Showing 39001 words to 42000 words out of 65323 words
d'a ya rik'a wa
mamansa k'arya" batasan sanda ta rushe da kukaba tace "Ammey k'udi sune maganin ko wane
matsala?"
Ta tambaye ta abinda yafi komai damunta a rayuwarta
" Injiwa?
Duk wanda ya fad'a miki wannan k'arya yake ko waye yana yaudarar kine kawai, amma akwai
abinda k'udi bai isa yayi maka shi ba da yawa ma a duniya dan haka duk wanda ya fad'a miki
hakan yayi karya ya fad'i son ransa ne kawai"
Ta fad'a tana shafa kanta nan "Mama ce koya ta ganni a cikin damuwa sai ta d'ebi manyan
kud'ad'e ta bani tace zasuyi min maganin ko wace irin matsala a duniya" duk da cewa tasan
zata iya jin abinda yafi haka daga d'iyar tata ma amma hakan sai yayi masifar d'aga mata
hankali tace
"Tana iya miki kyautar nawa lokaci guda?" Ta tambaye ta cikin tsantsar tashin hankali "har dubu
d'ari biyar cash tana bani tace muje mu kama waje muyi d'an kwarya kwaryan walima wai na
jikina ma su mori arzik'in ubana"
"Kina yi?"
Ammey ta k'ara jefo mata wani tambayan "da inayi amma yanzun tara k'udin nakeyi da sukayi
yawa na sai gida kuma da wasu kusan 7 million a d'akina har sani fa take na d'ebo mata k'udin
Baffa kinsan baya k'irga wa yake ajiyewa"
"Innalillahi wainnailahi raji un" shine abinda Ammeyn ta fad'a cikin tashin hankali "Allah sarki
Nanne da Anty shamsiyya yau ga abinda kuke fad'a min yana shirin faruwa tayi maganar cikin
zubowar wasu zafafan hawaye.
Da sauri ta share hawayen tace"kin yarda dani zaki iya bani ajiyar duk abinda kika mallaka?" Ta
tambaye ta cikin rawan murya
" Eh Ammey me zai hana ta bata amsa yayin da wani irin sanyi yake kwaranya aranta
"Yayanku fa?" ta k'ara tambayar ta
"Tab'ni bazan bashi ba mugu ne gashi masifaffen tsiya ta fad'a tana hararan gefe.
Murmushi Ammey tayi shi kanshi Muhammad dake bakin k'ofar maganar ta ya bashi dariya dan
haka ya d'an murmusa yana shafar k'irjinshi a hankali kamar wanda wajen yake masa ciwo
"Kece baki gane halinsa ba amma yana da kirki sosai kuma zai kula daku sosai koda ace yau
babu Baffa baku da sama dashi SHINE GATANKU"
Tab'e baki tayi ta mik'e tana cewa "anjima zan kawo miki A T M d'ina Mama bata san dashi ba
saboda shegen kashe k'udin ta idan ta sani duk saita rance kuma ba biyana take ba, tunda
kince kin yarda dashi sai ki bashi zan had'a shi kuma da na siyi gida ta hanyar sa wallahi ya
cinye kwandala ta bazai yi ciwon kai ba biyana zaki"
Duk yadda yaso dauerwa saida ya fashe da dariyan maganta domin ta bashi dariya sosai
wallahi, ita kanta Ammeyn murmushi take kafin tace "yanzun to ina zaki naga ko abinci baki
ciba"
Eh banjin yunwa zanje shopping, ina Nassar ya rakani?"
"Za daiki siyan kayan zakin da kika saba maza muje yau nima na fanshi hajiyan tunda bata nan
muje na baki da kaina tunda ta gama shagwab'a ki"
Sai taji ta kasa yi mata musu tana zuba mata abincin kafin ta fara bata MD ya shigo wajen da
sallama Ammey ta d'ago ta dubeshi ganinsa da kayan gida tace "yau kuma ina uniform d'in?"
"Banje office ba yau?" Ya fad'a yana zama facing d'in Maryam datai wani kicin kicin da rai,
murmushi ya saki lokacin da ya juyo da hannun Ammey santar bakin sa ya amshe abincin da ta
d'ebo zata kaima Maryam baki, bata san sanda ta b'alla masa wata shegiyar harara ba ta juya
ta kalli Ammey a marairaice tace Ammey"
"K'yale shi baby in yasa tsiya yanzun zan korashi amshi maza kici ki k'oshi kinji yarinyar kirki ta
fad'a tana bata, sosai taci abincin, tunda take zata iya runtsawa cewar bata tab'a samun farin
ciki irin na yau a rayuwarta ba sai taji Ammey ta bala in kwanta mata arai.
tana gamawa tasa tusio ta goge bakinta ta zari mukullin motar ta"sai na dawo Ammey"
"Baki ba Ammeyn ta fad'a tana mik'ewa ta k'arasa kusa da ita kanta ta dafa tayi mata addu'a
sosai kafin tace "Allah ya tsaremin ke ki kula da kanki ki kare mutuncin ki domin shine Martaba
ki"
Wani irin sanyi Maryam taji aranta ta rungumeta ta tace "na gode sosai Ammey dan Allah ki rik'a
min haka please"
"Kullum nake miki haka amma ba kusa da kusa ba amma ko yaushe kece farkon wacce nake
fara yiwa addu'a kafin nida kaninki da sauran makusanta na"
"Allah Ammey?" Maryam ta tambaya ciki farin ciki tare dajin yadda matar tak e k'ara bin dukan
jikinta, dama haka halin Ammeyn yake amma mama tace muguwa ce.
MAMAN ISLAM CE
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 30
Rungumeta ta k'ara yi tace "na tafi Ammey na"
"Sai kin dawo'yar albarka"
"Nima zan rakaki zaki siyamin chocolate?"
Yayi mata yadda Nassar yake mata, batasan sanda ta saki murmushi ba ta fice a daga wajen
cin abincin, binta yayi shima domin yi mata rakiya.
Tayi zaton shi zai jasu, sai kawai taga ya bud'e wajen mai zaman banza ya k'ame abinsa, tura
baki tayi tana d'an hararansa ta gefen ido, sarai ya ganta sai ya mai da kansa gefe yana d'an
murmushi hakanan yanzu komai tayi burge shi take.
Sai da ta zauna ta sakarwa mai gadi k'aton hon wannan ba sabon abu ba ne awajenea sam
indai zatayi tuk'i batayin na nutsuwa tun lokacin data ke a matsayin Maryam ba yanzun da ta
zama mero ba lolí ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
Shi kanshi Muhammad sai da yai mamakin ganin yadda ta wani figi motar da masifar gudu bai
san sanda ya juyo yana kallonta ba "ke baki da hankali ne?"
Ya fad'a lokacin dayaga ta kusa fad'awa wani d'an rami dake tsakiyar titin data hau tayi wani irin
kaucewa ramin
"Princess tsaya" ya da sauri yana dafe kan sa da duka hannayensa.
Babu musu ta nemi waje ta faka dama da biyu ta keyi dan ya amsa banda son banza tana tare
dashi d'in zata zauna ta jashií ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
Canjin wajen zama sukayi ya amshi tuk'in yana fad'in"naga alamun ke kin shirya mutuwa ni kam
gaskiya bana so na mutu banyi aure ba"
Ya fad'a cikin barkwanci.
Murmushi kawai tayi bata tanka masa ba, sai ma wayar ta data d'auko ta bud'e data tana chat
da friend d'inta tana duba no d boy babu shi kwata kwata a jerin contact d'in ta da gaske yake
ya goge.
D'an kallonsa tayi sai akayi sa a shiama ya wago yana kallonta ta gira ya dage mata alamun ya
dai?
D'auke kai tayi tana tuna hargagin sa na d'azu akan mama wani lokacin bata cika ganin lafim su
ba domin halin mama sai mai hak'uri.
Kusan sau uku tana kamashi yana kallonta kuma duk sanda zasu had'a ido sai yamata alaman
yadai?
Sai kawai ta hak'ura bata k'ara kallonsa ba har suka isa sper market d'in da yawanci anan suke
siyayya duka 'yan gidansu.
Bayan ya samu waje ya faka ya bud'e ya fito sannan ya zagayo ya bud'e mata bayan tagama
gyara mayafinta ta fito a hankali ya Mai da motar ya rufe ya kama hannunta suka fara jerawa
cikin wajen.
Duk inda suka gifta sai idanu sun bisu saboda masifar kyawunsu da kuma yadda sukayi macin
d'in da mutane sukayi da juna.
Sunzo shiga shi Kuma d boy sun zo fita shi da abokansa ya gansu sai da gabansa ya fad'i
ganin ta tare da wannan gwaskan yayan nata ya wani kafesu da ido har suka k'araso inda suke,
sai lokacin ma Maryam ta kula da d boy ta d'an saci kallon MD wanda gaba d'aya hankalin sa
yake kan wayar sa.
Sai da tagawa d boy hannu ne shi kuma kamar wanda akace ya d'ago sai kawai yabi hannunta
da kallo lokacin shima d boy ya d'ago mata tare da wani irin mumushin farin cikin ganin da yayi,
kafesu yayi da wani fitinannen kallo zuciyar sa ya hau wani fat fat fat ko ko kad'an bai damuwa
da labarin mutane amma ko cikin miliyan sai ya fidda d'an jakin mutumin can, kuma ko da ace
shi bai son Maryam wallahi datayi mu 'amala da wancen gwamm ace masa ta mutu ne shi zai fi
masa sauk'i.
Sam bata kulla da kallon da yakafe d boy da shi ba amma shi d boy yana ankarewa take jikin sa
ya hau rawa ta ina zai manta da wannan basumuden mutumin wanda babu abinda ya ajiye sai
mugunta tsantsar ta, kafin Maryam tayi wani motsi d boy ya b'acewa ganinta, ta d'ago kai da
zummar yiwa MD magana yadda taga yayi kicin kicin da rai sai da gabanta ya fad'i ta d'auke kai
aranta tana tunanin anya wannan bashi da aljanu?
Duk abubuwan data siya shine ya biya k'udin, suka fito daga wajen har lokacin babu annuri
atare da shi dan haka taja bakin ta ta tsuke bata k'ara kallon inda yake ba.
Mai makon ya wuce gida kai tsaye taga ya d'auki wani hanya daban amma dake haushin sa
take ji bata dube shi ba bare tayi masa tambayar inda zai kaita, har suka isa wani d'an
madaidaicin gida mai kyau ya faka motar a k'ofar gidan ya fita ya kwankwasa aka bud'e masa
wanda m Bash ya ganine yasashi hangame baki
"Amma dai b'atan hanya kayi ko MD" m Bash ya fad'a yana d'an rik'e baki, harara MD ya zafga
masa yace "aini gwanda ni na kawo maka ziyaran kai yaushe rabonka da inda nake? Kuma
yanzun ma ba wajenka nazo ba wajen madam nazo tana dai ciki ko?"
" Hum tana ciki mana ina zata bayan gani yawo ai sai ku manyan gwaraye"
Harara ya galla masa batare da yace masa koma mota, har lokacin bata saki ranta ba hannunta
kawai ya kama batare da yace mata komai ba ya nufo gidan.
Ido ta d'an waro lokacin da suka tunkaro gidan, yayin da shi kuma ya sakar mata
murmushi,itama murmushin tayi masa ta d'an rusuna ta gaida shi kafin ' yace ta wuce ciki,
Kallo MD ya bita dashi har ta shige kafin ya maida hankalin sa kan m Bash da yafe shi da ido'
" Muje man munafiki ka wani zubamin ido kamar zaka cinye ni" murmushi m Bash yayi kafin
yace "SON TA KAKE KO?"
"Na fad'a maka"
"Sai ka fad'amin gashi nan ina ganin sa acikin idanunka"
" Hum abokina ban san sanda yarinyar nan tayi tsalle ta daki zuciya naba lokaci guda sonta
yamin wani irin kamu wanda har ya fara tab'a wasu daga cikin al'amurana na yau da gone"
"Ka fad'a Mata?"
"Ban fad'a mataba"
"Me yasa?"
" Inajin tsoron kar tace bata sona duk da nasan cewa idan nace ina sonta ko bata so sai an bani
ita"
"To kajarraba Mana"
Ta yaya bazan iya ba ina matuk'ar jin tsoron kada tace a a" ya fad'a cikin tsananin damuwa
sosai
Sosai m Bash yaji yana jin tausayin abokin nasa dafa kafad'ar sa yayi yace "abokina kada ka
bari ya huce" daga haka yaja hannunsa zuwa cikin gidan.
Har Hajara matar m Bash ta tarb'eta duk da cewa bata santa ba amma ta cika mata gabanta da
kayan makulashe suna d'an tab'a hira sama sama dake Maryam bata da bak'unta sam.
Kusa da ita MD ya zauna yana kallonta tare da tunanin ta yadda zai fara taranta da maganar
musamman idan ya tuna irin kallon da take masa.
Ji ta ta takura da kallon daya takura masa dashi d'agowa tayi ta d'an kalleshi kafin ta kauda
kanta tana hararan gefe
Taku ce MAMAN Islam
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
í ½í´¥ BA JININA BACEí ½í´¥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 31
Kayan da Hajara ta aje mata ya kalla yaga babu abinda ta tab'a, sai ya d'an dubeta yaga yadda
take ta faman hararan gefe ta wani turo baki gaba baisan sanda ya saki murmushi ba, yasa
hannu ya d'ago hab'an ya kafeta da wani shegen kallo.
Ganin haka yasa m Bash ya janye matarsa suka bar musu falon, kasa daurewa kallon nasa tayi
sai kawai tayi saurin rufe idanunta.
"Waye shi?"
Ta tsinci muryarsa yana mata tambayar da bata san inda ya dosa ba kallonsa take da alaman
tambaya a fuskar ta itama?.
"Wanda ya d'auke miki hankali a sper maket?"
Yanzu kam kallon shi take da madaukakin mamaki, yadda yai bala in d'auke mata kai har kawo
zuwansu nan batayi tunanin zai kula da hakan ba.
"D boy ne yaron daya dakeni a schl"
"Meye hadinki dashi?"
Sai data d'an K'are Masa kallo, irin kallon dayake binta dashi sai kace wani tsohon maye yasa
tayi saurin d'auke kanta.
"Mutunci ne tsakanina dashi?"
Ta amsa tana jan tsaki aranta ganin yadda ya fitineta da kallo.
Juyo da fuskar ta yayi saitin tasa ya k'ura mata ido yana mamakin furucin ta lallai ta sauya ba
dan kad'an ba tunda har ta kula d boy wanda yagama wulak'anta ta a bainar jama'a.
"Amma baki da zuciya princess, mutumin da ya gama gurza miki rashin mutuncin a tsakiyar
makarantar ku ke yamzun har akwai wani mutunci da zai had'a ki da shi?"
Shiru tayi saboda kallon da yake mata ya masifar ta kurata dan har jikinta ya d'an soma rawa
rawa.
"Ni kadaina min wannan kallon" ya tsinci muryanta da yayi can k'asa sosai tana fad'a, kallon ya
cigaba da binta dashi yayin da ya dad'a kusanto da fuskarta daf da tashi wanda har suke iya jin
saukar numfashin juna.
Take jikinta ya kama rawa ta soma k'ok'arin kwace fuskar ta daga hannunsa, sai dai bai bata
damar hakan ba dan ya rik'e ta gam
"Babu abinda yafi min dad'i kamar kallon ki kuma hakan yana saukar min da nutsuwa sosai, dan
Allah Kar ki haramtamin kallon fuskar ki yin hakan zai cutar dani sosai.
Yanzu kam gaba d'aya ta ware idanunta akanshi Al 'amarin bross d'in nasu ya fara bata tsoro
anya bai samu wani ciwon ba kuwa?
Yadda yake mata d'innan gaskiya ya kamata a bincike shi
"Zaki iya min wani alfarma?"
Ya tambaya yana cigaba da kallon ta kuma har lokacin bai saki fuskar ta ba,
"To kasakar min fuskana sai muyi maganar"
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya sake tan kamar yadda ta buk'ata, ya kwantar da
kansa jikin kujeran da suke kai yana maida numfashi.
Kafe shi tayi da ido aranta tana mamakin yadda yake da zallar kyau da mugun kwarjini.
Tana tsaka da kare masa kallon ne ya ware idonsa akanta yadda take binsa da kallo ya bashi
mamaki
"Yadai yarinya? Irin wannan kallo haka ai sai kisa naji kunya" ya fad'a yana d'an gyara
zamansa.
Ai kuwa wani irin fitinanniyar kunya ne ya kamata yadda ya kamata dumu dumu tana K'are
masa kallo da k'arfi ta runtse idonta gam gam, yasaki wani murmushi ya d'an matsa daf da ita
batayi aune ba sai ji tayi ya sakar mata wani kasalallen kiss a idanunta ai da sauri ta yunk'ura
zata gudu bisa ga tsausayi sai taci karo da kayan da Hajara ta ajiye mata tun d'azu, saura
kad'an ta kife wajen yayi wani irin fisgota ta fad'o jikinsa, wani irin ajiyar zuciya suka sauke
atare.
K'ank'ame ta ya kumayi acikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi wani irin abu na mai yawo
acikin jikinsa ji yai wasu irin hawaye suna k'ok'arin zubo masa wanda bai san dalilin faruwar su
ba.
"Zaki aure ni?"
Ta tsinci muryarsa da yayi wani irin mugun sanyi, a wani irin firgice ta d'ago kai tana kallonsa,
har lokacin idanunsa a rufe suke gashi ya wani irin cukwaikwauye ta, shikenan hasashen ta ya
tabbata yayanta yana da matsala banda haka ina aka tab'a auren JINI D'AYA?
K'ok'arin kwatar kanta ta soma amma ko gezau saima k'ara rik'e ta da yayi
"Ki bari mu fahimci juna dan Allah princess ina son na aureki zaki aure ni?"
Ya kuma k'arasa zancen da tambayarta, jitai hankalin ta yai masifar tashi take maganganu
Maryam wanda su yi dad'ewa ya soma dawo mata inda take ce mata
"Da kyar inba sonki wannan bross d'in naku yake ba yadda yai mugun saka miki idonnan da
alama dai bazai bawa wani daga waje damar d'auke masa wannan tsaleliyar