Showing 36001 words to 39000 words out of 65323 words

Chapter 13 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3565

BACE🔥
2021

NA


HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM








Page 27




Bud'e motar yai ya wulla baya kusa da Nassar sai uban kuka take jijiyan kanta sunyi wani rud'u
rud'u fuskar nan tayi jajur tsabar kukan da takeci.






Shiru Nassar yayi yana kallon yadda Adda nashi take kuka ga ruwan dayake ta faman diga
daga jikinta rawan da jikinta yake kawai ya tabbatar masa da akwai zazzab'i atare da ita.

MD tuk'in yake amma ba acikin nutsuwa ba domin ba k'aramin bugun zuciyar sa kukanta yake
ba ko kad'an baiji dad'in abinda yayi mataba sai dai ko kad'an zuciyarsa ta kasa amsar laifin
ganinsa bai kamata ace ta tsaya magana da wani k'aton agabansa sosai abin ya masa zafi
aransa, wata zuciyar Kuma cemai tayi inbanda abinka kasan waye da har zakayi saurin fushi
haka "zai wuce d'an iskan mate d'in nan nata" ya fad'a asarari Kuma da k'arfi, duk suka bishi da
kallo har Maryam datake kuka sai data tsagaita jin yadda ya bugi sitiyarin da mugun k'arfi.








Suna zuwa gida taba tsaya amsar wayanta ba ta balle murfin motar tayi cikin gida da gudu tana
shashshek'a ta wuce mama da Ammey a falon duk suka bita da kallo, saida tasawa d'akin key
tasan sarai sai Mama ta biyota jikak'k'un kayan ta cire ta shiga ta had'a ruwa mai mugun zafi
har lokacin rawan sanyi take sosai ta shige cikin ruwan tana faman sauke ajiyan zuciya sai da
ta gasa jikin ta sosai kafin tayi wanka ta fito ta shafa mai ta haye gado ranan bata had'u da
Baffanta duk da irin yadda tayi kewansa.







Washe gari ma bata fito da wuriba sai da ta gama duk nuk'u nuk'un ta sannan ta salla wanka ta
ta tsara kwalliya mai kyau da d'aukan hankali ta fito cikin nutsuwar ta duk suka bita da kallo har
tayi wani fayau da ita.






Baffa ya dubeta yana murmushi ya mik'a ta hannu"zonan ki zauna, ya fad'a yana nuna mata
gefensa nayi kewan ku sosai yarana" ya fad'a yayin da tasako hannunta cikin nashi ya zaunar
da ita a kujeran kusa dashi.

Tunda ta fito ya kafeta da ido sai yaga ta k'ara masa wani fitinannen kyau, gaida iyayen nata
tayi, kamar ta share shi sai kuma ta gaidaahi cikin sanyin murya amsawa yayi yana k'ureta da
ido, tai masifar had'e rai tana had'a tea.







Su Mama suna gama karyawa suka bar wajen suka koma falon Baffa da akwai abinda suke son
tattaunawa.



Yana ganin fitar su ya ture nashi abincin ya kwantar da kansa saman tebur d'in yana binta da
wani fitinannen kallo Nassar na ganin haka ta d'auke ragowar abincin sa yabar wajen.





Gaba d'aya ya takura da wannan banzan kallon nasa sai dai bata son tayi abinda zai gane
hakan, kasa cin abincin tayi sai ruwan shayin da take ta karb'a tashi yai ya dawo kusa da ita
kofin shayin ya karb'a daga hannunta ya zauna ya kai bakin ta, d'auke kanta tayi tareda k'ara
tamke fuska.






"Kiyi hak'uri dan Allah, ya jikin naki?" ya fad'a yana shafar gefen fuskar ta, banza tayi da shi
idanunta yana cikowa da hawaye ko abinda d boy yai mata bai sosa mata rai kamar na MD ba.





Juyo da fuskar ta yayi kusa da shi yana k'ara kai mata abincin bakinta "karki min kuka, kiyi

hak'uri dan Allah" ya fad'a cikin sanyin murya, batare da tace k'ala ba ta yunk'ura zata bar masa
wajen ya daka mata tsawar dayasa ta koma ta zauna batare da tasan tayi hakan.





"Wallahi yanzu sai na tattaka ki dan kinga ina lallab'a ki shine kike neman ki kawo min rainin
hankali karb'i dalla malama" ya fad'a yana kai mata abincin baki ganin yanda yai kicin kicin da
rai yasa ta bud'e bakin ya zuba mata abincin haka ya dinga bata tana karb'a tana hawaye har
saida ya tabbatar ta k'oshi kafin ya bata ruwa tasha ya kama hannunta ta suka nufi part d'insa.







Duk jiya bai iya runtsawa ba saboda tunanin abinda yayi mata iya binciken sa nason gano
dalilin yi mata haka amma amsar d'aya ne tayi waya da wani agabansa dalilin fushin sa akan
hakan simple words INA SON TA duk ta yadda ya juya al'amarin amsar d'ayace abin ya masifar
tayar masa da hankali bai tab'a tunanin hakan daga zuciyar saba sam batayi masa adalci ba
kuma ta zalunce shi tayi mai abinda zai hana shi cika alk'awarin daya daukarwa Baffa, dan iya
jiya kawai ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin data shiga sosai ya bama kansa
laifi akan abinda yayi Mata.






Suna shiga falon ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta yana
murzawa a hankali wanda hakan yasa taji wani irin yarrrrrrrr ajikinta da k'arfi ta k'wace hannunta
ga mamakinta sai ji tayi yace "bani da lafiya" shine abin taji ya fad'a cikin wata irin murya wadda
take taji wani irin kasala ya rufeta saboda salon dayai maganar kasa ce masa komai tayi sai ma
k'asa da ta maida kanta tana faman cukwaikwauye gefen d'ankwalin doguwar rigan da yake
jikinta

"Ni kaina bansan abinda yasa nayi miki hakan ba princess nasan ban kyautaba abinda nayi,
abin yayi mugun damuna na rasa yadda zanyi na kasa runtsawa saboda neman dalilin da
yasaka nayi miki hakan, sai dai dalilin dana samo bai min dad'i ba ko kad'an Maryam" ya
k'arasa da kiran ainihin sunanta wanda sai yaune ta tab'a jin ya kira sunanta iya tsawon rayuwar
ta, sai taji wani iri aranta sai dai bata d'ago kaiba bare tace wani abu.




Ga mamakinta sai ya kamo fuskar ta ya juyo da ita saitin tashi ta d'an kafe shi da ido yadda
taga yayi mugun yin kalar tausayi idanunsa da ta kalla kuwa sai da gabanta yai masifar fad'uwa
da sauri ta mai da kanta k'asa.






Abinda ya k'ara bata tsoro yadda ya zame ya durk'usa agabanta yana kallon cikin idonta yace
"dan Allah princess in rok'i wani alfarma a wajen ki?"


Yadda yayi matan ne yasaka batasan sanda ta d'aga masa kai ba alaman shi take sauraro "
dan Allah princess ina so na zama amininki na k'ut da k'ut yanda komai zakiyi sai kin sanar dani
nima duk abinda zanyi sai na sanar dake sannan dan Allah yaron jiya kar ki k'ara d'aga kiran shi
namayi blocked d'insa dan Allah kimin wannan"




"Aini bazan iya abota dakai ba kai mugune baka da tausayi daman ai su sojoji basu da imani shi
yasa na tsan"..........bai bari ta k'arasa ba yayi saurin rufe mata baki da hannunsa cikin sanyin
murya yace "zokiji Allah na daina daga yau bazan kara b'ata miki rai ba"





Idan na tabbatar da hakan sai na zama friend d'in naka amma ni yanzun banyin abota dakai
yasin dan zaka iya kashe ni wata rana ai dama Mama tace komai dad'in ka da 'yan " ke"

Ya buga mata wani shegen tsawa "wallahi kika Kuma min zancen d'an ubannan sai na sab'a
miki kammani yanzun nan haba kin ishe ni da wani'yan uba'yan uba'yan uban............ya
dank'aro k'aton asher ya dank'ara kafin yaci gaba da fad'in duk wanda yasa miki wannan
tunanin jakine shi dabba ne mai kwakwalwan kifi Kuma daga yau ina so kisa aranki cewa baki
da wani d'an uba duk uwa d'aya uba d'aya muke agidannan tashi ki fita" ya fad'a cikin daka
mata tsawa yana nuna mata k'ofa ai da gudu ta fella cikin rawan jiki dan yanayin sa ba k'aramin
firgita ta yayiba.





Komawa yayi saman kujeran da ta tashi ya zauna tare da kwantar da bayansa yana fitar da
wani mugun huci me azabar zafi aduniya bai tab'a ganin matar daya tsana kamar Sailuba ba ya
tsane ta ya tsane ta ya tsane ta har baisan yadda zaiyi ba








MAMAN ISLAM CE
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM




. page 28



Tana shiga d'akinta ta mai da k'ofar ta rufe kamar ance ya biyota ne, k'arasawa tayi bakin gado
ta zaune tareda dafe k'irjinta da har lokacin bai bar bugawa ba ta "jarababbe kawai mutum babu
abinda ya aje sai masifa ta fad'a tana kwanciya akan gadon bata jimaba kuwa bacci yayi awon
gaba da ita.





Tunda ya zauna ya lumshe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, so yake kota wane hali sai ya
raba Maryam da haj. Sailuba domin wannan matar bata da maraba da matar shed'an muguwar
hatsabibiya ce tasan takan mugunta shi kansa yana tsoron shirin da take kan 'yar mutane
domin yafi kowa sanin cewa ba rainon banza haj. Sailuba tayi wa Maryam ba dan bata aikin
banza shi yasa yake son ko ta wane hali ya yakice Maryam daga jikinta kafin ta kai ga halaka
ta.







Ganin zaman sai k'ara bijiro masa da wasu irin tunaninka yake yasa yai wanka ya bar gidan.





A falon Baffa kuwa bayan sun gama d'an tab'a hiransu kamar yadda suka saba Baffa ya d'an
dubi matan nasa yace "yau ina so naje k'auye ba kuma zan dawo yau d'in ba sai Allah ya kaimu

gobe"




A matuk'ar firgice haj. Sailuba ta d'ago tana duban Baffa cikin tashin hankali yaushe tayi
wannan saken ca take ta riga da tagama da babin wannan tsohuwar me shegen taurin kan tsiya
ai kuwa zata gyara mata zama yanzu dai ba ta ita take ba ta wannan 'yar matsafin mutumin da
aiki baya cinta take.





A fuska ma nunawa tayi tafi kowa murnan zuwansa a bad'ini kuwa ji take kamar tayi ta ihu
domin har ga Allah tun lokacin da Inna ta bada shawarar ayi mata kishiya ta sha alwashin sai ta
d'an d'ana mata guba fiye da wacce ta d'an d'ana mata.







Sai da ya fara zuwa wajen malam Babba kamar yadda ya saba yauma saida ya bashi rubutu
yasha ya shafe jikinsa sannan yake bashi a duk lokacin dayake gari, kafin ya sanar dashi zaije
ganin gida ba k'aramin dad'i malam yajiba domin hasashen shi yazama gaskiya cewa Baffa
rabashi ake son yi da mahaifiyarsa shi yasa yaji sam baya son zuwa, amma duk wanda yake
wannan abun sam bai kyautawa kansa ba.







Bayan fitar Baffa babu jimawa itama ta shirya ta fice bata zame ko ina ba sai wajen bokanta
kasancewar haj. Zakiyya sunbar k'asar da mijinta yasa batama tsaya b'ata lokacin tab'a ta wuce
abin ta.

Bayan tagama korawa bokan ta bayanin aikin da take son yayi mata ya jima sosai yana zane
cikin k'asa kafin ya d'ago ya dubeta yace. "akwai abubuwa da yawa wanda kika jima kina
k'ullawa duk tunaninki basa yiyuwa?"
Ya fad'a yana kallonta, shiru tayi domin batayi tunanin aikin da take yana ciba dan bata ganin
nasara a ciki.






Aikin ki yana ci kuma abubuwan da kike sunyi yawa kuma duk ta sigar da kika d'auko hanyar
wargaza komai tanan zai wargaje zaki sha mamakin rana da lokaci da waje amma kuma akwai
cin amana da bayyanuwar asirinki daga baya daga wajen mutum mafi kusa dake wannan shine
ki tashi kije da baya banda waiwaye daga yau bazai k'ara zuwa wajen uwarsaba sai dai ita tazo
shi da garin nan sai dai yaje gaisuwar ta bayan ta rasu.








Tunda takwanta take waau irin mafarkai marasa kan gado sosai take jujjuya kai tana gumi babu
abinda yafi rud'a ta sai tsintar kanta da tayi a wani a hali mara dad'i tana cikin jujjuya kai kamar
wacce aka tasa ta bud'e ido a firgice, sai da tayi addu'ar tashi a bacci kafin ta mik'e cikin tashin
hankali ta hau karanto hasbinnallahu wani imal wakil sosai abin ya tsaye Mata arai.




D boy ne a office d'in babanshi suna hira yake sako masa maganar Maryam Abba AL HASSAN
yace " 'yar waye?"
" 'yar Baffa Abubakar ce"
" Kai k'arya ne wallahi badani ba ka rasa wa zaka d'auko min a matsayin suruka sai k'anwar
wannan bom d'in wallahi ba isa ba baka isa ba nace dan ubanka"

"Ni wallahi Dad ita nake so dan haka banga wanda ya isa hanani aurenta ba waima Dad meke
tsakaninka da yayannata ne naga ko sunan su kaji saika firgita?"






"Ban sani ba dan uwarka kuma muddun nine ubanka ban yafe maka auren wannan irin masifar
ba"
" Muddun kaga ban aure taba ka tabbatar mutuwa nayi amma kai baka isa hanani auren taba
wallahi" ya fad'a cikin dukan teburin tsakiyar su cikin murgud'a baki kamar wani sa 'ansa,

Wannan ba komai bane a wajenshi dan al amarin gidan Abba AL HASSAN babu tarbiyya ko
kad'an da gaba d'aya sun gama sangarta d'an nasu kasancewar shi kadaine d'an da suke da.





"Tunda haka kace to wallahi babu ruwana duk abinda ya biyo bayan ka kar kasawa ranka cewa
na san ka dan wallahi ko kallon inda kake bazanyiba.




"Ba damuwa" Kamal ya fad'a yana ficewa daga office din





Plss manage




Daga taku MAMAN ISLAM CE

مسب الله نمحرلا رلا ميح

*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM




Page 29

Wanka tayi ta tayi alwala dake lokacin an fara kiran Azhar dan haka tana gabatar da sallar ta
shirya tareda daukar bag d'in ta ta fito babu kowa a falon sai Ammey.




"Ina zaki haka?" Ammey ta tambaya tana kallon fuskar ta dayake cike da damuwa' kamar
bazata tanka mataba sai kuma tace "shopping" kamar maijin tsoro tayi maganar"
"Zonan" Ammey ta kirata kallon Ammeyn tayi kamar tayi mata gardama sai kuma ta karasa
kusa da Ammeyn ta zauna ta d'an jingina jikinta dana Ammeyn,abinda bata tab'a yiba iya
tsawon shekarun datayi a hannun haj. Sailuba batama samu anbar ta taje inda take ba bare ta
rab'etan.

Wata irin ajiyar zuciya Maryam ta sauke mai k'arfin gaske lokacin da ta kwantar da kanta jikin
mahaifiyar ta ita kanta Ammeyn sai dataji wani iri aranta bata san sanda wasu irin hawaye suka
zubo mata ba tayi saurin gogewa dan kar tagani.



Duk inda uwa take ko a ina ne ko a wane hali take ta fita daban hakanne ya kasancewa
Maryam jitai wani irin nutsuwa na shigarta tareda wani d'an Karen sanyi da ya dirar mata lokaci
guda alamun zazzab'i keson kamata.




Haka nan batasan dalil ba kawai taji ta kama hawayen da batasan ko na menene ba tun iya
hawayen ne har tafara shashshek'a, a rud'e Ammey ta d'ago fuskar ta tana kallon yadda take
shashshek'a kallon lips d'inta tayi yadda suke rawa sosai batasan sanda ta k'ara k'ank'ame ta
ba tana d'an buga bayanta kad'an kad'an batare da tace komai ba domin tasan tabbas itama
idan tayi magana nata kukanne zai fasu.






Sai da suka shafe ak'alla mintuna uku kafin Ammey ta d'ago ta ta fara share mata hawayen "me
yake damunki?"
Ta tambaye ta ahankali kamar tana jin tsoron wani yajita tace "Ammey jikin yafi na Mama dad'in
kwanciya kuma ga d'umi,dan Allah Ammey nima ki rik'a rungumeni kamar yadda kike wa
Nassar"





"Naji amma sai kin fad'a min abinda yake damun ki kwanakin nan, na lura kina da damuwa keep
ki fad'a min koda ahawaran da zan baki" kallon Ammeyn ta dingayi babu k'ak'k'autawa yayin
data ta dinga jin wani abu mai sanyin gaske yana ratsa ta, tunda take da maman ta bata tab'a
tambayar ta damuwanta ba sai dai idan taganta a damuwan ta d'ebi manyan kud'ad'e ta bata
tace taje ta kore damuwan ta.

" Ina jinki'yar albarka maza ki fad'amin ki d'auka cewar kina fad'awa mahaifiyar ki ne kima sa
aranki cewa ni mahaifiyar kine zan miki maganin duk wani damuwaki a duniya,wanda kuma yafi
k'arfi na zan fad'a wa ubangiji na"





Ammey ta fad'a tana saurin goge hawayen daya zubo mata dan kar ta gani Muhammad dayake
tsaye bakin k'ofar tun sanda Ammey ta kira Maryam ya saki wani boyayyar ajiyar zuciya aransa
yana fatan Allah ya karya ak'adarin haj. Sailuba.







"Ba komai" ta fad'a a hankali "kwai baby command fad'a min kinsan babu kyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login