Showing 51001 words to 54000 words out of 65323 words

Chapter 18 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3872

ita har takai ga tafara
temakonta.







Bayan tafiyar Halima Maryam tayi wanka ta fito duk a dining room ta samesu har Baffa sai
mama da har wannan lokacin bata dawoba, kujeran kusa da Baffa ta jawo ta zauna suka
sakashi atsakiya ita da Nassar yayin da Ammey tata kujerar ke kallon ta Baffa "ke uwar taki
bata fad'a miki inda ta tafi ba yau gashi har anyi issha?" Dan yamutsa fuskar ta tayi itama yawon na mama yana mugun damunta tace "zai wuce gidan
waccen haj. Zakiyyar ni bata fad'a min inda zata"
Kwafa Baffa yay cikin b'acin rai kafin yace komai MD ya shigo wanda gaba d'aya kamshinsa ya
cikasu kujeran dake kallon ta Maryam ya ja ya zauna ya wani kafeta da ido ko kunyar su Baffan
bayaji.




Tana ganin haka ta wani tsare gida yayin da Baffa yace "zamu yi magana daku keda Sailuba
idan ta dawo a yawon nata"

Had'e rai Ammey tayi amma bata tanka ba yayin da Maryam ta sunkuyar da kanta k'asa tak'i
yarda koda wasa ta kalli inda MD yake shikam ko ajikinsa ya fitineta da kallo yana cin abincin
sa, bata wani ci abin kirki ba saboda yadda ya takurata ta mik'e , Ammey ta dubeta tace "ya
haka baby banason fa zama da yunwa"
Had'e rai tayi tana hararan MD k'asa k'asa tace "k'oshi nayi ne" daga haka bata jira cewar suba
ta bar wajen, duk suka bita da kallo, shima MD kad'an ya k'ara ya mik'e direct d'akinta ya wuce

ilai kuwa ya sameta tayi d'ai d'ai asaman gadonta da ice cream tana faman sha sam bai ma
kula da abinda takeyi ba sai da ya buga uban sufa ya fad'a kusa da ita sannan ya kula da kayan
sanyin da take sha k'ala bai ce mata ba ya zare robar a hankali ya kai saman frich ya aje ya
dawo ya kuma kwanciya tareda d'ora kansa saman kafafunta a wani firgice ta kai idanunta
saman fuskar shi idanunsa ma shi a lumshe suke take jikinta ya kama wani irin rawa cikin
tsantsar tashin hankali da rawan murya tace me mey meye ha ka ni fa ban a son is Kan ci tayi
maganar a rarrabe tsabar tashin hankalin data shiga, wani muskilin murmushi ya saki yace



Muje zuwa daga

MAMAN ISLAM
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021
NA


HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM


Gaisuwa ta musamman gareku hazikai kuma jajurtattu a kungiyata

Princess Aisha
Miss flower
Maryam H
Allah ya kara muku juriya da hak'uri. Allah ya kara had'e kanmu first class mu dad'e muyi k'arko

💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿






Page 37
"Nine d'an iskan princess?" Ya fad'a yana kallonta ko k'ibtawa bayayi had'e rai tayi tareda fashe
wa da kuka maimakon ya saketa kamar yadda take buk'ata sai kawai ya rungumeta take
zuciyar ta yayi wani irin mahaukacin buga ta fara k'ok'arin tureshi amma ina k'arfin ba d'aya
bane.
"Na tsaneka" ta fad'a cikin kuka sakinta yayi a firgice yace "ni d'in baby ni Muhammad dinki kike
cewa kin tsana?"
Harara ta galla masa da idanunta da suka koma launin ja ta murgud'a masa baki ta fice daga
d'akin tayi d'akin Ammey wacce itama bata d'akin ta fat d'in Baffa.


Bata jima ba Ammey ta shigo hannunta d'auke da Leda da kaya aciki Nassar na biye da ita
yana mitar ta hana Baffa siya masa ways.

Da kallo tabi Maryam wacce ta takure waje d'aya asaman gadonta, kana kallonta kasan akwai
abinda yake damunta "Ammey zoki zauna dan Allah muyi magana" tayi saurin katse Ammey tun
kafin tayi mata tambayar da bata da amsa,

A hankali Ammey ta tako kusa da Maryam tasamu ta zauna ita kuma tayi saurin d'ora kanta
ajikinta tana sauke ajiyan zuciya sannan tace "Ammey zan iya auren MD?" ta fad'a kamar
yadda ta tab'a jin m Bash ya kirashi da sunan


Gaban Ammey ne yai masifar fad'uwa a d'an razane ta dubeta tace "waye kuma hakan?" Ganin
yadda tayi saida tai mugun bata dariya kafin tace "Muhammad dinki nefa MD nima abokansa
naji suna fad'a shine na d'ana" ta fad'a tana b'oye face d'inta ajikinta.



Wani irin sanyi Ammey yaji har batasan sanda ta rungumeta ba tace "zaki iya mana baby me
zaihana ai bazaki tab'a samun kamar saba kamilin mutum managarci wanda yasan darajanki"


"Oh ji Ammey saboda shi d'in na wajen kine kike irin wannan zuzuta shin?"
Dariya Ammey tayi ta lakace mata hanci tace ba haka bane baby ai d'ana d'aya ne tamkar da

dubu nasan shi nasan halinshi yana da halin kwarai zakiji dad'in rayuwa da shi domin yana da
kyautawa"



"Shikenan Ammey tunda kema kin amince da nagartar sa naji na amince zan aureshi kamar
yadda ya buk'ata amma fa na sanar dashi cewa bana sonshi hasali ma ni ban tab'a jin sonsa
araina ba kamar yadda babu son kowane d'a namiji a zuciyana, to yace yaji ya amince shikenan
magana ya kare" daga haka ta mik'e dan fita daga d'akin Ammey ta bita da kallo har ta fice ba
k'aramin farin ciki ta tsinci kanta aciki ba duk da cewa maganar ta na k'arshe bai mata dad'i ba.



Ba k'aramin mamaki tasha ba ganin har lokacin MD yana d'akinta akwance ya wani yi mata
d'are d'are asaman gado kafeshi tayi da ido tana k'arewa baiwar ubangiji kallo MD ba k'aramin
mai kyau bane ta ayyana hakan cikin ranta.


A hankali ta k'arasa rufe k'ofar ta tafi cikin sand'a tana lek'a fuskar shi ya kuwa fisgota da k'arfi
ta fad'a kanshi ta bud'a baki zata zunduma ihu yayi saurin toshe mata bakin da hannunsa, tashi
yai ya zauna itama ya zaunar da ita suna kallon juna yadda tayi wani tsuru tsuru da ita abin
yaso bashi dariya sai kawai ya murmusa baice komaiba ba sai faman kallonta yake.

Yadda yake faman kallonta ba k'aramin takura ta yayi ba ta wani had'e rai tana tura baki bakin
ya sumbata ta wani zaro idanu tana kallonsa da k'yar tace "Allah saina fasa aurenka idan
kanamin irin wannan abun"
"Yi hak'uri my happiness na daina, amma kisani iya hakan ma ba k'aramin kokari nake ba
princess sonki yamin illah bansan lokacin da sonki yayi min irin wannan kamun ba yabi jinin
jikina ya mamaye JININA ba dan Allah ki zauna dani koda bakya sona zanfi samun nutsuwa
idan kina kusa dani" daga haka bai jira cewar ta ba ya sumbaci goshin ta ya sauka yafice daga
d'akin, binsa tayi da kallo kafin ta saki murmushin dabata san ko na menene ba asarari Kuma
tace "maye kawai" sai kuma ta shek'e da dariya tana buga cinya.




Cikin sauran kwanakin hutunsu ba k'aramin hanata sakat MD yayi ba tun tanajin haushin sa har
ta fara sabawa ya masifar nanuk'e mata duk inda zata sai ya bita matuk'ar yana gida idan ya fita
office kuwa kafin ya dawo tana samun kiransa fiye da ashirin tun tana jin haushin sa har ta
daina saima wani mugun shak'uwa da yafara shiga tsakaninsu sosai ta fara kamuwa da son MD
batare da tasan hakan ba ita dai tasan cewa muddun yana nesa da ita ta rik'a kewar sa in yana
kusa da ita kuma tana samun nutsuwa da farin ciki bata gajiya da daddad'an kalaman shi masu

sanyata nishadi.



Cikin haka hutunsu ya kare suka koma makaranta karatu suke babu sauk'i kasancewar suna
shekaran su na k'arshe hakanne yasa Maryam bata da sukuni har rama ta somayi duk da
kasancewar tana samu temako daga MD dan shima idan baku manta ba saida ya fara karatun
likita kafin ya koma ya zama soja.





"Na fad'a miki kiyi hak'uri ta k'arasa karatun kafin na tarwatsa komai"
"Bazan iya ba boka itace fa ta wargatsa min shirina na shekara ashirin da d'aya shirina na
tundaga ranan haihuwar ta har zuwa yau boka badan ina tsoron rayuwar kurkuku ba da wallahi
da hannuna zan kashe ta kamar yadda ta kashe min farin ciki na"


Shi kenan tunda kince haka amma kada kiyi kuka dani duk abinda yafaru ki kuka da kanki
kasancewar idanunta sun riga da sun rufe tace taji ta gani kuma ta amince.



"Boka ana gama mata aikinta nima nawa yasamu kamar yadda muka alk'awarta"

"Ke zakiyya burinki zai cika kuma Deedah bata da irin halin ki gaskiya tana da wankakken
zuciya amma fa wannan buri naki ba makawa zai cika sannan kuma komai zai wargatse"



Maguguna ya had'a musu tare da fad'a musu yadda za ayi kamar yadda aka saba sosai taji
dad'in shirin su na wannan lokacin.



Suna fitowa haj. Zakiyya ta dubeta tace "maganar mu na zuwa India?"

"Yana nan amma ba yanzu ba sai komai ya kammala sai kawai nayi b'atan dabo aneme ni
arasa koya kikaga?"

Suka shek'e da dariya haj. Zakiyya tace Allah k'awata kinsan takan tsiya kina ta sha'aninki

hankali kwance"

"Inafa kwanciyar hankali buri bai cika ba ai CIKAR BURINA shine kwanciyar hankali na"


Haka suka tafi suna hiransu na mugun abu har suka cimma inda suke faking idan sunzo


Wannan karon zuwan bazata Baffa yay musu sai ganinsa kawai sukayi ranan ma Sailuba taje
yankan busa dan tafiyar su yana ta matsowa kai ranan Baffa ba k'aramin ruwan tujara ya zubar
ba ya addabi Ammey da fitina wai duk laifin tane da bata sanar masa abinda ke faruwa.



Cikin b'acin rai Ammey tace "kaga malam kada ka isheni ni nake aurenta da zan samata ido?
Tsayama da zakace haka naga agaban kama ficewar ta takeyi kataba cewa dan me saini daka
raina zakasa agaba da bala i wallahi nagaji kar ka k'ara sakani a shirgin ku da matarka matuk'ar
kana son zaman lafiya a tsakaninmu idan Kuma tashin hankalin kake so nima na iya"


Daga haka ta bige zaninta tabar masa wajen cikin b'acin rai, shima yasani k'ureta yayi shiyasa
ta zage yau take mayar masa da martani.




Muje zuwa



MAMAN ISLAM CE

مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap

p
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM





Page 38


"Dad dan Allah ka taimaka min na rasa yadda zanyi na fad'awa yarinyar nan irin son da nake
mata gashi saura sati biyu mugama karatun mu kasan tare zamu gama dan Allah dad kayi min
rai"



Wani mugun kallon Abba AL HASSAN ya jefawa d boy kafin yace "kaga Kamal ka fita daga
idona na rufe karaba ni da wannan shed'anin yaron dan wallahi ko mata sun kare a duniya
bazan bari ka auri wannan yarinyar ba yayanta da kake gani ba k'aramin aljanin mutum bane
bashi da mutunci ko kad'an d'an iska kamar mai gani har hanji duk sanda kayana suka shigo
saya yajamin babbar asara"



Fashewa da kuka d boy yayi dan har ga Allah yana masifar son maryam ga Dad d'in sa idan
yakafe akan abu shegen taurin Kaine dashi.

Mahaifiyar sa ya kalla yana kuka sosa yace "mammy dan Allah kisa baki dad ya barni da wacce
nake so"
"Uwata ce ita da zatasani yin abinta banga dama ba dagakai har Maimunan wallahi sai na had'a
ku naci kaza kazanku" ya antayo musu wani zagi mai rai da lafiya.

Take ran haj. Maimuna ya b'aci ta kasa daurewa tace "ka daici naka uban me na maka kaji
nashiga maganar ku bare ka dagamin hankali tsabar neman fitina kasan bazaka tab'a min in
k'yale kaba wallahi tunda kai mutumin banza ne mara mutunci kawai"

"Iyayen kine marasa mutunci yar marasa tarbiyya wadda batasan girma da martaban na gaba
da ita ba"

"Iyayen kadai sune iyayen banza suna kallon d'an su yana hark'allar miyagun k'wayoyi amma
basa iya tab'uka komai tur da iyaye irin naka wallahi, ni kuwa iyayena sun bani tarbiyyan da har
ka gani ka yaba kuma ka aure"

Nanfa rigima ta balle harda mare mare dan haj. Maimuna bata ragawa Abba AL HASSAN ko
kad'an tunda ta fahimci tantirin d'an duniya ne ga zagi nacin mutunci.



Cikin fushi d boy ya fice yabar musu gidan yana hawayen bak'in cikin wannan halin na iyayen
sa wanda ko kunyar idanunsa basaji idan fitinar su ya motsa.






Tun bayan da ta shige d'akin ta Baffa bai karajin d'uriyar taba ya tabbatar da fushi tayi, maganar
gaskiya yana mugun tsoron fushin Amina dan bata iya fushi ba idan tayi masa fushi yana
matuk'ar shan wahala.



Yana shirin tashi yabita har d'akinta haj. Sailuba tana shigowa fasa tashin yayi ya koma ya
zauna ya kafeta da ido, ganin irin kallon dayake binta dashi yasa ta d'an sha jinin jikinta sai ta
wayance da fad'in


"La Baffa yaushe ka dawo irin wannan dawowa haka babu sanar wa? sannu da zuwa" nan dai
tahau masa borin kunya.


Shi kam k'ala baice mata ba kafeta kawai yay da Ido hukunci yake mata da haka, yayin da ta
rasa yadda zatayi, sai da ya tabbatar da yagama sanyaya mata jiki sannan yace.

"Waye naki agarin nan da har kullum bakinan me kike fita yi ko me kike nema wanda baki
sameshi anan gidan ba?"

Shiru tayi ta kasa magana sai faman rarraba ido take yayin da Baffa yaci gaba da cewa
"maganar gaskiya Sailuba wannan shegen yawon gantalin naki ya isheni haka idan kuma baki
gyara ba zan d'auki mummunan mataki akanki"

Hak'urin munafurci taita bashi har da kukan k'arya kafin yace ya hak'ura sannan ya d'ora da
fad'in "tunda gobe weekend ne ki sanar da Maryam ta shirya zamu wajen Inna"

A mugun firgice ta d'ago tana duban Baffa yayin da maganar boka yafara kara kaina cikin
kunnen ta kamar yanzu yake fad'a mata kar ta sake ta yarda Maryam ta had'u da Inna domin
akwai babbar matsala ga had"uwar ta tasu domin Inna zaya ruguje musu komai ta yadda har
abada bazasu tab'a nasara akanta ba kamar yadda har yau har gobe suka kasa akan Nassar
domin akwai dafa in datake bashi yake sha.




"Lafiya wai me kike nufine Sailuba da hana maryam kusantar mahaifiya ta idan ke kin gujeta so
kike yata ma ta guje rabon Maryam da taje garin nan tunda aka yayeta sai dai idan Innan ce
tazo ta ganta so kike ki raba yata da mahaifiyata be?"


Cikin dauriya da k'arfin hali tace "a a Baffa ni wacece da zan raba baby da Inna naga nima
Innan nan uwatace dan Allah ka daina yimin irin wannan bahaguwar fahimtar"


Nan dai ta kalalleme shi da dad'in baki har ya sauka daga fushin daya dauka sannan ta wuce
d'akinta da tarkacen da tazo dashi daga wajen bokanta.





Karfe shida daidai ta dawo daga makaranta a mugun gajiye ga d'an banzan yunwar da ta kwaso
tsabar yunwar har wani jiri jiri take gani ta fito a motar ta tana had'a hanya, shima MD shigowar
babu dad'ewa wanka yai ya fito ya hango ta tana takawa kamar mai koyon tafiyar murmushi ya
d'an yi kafin ya taka a hankali zuwa inda take ya d'an hura mata iska a fuska a d'an tsorace ta
juyo dan bata ji zuwansa kusa da itaba tsabar bata nutsuwar ta jarrabawan yau ya azabtar da
su fiye da tunanin mai tunani.

Kallonsa tayi da lumsasun idanunta wanda tsabar yunwa yasa suka wani d'an shige "me yafaru
happiness naganki haka?"

"Yunwa" tace dashi tana dafe cikin ta da ya isheta da k'ugi "ayya baby muje ciki maza Ammey
tagama tuwon dare" da sauri ta kalleshi "Allah tuwo tayi? kasanfa ina son tuwo sosai" d'an
murmushi yayi danshi tsokanar ta yakeyi yayi zaton irin Nassar ce itama batason tuwo kamar
sa.
"Tsokanar ki nake Baffa kawai Ammey tayima"
" Ai kuwa nima tuwon zanci yasin" ta wuce kanta tsaye dining room d'in, saida ta fara had'a
ruwan zafi ta gasa cikin ta kafin ta bud'e tuwon Baffa da Ammey tagama shiryawa gwanim ban
shi'awa ta d'auki malmala tasa aflat ta zuba miya ta soma ci a nutse, duk da bak'ar yunwar dake
damunta hakan baisa ta rud'a kanta tayi irin cin yunwar nan ba, Ammey da ta shigo dan daukar
abincin Baffa tsayawa tayi tana kallon Maryam dake aikawa da tuwo batare da tasan cewa
Ammeyn tazo wajen ba, sai data k'arasa wajen Maryam ta ganta tayi wani wuri wuri da ita can
kuma tace "wallahi Ammey bross ne yace kinmin tuwo"
"Na tambaye kine?"
Ta fad'a tana wurgawa MD harara wanda yake gefe yana d'an murmushi wayarsa a hannu yana
faman daddannawa, bata k'ara magana ba ta d'auki d'an kwandon data jera abincin tayi waje
MD ya dungure mata kai yace" da so kikai ki had'a ni da uwata ko?"
Bata ce komai ba sai harara data galla masa taci gaba da cin abincin ta sai data jita daidai kafin
ta mik'e tana hamdala tawuce kai tsaye d'akinta ta nufa wanka tayi ta yo alwala tayi sallar la

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login