Showing 12001 words to 15000 words out of 65323 words

Chapter 5 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3548

miki akwai yara atsakaninsu Kuma dole zata haifesu sai
dai zaki iya yin yadda kikaga dama dasu shine kawai abinda nasani"





Bayan sun baro wajen boka suka dawo gida nan ta ninka kulawar datake bata har zuwa kusan
sati tana tunanin yadda zata aiwatar da shirinta batare da wani abu mai kama da zargi ya ahiga
tsakaninsuba wannan kenan.

Yau kam Amina tashi tayi sam batajin dad'i sai dai dauriya data rigayi dan kar ta d'aga hankalin
mutanen gidan ganin yadda suke dai dai bakin gwargwadonsu akanta.






Tana zaune afalo saman dugowar kujera hah. Sailuba ta rako k'awarta Zakiyya har inda take
haj. Zakiyya ta k'araso suka gaisa tayi mata sannu da jiki, da ido tayima sailuba alamar kawai ta
aiwatar yau.






_________________________



Koda ta rakata ta d'an Jima suna tattaunawa da k'awar tata kafin suyi sallama inda ta barta nan
ta dawo tasame ta sai dai sab'anin d'azu yanzun idanunta alumshe suke alamun barci yafara
fisgarta wani kayataccen murmushi ta saki ta wuce kicin dake ranata d'anyi dan d'aya ya wuce
abincin mutum biyu ta dafa mai rai da lafiya daga ita sai Baffanta dan tasawa ranta yau abincin
nan bazai ciyu awajen Amina ba.




Hakan cewa kuwa yafaru bayan ta gama dai dai lokacin ana kiran sallah ta fito da nufin tashinta
sai k'eyar ta ta hango tana shigewa d'akinta, tabita da wani shegen harara aranta tana fad'in
zanyi maganinki ne, daga haka itama ta wuce nata d'akin danyin tata sallar bayan sun idar
kusan atare suka fito da Amina wacce takejin wata mahaukaciyar yumwa har hautsina cikinta
yake saboda tsabar yunwar dake d'awainiya da ita ganin haka yasa Sailuba shigewa kicin da
sauri ta had'o mata ruwan lipton ta kawo mata tace





"Kinga k'anwata fara da wannan naga yau du bakici komai ba bazai yiyu ki farada abinci Kai

tsayeba" sosai hakan yayi mata dad'i dan tana da buk'atar hakan, batare da wani tunaniba ta
kafa kai tashanyen tas tun kafin ta dire kofin cikinta yai wani irin masifaffen murd'awa wanda tun
jiya takejin hakan, da mugun k'arfi ta dafe cikin gami da fad'in washhh, wani b'oyayyen
murmushi tasaki ama azahiri k'arasowa tayi da sauri ta kamata "lafiya kuwa k'anwata?" Ta bud'a baki kenan zatayi mata magana kenan cikinta yayi way irin fitinannen murd'awa sai
cewa tayi"babu" cikin pretanding tace "babu me?"





Kasa magana tayi saboda azaba Saida ta Jima kafin ya lafa mata ta dubi Sailuba tace "dan
Allah anty ki taima kamin ki Kira Baffa yazo yakaini asbiti mutuwa zanyi"




Da sauri ta nufi hanyar d'akinta tana fad'in "to bari na kirashi gwanda yazo kar wani abun yazo
yafaru mushiga uku"




Tana shiga d'akin tasaki wani uban tsalle tana d'ebo shoki farin ciki fal ranta yau burinta zai cika
zatayi kwanan farin ciki wannan alak'ak'an cikin zai bar gidansu ta huta daganin tashin hankali.







Muje zuwa
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥

2021
NA

HASSANA ABDU AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM





Page 11


Anan ta k'yaleta tana ta faman murk'ususu yayin da tai kwanciyar ta saman gado tana waya da
haj. Zakiyya a maimakon Baffa sosai suke shewa, Jin kamar motsi yasa tayi saurin katse Kiran
tana laluben wayan Baffa.





Anty shamsiyya ce ta shigo arud'e domin sanda ta shigo har Amina ta sume ga uban jinin
dayake malala ta k'asan ta tana ganin haka tayi d'akin haj. Sailuba arud'e, sai dai tashin
hankalin data gani akan fuskar sailuba yaci uwar nata dan hawaye tagani shab'e shab'e a
fuskar ta tanama Baffa bayani halin da Amina take ciki.




Cikin tsantsar tashin hankali yabaro kamfaninsa wanda yake ziryata a irin ranan dan ganawa da
manya da k'ananun ma aikatansa.

_________________________

Wuya ita wuya Amina tacishi kafin tasan inda kanta yake sai da tayi kusan sati guda acikin
asbitin kafin tasan inda kanta yake ciki dai Kam babu shi domin ya riga da ya zube tun aranar.




Sosai haj. Sailuba ta rik'a bawa Amina wata irin kulawa dan hatta Nanne wacce Sam bata yarda
da Sailuba kuma tana nusar da Amina ta kula da takun matar dan dai sunk'i d'aukan abinda
mahimmanci ne saida tazuba ido wannan karon ta k'yale sailuba da Amina amma duk wani
takunta tana ankare gane hakan yasa Sailuba matuk'ar taka tsantsan.




Babu wanda yakai Inna takaicin rashin cikin sai dai tayi musu addu'ar Allah yabada na aike
tareda yiwa Baffa nasiha mai kamar jirwaye cewa ya kula da matansa ya sanya ido akansu da
takunsu, duk da cewa bai gane me take nufiba yayi mata godiya ya maidata har gida dan bai
tab'a yarda Innarsa tahau motar haya.




_________________________


Kusan sau hud'u hakan yana faruwa wanda hakan yasa Baffa ya rufe ido yanama Amina bala'i
da tambayarta nufinta akanshi ya lura haihuwane batasonyi dashi daga baya har k'asa ya
durk'usa mata yana rok'on data taimaka ta haifa masa koda d'a d'aya ne yamata alk'awarin duk
abinda takeso zaiyi matashi amma dan Allah kada ta k'ara yimasa asaran gudan jininsa.



Hawaye hawaye fa take gani a idanunsa Baffa ne yake mata kuka da rok'on ta haifa masa
'ya'ya yana nufin ita ke zubar masa da yara idan tasamu ciki.

Itama fashewa tayi da kuka mai k'arfin gaske zuciyar ta yana wani irin suya take kalaman anty
shamsiyya suka shiga dawo mata akaro na hud'u data sake rasa cikin dayakai kimanin watanni
biyar wanda har sunfara saka rai da shi tunda yafi sauran ukun jimawa.




"Amina nifa nafara zargin kishiyarki akan wannan b'arin dakike yi ajere ajere duk dana san cewa
komi dayake faruwa daga Allah ne kuma dama can Allah ya hukunta wannan cikin da suka
lalace bamasu taka k'asa bane amma akwai sula kuma Koda ba haka bama idan kin zauna
kinyi tunani taya ita bata haihuba zata bar wata tazo da daga baya ta cika gidan aikinsan dole
zatayi wani abun akai duk wannan soyayyar da kulawar datake baki duk na banzane ga uban
bautar dake da take a siyansace tunda kikazo gidannan baki gaba baki baya kullum ak'are ya
kud'in guzuri inzaki farka ki gane ki farka sannan maganar gaskiya Amina ta inda zaki gane
cewa magana na gaskiya ne idan kin sake samun wani cikin ko Baffan kada ki sake ki fad'awa
sai dai su ganshi tunda na lura ke ba mai girman ciki bane irin girman cikin bane irin cikin Umma
ne dake wanda inda anganshi to bazai k'ara sati guda ba zai fito duniya dan haka duk irin
wahalar da zakici ki daure ki cije ki raini abinki dan tun mahaifarki tana iya d'aukan ciki zata zo
ta gaza kema azo ana samun wata matsalar kinga kunyi duro kenan burinta ya ciki ke babu ita
kinga anyi one one kenan daman abinda take so kenan.





Ganin tayi tsaye ga hawaye na tafaman shatatowa daga idanunta yasa ya kamo hannayenta ya
zaunar da ita asaman cinyar ta yana cigaba da hawayen tare da rok'on ta daure ta daina Yi
Masa ganganci idan tasamu ciki, ganin cewa ko me zata ce ba fahimta zaiba yasa ta tsuke
bakinta amma ranta banda suya babu abinda yake mata.




_________________________




Wannan karon Saida tayi wajen wata hud'u kafin Allah yabata wani cikin mai d'an Karen laulayi
dan haka kamar yadda 'yar uwarta ta bata shawara ta rik'a daurewa tana shanyewa dan tanaso

ta tabbatar da abinda ta fad'a mata akan wannan kareemar matar ma kula da ita da damuwa da
al'a muranta







Hakan kuwa akayi duk yadda taso ganewa bata bata damar hakan ba haka ta rik'a daurewa
tana nuna babu komai duk da kuwa irin bak'ar azabar datake sha wajen cimaka da kuma rashin
son wani k'amshin haka ta dinga daurewa har zuwa lokacin da cikin shiga wata bakwai bai
fitoba amma komai nata ya k'aru domin Amina macece mai matuk'ar kyau da diri gata fara tas
babu ta inda ta baro mahaifiyar ta bafulatanar asali mazauna wani daji.








Bayan wata guda lokacin cikin ya shiga wata na bakwai Kuma cikin kariya da k'udura na Allahu
S W T A daga Baffa har Sailuba babu wanda Allah yasa ya gane cewa Amina tana da ciki, yayin
da Baffa yadamu sosai har yana cewa kodai wani abun tayi dan karta haihu dashi?





Tun bayan da cikin ya shiga wata na biyar ta daina duk wani laulayi sai dai dan banzan kwad'ayi
kasancewar Koda yaushe itace a kicin tana bauta da aiyukan gidan hakan yasa duk abinda
ranta yake so shi take dafawa taci son ranta kayan kwalam kuwa Baffa baya rabo da kawo
musu dake ita Sailuba tafi ganewa ta narki abinci aci kaji da su kifi duk wannan abubuwan basu
dameta ba haka Amina zatayi taci ta kuma bawa duk mai rabo dan itama mutum ce mai yawan
kyauta kamar Baffa, sannan kuma duk wani irin kyau da shek'i data k'ara hakan baisa Sailuba
ta ganeba kasancewar dama can ita d'in Mai kyaun ce, Baffa ne kad'ai ya kula da hakan saidai
bai tankaba domin ya lura da ita a y'an kwanakin wani bin sai tayi ta k'unci irin dai abubuwan da
ba a raba mai tsohon cikin dashi.

Ranan wata laraba Amina ta tashi da matsanan cin ciwon mara cikin dare Allah yasa Baffa
ad'akin ta yake ganin irin murk'ususun wahalar datake yasa yayi tunanin ko wani cikin tasamu
zai fita dan haka yadda take kuka tana fad'in ya taimaka mata haka shima yake rok'on dan Allah
karta bari wannan karon ma yayi asaran cikin dakyar ta iya bud'an baki tace"dan Allah ka
taimakamin Baffa ba bari bane wannan karon haihuwa zanyi d'a zan haifa Baffa da sam bai
gane abinda take cewaba ya fita da gudu zuwa d'akin Sailuba dagashi sai gajeran wando ko
riga babu ajikinsa haka ya fice yatasota tasha mamakin ganin yadda Amina take murk'ususun
ciwo wani b'oyayyen murmushi ta saki tana fad'in aranta magani yabi jiki Kennan, ita ta
taimakawa Baffa yasa kaya yasunkuci Amina da gudu yayi waje sam kasancewar sa na likita
bai kamata ace har irin haka yafaru a gidansa ba matarsa da suke kwana su tashi tare har
tasamu ciki ya kai tamakin haihuwa duk bai saniba, amma idan mukayi duba da cewa Allah
shine me yadda yaso Kuma asanda yaso sai muga hakan ba abin mamaki bane.






Labarin yafara sauyawa ne daga lokacin dayagama dubata ya tabbatar da abinda ya gani bai
k'ara tabbatarwa sai da yayi mata scainin, tashin hankali yatad'a a rud'e domin ganin dan
mutum muraran yana neman hanyar isowa wannan duniya mai cike da abin al'abi da mamaki.





Kasa control d'in kansa yayi yafashe da wani k'arkarfan kukan dayasa Sailuba danno kai cikin
d'akin da mugun gudu zuciyar ta kamar takarda tsabar haske tasani wannan kukan na Baffa
yana nufin wannan karon ma sunyi messing babynsu saidai kuma abinda tagani ba k'aramin
kad'uwa tayiba domin har lokacin bai kashe na'urar ba ga babyn nan wanda basu gane wane
jinsi bane na ta wutsulniya sosai ta daskare a jikin k'ofa zuciyar ta yana wani irin masifaffen
bugu.

Wani irin juyi Amina tayi gami da sakin wani k'arkarfan nishi da gudu Baffa yatarota dan saura
kad'an ta fad'o daga gadon tarotan yayi daidai da sallamar babyn izuwa duniya wadda ta fad'o
ita da mahaifar gaba d'aya rasa yadda zaiyi yayi sai kawai ya zube gwaiwoyinsa ak'asa yayi
sujjada shukuriyya kafin yayi saurin Kiran ma aikata suka shigo dakayan karbar haihuwa shi ya
gyara matarsa da 'yarsu takafin ya rungumeta ajikinsa yana tofe ta da addu o I kala kala.





Wani abin mamaki tun kafin Baffa ya sanarwa kowa haihuwa Muhammad yafara sanarwa
haihuwar Wanda a yanzun yake shekara ta uku amatakin karatuntasa Wanda yakeyi Kuma
zab'in Baffansa yayin da ak'asan ransa Kuma yasha alwashin bayan ya gama zaije yayi na soja
wanda shine zab'i da ra'ayinsa amma yanzun kam zab'in mahaifinsa yabi yake Wanda ya zabar
masa.






Hakanan ya tsinci kansa da wani irin farin cikin kasancewar ganin Baffansa cikin tsantsar farin
ciki, haka ma Inna ana fad'a mata haihuwar da kanta ta taso abinda bata tab'a yiba wato kwana
agidan Baffa wannan karon cewa tayi ita zata kula da maijegon da'yarta wannan karramawa ta
Inna ya k'ara mata kima da mutunci a wajen iyayen Amina.





Ranan suna kuwa Saida Muhammad ya yabaro makaranta yazo suna yasha fad'a wajen Baffa
domin a lokacin suna shirin jarrabawane, a lokacin murmushi yayi yace kasa daurewa ne.






Tunda yai arba da kyakykyawar yarinyar yaji ta masifar shiga ransa shikenan Kuma ya tare a
d'akin domin kullum ya fito daga b'anga rensa yana d'akin Ammey kamar yadda itama Baffa
yasashi fad'a mata har zuwa sanda yakoma makaranta dakewar MARAYAM kamar yadda taci
sunanta wanda take Ammey tace sunan mahaifiyar malam ne hakan kuwa yayiwa malam dad'i

kulawa ta musamman yake bawa yarinyar kullum sai ankai Masa ita ya tofeta da addu o in tsari






Sailuba kuwa





Takuce maman islam
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
BA JINANA BACE
2021

NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM






Page 12

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yayin da Sailuba sukayi amanna da malaman tsubbu wani
lokacin suyi sara kan gab'a wani lokacin kuma sai b'ata lokaci da nesan ta kai da mahalicci.





Wata rana Sailuba takaima k'awarta haj. Zakiyya ziyara anan ne take cewa "k'awata ni kuwa me
zai hana ki karb'i Maryam?"





Wani d'an iskan kallo ta watsa mata tace "amma k'awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da
zakice na karb'a na raina da hannayena masu albarka"






"Hum k'awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da
kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji" tajawo tayi mata rad'a,
bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna.









Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk'ata
haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin
wannan matan bane da suke son jan d'an wani jikinsu.

Sai dai abinda yai masifar d'aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita
Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k'ara haihuwa ba, ita kuma Amina
yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok'ar mata ita ta
temaka tayi mata wannan sadaukarwar.





Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani
fitinannen kuka mai mugun k'arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa
yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b'oyayyen murmushi take saki azahiri
Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta
durk'usa agabanta tareda rik'o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace.








"Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah
(S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk'awarin Maryam bazata tab'a sanin
zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik'eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da
yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon 'yar uwata" ta k'arashe tareda zubowar wasu
hawayen Mai uban yawa.








Wani irin tausayin tane ya rufe Baffa yasawa ransa Koda wannan ce kad'ai kwansa a duniya ya
baiwa Sailuba ita halak malak ko ba komai Sailuba 'yar uwarsa ce jininsa Koda baya raye ita
mai rik'e masa 'yarsa ne.

Ta ko Amina wani mugun kallo ta watsawa Amina kuma tasaki wani mugun tsaki mai k'arfin
gaske tace"Allah ya baki naki kema maman Maryam shine sunan data rad'a mata tun bayan
haihuwar Maryam amma kisani kome zai faru bazan iya baki 'yata ba domin wannan ai zakunci
ne ace an rabani da d'iyata wannan sam bazai yiyuba wallahi" ta k'arashe tana kuka bil hak'k'i
domin yanayin kallon dataga Baffa yana mata shi yake nuna jin d'acin kalamanta, batareda ya
k'ara duban inda takeba yacewa Sailuba





"Karki damu insha Allahu babu wani abu dazaki nema kirasa shi matuk'ar yayanki Baffa yana
raye dan haka bazakiyi kuka rayuwarkiba" daga haka ya tashi ya d'auko Maryam dake d'akin
uwarta tana baccinta hankali kwance ya dawo inda suke har lokacin Sailuba bata bar kukan
datake ba yace.




"Gata nan na baki amanar ta ki kulamin da ita karki bari wani abun yasameta Kinga itake nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login