Showing 27001 words to 30000 words out of 65323 words

Chapter 10 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3555

besty hakan za ayi"






Daga nan direct unguwar su Maryam dake tayima Abbanta waya ya dawo yana jiransu sai da
suka fara gaida mamanta kafin tayi mata iso har d'akin Abbanta sosai kwarjinin sa yaima
Maryam dan daka ganshi kaga kamilin mutum mai cikar Kamala da mutuntaka bayan sun gaisa
Maryam ta fita ta basu waje.






Kallonta malam Abdullah yace "yarinya me sunan kine?"
Tace "sunana Maryam Abba murmushi Abba yayi yace "d'iya tace ashe" itama murmushin ta
saki wanda ya k'ara mata kyau.






"Maryam tace kina son ganina Allah yasa lafiya?"
"Eh Abba lfy dama ina son siyen gidane to shine nakema Maryam magana tace kana harkar
gidaje"

Kallonta Abban Maryam yayi na d'an lokaci yana nazarinta sannan yace"ke yar waye ne 'yata?"
"Baffa Abubakar" ta fad'a atakaice sosai ya jinjina take mamakin yadda akai tasamu k'udi ya
d'auke tunda yanajin irin labarin jita jita cewa yarinyar tana mugun b'arin k'udi sannan akwaita
da kyautar girma irin na mahaifinta sannan ansakar musu k'udi suyi yadda suke so, kasancewar
su Kennan yaransa.

Kallonsa ya mayar kanta yace "to 'yata kamar wanne kike buk'ata?"
Abba na baka zab'i mai kyau nake so wanda bai gaza 7 million ba" da mamaki yake kallonta
kafin yace "shikenan 'yata insha Allah zanyi miki kamar yadda zanyiwa Maryam" daga haka
Maryam ta bashi dubu goma tace "Abba ga wannan ayi cefane"





Da k'yar tasamu ya karb'a dan shi d'in ba irin masu zarmewar zuciya bane.




Ba a wani dad'e ya samo mata gida mai kyau aka yi ciniki ta biya batareda sanin kowa nataba
tabar komai awajen Abban aminiyar tata.






Tunda ga ranan dataganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi sai tasai abinda tasan duk lokacin
data tashi zata siyar ta samu k'udinta.



Shin wai duk meye dalilinta nayin hakan muje zuwa daga
'yar mutan YAKASAI






MAMAN Islam CE
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM




Page 21


Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta
daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin
data ganta da wasu 'yan k'udi masu nauyi, yayinda wani irin shak'uwa mai ban mamaki ya shiga
tsakaninsu da name sake d'inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.






Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d'aukan fansa Abban sa ya taka masa
burki yace"kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K'are ba wannan yaron da kake
ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad'a maka nagaban kwatance
dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba 'yar kowa bace face'yar Baffa Abubakar"





Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda
baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d'umin karamcin
sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok'on yayanta da ya k'yale

shi haka duk da yadda ake fad'an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan
d'aukan fansa ya ruguje saima k'ok'arin son kulla alak'a da ita.








Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce
take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d'aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina
babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab'a sanin wainar da suke toyawaba.






Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa
hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita
gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d'in duk
abinda zai rik'a faruwa akaf gidan ta ko ina har d'akin Ammey batare datasan anyi hakanba.







Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan
lokacin tashinsu yayi ta fad'a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting
wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k'ala batace masaba kuma dama yasan basatace d'in
ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.

A hankali tafara takawa zuwa bakin get d'in tunda tafara zuwa makarantar shekara d'aya kenan
da d'an wani abun bai tab'a ajeta anan d'in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k'ofar kamar yadda
ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.





"Hey hey" taji muryan wanda bazata tab'a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko
da babu wanda ya tab'a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani
matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun
fusace ta d'ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.






Yana k'arasowa bata bari ya fad'a mata wani abuba tayi saurin cewa "wai kai wane irin mutum
ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?
Yau kuma takeni kake sonyi komai?
Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?
Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin
tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.







Duk abinda take fad'a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace 'Amincin Allah
yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai
dan na k'ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss
d'in yayan naki ya k'yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk'awarin
ko kallon banza bazai k'ara had'a ni dakeba pls pls pls" ya rik'a maimaitawa yayin da tayi
masifar d'auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi
zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok'on yafiyar ta bai ko damu da yadda
mutane suka fara taruwa awajen ba.

Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu
kad'an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa "meye haka dan Allah jifa har an fara
taruwa anan katashi"





"Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin"
"Tashi dan Allah" ta fad'a cikin sanyin murya "zantashi ne kawai idan kince kin yafemin"
"Na yafe maka amma bisa wani sharad'i to tashi" tasake fad'a can k'asan mak'oshi da sauri ya
tashi yana fad'in"na gode na gode sosai ko wane irin sharad'i ne ki fad'a na miki alk'awarin
tunda dai kin yafemin" fad'a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa
d'aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.






"Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d'abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik'a maka
shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin
tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d'innan dakake gani duk
abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara
akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar
nan banda kawa sai A A"

"Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk'awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da
sabgar kowa"
" Allah yasa" ta fad'a atakaice tana wucewa department d'insa.

Yana tsaye har ta shige murya k'asa k'asa yace "tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan
komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so 'yar wani wanin ma
wanda yai suna aciki da wajen k'asar nan"
(Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol🤣🤣🤣)






Yau kam da wuri suka koma gida dake lacca d'aya ke garesu suna gamawa babu wani jinkiri
Maryam ta nemi da A A ta rakata banki tana son bud'e sabon account, da mamaki AA take
dubanta kafin tace "ke kuwa name sake duk yawan asusanku wanda ba ayi miki iyaka dasuba
sai kin bud'a wani?" Bazaki gane bane sam mama bata barina da k'udi ita zata bani kuma ita zata dawo ta rance na
rasa abinda mama take da k'udi duk yawan kyauta irin na Baffan mu wallahi A A Saida mama ta
kureshi" haka dai suka tafi tana bata bad habits d'in mamanta wanda abin yake masifar
damunta ta kuma rasa dawa zata zanta taji sanyi saifa yanzun dataji ta aminta da ita.









Har sukaje suka bud'e account kud'ad'en da Maryam ta zuba a account d'in saida abin ya bata
tsoro yayin da Maryam ta dinga mata dariya daganan tace Maryam ta rakata kasuwa zatayi
siyayya sai da suka fara zuwa tasiyi kayan kwalliya da turarukanta dake Maryam mayyar
turarece zai wuya ka kusance takaji bata k'amshi domin ita d'in 'yar gayuce tagaban kwatance
hakan yasa take da masifar farin jini Saidai halinta bai barinta shiga sabgar mutane domin bata
da kirki ko kad'an.







Daga nan Kuma suka nufi wajen masu saida kayan abinci A A taga Maryam ta d'auki babban

buhu na shinkafa da k'arami sannan ta d'auki taliya carton biyu haka makaroni da cous cous da
semonvita irin buhunnan mai guda sha biyu shima guda biyu manja man gyad'a Maggi kanshi
saida ta d'auki carton guda banda sauran spacies data d'iba ita dai A A kasa daurewa tayi tace
"name sake nasandai abincin gidanku trela ake kawoshi me zakiyi da wannan abin da kike ta
loda?"
"Ba damuwarki bane" cewar Maryam datakewa mai shinkafar maganan ko zasu samu motar da
zai kwashe musu dukan kayan? dan adaidaita yayi musu kad'an.



"Akwai 'yar k'ur k'ura wanda shi dama aikinsu Kennan d'iban kaya sukai maka duk inda kakeso'
ya fad'a yana kwalawa wani kira.







Tun tambayar da tayi mata tace ba damuwanta bane bata k'ara tofa nataba abinda ya Kuma
d'aure mata kai shine ganin motar bai faka ko ina ba sai k'ofar gidansu da mugun mamaki ta
rik'a kallon Maryam wacce ta d'auke kanta batare data bari sun had'a ido ba.







Suna tsaye har aka gama shiga da kayan abinci sannan ta sallami mai motar suka bi mai
d'aukan kayan na k'arshe, shima ta sallame shi yayinda suna shiga suka tadda Umma da
Abban Maryam da shima shigowarsa Kennan gidan aka fara shiga da kayan daya fara tunanin
ko b'atan kai masu kai kayan sukayi amma yana ganin Maryam da Maryam sun shigo ya
dingabinsu da kallo fuskarshi da alaman tambaya.






" Ku zauna mana Abba"
Maryam ta fad'a tana zaran buta tayi bayan gida, sam Maryam batada k'yamar mutane
musamman inkana da tsabta dake it's mutum ce mai tsananin tsabta da k'yamar k'azanta, tana

fitowa tayi alwala tayi d'akin Umman su A A ganin haka yasa itama Maryam tayi alwalar tabita
d'akin.





Tana fitowa tanemi waje ta zauna tana gaida Umma da Abban kafin ta kalli Umman tace "nifa
yunwa nake ji Umma yau bross ko kari bai bari nayi agidaba wai ya makara a office"



Kallon mijin nata tayi yayin da yayi mata alamar data bata abinda suke dashi,shi kuma ya saka
takalmansa yayi waje Umma Kuma ta nufi kicin ta kawowa Maryam wake da shinkafar da suka
dafa da salak da tumatur da cocomber, ta aje mata ta koma domin kawo mata ruwa sai ga Abba
ya shigo da ruwan roba da lemo harda dafaffen kwai tunda yasan me aka dafa agidan.








Sam bata wani nuna bak'unta ba taja abincin taci ta k'osh har tana santi ita kam Maryam zuba
mata ido tayi tana kallonta batareda data iya cewa uffan ba saida ta gama ta wanko hannunta ta
dawo tasha lemon da ruwa sannan tace.







"Abba wannan kayan abincin nakane kai na siyowa dan Allah Abba kada ka k'ara zuwa kayi
dako insha Allah idan Baffana ya dawo zansa yabaka jari ka fara business kaima insha Allah
Allah zai dafa maka"

Rasa bakin magana Abba da Umma sukayi suka rik'a kallon Maryam da tsabar mamaki dama
Maryam taji sanda yake cewa saida yai dako ranan sannan ya samo musu abinda zasuci?





Sosai Abba ya gode mata sannan yayi mata fad'an abin yayi mugun yawa tace "Abba wannan
ba komai bane akan idan da ace Baffana na fad'a wa shi ya doramu akan wannan tsarin nida
'yan uwana" addu'ar da Abban Maryam ya rik'a yiwa Maryam da zuri arta harsaida yasata
hawayen farin ciki itama.




Sai bayan la asar ta baro gidan ta kamo hanyar nasu gidan dake suna da tazara sosai sai
yamma ta dawo maimakon Kuma ta shiga gida sai kawai ta shige gidansu MM wani class mate
d'inta wanda har yau suna mutunci dashi kasancewar su unguwa d'aya.









MAMAN ISLAM CE
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p

*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
NA





HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM






Page 22

Bata zauna ba data tadda jm bayanan nayi b'ata last page jm zance na manta nace mm, tana
zuwa bakin get taji mai gadi yana cewa "gatanan yallab'ai" MD daya gama rud'a driver da bala i
saboda kawai yace tun biyu saura su Maryam suka bar makaranta kuma alhalin ba ama turashi
ba sai wajen biyar saura shine fa MD ya hana shi sakat da masifa sai da ya koma makarantar
har sau biyu.




Sannan kuma Ammey ta tabbatar masa da cewa tun fitar da sukayi tare bata dawoba amma kar
ya damu wannan ba komai bane a wajen su dan takan fi hakama awaje, sosai ransa ya b'aci da
jin abinda Ammeyn ta fad'a masa ya fito Kennan cikin wannan halin mai gadi da ba shine driver
ba da ya had'a ya hasu sakat yace ga Maryam d'in nann

Duk zubawa get d'in ido sukayi yayin da Maryam ta shigo hankalin ta kwance babu wani
damuwa tattare da ita, tana tafe cikin nutsuwar da Koda yaushe ka ganta zaka ganta tattare da
ita.

Ran MD ne yai mugun b'aci cikin bak'in ciki ya k'arasa inda take wato shi yana nan hankali
tashe ita Kuma tana can yawon gantalin ta hankalin ta kwance' wata irin fincika yayi Mata da
mugun k'arfi har saida ta saki k'aran azaba, jakarta da wayarta sukayi nasu waje yayin tayi taga
taga zata fad'i yayi saurin tareta ta fad'a jikinsa.






Wata irin ajiyar zuciya ya sauke jin ta cikin jikinshi take ya ji wani irin abu ya tsarga masa
tundaga tsakiyar kansa har zuwa babbar yatsarsa ta k'afa.






Ita kam Maryam wani irin takaicin jinta ajikinsa ne ya kamata batasan sanda hawaye ya sulalo
mata ba saboda bak'in ciki kwace jikinta tayi daga nasa tace murya k'asa k'asa "ban yafe ba
d'an iska kawai aidama Halima tace duk wanda yake irin aikinka to manemin mata ne anje
neman na bariki ba asamuba shine akazo latsa k'anwa dan abin kunya tur" ta fad'a tare da
fashewa da kuka.






Tunda ta juya tabar shi nan tsaye yake cikin suyar ran kalamanta tunda yake babu wanda ya
tab'a fad'a masa maganar daya k'untata masa irin yau ba,amma sosai abin ya rik'a sukar
k'irjinsa temakon da Allah yayi masa cikin rad'a tayi masa duk wannan wulak'ancin da cin
fuskar.





Sai dai hakan baisaka yajanye alk'awarin da yayiwa Baffa da Ammey ba yayi musu alk'awarin
zai ja Maryam ajikinsa yanda zasuyi sabon da duk abinda zaisa ta bazata tab'a Musa masaba
ta hakane Ammey take ganin zasu samu hanyar gyarawa Maryam zama.

Bayan an idar da sallar issha suna d'akinta ita da Nassar tana tayashi assignment d'in da yazo
dashi saiga sallamar shi abakin k'ofar ba k'aramin fad'uwar gaba ta tsinci kanta aciki ba d'azu
bayan tagama masa fitsaran ta dawo d'akin tace sam saitaga bata kyauta masa ba kome ya
mata ya kamata yaci darajan shi na d'an uwanta JININTA.





Bata samu damar amsa masa ba sai Nassar ne ya amsa masa ya k'araso gefen da take ya
zauna daf da ita tanaji Nassar yana gaidashi takasa had'a ido dashi bare wani gaisuwa ya
had'asu.






"Nine d'an iska mai bin mata ko?"
Ya tambaye ta cikin wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login