Showing 1 words to 3000 words out of 65323 words

Chapter 1 - BA JININA BA CE Part 1 by Maman Islam .pdf

15 Apr 2025

3546

مسب<><><>رلا><><><<>><><><<>><><><<>
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

🔥BAJININA BACE🔥
2021
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM






Bismillah Rahmanir Rahim Allah kayi dad in tsira da aminci ga shugabanmu jagaba fiyayye
annabi muhammadu S A W tareda dukan ahalin gidan sa da sa habbansa baki d'aya




Wannan shafin naku ne JININA ABDU WAHAB ABDULAZIZ
TARE DA
ADAMU ABDULAZIZ
Ina matuk'ar farin cikin tayaku murnan k'aruwan yara maza da kukayi Ahmad Adam da
muhamma Sani Abdul WAHAB Allah ya albarkaci rayuwar su yasa cikon addinin musluncine
Amin


Page 1

"Ke Maryam naji wata ’yar matashiyar budurwa tana kira cikin muryar rad'a" da sauri naga
yarinyar da aka kira da Maryam ta waigo fatabarakallahu asanulkalik'in shine abinda na fad'a
lokacin da idanuna suka arba da zankad'ed'iyar kuma matashiyar budurwar aka kira da
MARYAM wani shegen murmushi tasaki tace "ba saikin fad'aba Halima nasan abinda yasa kike
wannan kiran sai kace makauniya' a d'an dame Halima tace "kinsan halin wannan bros d'in
nakifa baida mutunci yanzun saiya b'ata mana shiri"




Wani d'an iskan kallo Maryam ta sakarwa Halima tace "ke ya dama ni kam banga wanda ya isa
hanani abinda naga damar yiba uwata da ubana basu ta kuraniba sai wani can daban, kinga
malama aje acigaba da shirya wajen ayi yadda zamufita kunyar abokanmu"




kai kawai Halima ta jinjina batare da ta ce komai ba domin tasan halin Maryam da shegen taurin
kai idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya juyata sai YAYA MUHAMMAD daya daneta ya
shanye a taurin kai gashi bala e en sojan dana k'asansa suke masifar tsoronsa gashi miskili ne
shi na gaban kwantace inba ta k'ureba zai wuya kajishi yana yawan magana hatta abokansa da
abokan aikinsa sun saba da halinsa sau tari da ido yake basu umarnin abinda zasuyi kuma su
aikata domin sun riga sun saba da halinsa.




Ta juya kenan zata gidan su anwar wani mate d'inta ne yayansu yana d'inki to duk kayan da
zata buk'ata shi tabama d'inkinsu, saiga Nasser ya k'araso da gudu yace "Adda Maryam kizo inji
Ammyna" wata shegiyar harara ta galla masa tace "kaje kace tazo tajani bazan zoba inkuma
zata iya tazo tajani"


Shima hararan ya maida mata dan babu ragayya a tsakaninsu ko kad'an yace "kada Allah yasa
kizo d'in banza wacce batasan darajan nagaba da itaba"



Cikin b'acin rai tayi Kansa tace kai dan uwarka ni kake zagi?"
"Anzage kin ni uwata sa ar wasanki ce da zaki zauna kina aikena da wannan banzayen
zantukan?"

Kansa tayi da nufin mammake shi ya d'ebi sauri tabishi tana cigaba da gaya masa bak'ak'en
maganganu akan mahaifiyar sa, shi kuma koda wasa bai saurara mata ba duk zagin data masa
Sai ya maida mata martani acewar sa tunda ita Allah baiyota da ruwan mutunci ba baiga dalilin
da zaisa ya kyaleta ba.



Yana bud'e get ya hango bros wani shu'umin mirmushi ya saki sannan ya tak'ark'are ya
zunduma wani uban ihu har Sai da bros ya to she kunnensa ya juyo afirgice dan jin wannan
ihun tayi zaton kunama ne ya d'alleshi ganin shi yai yana nufoshi yana cigaba da kukansa wata
uwar harara ya maka masa wadda tasa nan take ya had'iye kukan ya k'araso kusa dashi, da ido
yake tambayar shi abinda akayi masa yace





"Ba Adda Maryam bane kawai dan Ammyna tace na kirata shine ta hau zaginmu nida Ammeyn
danna ce badai Ammeyna ba shine ta mareni kuma ta biyoni wai zataje gaban uwar tawa ta
takamin kai taga inda abinda ta isa tayi"




Kafin yace wani abu saiga maryam d'in ta shigo a fusace kuma har lokacin bata bar fad'ar
bak'ak'en maganganun da take fad'awa Nassar ba, abinda ya dad'a b'ata ran bros kenan yayi
mata wani mugun kallo wanda sam bata kula daahi ba Sai da tashigo tsakiyar gidan itama had'e
rai tayi ta bala in d'auke kai tai kamar batasan da zaman su awajen ba.


.
"Ke zo nan" ya fad'a cikin dakakkiyar muryarshi da babu alamun wasa aciki had'e rai tayi tare
da kuma galla masa harara sannan ta saki tsaki tayi cikin gidan abinda yai masifar k'ona masa
rai kenan ya kama hannun Nassar suka nufeta ai tana ganin ya nufota ta taka aguje tayi ciki'
mamanta da Ammey suna zaune afalon suna d'an tab'a hirar su dake babu laifi basu cika fad'a
da junansu ba saboda hak'urin haj. Amina da kuma tsantsar biyayyar da take wa abokiyar
zamanta haj. Lubabatu hakanne yasa ba ajin kansu indai ba Maryam aka tab'owa haj. Luba ba
yanzun zakaji ruwan masifar ta da bala I.

Suna cikin hirar Maryam ta shigo da gudu ta shige bayan mama cikin shagwab'ar daya zame
mata jiki tace "mama kinganshi ko zai dakeni "



"Wa kenan?" mama ta tambaya tana duban hanya ai tana ganin wanda ya shigo tai masifar
had'e rai dan a duniya idan da wanda taiwa masifaffiyar tsana to Muhammad ne dan ya riga da
ya hana ta sakat ya shige mata hanci da k'udundune tarasa yadda zata fyato matsiyaci ta huta.





Sosai tai masifar had'rai tace "dan ubansa idan ya isa yazo ya tab'aki tsabar masifa da jaraba
abi a hana yarinya sakat to wallahi ni na gaji bari alhajin ya dawo dole yayi mana tsakani dakai
dan 'yata na baiwa bace"




Kafin takai ga dire jarabar da take Muhammad ya shammace ta ya fisgo Maryam ya d'auketa da
wani gigi yaccen mari wanda yasa nan take ta shid'e numfashinta ya tafi yajin aikin hucin gadi
kafin tasaki wata azababiyar k'ara, karar ce ta ankarar da mama ai har mayen ya damk'eta
sunan da tasaka masa kenan dan duk inda takai da bala I matuk'ar yayi niyyar mata hukunci
babu wanda ya isa ya hanashi sai Baffa wato mahaifinsu




Ranta yai masifar b'aci cikin bak'in ciki tace "matukar ka kuma dukanta Allah ya isa ban yafe
makaba shege mugu azzalumi ta Allah batakaba munafiki wallahi bari alhaji ya dawo sai yayi
mana tsakani dakai tunda kai Allah yayi ka da zuciyar kafurai.




Duk zagi da munanan kalaman da take binsa dashi bai saurareta ba saida ya tabbatar ta
turarawa Maryam jikinta sannan ya wulla mata ita jikinta ya juya ya fice yana huci yayin da

mama taci gaba da zagi tana la antarsa.




Rungumo maryam tayi wacce take rusar kuka na fitar hankali domin ba k'aramin dakuwa tayiba
jikinta kuwa banda azaba babu abinda yake mata abinka da farin mutum fatar nan tayi jajur tayi
rud'u rud'u, suna had'a ido na Nassar tayi mata gwalo ta hayagagar ta tace



" wannan munafikar uwar taka ita kayima gwalo dan uwarka shege mai kama da d'iyan
aljanu🤣🤣🤣🤣dole na dara domin duk wanda yaga Maryam yaga Abdul Nassar yaga JINI





Tana dire zagin bros yana dad'a danno kai daman a bakin k'ofa yatsaya domin ya San da cewa
dama bazatayi shiru ba dole zata fad'i wani abun.






Comments and shere





Maman isi ce
مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________

🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM


Goron Taya murna
Ga
Shugaba ummy khaleel tasamu k'aruwan baby girl Allah ya rayata yasa cikon addinin
musluncine amen



Ina gaidaku daukacin y'an kungiyata ta first class Allah ya k'ara daukakamu ya yabamu ikon
rubuta abinda za a amfana dashi dan fiyayye Annabin rahama Amen

Page 2
Tana ganisa ta shige d'aki da gudu ta datse k'ofar da key dan tasan k'aramin aikinsa ne ya
biyota har d'akin yacasa kayarsa.



Sai da taci kukanta ta gaji sannan ta mik'e ta shiga wanka fasa amsar d'inkin da tai kenan,
bayan ta fito a wankan ta zauna ta d'and'asa kwalliyar ta tai matuk'ar kyau dan dama maryam
mayyar kwalli yace duk da tsantsar kyawun da Allah yai mata akwaita da son kwalliya.



A can b'angaren Halima kuwa ad'ari d'ari take komai domin ba ta da tabbacin fitowar Maryam
tunda wannan mayen bros d'in nasu mai fad'an tsiya ya dawo.




Sosai masu docuration d'in suka k'ayata wajen sai kace wani bikin aure ba walima ba.

Maryam kuwa duk da tsamin da jikinta yai mata saboda azabar dukan datasha bata fasa shirye
shiryenta ba dan bata tsoron bros ko kad'an acewar ta ai dukane kawai guda zai daka kuma
guda zai bari.




Bata samu damar karb'o kayan ba sai wajen k'arfe hud'u da sauri tazo ta shirya cikin wani
d'anbanzan swess mai azabar kyau da tsada ita da kanta tasan cewa babu k'arya tayi masifar
kyau ba na wasa ba.




Tana shirin fita suka kicib'us damama tana shirin shigowa galala tayi da baki tana kaonta da irin
kyaun da tayi rumgume maman tayi tace "mamana na shirya, nayi kyau kuwa?"

" fad'a ma ai b'ata bakine 'yata kyawun da kikayi bazai fad'uba fatana dai ki kula da kanki kinji
ko karki bari wani abin yasamar min ke in hakan yafaru bazan yafe ma kainaba?"




Wani lallausan murmushi ta sakar mata tareda manna mata kiss a goshi tace karki damu
mamana insha Allahu babu abinda zai faru, yauwa ansaka min duk abubuwan da nace amitar?"




" komai ya kammala kije driver ke yake jira kar ku b'ata lokaci"
Had'e rai tayi tayi kicin kicin da fuska, take naga hankalin maman ya tashi tajawo ta jikinta tace
"me kuma ya faru baby? muna maganar mu lafiya yanzun kin canja?"



Cikin shagwab'a tace "mama nafa ce miki da kaina yau zanja shine zakima driver magana
gaskiya nidai ni da kaina zanje" murmushi maman ta saki tace "yanzun ke da wannan shine
zaki b'atamin ranki abanza gashi" ta fad'a tana mik'a mata mukullin ta amshe tare da kuma
rumgumeta ta sakar mata kiss a kumatu tace "ina k'aunar ki mamana sai na dawo" ta fad'a tare
da yin waje aguje.

A d'an farfajiyar gidan ta tarar da Ammey tana kiranta amma ko kallon banza bata isheta ba
balantana na arzik'i, tun kafin ta tada motar ta saki wani d'an banza hom ai baba mai gadi
yanajin haka yataso aguje ya bud'e mata k'ofa dan yasan order ta ya fita daban dana kowa
acikin gidan.



Ammey na tsaye har tafice sannan ta girgiza kai aranta tana mata addu ar sauka lafiya.




Ba d'an k'aramin gudu maryam take ba domin acewar ta wai ta b'ata lokaci abokanta na cen
suna jiranta ga wani uban kid'a data k'ure wanda zai sa Sam bazata fuskanci ko gane abinda
zai fad'a mata ba, wannan tabi ar tace sam maryam bata da mutunci ko kad'an bata sami
tarbiyar kwarai daga maman tata ba ta nuna mata kudi sune komai na rayuwa dan haka tayi
komai babu komai kud'ad'en mahaifinta zasuyi mata maganin duk wata damuwa.





Cikin k'ank'anin lokaci ta isa wajen, tasami gu tayi parking saida ta fara manna arnan glass d'in
daya dace da kwalliyar tata kafin ta zuro kyakyawar farar k'afar ta waje ahankali take takawa,
yayin zuciyar ta ya falfala da gudu cikin wajen saboda kid'an data ke jiyowa awajen da maryam
gwana ce wajen rawa gata mayyar rawar ce biki ko batasan maishiba taje sai ta taka.



Tunda ga sanda ta faka motar yakafe wajen da ido har zuwa lokacin data fito cikin yauk'inta
datakun ta mai tafiyar da hankalin 'yan maza kai har ma da matan bak'aramin mummunar
fad'uwa gabansa yaiba ganita gashi babu damar shiga wajen domin lokacin shiga meeting d'in
da zasuyi yayi dole ya wuce amma aransa yana fatan har sugama bata bar wajen ba tunda
yaga wajen data shiga yasan cewa wani bikinne tazo.

Ita ko maryam tana ganin ta shiga wajen har ta fara wata irin rawa da juyi karab idanunta suka
sauka akansa, take ta aro wata irin nutsuwa ta arawa kanta dan tana masifar gudun abinda zai
b'arar da ajinta wajen masoyin nata kuma abin k'aunarta Muhseen.




Abokanta na hangota suka saki shewa da ihun murnan ganin ta da sauri suka k'araso wajen
wasu na d'aukar ta pic yayin da wasu ke suka take mata baya har suka k'arasa cikin wajen.




Kujerar da aka tanada mata wacce ta kasance kusa da Muhseen ta zauna kamar wasu amarya
da ango tunda shigo wajen akan idanunsa har rawa data soma amma sam bai nuna ya gantaba
domin maryam ba k'aramar 'yar disgi bace shi yasa yake masifar kame kansa agabanta.





Ba tare da b'ata lokaci ba aka fara gudanar da abinda ya Tara su awajen sukaci suka sha
sannan ta rarraba kyautukan data tanada domin abokanta duk Halima ce ta kula da wannan
yayin da maryam ta masifar kame kanta agaban Muhseen sai da za ayanka cak ne ma ta d'an
dubeshi k'asa k'asa ta gaida shi murmushi ya sakar mata ba tare da ya amsaba ya tashi suka
k'ara wajen, wa ashe na murnan zagayowar haihuwar muhseen abin ya k'ayatar dashi yadda
ya kamata yadda maryam take 'yar bidiri to shi har ya dameta ya shanye bayan gama yanka
cak ne aka bud'e musu filin rawa suka shiga suna wani irin taku mai ban shi' awa da burgewa,
juyowar da zatayi kawai idanunta suka sauka hakansa yana tsaye sanye cikin kakinsa dayake
masifar yi masa kyau ya hard'e hannayensa a k'irjinsa ya kafeta da fitinannen kallonsa, take
gabanta yai masifar fad'uwa hankalin ta yai mugun tashi ba dan komai ba sai dan gudun kar ya
disga ta agaban saurayinta da abokanta musamman da ta kalli idanunsa taga sunyi wani irin
rinewa sabo da b'acin rai, amma dan k'arfin hali irin nata kawai sai ta basar taci gaba da
rawarta, abinda yai masifar k'ona masa rai yafara takawa cikin tafiyar sa na ingarman namiji
batasan ya isota ba sai dayayi mata wani mugun damk'a kamar zai karyata saida ta saki k'arar
wahala Muhseen kuwa yana ganin haka ya cika wandon da iska dan yasan sojoji ba imanine
dasu ba yanzun sai suyi masa walmakalifatu.





K'ok'arin kwacewa ta soma ai kuwa yana juyowa ya d'auketa da wani azababben mari wanda a

take hancinta ya balle da jinitayi luuuu zata fad'i saboda tsabar gigita ya fisgota ta fad'o jikinsa
ya dad'a d'auketa da wani marin har guda biyu tsabar wahala da azaba bai barta ta gane inda
take ba ya fincike ta daga jikinsa ya hau janta har jikin motar sa ya wullata ciki har Sai da ta
gwaru da murfin motar saura kad'an ya had'e da hannunta wajen rufewar mukullinta ya jefawa
driver da ya kira shi kuma ya tada tasa yabar wajen da masifaffen gudu yayin da yabar
k'awayen ta da abokanta da jimami da tausayinta Allah ya had'ata da jarababben d'an uwa
mara mutunci d'an hana ruwa gudu.





Daga yanayin order dayake ma mai gadi yasan cewa babu lafiya wannan jarababbiyar yarinyar
ta tab'oshi, da sauri ya bud'e masa get yai saurin matsa gefe dan yasan cewa ba shigowar
dad'in rai zaiyi ba ilai kuwa saida yayi wani irin masifaffen cin taya sannan ya danna hancin
motar ciki, Nassar da dawowar sa kenan daga masallaci ya kwasa da gudu yai cikin gida domin
yasan indai yayan nasa yana cikin zafi to kan mai uwa da wabi yake duk wanda yasamu bi yake
ta kansa.






Maryam kuwa zuwa lokacin ta gama shiga wani hali tsabar wahalan dukan data sha haka ya
kuma fincikota yajata ciki keeee ya gwara da kujera yana huci sai kace mayunwacin zaki a
idanun haj. Luba ya watsar mata da 'ya kamar kayan wanki nan kuwa ta hau jaraba tana tsine
masa ko kallon ta baiyi ba yayin da sai da ya kuma lallasata sannan ya d'ago yana huci ya kalli
Ammey dake karatu cikin wayar ta bata ko kalli inda suke ba yace.







" Ammey yakama ta ace kinsa ido akan yarinyar nan domin kuwa kema 'yar mijinki ce dan haka
kina da hakki akanta bai kamata ace kinsa ido ana watsa tarbiyyar yarinya ba idan ba haka ba
idan Baffa ya dawo zan fad'a nasa irin rashin d'ar da yake faruwa agidan kamilin mutum kamar
sa"

"Uaban Kane ya koya mana bad'alar nace uban kane bad'alalle d'anb iska mara mutunci kai
dan ubanka tarbiyyab'ace da kai kai dazaka zauna kana gayan magana d'an iska mara zuciya
dakana da zuciya da tuna ka fita harkana da 'yata amma dake kai zuc..................take ta had'iye
sauran maganar saboda wani matsiyacin kallo daya watsa mata duk bala inta tana tsiron
Muhammad domin ba shi da mutunci idan ransa ya b'aci MD kenan kamar yadda abokansa
suke masa lak'abi.





Sai data yi jinyar jikin ta na kwanaki biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login