Showing 42001 words to 45000 words out of 65323 words

Chapter 15 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3869

budurwar ba"

Sanda maryam tai maganar hararan ta tayi tace "da alama kin sami b'acewar tunani name sake
banda haka babanmu fa d'aya da kike wannan zancean aman babu tashin zuciya" ta k'arasa
tana wani irin kallon Maryam d'in da kuma yin kamar da gaske aman zatayi.

A lokacin murmushi Maryam ta sakar mata tace "ai lokaci zai nuna kuma kinsan lokaci baya
k'arya"

"Hmm amma wallahi name sake ban tab'a tunanin kina da tab'in hankali ba sai yau"

"Zaki ce na fad'a miki wallahi kallon SO bross yake miki bana sister ba kuma zaki tabbatar da
magana na wata rana"



Ji tai wani irin fad'uwar gaba ya rikito mata lokaci guda ta ware idanunta akanshi tayi wani
mugun tureshi da k'arfi ta mik'e daga jikinsa, ta doshi hanyar fita hankali tashe.
Shima ji yai hankalinsa yayi mugun tashi ya bita yana kuranta bata ko juyo ba bare yasa ran
zata amsa sai ma wani maganar na Maryam da yake dad'a dawowa kanta a yanzun.

"Ki duba da kyau Ammey batayi shekarun da zata haifi mutum kamar bross ba sai dai ko
k'aninta kuma idan kinje gida ki tambayi Mama"
Tsayawa tayi a jikin motar MD ya k'araso yana kallon ta hankali tashe' yayin da Hajara da m
Bash ma suka fito domin yadda MD yake kwala kiran Maryam princess princess ba na lafiya
bane sai dai duk nacin m Bash wajen son jin abinda ya had'a su babu wanda ya tanka musu

Da k'yar Maryam ta iya d'ago idanunta da sukayi mugun ja tsabar damuwar daya kawo mata
farmaki lokaci guda ta kalli Hajara ta daga mata hannu har da murmushin k'arfin hali tayi mata.

Shi ko MD bai iya yace komaiba ya figi motar da mugun k'arfi,duk da yadda hakan ya kad'ata
yadda taga yana musu ganganci da rayuwa, amma bata d'ago ba saima mai da kanta datayi
k'asa batare data shiryawa hakan ba wani fitinannen kuka ya kwace mata, wani irin wawan
burki ya taka wajen wasu bushiyoyo ya faka ya kafeta da ido kafin a hankali ya d'ago da kanta
yana kallon yadda take rusgar kuka sai kace wacce aka ce mata Baffa da Ammey ne suka mutu


"Ki rufamin asiri dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki daina kukan nan haka"
Kallonsa ta kumayi yayin da kukan ya dad'a kwace mata wanda shi kukan nata yafi komai d'aga
masa hankali
"Pls" ya fad'a a hankali amma ina bata saurare shi ba "dan Allah" ya kuma fad'a a hankali yana
d'an janta kusa dashi ya soma share mata hawayen da k'yar yasamu tayi shiru amma bata ce
masa kanzul ba.

Har sukaje gida bata k'ara yarda ta tanka masa ba duk irin yadda yake rarrashin ta kuwa,
Yana fakawa ta balle murfin motar tayi cikin gida da sauri ko kayan da suka siyo bata tsaya
d'auka ba, binta yayi da kallo har ta shige kafin yasaki wani irin ajiyar zuciya mai k'arfin gaske.

Har lokacin Mama bata dawo ba dan k'ofar ta yana nan a yadda ta barshi da zata fita wani irin
mugun tsaki tasaki wanda yasa Ammey dake fitowa daga d'akin ta zata shiga kicin, da kallon
mamaki Ammey ta bita ganin yadda tayi mugun fita a hayyacin ta.


"Ke lafiyar ki 'kalau ina yayan naki?"
Ammey ta k'arasa tana tambayarta ta fad'awa tayi jikinta tare da fashewa da kukan da yake ta
cinta, rik'o ta Ammey ta yi hankali a tashe tajata zuwa d'akin ta zaunar da ita tayi abakin gado ta
d'ago kanta tana share mata hawayen kafin tace
"Me yafaru, ko wani abunne ya samu yayan naki?"
Girgiza mata kai Maryam ta yi " to me ya faru?" ta k'ara tambayar ta hankali tashe " Ammey
kece kika haifi Muhammad?"
Maryam ta tambaya tana kafe Ammeyn da idanunta da suka kad'a sukayi jajur,

"Me ya faru da har ya daga hankalin ki haka kike min wannan tambayar? ji dan Allah yadda ki
koma ji yadda idanunki yadda suka kubura tsabar kuka, bana san haka karki karamin irin haka ji
yadda kika tashi hankalin ki nima kika tayar min da nawa?"


Duk abinda yafaru ta kwashe ta fad'a wa Ammey, wani irin sanyi ne ya kwaranya mata arai ta
rungumeta tana fad'in "yanzu ke dan wannan abun kike tayar da hankalin ki ai wannan ba abun
tada hankali bane Kinga shikenan zai samu mai kula dashi ko"?

Ammey ta d'igawa dogon sharhin ta aya "kamar ya zai samu mai kula dashi ban gane ba
Ammey?"
Eh kinsan Abban ku Hassan?"
Na garin su Inna?"

Itama ta tambaye ta
"Yauwa d'iyar albarka shifa ina d'an sa da matarsa ta haifa ta mutu ta barshi?"
"Ba ance yana k'asar waje karatu ba?"
"An fad'i hakane kawai saboda wasu dalilai amma ba kowa bane face Muhammad"
Idanu Maryam ta zaro duka waje tana kallon Ammeyn da madaukakin mamaki
" Hum shine" Ammey ta fad'a tana daga mata kai ganin irin kallon da Maryam take mata.

Nan ta bata labarin MD kamar yadda Baffa ya bata tundaga haihuwar sa da mutuwar mamansa
wanda ko abinda ta haifa bata sani ba da yadda Inna ta raune shi har ya girma da yadda matan

banansa suka soma azabtar da shi duk da cewa ba gida day'a suke ba har dai MD ya fara wayo
ya daina zuwa gidan har zuwa d'auke shi da Baffa yayi har yanzun da yazama wani abun sosai
Maryam taji tausayin sa yayi wani irin kamata Allah sarki bawan Allah shi baima tab'a ganin
mahaifiyar sa ba ta ayyana aranta "Allah ya jikanta da rahama" ta fad'a tana share guntun
hawayen da ya zubo mata
"Amen" Ammey ta fad'a tana shafar kanta kafin tace "maza jekiyi wanka kiyi salla kinga lokacin
ta ya shiga Kuma yanzun hajiya zata iya shigowa tunda magriba yayi kar ta ganki anan"

Batace komaiba ta fice a d'akin.






Taku ce

MAMAN ISLAM

مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM

Page 32


Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan
sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata
kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta
b'ata mata shiri.


Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan
matsiyatan ba?"
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano
kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango
tsantsar tashin hankali atareda maman tata.




"Lafiyan ki kalau mama?"
Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar
tashin hankali.



Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya
jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da
mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa.


" Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?"

" Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar
yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?"
Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali.


Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace
"Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?"

"Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us"


"Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma"



"Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa"
Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje.





Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai
kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta
shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama
sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da
kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad'i dan tun d'azu take ta faman juya labarin da
Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani
ba amma rashin mahaifiya ba d'an k'aramin gib'i bane ga rayuwar yaro.



Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo
bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k'arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya
dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar
kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani
arnen tsaki tsanar yarinyar yana k'ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai
aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD.




Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k'ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi
k'arfin halin kama mabud'in k'ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu,

Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin
kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace
ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa.

Jin motsin bud'e k'ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k'ofar shima bugun zuciyar sa yana
kara yawaita bugu ya wani irin kafe k'ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d'auke da
siririyar sallama da k'yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad'a binta da kallo ta d'an
kalleshi suka had'a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani
sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak'uri shi yasa.




Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad'anta "babyna me kike sone
kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?"


Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace "ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace
tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?"

"Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k'arfi na kasa koda hadiyar yawu" binshi tayi da kallo
mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace "kasha magani me yake
damun ka bross?


"Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala
na, kuma jin dad'i na, Maryam kece komai na" yafad'a cikin muryan daya mugun karyewa ta
daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi
" Kazo muje"
"Kije zanzo yanzu"
"Ni dai Baffa yace k'afa na k'afar ka"
"To jira nayi wanka"
Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu.


Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa
kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake.



Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik'o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata
kyau ga wani fitinannen k'amshi dayake yi ma mugun dad'i, har sukaje bakin falon babu wanda
yace da d'an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin
nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d'an saki kafin ya rufa mata baya

Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da

tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace "maman malam daga aike kuma sai
najiki shiru?"

Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d'ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin
fad'a yay saurin cewa "sanda taje ina wanka"

"To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka"

"Nima Baffa akwai abinda nake son fad'a maka tun kafin kaje wajen Inna kuma naso binka sai
bansan katafi ba"


Dafa kanta yay yace kar ki damu wannan zuwan ma sai da Inna tai fad'a sosai na rashin
ganinki, laifin mamanki ne da tafiya ya tashi sai ta kawo uzurin da dole ake fasa tafiyan dake
shiyasa Nassar kawai Inna tafi sani.


Yay maganar yana kallon haj. Sailuba da tayi wani kicin kicin da rai zuciyar ta nayi mata mugun
sak'a.


Shima daga haka ya wuce falonsa Ammey ta tashi ta rufa masa baya dake yau ita ce da girki.

Suna barin wajen ta juyo da niyyar zuba abincin dan har ta k'agu taji neman da Baffa yake mata
sai karaf idanun ta suka sauka cikin nasa ya wani yi tagumi ya kafe ta da ido, a ranta tace
gaskiya wannan mutumin da bansan shi ba babu abinda da zai hana nace maye ne yadda yake
da jarababbe kallon nan.
Azahiri Kuma abincin da zata ci ta d'iba a flat ta mik'e zata bar masa wajen, gane hakan da yayi
ne yasa yayi saurin dafe hannunta yana binta da wani marai raitaccen kallo "dan Allah kar ki tafi
ki barni"



Ya fad'a kamar zai mata kuka, binshi tayi da kallon mamaki, yayin da shi kuma ya k'ara wani
marai raice mata sai ta samu kanta da kasa yi masa musu ta koma ta zauna, shima tsulum ya
taso daga inda yake ya dawo kusa da ita "lafiya?"

Tace dashi tana kallon yadda yake wani faman shafa cikin sa d'an marairaice mata yayi
yace"yunwa nakeji nima"

Abincin da ta zuba zata ci ta tura masa ta d'auki wani flat d'in yay saurin dafe hannunta yana
girgiza mata kai ta d'an kafe shi da ido dan neman k'arin bayani "ki bani mana" ya fad'a yana

kallonta ta d'an had'e rai shi kuma ya kafa mata naci sai da ta bashi haka kuma shima yabata
suka ci suka k'oshi.


Da alama nacin MD ma kawai zai sa yasamu yadda yake so lol🤣🤣🤣🤣🤣






















Maman Islam ce

مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021

NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM




Page 32


Tana fitowa daga d'akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k'yar abakin k'ofar Ammey dan
sam bata son had'uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata
kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b'aci babu makawa wannan la'a nanniyar yarinyar ta
b'ata mata shiri.


Tsawa ta buga mata tace "ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a'mala da wadannan
matsiyatan ba?"
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano
kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango
tsantsar tashin hankali atareda maman tata.




"Lafiyan ki kalau mama?"
Kallonta mama ta d'an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b'angaren ta cikin tsantsar
tashin hankali.



Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad'awa a masallaci ba ta zari waya
jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da
mugun mamaki ta d'aga kiran tana cewa.

" Ya akayine k'awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?"

" Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K'are na shiga uku zakiyya da wannan la'ananniyar
yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?"
Ta fad'a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali.


Ita kanta wani irin fad'uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace
"Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had'u?"


"Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had'u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib'us"


"Allah yasa bakice zakiyi mata fad'a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma"



"Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa"
Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje.





Ganin yadda maman ta d'aga hankalinta har tayi hanyar d'akin sai kuma ta fasa aranta tace ai
kina da kud'i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d'akin ta batare da wani damuwa ba ta
shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d'an yi kwalliya sama
sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da
kallo babu MD awajen duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login