Showing 57001 words to 60000 words out of 65323 words
aikatawa da wanda baza tayi ba, ya rasa mai Inna tayi mata da zafi haka
da ta daina zuwa inda take kuma ta hana maryam ta kusance ta matar da ta rik'e ta ta kula da
ita bata bari tayi kukan maraici ba yau itace abar wulakantawa awajen ta kwafa yayi ya fice cikin
tsantsar b'acin rai da bak'in cikin yadda yake kasa d'aukar mataki akan abinda take masa ko
yaso hakan sai tayi masa wani irin kwarjini yaji tausayin ta ya baibaye shi.
Maryam kuwa yau cikin wani irin farin ciki ta tsinci kanta bakin ta yak'i rufuwa tsabar jin dad'i,
baza tace ga lokacin da sukayi doguwar tafiya irin wannan ba.
D'an d'ago kanta tayi daga kafad'ar Ammey ta dubeta "Ammey wai me yasa Mama bata son
naje wajen Inna kinga fa bansan garin ba gashi Baffa yana yawan zuwa da Nassar amma ni sai
ta hana me yasa bata zuwa kuma bata so naje?"
Wani irin abu mai mugun tauri yayin da taji zuciyar ta babu dad'i ta rasa bak'ar zuciya irin na haj.
Sailuba matar nan fa k'anwar mahaifin tane uwa d'aya uba d'aya sannan kuma mahaifiyar
mijinta amma wofintar da ita irin haka ta rasa wane irin mugun hali ne da matar nan haka.
"Ammey dama kece kika haife ni ba Mama ba wallahi na tsani halinta"
Gaban Ammey ne yay wani irin fad'uwa ta k'ara jan maryam cikin jikinta hakanan take jin
zuciyar ta yana yawan tsinkewa, tsoron ta d'aya kar wani abun ya samar mata 'ya dan 'yan
kwanakin nan mafarkin da take da maryam ba mai dad'i bane hakan yasa bata runtsawa kullum
tana nemar mata sassauci wajen lillahi.
"Allah yasa ta gyara halayen ta"
Mayarm data gane inda Ammeyn ta dosa tace amen.
Na fara ganin sauyi yawan comment yawan typing dan haka inna ruwan comment zan kara
yawan page na gode masoyana ina alfahari daku
MAMAN ISLAM CE
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 41
Ammey ta rik'a jan ta da hira cikin hikima take nuna mata aibun mugun halin da haj. Sailuba
take son d'ora ta wanda ba mai b'ullewa bane, tacigaba da cewa.
"Mutuncin ki shine martaban ki darajanki a wajen mijinki shine ki rik'e Martaba da mutuncin ki
karki yarda ki zubar da kimar ki ta d'iya mace duk randa akace kin rasa martaban ki wannan
abun zaiyi ta bibiyarki har jikoki, bayan haka kuma ita kanta zina tana da mugun illah kuma
yad'o abin yake yay ta binka dan haka ina so ki rik'e min Martaba da kimar ki na d'iya mai
tarbiyya hakan zaisa na samu salama har cikin kabari na"
Gaban ta ne yay wani irin fad'uwa jin Ammey na kiran mutuwa sai take jin kamar mutuwar
zatayi ta d'an dubeta a sanyaye tace "Ammey bangama jin d'umin ki ba ban gama sabawa dake
ba insha Allah bazaki mutu yanzu ba sai mun tsufa kin ga 'ya'ya da jikoki na"
"Kayya'yar nan ita mutuwar ai intazo bata sallama sai dai kawai kiji tayi wuf da mutum fata dai
Allah yasa muyi kyakykyawan k'arshe"
Jiki a san yaye tace "amen" duk sai taji hiran yafita daga ranta dan haka ta lumshe idanunta
kamar mai bacci yayin da k'irjinta yake d'an bugawa sai ta kasa nutsuwa daga hiran da sukai da
Ammeyn.
Ba k'aramin farin ciki momma tayi da ganin Ammey da maryam ba lallai ta ga sauyi tattare da
'yar uwar tata rungumeta tayi tsantsan a jikinta duk k'arfin zuciya irin na momma sai da tani
hawaye ya cika mata idanu ta d'ago Maryam a jikinta ta manna mata kiss a goshinta da gefen
fuskar ta tana jin wani irin farin ciki da k'aunar 'yar k'anwar tata.
Tana rike da hannun maryam suka shiga k'aton falon momman wanda ke d'auke da wasu
had'ad'd'un kukeru masu kyau da numfashi.
Shigar su yayi dai dai da ahigowar yaran mamma 'yan mata guda biyu saiga k'aramar sun
nanma ta shigo tana kukan wai sun barota amota babu wanda yabi ta kanta suka shige da gudu
suka rungume maryam dan sun santa sosai a hoto duk da cewa tun tana yarinya ne irin wanda
Ammey take fakar idon haj. Sailuba tayi mata, amma Kuma ai ga kama nan domin babu ta inda
Maryam tabar Ammey.
Ita kanta Maryam tayi matuk'ar farin cikin had'uwar ta da su yayinda wani irin so da k'aunar su
yayi ma zuciyar ta kamun farat d'aya.
Nanfa falon ya gauraye da hayaniyan su dan maryam dama can bata da bak'unta dan haka ta
sake a cikin su suna kwasar shafta sannan Kuma duk wanda yay mata ta mangare shi kunsan
babyn ba hak'urií ½í¸‚í ½í¸‚
Hakan ba k'aramin nishad'i yasaka momma ba hatta abinci ita ta rik'a bata a abakin ta da k'yar
su mardiyya sukayi nasaran janye maryam zuwa dakinsu.
Haj. Shamsiyya yayar Ammey ce inajin nayi muku wannan bayanin tun farko itama mijinta
babban d'an kasuwa ne yana da rufin asiri mai yawa dan shima Allah yayi masa farcen susa
Yaran ta biyar na farkonta 'yan biyu ne duk maza Abdul Malik, da Abdul jabbar, dukan su sanyi
aure da yaransu, sai Fadeela itama yanzun haka yaranta biyu dan tun kafin auren Ammey aka
haifesu da wayon suma akayi bikin Ammey da Baffa.
Daga bayan sun fidda rai da sake samun haihuwar ne kuma Allah ya sake bata wasu 'yan biyun
duka mata Mardiyya da Fauziyya sai autar su Hanifa wacce itama ak'alla su mardiyya sun bata
kusan shekara goma dan duka yanzune suke shirin zana jarrabawan su na shiga jami'a.
Suna barin gidan Ammey ta dubi haj. Shamsiyya sai hawaye shar shar haj. Shamsiyya ta
dubeta tace "a yada haka Kuma?
Memakon ki farin ciki ki godewa Allah 'yarki ta dawo gareki" rungumeta Ammey tayi tace anty
sai kuma ta kuma fashewa da kuka.
Sai da taci kuka sosai kafin ta d'ago daga jikin'yar uwar tata kafin tace "anty dan Allah idan na
mutu kada kibar Nassar a hannunta zata gur b'ata masa rayuwa" K'are zancen cikin zubowar
wasu sababbin hawayen.
Had'e rai haj. Shamsiyya tayi tace me kuma ya kawo zancen mutuwa ana zaune kalau kadama
ki sake wannan maganar insha Allah tare zaku girma da yaronki har kiga auren shi"
"Karki ga yadda ta tsaneni tana yarinya karkiga halin dana shiga akan ta naci wuya anty yau
zan fad'a miki abinda baki sani ba, INA DA CIWON ZUCIYA, duk a sanadin halin danake
ganin'yata a ciki kuma bani da ikon magana yarinyar tayi wata irin rayuwa ne mara dad'i mara
ma'ana.
Sosai haj. Shamsiyya ta kafe Ammey da ido jikinta yana rawa sosai tace "CIWON ZUCIYA
Amina wannan wane irin mugun hali Allah yayi miki na barin abu arai bazaki fitar dashi kiji sanyi
ba haba Amina" ta karasa maganar cikin fashewa da kuka sosai, taci gaba da cewa "ashe duk
fad'an da nake miki na ki janye 'yarki bakiyi hakan ba kikayi tasa abu aranki har ya zamar miki
ciwo arai, kar kimin haka Amina dan Allah" momma take maganar cikin gurshek'en kuka dan
tasan tunda har Ammey ta furta tana da ciwo to abinne ya girmama.
"Ki yafemin dan Allah anty bana son sakaku adamuwa ne banda ke babu wanda yasan ina da
ciwon dan Allah kar ki bari su Baffa suji hankalin su zai tashi"
Rungumeta momma tayi cikin tsantsar tashin hankalin da tausayin 'yar uwar tata yayin da
Ammey kuma taci gaba da bawa yayar tata labarin irin rayuwar da maryam tayi tare da irin halin
da ta rik'a kasancewa a ciki a duk lokacin da Baffa ya juya mata baya, akarshe kuma dad'a
jadaddawa antyn tata take ta kular mata da yaranta idan ta mutu, nan kuma ta kuma bata
labarin irin mugun mafarkan da takeyi mara dad'i wanda tasawa ranta akwai abinda wannan
makirar matar take shiryawa.
Sosai hankalin haj. Shamsiyya ya tashi amma sai ta danne nata damuwar ta rik'a tausar 'yar
uwar tata har sai da taga ta samu nutsuwa, anan take sanar mata Baffa ya tsaida lokacin auren
Maryam d'in da Muhammad, ai kuwa ba k'aramin dad'i hakan yayi mata ba dan ta jima tanayi
wa Maryam d'in shi'awar auren MD saboda nutsuwar yaron.
Acan d'akin da su Maryam suka bajakolin hirar su kuwa Fauziyya ce ta dubi Maryam tace "dan
Allah sis ki rik'a biyo Ammey kuna zuwa wallahi munji dad'in zuwanki ke d'in fa JININ muce"
murmushi Maryam ta sakar mata tace "shikenan sis zan rik'a zuwa dan nima naji dad'in
kasancewar mu tare Allah ya bar k'auna.
Acan gida kuwa MD ji yai hankalinsa yayi wajen Maryam kamar ya bita sai dai yana binta
Ammey zata gane saboda Maryam ne hakan kawai yasa ya yanke shawaran yakai ma m Bash
ziyara.
Kar ku manta Baffa bai sanar da MD maganar aurensa da Maryam ba hakanan haj. Sailuba
bata sani ba, bawai kuma saboda wani abu yak'i sanar da ita ba sai dan b'ata masa ran da tayi
na barin Ammey ta tafi da maryam d'in alhalin yana son zuwa da ita wajen Inna wanda dama
zai jene dan sanar da ita maganar auren Maryam da MD d'in ne.
Ku muje dai masoyana
Ina alfahari daku duk inda kuke a fad'in duniya
MAMAN ISLAM taku ce mai matuk'ar k'aunar ku
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 42
Bayan ya gama shirin sa ya fito cikin k'ananan kayan da suka matuk'ar amsar sa,ya fito yana
baza k'amshin sa mai kwantar da zuciya.
Yana sako kai haj. Sailuba na fitowa daga lambum kusa da Pat dinsa cikin wani irin sauri tana
wage wage gudun kar wani ya ganta da ganinta ba abin arzik'i ta shuka a wajen ba, wani
mugun kallo ya bita dashi cikin tsana sannan ya yaja wani uban tsaki ya shiga lambun dan haka
nan yaji yana son ganin meta aikata awajen.
Da kallo ya rika karewa wajen kallo har idanunsa suka sauka kan wajen da aka hak'e da alama
wani abun aka bunne awajen, gabansa ne yai mugun fad'uwa ya taka a hankali cikin nutsuwar
sa ya karasa yana nazartar wajen kafin yayi Bismillah ya durk'usa dan tsabar saurin da take
hatta abin hakar bata d'auke ba ta manta da shi a wajen.
Sai da yai addu a sosai kafin ya fara hak'a ramin da tayi, yayi mamakin yadda ta iya hak'a rami
mai uban zurfi haka, yajima yana hak'a dan har ya fara tunanin babu abin da ta binne kafin yaji
hannunsa ya caki wani abu mai mugun tsini da sauri ya janye hannun saiga jini yana bin
hannun nasa wanda jini ya fara bi ga wani mugun radadi da ya zuyarci har kwakwalwar sa,
mamakin hakan yasa kashi saurin lek'a ramin haba da sauri ya janye kansa yana sauke wani
irin wahalallen numfashi sabo da wani fitinannen wari daya daki hancin sa, sai dai abinda ya
gani yasa shi saurin komawa tare da dauke numfashi dan tabbas wannan masifar zai iya masa
illah.
Mikewa yayi ya koma d'akin sa hankali a tashe ya d'auko hanglob jikinsa har wani rawa rawa
yake sosai yazo ya hau fito da abin bakinsa d'auke da addu'a, yanzu kam rawa jikinsa ya kama
sosai saboda tsabar mamaki.
Kan mujiya ne jikinsa duk wasu irin manyan allurai sai kuma wata 'yar k'aramar benu da aka sa
wata katuwar allura aka caki daidai zuciyar ta sai numfashi take fitar wa da k'yar ga wasu irin
curin layu masu yawa suma a saman wata tsuntsu da baisan ko ta mecece ba itama daga gani
ajikace take tama kusa mutuwa.
Idanunsa da sukayi wani fitinannen ja ya runtse da mugun k'arfi ya zauna dab'as a wajen cikin
ciyayin gun ya dafe kansa da yake mugun sara masa da k'arfi yace "innalillahi wainnailahi
raji'un Maryam ko Ammey zata kashe?"
Dan shi abinda ransa ya bashi kenan na ganin wannan masifar alluran dake jikin tsuntsayen da
suke da rai ya fara zarewa kafin ya cire na jikin mujiyar gaban sa na wani irin mugun fad'uwa
hankalin sa a masifar tashe bai ma yarda da kona kayan kai tsaye ba sai da yayi musu fitsari
kafin yasa fetur ya Kone.
Tunda taga Ammey ta fara shiri tace itafa sai gobe zata dawo dan gajiyan hanya bai gama
sakinta ba sosai Abdul jabbar da yake ta binta da kallo yasaki murmushi yace "kawai ki k'yale ta
Ammey ma kawota nida Abdul Malik"
"Rufamin asiri Abdul jabbar Baffanku baisan nazo da itaba, kabari tunda bikin ta za ayi tazo tayi
muku kwana biyu" sai da gabansa ya fad'i da yaji wai bikin ta za ayi dan har ga Allah tayi masa
sosai.
"To 'yata sai kinzo gyaran jikin ni da kaina zanwa 'yata gyara na musamman, dake sana 'ar
tane gyaran amare da haka sukayi sallama.
Tana zaune cikin jin dad'in cikar burinta haj. Zakiyya ta kira tana d'agowa tace "ba nutsuwa ba
kwanciyar hankali ita ba mahaukaciya ba kuma ba mai hankali ba sannan ita ba rayayya ba
sannan kuma ba matacciya ba" hhhhhhhhh suka saki wata muguwar dariya haj. Zakiyya tace
an aikata ke nan?"
Me zan jira k'awata kinajifa boka yace uban yatsaida aurenta da wannan tsinannen yaron dana
fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan bar wannan banzan auren ya faru ba na rantse
kuma" ta k'arasa maganar tana huci
Har lokacin MD yana d'akin sa cikin tsantsar damuwa da nazarin son gane shin cikin Ammey ko
Maryam wa akayi wannan bak'in asirin dayai masifar d'aga masa hankali?
Ya sandai wannan tarkacen bala in ba abin arzik'i aka shuka a cikinsu ba.
Kamar wanda aka tsikara ya mik'e zumbur domin kaiwa haj. Sailuba fatanyar ta da ta manta.
Yana fitowa ana budewa motar su Ammey gidan, dan haka ya dakata har driver ya shigo ya
faka motar duk suka fito da gudu Nassar ya k'araso ya rungume MD wanda yai kasak'e yana
kallon su, yana mai murnan ganin yayan nasa.
Da wani irin kallon mamaki Ammey tabi kayan hannun MD yayin da Maryam ta wuce ciki tana
mai dok'in ganin mamanta.
"MUHAMMAD wannanfa me kayi dasu naganka futu futu haka?'
" Ammey" sai kuma yai shiriu zuciyar sa na wani irin zafi yay saurin dafe kansa kafin yace "wa
take son kashewa Ammey ke ko ZUCIYA TA?
Muje dai
DAGA MAMAN ISLAM
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 43
Kallon Ammey yake dafe da kirjin sa wanda zuciyar sa take barazanar fitowa, itama kallonsa
take da son k'arin bayani.
Dak'yar ya bud'a baki yace "Ammey wani aikin nayi mai wahalarwa Ammey me waccen matar
take nufin yi ne akan ni da matata Ammey na rantse da Allah wani abu yasamu matata ni da
kaina zan d'auke kanta da wu'ka da wadannan hannayen nawa.
Ya fad'a yana d'aga hannun nasa wanda suke wata irin rawa sama.
Da wani irin rawa Ammey ta danki hannun MD jikinta na kakkarwa tace "wayyo Muhammad rik'e
ni zan fad'i" tayi luuuuuu da wani azababban zafin nama MD ya rik'o ta cikin wani irin rikitaccen
yanayi yace "Ammey lafiya kuwa"?
"Kaini d'akina Muhammad banida lafiya" da sauri ya d'auke ta akafad'unsa yayin da jikinsa yake
wani irin rawa jikinsa kuwa ta ko ina gumine yay masa wanka.
Da sauri ta janye wayar daga kunnenta tana fad'in "zan sake kiranki anjima k'awata"
nakamakon juyowa da tayi sukayi ido biyu da Maryam da tajima abakin k'ofar tanajin irin mugun
abun da maman tata take k'ullawa tambayar da Maryam take wa kanta shine
"Shin waye za'a haukata?
Waza a tozarta ya wulak'anta?
Waye zai zama abin k'yamar al'umma?
Me yaye mata take son ya zamo kamar mujiya?
Akan me take so yayi warin jab'a?
Shin dama mama tana yawon bin malamai ko yanzun ta fara?
Ta yarda da daukar wannan babban zunubin ko kuwa?
Dawa take wannan Killin?"
Inda haka ne mama baki da