA.pdf
LAST PAGE OF PART 3
BAUCHI
AFTER ONE WEEK
Duk baran da Da Kamal yaye yau bai samu abinchi ba sai dai ruwa a bakin masallaci , yasha
wahala kasancewar yau anyi ranan gashi ko abinchin bai samu ba har rana ta fad'i haka ya
kuma China bayan gari ya kwanta a 'kasar wata bishiya daga nisa yakan iya hango wane
tsaunin gini kamar dai a kewayenta da zama hakan na nuni cewa akaiw mutum a cikin haka ya
isa bakin fillin yaye ta bara "karshin wane bakin mummunar mutum yazo ya koreshi haka ya
hau anan bishiyar yana iya leqo abunda ke faruwa a ciki ,,
'karar mota ce ta farkar fashe daga gingid'in da yakiye bud'i idon sa yaye da kyau ganin wane
babban mutum da matarshi sai 'karamar yarinyar da anganta anga a tsorachi take mirza idon
yaye kasancewar yanzu kumburin ya sake yana iya ganin kadcan kad'an yarinya da ta bashi
ruwa ranar a bakin tasha yagani je yaye kamar ya sauko anmman ya kasa 'to bare naga me
yasa aka kawo yarinya nan a wanan gun mummunar mutum" yace shiga cikin zanar dukka su
ukku sukaye nan Kamal ya tashi tsaye don ganin jin yanda ya kawo su ,,
gaisuwa sukaye cikin wane irrin amo mutumin ya tashe ya fara tsalle tsalle ya e wanan yarinyar
ittace aka samu , nan chairman yqce "kwarai kamar yanda kace baka bukatar akawo yarinyar
da ta saba ma haifar kaba don haka wanan marainya ce kuma shikkaranta bakwai kachal a
duniya " nan Hajiya Binta tace mun chiyar da itta kayan da'di na tsawon wata guda gata nan
burin mu kawai a wanan karon mijina ya ji zance na reps Ina tabbatar maka duk abunda kakiso
zamu chikka nashi " dariya mutumin yaye yace aikin ku yakamata tsawon kwana bakwai zanyi
da ita ina mata fyade daga nan zan d'ibi duk wane abinda ta fittar koda jinin ta hakan ne zaisa
aikin ku ya kammala " rass gaban Hajiya Binta ya zube tsoron kar ya fitar ta mutu a hanun sa
tunda itta yarinya ce shikuma jibgigigine ,,
Mammaki ne ya chika zuchiyar Kamal da irrin wanan mutanen tunda yaji kalmar fyade hankalin
sa ya fara barin ganganr jikinsa haka suka fitta da cewa zazo dawo sosai Rugayya take kuka "
Mommy kar kubarbe a hanun wanan ba'kin mutumin kashi ne zaiye wallahi Daddy 'kankwanme
hanun Daddy taye sharita yaye ya bata "ke don Allah bar jikin na chan zakiye ne ba dadddyn ki
bane kinji ko sha sha sha burina samun kujera reps baki ba" haka suka juwa ganin haka wanan
boka yafara kashi baki yarinya zo ki amshi abu mai dadi kinji ko ture shi tafara ye gsnin yana
tatta'bata , ba'abunda ya fad'o mata a rai sai maganar da Mama marayu take musu na cewa su
kuji mutumin da zaina tab'a musu jikin su ba mutumin kirki bane zare wandon sa yaye ya fittar
da doguwar jilarsa yana shafa mai wasu abubuwan tsafin sa na magani zare ido kawai Rugayya
takiye nan yazo ya danne ta yana junna nata abun wai ta gogge mai da 'karfe Kamal ya sau'ko
daga saman ittace da ya karya wane rishin bishiyar shiga yaye ko excuse babo boka da hankali
da bakan saura abunshi a gaban Ruqayya bai masan an shigo ba itta kuwa sai turjiwa takiye
tana " Allah ka taimaka min waye mai taimakon nawa " shigowar Kamal yaye dai dai da
……………….
ABUJA
Haka Alhaji Ali ya amsa kirar yaron gidan sa cewa an samu wasu mahaukata biyar sauran biyu
a cikin jahar Kano don haka yace a 'boyesu har sai ya dawo daga Abuja a nemo sauran kuma "
budygurd ne ya bud'i masa motar ya fitto chikin shigar kamala fuskar nan tashi a ya motar burin
sa kawai ya shigo yaga halin da matar shi take ciki domin a daren jiya ya kasa barchi sakamako
jin sautin muryar ta a cikin wane halin ,,,,,,
Jamal ne ke zaune kwana nan ya rasa abinda ke damunshi akan muna nan mafarki da yakiye
wane zubin kuma yana ganin fuskar yarinyar nan da ya baiwa taimako a cikin gidauniyar
marayu,,,, sallamar mahaifin sa yaji da gudu ya masa oyoyo daga sa sama Alhaji Ali yaye ya
sumba ce shi a neck nashi yace i miss you my boy " a i miss you too Daddy nayi kewarka
zauna a kujeru sukaye where is your mom abunda yace kinan kallon sa Jamal yayi yace ammm
Mommy ai nata nan I think yanuz kusan one week Bata Nan " what cewar Alhaji Ali da ya Micki
shidai Jamal kallo kawai yakibinshi dashi ganin bakin fuskar sa
(ne kuma 'kanwar soja nace Jamal kai yaro ne bakaga komai ba indai a fuskar uban nan naka
ne ).......
Kiran ta yaye a waya kusan two misscall bata amsa ba , hakan ya hargitsa tunanin sa
anmman cemin taye tana gida daki kawai ya shiga ya kwanta tunani fal a cikin ranshi.
lokacin da Alhaji Ali ya kira Maryam suna wanka da saurayin ta don haka batsa ma me ke
faruwa tana fitowa yaye dai _dak da kiran sa na ukku tsaki taja ta amsa mu honey " hararra
saurayin ya buga mata wai kishi yakiye hawa kan 'kafarsa taye tana hargitsa 'kashin kansa
tama waya 'umm na'am ranka shida'di ,inajinka barchi nakiye shiyasa " danne abun yaye yace "
ammm ina Jamal " honey Jamal nan kasan yau weekend yazo mun gaisa ya kuma part nashi
okay no proplem Ina hanyar shiga Abuja yanzu kimin tanadi na musamman amsawa taye
badon taso ba …
a gaggauce ta shirya ta sallemi saurayin nata ta shiga mita da security nata ta iso gidan zaune
Alhaji Ali da Jamal akan kujerar ta iso rass gabanta ya fad'i nan tafara kakkarwar zaza'bi nan
Alhaji Ali ya mi'ki tsaye yace "............
****************************************
MAIDUGURI
Saukar Buba a tashar motachi Maiduguri yaye kimanin awa ukku mai kyau saboda rashin
sanin cikakken me takawo shi garin nan kuma ina zai sauka wacce irrin hatsabibiyar rayuwar
zai fuskanta a wanan yanayin hawaye ne suka sau'ko a bisa kumatun sa bai hana su zuwa ba
kuma bai shari su ba domin kuka ma rahama ne a garishi
dai dai da tahuwar malam Salihu a cikin napep yazo domin d'aukar matarshi da tadawo
Adamawa tsayawa yaye a inda Buba ke zaune yana ta zuba hawaye kamar da bakin 'kwarya
haka adda salma'' ta iso fillin ganina bunda Mallam Salihu ke kallo taye hala kawai zuchiyar tace
ta buga da 'karfe ta e "Mallam mujee ko shiga napep nin taye ya taimaka mata da shigar da
kayanta nan ya juya zai shiga ya tu'ka Buba ne ya 'kama 'karfin '"bawan Allah ka taimaka min
da fillin da zan kwana banda kowa a cikin garin nan ne ba'ko ne ina samun sana'ar da zanyi zan
bar ma gidan anmamnn ka taimaka yanzu don Allah " hana bawan Allah sanin kanka ne duniyar
yanzu tazama abun tsoro a garimu taya zamu yarda da kai har mukaika gida idan ka cutar
damu fa,?"
Murmurshi mai 'kuna zuchiya da ciwo Buba yaye yasa hannun dama ya gogge guntun
hawayen yace" ne bamai cutarwa bane kuma ne ba mugu bane taimakon kawai naki nema
shikkinan ku tafe idan Allah ya tsara min rayuwarta ba abunda zan iya aikata wa 'kaddara tace "
ya juya ta da napep yaye nan Adda salma'' ta tsure kamar ta janyo shi ta shigo dashi nan da
nan tace " Mallam " birki yaye da yasa Buba juyuwa a tsorachi yana zazzare idano yana kallon
abinda ke iya faruwa ta chikin napep nin nasu.............
LAGOS
Iro ne ke tsaye a wane teburin mai shaye sai ganin mutane dake zirga zirga a cikin tashan
yake gabaɗaya ya tsure ganin abinda baya tsammanin. Lagos nen tunanin yakiye ya za'ayi ya
samu inda Hashim yake a wanan garin gashi wayar tashi ma kashe wane ne ya tsaya a kusa
dashi mai motar taxze yace " ina zuwa Mallam "amsawa yaye da cewa unguwar goni zani nawa
zaka kai ne ɗari biyar "suka shirya nan ya shiga yana shan ruwan purewater da ya saya kallon
sa ta madubi mutumin kiye inda ya zauna a baya da wasu mutane biyu a ciki sai na gaba chan
suka yanko wani dajin tamkar ma fi kusa da 'kauye ce zagaye sa sukayi nan ido yafara raina
fata yace "....................
Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️✍️✍️
Alhamdullah the end of part three dukka dukka Anam na dasa al'kamin na ya huta , nima
na huta kuma ku huta , ina godiya sosai bisa so da 'kauna da kuki nunamin , Allah bar "kauna ...
mu had'u a part four shine 'karshin labarin da yardar Allah..
DUHU CIKIN HASKE
Dark in light
60% true life
story
by
'kanwar soja ✍️
The writter of Mijin Mage , Ruhi biyu & now
DUHU CIKIN HASKE
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma
nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
مسب الله نمحرلا *ميحرلا
ىلصو* الله لع يبنلا *ميرکلا
The game was begins, everything that has a beginning must have and end
_Page_
3️⃣1️⃣➡️3️⃣2️⃣
GOMBE
" In sha Allah zamu kasance masu rigon marainyar Allah wallahi rashin haihuwa tsawon
shekaru ashirin mun gaza jurewa shiyasa mukazo nan domin neman taimakon ke uwar marayu
na gidan gidauniya, ke kad'aice zaki shari mana hawayen mu ke bamu i'ya macce zamu
kasance masu kulla da al'amarin ta tamkar mu muka haifeta, " cewar Hajiya Binta tana matsi
idon ta da ke hawaye , dafata chairman yaye idan zamu samu yarinya kar ta wucce shikkaru
bakwai a duniya don Allah ke taimaka mana mun san darajar d'an adam kinsani " murmurshi
Mama taye " shikkinan yi da ace ba ku samu bane bazan baku ba anmman kun kasance masu
taimakon rayuwar mu kuma har dad'in kowa kuki baku da matsala Allah ya mana maganin
komai zan baku i'yata. cikin yarana zan bada umarnin a kawo biyu ku za'ba d'aya ," kafin
tagama maganar Hajiya Binta taye charaf" ai ranki shidaɗi mu ko biyu ma zamu iya rainon su ko
Alhaji " girgiza kai yaye alamar ey kallon su Mama nan take bata gamsu ba taceAllah sarki kar
kaddamu chairman d'ayan ma ya wadattar " ba matsala fitta Mama taye ta kira committee
member ta mata ukku ne nan suka shiga sukaye magana Husna da Ruqayya aka sa agaba nan
suka zo suna muzurai da idano kuwa na addu'a kar yabar gidan Mama ,don ansaba zuwa
d'aukan marayu a wanann gidan ,,
Hajiya Binta ce ta shafa gashin kan Ruqqaya "yarinya kyakyawa kamar buzuwa me sunanki
"tunda Rugayya ta ganta taki sam matar bata kwanta mata a rai ba nan tace " sunan nan
Ruqayya wanan kuma Husna 'kawatace kullum bama rabuwa " cikin zuchiyar Hajiya Binta tace
"don ubanki kuwa dole ku rabu a daren yau " a zahiri kuma tace "Allah sarki yarinya da ido
tayewa mama magana tace " zaki zauna dane zan baki gata sosai daga yau ma sunana
Mommy kinje ko wanan kuma dadddyn kine "nan akace Husna ta tafe a karshin dai da kuka da
da burgiwa aka raba Ruqayya da asalin ta wanda Husna ma sai kukan takiye da kyar aka raba
su nan Hajiya Binta da chairman suka dauki hanyar zuwa dad'in kowa sai mucce ......
Maraya dai amanar Allah ne duk wanda ya karya alƙawarin ya tunatar da Maraya tun a duniya
Allah zai masa sakamako ,
sai bayan tafiyar su abada Mama ta tuna da wanan akwatin da aka bata nan ta kira sauran
committee ta gayyyamusu don kar rai yayi halinsa idan chairman yazo abashi ya kaimata a
zaton su zai dawo kawo musu tallafi yanda ya saba ,,,,,,
BAUCHI
****************************************
Tuni makiyayi nan ya gyara wa Kamal hanun sa ya juya ya tafe ya barshi a fillin tunda ya kasa
masa magana nuna mai hanya yaye yace "idan kana so fitta a daji. nan ne hanyar da zaka bi
dod'ar zai fidda ka cikin dajin nan" ,, kwanciyar yaye abu shi nan da nan barchi mai wahala ya
sacce shi a 'kasar bishiya chan yaje motsi a akan 'kaffarsa a hankali ya bud'i idon sa machiji ya
gani runtumimi yana hawa 'kafar sa baiye ihu ba kana bai motsa ba burin sa kawai majichin ma
ya kashe shi ya huta da wanan wahalar ta rayuwar sa ,, koda machiji ya zo har jinya sa ya
kuma runtse ido baki ya bud'i daa niyyar kai sarra sai yaye ihuuuu ya lankwasa ya warware jikin
sa daga na Kamal ya juya ya tafe da sauri abin ya bashi mammaki matuƙar gaske "me yasa
majichin juyawa haka ko dai shi nin bakin jinin garisa wanda majichin ba bazai chinye shiba"
buga 'kafar a 'kasa yaye ya chigaba da tafiya cikin wanan dajin ,,,,,,, da zarar yaga lokacin
sallah yana tafiya sai ya tsaya ya kwantanta sallah ya chigaba da tafiya har dare ya riske sa.
cikin wanan dajin anan iddo ya fara raina fatta ..
****************************************
HANYAR BAUCHI DA BUBA
Tunda suka sa shi a mazaunin baya mai zaman banza suka 'karawa motar su gudu baji bagani
gani don ganin irrin jinin da yake zubewa a kansa duk da cewa sun daure masa kai da 'katonn
'gyle basu isa ko ina ba sai babban asibitin cikin garin Bauchi a inda aka bashi tallafin gaggawa
domin ceton rayuwar shi " tabbas jami'an tsaron nan kunyi 'kokarin kawushi da wuri badon haka
ba da tuni ya rasa rayuwar sa " murmurshi d'ayan yaye ya gogge gumin fuskar sa yace "
alhamdullah taye akaiw wane 'boyayyin al'amari ne akan yaron tunda kuga ya kasance a raye
duk da matsala kai ne ya sameshi " nan doctor ya amsa da cewa "yawancin irrin wanan baya
kai minti goma mutum ke mutuwa tabass Allah ya bar mai rayuwar sa ta wane babban dalili "
kuɗi sosai suka bawa doctor da cewa sukam zasu tafe aikin so don haka ga ajiyar mara lafiya
idan ya warke kud'in account nin sukaye saura to abashi yaye tafiyar sa" ,, haka suka juya suka
tafe ,,