Showing 6001 words to 9000 words out of 65323 words

Chapter 3 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3547

ba saboda d'aukakar da Allah yaiwa mijinta lokaci guda ta hanyar kasuwancin daya
somo wannan kenan.





Matsalar farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa lokacin da Inna taga an kwashe
kimanin shekara biyar babu amo babu labari sai abin yafara damunta kullum bata da magana
sai na son ganin 'yan jikokinta, tun Baffa baya damuwa shima har abin yasoma damunsa,
magani kuwa suyi na gida suyi na asbiti,





Wata rana Sailuba ta kaima babbar aminiyar ta ziyara wacce tun zuwanta garin bata da aminiya
sama da ita bayan sun gaisa tasa ankawo mata kayan motsa baki mai aiki ta gabatar mata
dashi ta d'an dubi aminiyar tata Zakiyya tace "ni kuwa ina DEEDAH" babbar 'yar haj. Zakiyyan
kenan murmushi tayi tace "humm Deeda rikici zakice min tana can d'akin ta tana faman
kumbure kumburen banza wai sai nasa Abban ta yacanja mata mota, ni kuma banga abinda
motar ta yayi ba shiyasa nayi banza da ita ta cika fitina yarinyar nan wallahi"





'Yar dariya Sailuba tayi tace haba Zakiyya tilon 'yar taki kikasayi mata wani abu gaskiya baki
kyautaba tana ina ni tazo ta fad'amin duk kalar data ke so kiga aiki da cikawa" suka yi dariya
yayin da haj. Zakiyya tace "kina shagwab'a yarinyar nan da yawa Sailuba ya kamatafa ace
tasan cewa ba komai ne mutum yake so arayuwarsa yake samuba"

"Yauwa Sailuba ni kuwa ya batun maganin andace kuwa?"
"Wanne kenan cewar haj. Sailuba tana duban haj. Zakiyya na haihuwa mana" ta bata amsa
cikin gaakiya da gaskiya wata 'yar banzar dariya ta saki tace "wai ke anfad'a miki duk wahalar
da su Inna suke amfani nake da maganin?"




Kallon rashin fahimta haj. Zakiyya tayi mata sannan tace "ban fahimce kiba k'awata kina so
kicemin duk wahalar banza mukeyi bakya amfani da maganin?"





"To mai zai dameni dan ban haihuba kuma ni gaskiya koda zan haihun ma ban shirya yanzun
ba saboda haka kuma daina wahalar da kanku da kud'ad'en ku wajen nema min magani domin
ba na amfani daahi"







"Ke kuwa mai yakaiki aikata wannan d'anyen acikin k'awata kuma naga ko ba komai ai 'ya'ya
rahama ne bakisan wanda zaki moraba sai Allah"




"Nifa kin fara takuramin da wani wai haihuwa haihuwa ki k'yaleni mana dan Allah a a haka
kawai nifa babu abinda na nema na rasa mijina bai tauyeni ba haka mahaifiyarsa nima uwata ce
bata d'aukeni suruka ba dama can ni 'yar k'anwar tane kuma rainonta dan haka banga abinda
zaisani wahal da kaina dole sai na haihu ba"



"Bakya tunanin wata rana idan mijin naki ya gaji yace zai auro wacce zata Haifa masa yara

kinsanfa babu wanda bayason ganin kwansa a duniya?"





"Ke dallah saurara taya kike tunanin zan bari hakan yafaru"? Baffa bashi da wata mata a duniya
bayan SAILUBA kisawa ranki haka sannan kisa aranki cewa duk yadda yakai ga son yara dole
ya hak'ura tunda mahad'in rayuwar sa bata buk'ata kin gane?






Haka rayuwa tayi ta tafiya Sailuba da mai gidanta Baffa ana cin uwar soyayya yayin da inna taci
gaba da damun kanta akan rashin jikoki shi kuwa Baffa ko ajikinsa acewar sa haihuwar ma
lokacine.





Ana haka ya kammala k'asai taccen gidansa an an wata unguwa tsaka tsaki yabar jerin gidajen
ma aikata ya koma nasa, hakan kuma yasa yasamu cigaba sosai dan yakan d'auki wasu daga
matasan unguwar irin maau zaman ban zan nan ya bud'e musu wani kasuwancin hakan ba
k'aramin kima da daraja yajawa Baffa a idanun iyayen yara ba suna matuk'ar ganin girmansa.




Ganin lokaci yana taja yasaka Inna tace lallai lallai dole Baffa ya nemo mata ya k'ara aure
domin bazai yiyu ace suyi ta zama babu aure ba tofa sai lokacin hankalin Sailuba yay masifar
tashi dan batayi tsammanin hakan daka ta wajen innan ba.




Muje zuwa

Plss commmen and shire




Takuce maman islam
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MANAN ISLAM


Page 6
Takasa zaune takasa tsaye dole ta bazama gidan haj. Zakiyya neman shawarar ta, karfa kuyi
tunanin haj. Zakiyya yarinya ce kamar sai luba ko d'aya kawai dai irin k'awancen nanne na
yanzun dan ak'allah Deedah d'iyar haj. Zakiyya zatayi kusan shekara ashirin sannan bayan ita
tana da manyan 'ya'ya guda biyu da suke karatu a waje yayin da Sailuba a lokacin batafi irin
shekaru ashirin da kwai zuwa da takwas dinnan ba domin lokacin da aka yi aurenta da Baffa
duka batafi shekara sha takwas ba kunga kenan ak'alla yanzun suna da shekara goma da aure.






Tunda ta gama karanto mata damuwar ta tayi shiru tare da zubawa haj. Zakiyya wacce tai shiru
tana buga k'afafunta ak'asa idanu, wata ajiyar zuciya ta sauke tace "kin yi shiru bakice komai ba

k'awata kinsan cewa fa wannan ba maganar wasa bane domin nafi kowa sanin cewa duk
abinda Inna ta zartar ya zartu domin Baffa baya iya tsallake maganar ta"






"Kuskuren da kikayi kenan Sailuba tun farko saida nace miki ki tashi tsaye ki kama Baffa a
hannun ki kikace aike daga shi har uwar sa suna tafin hannun kiyanzun ai kin gani dama wacce
uwace bazata so ganin jikokinta a duniya ba kika ce ke duk abinda kike so shi kike samu dan
haka bazaki komai ba ai yanzun gashi nan naga ikonkine yake sama da umarnin innan awajen
Baffa ko?"






"Dan Allah k'awata duk mubar wannan maganar naji nayi kuskure yanzu dai so nake mu samo
hanyar da zan gyara kuskure na kuma mu to she duk wata hanyar da zata kuma b'ulluwa mai
kama da wannan" wani shu'umin murmushi haj. Zakiyya ta saki kafin tace komai saiga mijinta
ya shigo da sallama kamar mara gaskiya ya soma sand'a zai wuce "kai" ta buga masa tsawar
da sai da tasaka Sailuba ta zabura tace "kai wanne irin dak'k'ine dan Allah me yasa bakajin
magana duk abinda zan fada maka baya shiga kunnen ka wallahi alh. Lawan duk randa ka kaini
bango agidannan bazamu kwashe ta dad'i dakai agidannan ba"





"Jiki na rawa alh. Lawan yace " dan Allah haj kiyi hak'uri ban kula daku awajen bane" sannan ya
k'araso gaban haj. Sailuba ya durk'isa har k'asa ya gaida ita a sanyaye ta amsa idanunta har
sun kawo ruwa tsabar tausayinta daya kamaahi sannan ya tashi sum sum ya wuce sama "kuma
ka gyara min d'akin kafin na hawo" "To" kawai yace mata ya wuce.





Dafa Sailuba tayi tace " kinga k'awata muddun kikace zaki saka tausayi aranki to aikin ki bazai
tafi yadda kike soba kuma ko sune suka samu dama abinda zasuyi miki sai yafi wannan domin

sai sun kacaccala rayuwarki"




Haka dai haj. Zakiyya tayi nasarar yi mata hud'ubar shed'an akan su maida Baffa rak'umi da
akala akan komai kamar dai yadda taga tanayiwa mijinta, cikin k'ank'anin lokaci aka rushe
maganar auren da Inna ta da Baffa basu k'ara d'aga zancen ba har zuwa wani lokaci yayin da
Sailuba tasamu hanyar sarrafa Baffa iya son ranta baya aiwatar da komai saida umarnin ta
hatta abu idan zaiwa inna sai ta amince inbata yardaba anbarshi.






Akwai wani malam Babba anan k'asan layin da suke shi mutum ne na kwarai wanda yake
amfani da ilimin da Allah yabashi shiyasa yasa yake da matuk'ar kima da daraja a idon mutanen
unguwar duk lalacewar yaro badai kaji mummunar kalma daga bakin malam babba ba saida
fatan shiriya da sanya albarka wannan yasu masa farin jini sosai wajen yara da iyayen su yana
damatuk'ar kima a idanun matasan earia dama na kewayen hakan yasa ya bud'e makarantar
ialamiyya wanda ake zama daga magriba zuwa sallar esha ranan alhamis da juma a yara da
manya haka suke cika amakarantar.






Baffa yana d'aya daga cikin d'aliban makarantar haka kuma bashi uban dayafi malam babba kaf
unguwar domin shine mutumin da baya duba girma ko matsayinka zai fad'a maka gaskiya kai
tsaye komin d'acin ta kuwa, haka duk sanda Baffa yake gari bashi da wajen hiran yamma sai
wajen malam babba haka nan cikin hikima yake dad'a yiwa duk Wanda suke tare nasiha da
hak'uri da zaman lafiya da kowa tare da rok'awa duk Wanda ka gani ba akan daidai ba shiriya
bawai ka rik'a zaginsa ko la antarsa ba domin hakan ayace wata rana sai ya faru akan ka ko
akan d'anka.





Cikin matasan da alh. Baffa ya bawa aiki akwai 'ya'yan malam Babba guda biyu Kamalu da
kuma Usman yana matuk'ar jin dad'in aiki dasu saboda ingantaciyyar tarbiyyar da suka samu

daga mahaifin su.





Oh na manta ban muku bayaniba tun lokacin Baffa yana k'auyen su yana da aminiya gsai d'aya
Hassan Wanda suka kasance tamkar uwa uba d'aya koman su tare sukeyi hatta wajen kwana
ma idan ya sun kwana agidan su Baffa to gobe agidan su Hassan zasu kwana Wanda har
hakan yaja wa iyayen su kusanci suka zamo kamar 'yan uwa na jini.







Sai da aka shafe shekara guda Inna bata kumayiwa Baffa maganar k'arin aure ba saboda
danne tan da akayi da k'arfin asiri sai lokaci guda yaje garin Wanda alokacin ma rabon data
sanyashi idanunta ma an d'ebi wata kusan biyu mutumin da duk k'arshen sati sai yaje ya
ganada mahaifiyar ta ya kai mata abubuwan bak'ata yanzu kuwa sai gimbiya Sailuba tabada
umarni wannan kenan








Taku maman islam
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap

p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASA

MAMAN ISLAM


Page 7

Bayan sun gaisa da tare da tambayar juna bayan rabuwa yabata uzuirin cewa baya zama ne
shiya sa ta d'an jima bata ganshiba da mamaki ta rik'a kallon sa domin bata tab'a ganin uzurin
daya hanashi gaida itaba Sai a wannan lokacin sai dai ta alak'anta hakan ne akan maganar
auren data dameshi da ita hakan yasa tace "Allah ya kyauta"


Gyara zaman ta tayi tace "Baffa kamar dai yadda na takura maka na matsa maka har hakan
yasa kake ganin kamar na matsa maka dayawa to Baffa inaso kasani 'ya'ya suna k'arawa
mutum martaba da kima idon al'umma kuma 'ya'ya rahama ne sannan ni'emane da ba kowa
Allah yake yiwad,,,irin wannan baiwar ba, kai yanzun ba abin alfaharinka bane ace yau ga
sanyin idaniyar kaba kana dubansu kanajin dadi? to inaao ka saurareni da kyau yau muna biyar
ga wata dan haka na baka daga nan zuwa k'arshen wata kafito da mata ka aura ko kuma ni na
zab'a maka kamar yadda nayi maka na Sailuba"






Shiru yayi yana sharce gumin dayake tsiyayar masa har saida Inna ta kula da halin dayake ciki
amma sai tai kamar bata ganiba gyara zaman sa yayi yace "dan Allah Inna ki d'an k'aramin
lokaci zanyi yadda kike so amma Inna taya zan fara fad'awa sailuba wannan labarin?"





Sosai inna ta hasala abatunsa ta lura saboda bayason bacin ran Sailuba ne baya so dan haka
ta had'e rai tace "au saboda b'acin ran Sailuba ne kai baka son barin baya to wllh kaji na rantse
muddun ka bari k'arshen watannan yazo baka nemo matar aure ba ni zan nema maka ance
maka ita Sailuban haihiwar take sone da tana so ai bazata rik'ka to she mahaifa tana d'inketa ba

ko ance maka bansan halin da kuke ciki bane to ita aminan nata da tad'auki amanar zuciya da
rayuwanta ta damk'awa sune suke kewayowa suna kawomin labarin komai dan haka ni na
gama magana idan kuma ka isa kai d'ane ka k'etare magana ta kagani duk duniya babu wanda
yakaini son Sailuba domin ita d'in 'yatace halak malak kuma JININA CE sannan rainona ce sai
dai a irin tarbiyyan da nabata babu wanda take amfani dashi sai na banzayen aminanta da suke
d'orata a keken b'era har nagaji da fad'a mata gaskiya ta nuna bata buk'ata Allah yasani na
sauke hak'k'in ta da yake kaina nabata kula da tarbiyyan da ko uwar data haifetane iyaka kenan
dan haka na fita hak'k'inta sannan inayi mata fatan shiriya"





Tunda yake baitab'a ganin fushin mahaifiyar tasaba sai wannan karon domin daga shi har
Sailuba lallabasu Inna take amma yau kam yaga tsantsar b'acin ranta dan haka ya rik'a
lallab'ata har zuwa sanda yabaro garin.





Sai dai babban tashin hankalin sa yadda zai fuskanci gimbiyar tasa da wannan batun yasan
cewa ba abune mai sauk'iba ya tunkareta da wannan babban al'amarin, koda yadawo gida haka
abin yay ta damun sa arai har gimbiyar tasa tay ta tambayarsa damuwarsa yace babu.




Sau tari idan abubuwa suka sha masa kai yakan nemi shawarar malam Babba wannan karon
ma yazo wajen malam d'in kamar ko yaushe neman shawara tare da baran addu a kamar
yadda yasaba abin Allah kuma masu Karin magana sukace kaddara ta riga fata anan suka
had'u da Amina d'iyar malam wacce tunda yake Allah bai tab'a sawa sun had'uba sai ranar dan
dama ba wani sanin yaran malam d'in mata yayiba domin basu cika fitaba sai da babban dalili
kuma bayan haka ma dole bazai san Amina domin ko acikin gidan ma abune mai wahalar
gaske kayi katarin ganin ta atsakar gida domin koda yaushe tana d'aka.




Tunda yay arba da Amina ya nemi nutsuwar sa yarasa bai tab'a katarin had'uwa da abinda
lokaci guda yai tsalle ya shige zuciya lokaci guda ba sai Amina, itace tayi masa kamun dashi da
kansa ya kasa daurewa har saida ya furtawa malam Babba hakan, take batare da wani jinkiriba
yace ya bashi Amina halak malak yaje ya sanar da mahaifiyarsa kuma insha Allahu k'arshen

watan da muke ciki za ad'aura auren haka nan Allah yasanyawa malam Babba k'aunar baffa
saboda Baffa mutum ne dayasan darajar manya haka nan ya iya mu'a mala da duk wanda suke
tare daahi.





Cikin tsantsar farin cikin daya kasa b'oyuwa ya k'arasa gidansa fuskar nan d'auke da annuri
haka ya dinga abubuwa har dai Sailuba ta kasa daurewa ta tambayeshi yace mata babu komai
kawai dai yajishine fresh shiyasa yake farin ciki.




Bata k'ara tsinkewa da lamarin ba sai washegari dataga yana shiri ta tambaye shi inda zashi
yabata amsa da wajen Inna take taji 'yan hanjinta sun kad'a tace "naga yau dukafa kwananka
biyu da dawowa shine zaka kuma komawa?"



Dakatawa yayi da fesa turaren da yake ya dubeta yace "yanzu dai kina so kice dan na dawo
daga gaida uwata shekaran jiyaifi ne kenan dan na koma yau?"






"Ba lafi bane amma gaskiya bazaka koma yauba ina laifin ka bari zuwa koda k'arshen watane
amma daga dawowa sai ka wani kwashi jiki kace yau zaka koma nidai gaskiya ban amince ba"



Ta k'arishe da irin yaudararrun kalaman da malamain su yace su d'an rik'a had'awa dasu dan ba
ko dayaushe ne aiki yake amfaniba wani lokacin sai an had'a da kissa.





Wani banzan kallo ya watsa mata kafin yace "to uwata ai tunda kin isa sai ki hanani zuwa tunda
naga alama kin kai har kin wuce wuyanki yayi kauri" mts yaja dogon tsaki ya juya batare da ya

kalli inda takeba ya fice.





Sau tari wasu abubuwan dayake mata sai yaga kamar cikin tsoronta yake ga wani d'an banzan
Shankar ta dayake wanda indai zata bashi umarni sai ya bi.





Ita kanta Inna tasha mamakin maganar dayaje mata dashi ba k'aramin farin ciki tayi da irin da
ya nemoba dan ita kanta ganau ce akan irin tarbiyyan Yaran malam Babba dan haka batare da
b'ata lokaci ba ta tashi 'kaninta d'aya da k'anin Baban Baffa suje suka kai dukiyar aure da
kayan nagani ina so har da nasakun rana.



Babu yadda malam baiba akan su barshi ai shima Baffa d'ansa ne suka k'iya cikin mutuntawa
suka baro gidan malam Babba suna ta yaba karamcin sa.




Sanda Sailuba tayi ido biyu da kawun ta dana Baffa saida tasha jinin jikinta domin tasan cewa
banza baya tab'a kai zomo rafi.





Maman Islam ce
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM


Page 8


Haka nan dai ta yi musu sannu ta kawo musu ruwa da abinci kasan cewar dare yakawo kai
domin tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login