Showing 30001 words to 33000 words out of 65323 words

Chapter 11 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3868

irin murya mai kashe jiki wanda hakan yasata jin wani irin babu dad'i
"kayi hak'uri bross dan Allah" maganar ya kwace mata batare data shiryawa hakan ba.






Sosai ya kafeta da idonsa wanda sukayi wani irin kyalli saboda kwallan daya cikasu, tunda yake
babu wanda ya tab'a gasa masa bak'ar magana irin nata.

Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago idanunta dake duk'e kan littafin Nassar daya jima da ficewa
daga d'akin,ba k'aramin fad'uwa gabanta yayiba ganin kwallan daya ciki idanunsa sai dai bai
basu damar zubowaba saboda nayasan taga logonsa amma maganar gaskiya yaji zafin
maganar ta ainun wanda dama dan yaji zafin tayi masa.






Rasa yadda zatayi masa wani maganar tayi sai kawai ta fashe masa da kuka wanda zan iya
kiransa da kukan shagwab'a, take ya k'arasa zaman durshen agabanta tareda kamo hannunta
yace "haba k'anwarta me kuma nayi miki banfa yi miki ko mai ba" ya k'arasa maganar cikin
rawar murya domin har ga Allah jiyai kukan yana mugun tab'a masa zuciya.





"Kayi hak'uri" ta k'ara fad'a masa cikin muryan kuka "nayi" yafad'a mata da sauri cikin rawan
murya sannan ya d'an dubeta yace "k'anwata na miki wani tambaya mana amma ina son dan
Allah ki fadamin gaskiya tsakaninki da Allah"


"To" kawai tace masa tana faman goge hawayen da suke zubo mata har lokacin "to ki daina
kukan haka mana dan Allah kinji" yafad'a yana share mata hawayen data rasa dalilin k'in
tsayawarsu.







"Wai me yasa kika tsaneni ne?"
Yayi mata tambayar dayafi komai ci masa rai tun ranan data furta masa ta tsanesa har yau
baidaina jin amsa kuwwar abin cikin kunnen saba sosai abin ya tab'a shi.

"Ai nima baka sona nida mama ka tsanemu kafi son Nassar da Ammey kanawa mama rashin
kunya agabana baka dukan Nassar agaban Ammey amma ni kamar jaka haka kake jubgata ko
dan kaga Nassar d'an d'akinku shiyasa ni kake nuna min 'yan ubanci" ta fad'a cikin zubowar
sabon hawaye, maganar ta na k'arshe ya mugun bashi tausayi har baisan sanda yasa hannu
yajata jikinsa ba kamar jira take kuwa ta fad'a tareda sakin kuka irin mai cin rannan.






Dagajin yanda take kukan yasan akwai abinda yake damunta wanda ta barshi aranta takasa
fad'uwa kowa, saida yabari ta d'an yi kukan da d'an yawa kafin ya soma d'an bubbuga bayanta
har saida yasamu tayi shru da k'yar.







"Me yasaka ki kuka?" ya tambaye ta cikin sanyin murya, "ku kullum Ammeynku tana tareda ku
tana kulawa daku duk abinda kukeso tanayi muku bata yawan fita unguwa bare tabarku cikin
kad'aici, amma ni kullum mamana tana gidan k'awarta haj. Zakiyya danayi magana sai tabani
k'udi ko tace bari ta had'a min wani d'an party bathday d'ina kuwa ko manta date d'in batayi dan
Allah bross k'udi ne yake maganin ko wane matsala?"


Ta K'are maganan da tambayar abinda yake matuk'ar damun ranta,
"A a" yabata amsa cikin tausaya mata domin shima ya fahimci wannan abun yafara damunta
hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi masa a rai ba ko babu komai tunkafin ya fara tunanin hanyar
da zaibi dan shan kanta ta yadda zajata jikinsa su kulle har akai ga maganar da ake son
k'ullawa wacce babu wanda yasani dagashi sai Baffa sai kuma Ammey da Baffan yake jin tana
da hak'k'i akan tasan komai.

"Amma Maryam bamune muka tsaneki ba kece Kika tsanemu bakya mutantamu da Ammeynmu
ko kad'an har zaginta fa kikeyi taya kike tunanin zamu mutuntaki bayan bakya mutanta mana
mahaifiyar mu?"






K'are maganar dayi mata tambayar wanda nan take ta gano kuskurenta amma Kuma sai tace
"ai mama tace kada nasake nayi sabo da 'yan uba dan muddun nace zan dinga mu amalantar
ku to babu abinda zaisa baku kashe niba tunda Kuna ganin agabanku Baffa yake nuna yafi
k'aunata akan ku, kuma tace Ammey muguwace tun ina jaririya taso kashe mata ni kuma tace
Ammey ce take asiri take had'a ta fad'a da Baffa shiyasa kullum yake mata fad'a baya bata k'udi
saidai inya ajiye ta turani d'akin sa na d'ebo mata mai yawa amma baya isarta saita had'a
danawa.






Tsabar tashin hankalin jin wannan mugun zantukan baisan sanda ya zube ak'asan wajen yace
"maman?"
Yafad'a gamida zaro ido har saida yanayin sa ya mugun tsoratata.







Pls manage data taku har kullum






MAMAN ISLAM CE
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI



MAMAN ISLAM


Wannan shafin nakune gaba d'aya kuyi yadda kuke so


MUHAMMAD KAREEM

HAYATU BABA ZUBAIRU (YAYA HAYAT)
ITS ABBAS
Allah yabar kauna






Page 23

Jikinta take ya hau rawa tace "wa lla hi haka tace min, shi yasa kaga nima bana son
Ammeynku.

Kasa magana yayi da hannunta da ya kama ya rik'e gam cikin nashi, idanunsa kuwa kad'awa su
kayi suka yi wani irin ja,
Me wannan matar take nufi?
Takasa kula da amanar data dauka, Kuma tana son raba hanta da jini wannan ba adalci bane,
zalunci ne babba, ke baki kula da yarinya ba, sai ma d'ora ta da kikayi akan wata turba mara
b'ullewa.







"Zaki abota dani?"
Ta tsinci muryarsa cikin wani irin yanayi batasan lokacin data d'ago kai ta dubeshi ba sai dai
bata iya tace masa komai ba ganin yadda ya kafeta da runannun idanunsa






"Uhm?"
Ya k'ara tambayar ta again babu amsa sai faman murza idanunta take da d'aya hannun da bai
rik'e ba.





"Kema Ammey mamanki ce, ta tsinci muryar shi yana rad'a mata a kunne daga yau zamu rik'a
shiga d'akin ta muna hira tare dake, kuma kema duk abinda kike so ki tambaye ta zata baki,
kuma tama fi sonki damu idan kina musu ki gwada".






Ya fad'a yana cigaba da murza hannunta dake cikin nasa.
"Mama bazata barni ba ta tsaneku" ta fad'i abinda tasan kullum maman tana tusashi agabanta,
wanda tasan hakanne har cikin ranta.

"Ai bazata sani ba saboda kinga kullum bata zaman, gida Kinga kafin ta dawo munyi hiranmu,
bawai ki rik'a shigowa d'aki, ke kad'ai ba, Kinga tunani sai ya miki yawa"





Ya fad'a yana kallon ta, tabbas abinda ta fad'a gaskiya ne, tunani yana damun sosai wani
lokacin har sha daya mama tana kaiwa agidan hajiya zakiyya.






Shi kam zama ya gyara tareda zuba tagumi ya kafeta da idanunsa, yayin da tausayin ta ya
game mai jiki,yana mai jin haushin kansa, na yadda tun farko bai jata a jikin sa ba bare har
yasan damuwar ta.





"Zaki iya abota dani inzama amininki wanda zaki dinga fad'awa dukkan wani damuwar ki wanda
zai dinga magance miki duk wani matsalar ki da yardan ubangiji?".







Ya sake mata tabayan shi na farko,
"Idan mama tagan mu tare akwai matsala" ta fad'a masa haka, matsayin ta na wacce tafi kowa
kusanci da mama dan haka tafi kowa sanin halinta.

"Karki damu Baffa bazai bata damar raba masa kanmu ba, kinsan burin ko wanne ubane ya ga
kan yaransa ya had'u" ya fad'a yana d'ago hab'ar ta yana kallon, cikin idonta.







"Shi kenan na amince ta fad'a cikin sanyin murya"
Ihun murna ya saki tareda rungumeta"na gode my happiness na gode my Lovely sis dan Allah
daga yau ki daina wannan had'e min ran baya min dad'i"






Ya fad'a mata a hankali "to" tace masa daga haka ta maida hankalinta kan aikin da suke da
Nassar, tayata yayi suka gama aikin, daga haka ya rik'a janta da hira.







Waahegari motar ta ya iso, motar da Baffa yace bata gift idan taci jarrabawa, tun tana maganar
motan har sai datayi fushi ta daina maganan bata san cewa mak'alewar motar daga MD bane
shi ya hana saboda rawan kanta, yanzun ma sai yana yi yana sa mata ido sosai.







Washe gari kuwa tun kafin ya fito tuni ta shirya ta bar gidan a sabuwar motan ta sai da ya fito
yaga Abdul Nassar yana shiga cikin motar da yake kaishi makaranta.

"Kai ina Adda?" Nassar ya tambaye shi "tab'Adda yanzun ai ta jima a schl, kasan cewa tayi bari
tayi sauri ta tafi kar ka fito ka hanata kace Kai zaka kaita".






Murmushi MD yayi Yana shafin sumar kanshi daya sha gyara, daga haka ya juya ya shiga
motarsa security d'insa yaja shi suka wuce.






Uhm su o o anyi abun kai yaushe rabon duniya tunda bross ya dawo ya hanata sakat hatta
motar mama da take hawa sai da ya hana ta k'arfin bala i, dan haka yau take jinta cikin wani irin
farin ciki.







Tunda ta doshi cikin makarantar ido ya koma kanta domin motar tayi mugun d'aukar hankalin
mutane, da yawan su basuyi mamakin ganin wacce ta fito daga motar ba domin ansan tafi
k'arfin, wacce ta ninninka wannan ma, dan da yawa wasu suna mamakin yadda bata da motar
kanta sai dai akawo ta.




Maryam kuwa da gudu tazo ta rungumeta tace "eye had'uwa ta iso kenan" ta fad'a tare da
k'arasawa tana shafa motar, wani k'awata taccen murmushi Maryam ta saki tace "humm kinga

wannan bross d'in namu sai a hankali, nasan wallahi shiya hana akawo min motar amma Baffa
yafi shekara da biyan k'udinta"





Itama murmushin tasaki "ina ganin akwai wani abu tsakaninki da bross d'in nan"
"Kamar ya?
"Kamar yadda na gani bross sonki yake Maryam"
Manyan ta bata amsa
"Humm baki da hankali kin tab'a ganin inda akayi aure uba daya shifa d'an Ammey ne"


"Ammey shekarunta baikai ta haifi kamar bross dinku ba ki dai k'ara bincike"
"Humm kawai tace batare data d'auki abin serious ba.





Haka dai abubuwa suka cigaba da faruwa cikin k'aramin lokaci Maryam tayi wani mugun sabo
da 'yan gidansu batare da sanin maman taba wacce ta mik'a dukkan yarda da imaninta wajen
malaman tsubbu da 'yan bori dan haka bata da masaniyar cewa tufkar da take yi ta cikin gida ya
gama warewa tas.






Wata rana kamar yadda akasaba "Zakiyya takaiwa Sailuba ziyara akan yadda suka kasa
fahimtar jina ta waya,
"Nifa nagaji da wahala so nake na watsata tabi duniya ta lalace ta zama k'asaitacciyar karuwa
bana buk'atar akai ga d'aura wannan auren"





"Humm Sailuba kenan wani lokacin kwwnyar ki atoshe yake wallahi, banda ke da abinki
idanmma zatayi auren taya zamu bari tayi auren hutu?"

"Ni auren ne ma bana son tayi kwata kwata, so nake rayuwar ta ya wulak'anta fiye da duk wani
wulak'antacce a duniya.

Tofa



Muje zuwa






Daga taku maman islam
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM


Shafinki ne wannan'yar laleta SA'ADATU USMAN MUSA (ISLAM)
Allah ya rayamin ke tareda dukkan yayan musulmi badaya
Almustapha Usman Musa shalele na kenan kuma nagaban goshi Allah ya tsaremin ku.

Page 24



"Kina bani ciwon kai Sailuba nifa komai da kike gani da mugun shiri nakeyin sa, Kuma bana
bawa na kusa dani damar gane akwai wani abu a cikin raina dan haka zai wuya kiga idan nayi,
abu ayarda ni d'in ce nayi saboda babu fuskan da za a gane hakan, ke kuwa gajan hak'urin ki
kawai ya isa tonaki, Kinga alhajina da kike ganinsa bansa me shi da sauk'i ba saboda mugun
taurin Kai da Allah ya d'ora Masa, shi yasa kuma kikaga bana masa ta dad'i, domin naci bak'ar
wuya kan nasame shi, sannan Kuma kina ganin har yau tak'i amincewa ta saurari Deedah
shegiya mai kafirin wayon tsiya na rasa dalilin da yasa bata Sona"







Ta K'are dogon sharhin ta da k'orafin yadda Maryam take masifar d'auke mata kai 'yar dariya
haj. Sailuba tayi kafin tace" ashe kin manta da cewa nonon wannan shegiyar 'yaalaman tasha,
kai wannan mata ta zame min annoba a rayuwata nasa ta yadda zanyi maganin tsinanniya"






"Hum ai irin su idan dubunsu ya tashi cika saikin ji kamar kiyi musu kuka wallahi" cewar haj.
Zakiyya cikin ya tsina fuska
Sun jima suna k'ulle k'ullensu.

Tana tunkaro gidan ta tuna da yadda bross ya rik'a kwala mata kira tanaji ta d'iba da gudu dan
kar ya hanata fita, tunda suka sam d'an hutun nan ya wani sa mata ido yanzun ta lura aikin ma
ba sosai yake zuwa ba sai jifa jifa damma yanzun Allah yasa ko ba kowa zata shiga d'akin
Ammey suyi ta hira yadda Ammeyn take mata ne yasa ta jinjinawa k'aryar mamanta da tace
Ammey muguwace ko kad'an bataga hakan ba saima wani irin mugun shak'uwa daya soma
shiga tsakaninsu da Ammeyn ganin yadda take mata.







Sam ta manta da yadda ya rik'a kiranta ta gudu kanta tsaye ta shigo gidan har da yar wakar ta,
daman tun fitar ta yake dakon dawowar ta.






Tana shigowa taji anyi ram da ita ya damk'e ta a bazata taji an rik'o ta sai abin yabata tsoro ta
bud'e baki zatayi masa ihu yayi saurin toshe bakin da hannunsa yace "wa na kama?"
Sam ta manta da abinda ya farun dan haka ta hau rarraba ido tana neman hanyar gudu, gane
hakan da yayi ne yasa yaja hannun ta zuwa Pat d'in shi.






Dan" Allah bross kayi hak'uri banjika bafa"
"To in bakiji ba taya kikasan mai ya faru wato bakijin magana ko my happiness?" ya fad'a yana
kallon yadda tayi tsuruvtsuru shi wallahi dariyama take bashi, yadda duk ta koma kamar wadda
ta aikata wani babban abu tun ranan da suka shirya yake kiranta da wannan sunan hakama
Nassar ya daina kiranta da Adda ya koma my happiness.




Shiru tayi ba tare da ta tanka ba dan in bata ga dama ba itama wani lokacin muguwar muskila

ce sai kayi ta magana tak'i tankaka.





"Kina jina ko?" Ya k'ara sanda yake bud'e k'ofar falonsa, Maryam da take shirin bashi amsa
kasawa tayi saboda ganin irin had'uwa da tsaruwan falon kasa daurewa tayi tace "wow gaskiya
nima bari Baffa ya dawo wajena daban nima nake so kamar naka"






Ta fad'a tana shigewa cikin falon tana lumshe ido saboda daddad'an k'amshi da sanyin da ya
bugi hancin ta sai da ta gama k'arewa falon kallo sannan ta juyo ta dubeshi"waye yake gyara
maka wajennan?"
Ta tambaye shi saboda yadda taga wajen kalkal kamar d'akin mace.






D'an murmushi ya saki ya shafi fuskar ta "Ni nake gyara abuna indai ina so yamin yadda nakeso
amma yanzun tunda gaki na dunga maleji danaki ko?"





Ya K'are da tambayarta, d'an tura baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "hum um ai tunda maneji
ne kawai kaci gaba da abunka,
Zo kiga ya fad'a yana jan hannunta zuwa saman benan dake falon, ta bishi har zuwa d'akin
baccin shi take taga gado lafiyayye mai kyaun gaske "gyaramin zakiyi yau bani da lafiya" ya
fad'a mata yana kallon yanayin ta, kafin ya juya ya fita, tana ganin fitar sa tayi wani irin sufa ta
haye gadon tana wuntsilawa, wani irin taushi taji kamar auduga aranta kuwa fad'i take wallahi
da sake bari Baffan ya dawo nima komai irin na bross na ke so ji gadonsa dan Allah kamar na
wani yar sarkin ta k'ara nutsewa akan gadon.

Shi kam Muhammad har ya sauka ya tuna wayarshi da yabarta tun d'azun saman madubinsa
dan haka ya koma ya dan d'aukowa nan ya shagala da kallon yadda take ta faman tsalle tsalle
sam bataji motsin shigowarsa ba sai dai maganar sa taji.





"In kin gama Ammey tana kiranki" yafad'a yana d'aukar wayar shi datake saman meerrow ya
juya ya fice ya barta batare da ya Kuma kallon inda take ba,





Ita kam sai da ta gaji dan kanta kafin ta gyara har bandaki sai da ta wanke masa kafin ta fito
baya falon wani d'aki data gani ak'asan ta lek'a kawai sai taga computers da yawa aciki Maryam
da Karam bani sai kawai ta shige kafin takai ga tab'awa sai gashi ya shigo kamar an jeho shi.






Ganin abinda take k'ok'arin yi yasa yai masifar had'e rai yace "me kika ajiyemin aanan" ya fad'a
cikin dakakkiyar muryasa data sanshi da ita tun asali.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login