Showing 129001 words to 130495 words out of 130495 words

Chapter 44 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

zancan sure ta da Muhammad din fadilan sukayi,sosai Salima taji dadi






Saidai bayan dawowar Aliyyu Daga office ya tambayi ina iftihal tunda yasa anan take weekends,ya samu labari ta tafi ganin ummanta salima,fada ya dinga zabgawa,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,ya bata mata rai sosai,amma tunda Allah yaga niyyarta Kuma har murΓ dintΓ  ya cika shikenan,samira ce ta dinga bashi haquri domin itama ta fuskanci fadilan Daga baya,lokacin sunavtare fadilan na biya mata *minhajil Muslim* da Samira ke koyarwa a makΓ antarta,bai ko kula su ba sai da ya gama zazzagarshi ya wuce sashensa






*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*




πŸ“˜πŸ“˜πŸ“˜πŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ»βœπŸ»
[1/29, 5:33 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺






*PART 3*



4⃣8⃣




🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊


*WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GA DUKKANIN WANI MASOYIN LITTAFIN WA YASAN GOBE*




*_AHABBAKUMUL LAZI AHBABTANI LAHU_*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜πŸ˜










Kwana daya biyu yaso dauke mata wata kamar yadda tayi masa dif,don irin salon horonta da ba iso kenan Kayi masa a dauke masa wutΓ 
Sai dai inaaaa ya Kasa,ya yarda ya Kuma amince shi sadauki ne Kuma jarumi ta kowanne Fanni na rayuwa,saidai tuni ya dade da sanin cewa shi mugun rago ne indai bangaren abinda ya shafi Fadila ne






Bashi da jarumta kan fushinta,bashi da juriyar haqurin rashinta a kusa dashi,musamman kasancewarta tamkar uwa ga kowa dake cikin gidΓ n,jaruma ce mai juriya da kawaici yakanah da haquri,Duk wa su lΓ lurorin da matsalolin cikin gidan Matuqar baya kusΓ  zata sa kafΓ darta ta dauke su,koda ma wani lokacin yana cikin gidan takan bashi damar hutawa,Bango ce ita a cikin gidΓ n kowa na samun kulawarta






Zakayi mamakin yadda yaran ke qaunarta,kuwa Mamee Kasa,Mamee maza,hatta da Fatima sai Kayi zaton Bataan samira ce mamΓ rta ba,to itama Samira idan ta sabo tarin matsalolinta da shawarwarinta gun Mamee fadilan take saukewa,Tun danginta na ganin tamkar ta shanyetΓ  ne har daga baya suka fuskanta,ganin yadda 'yar uwa tasu ta sauya,Duke Kuma morarta ba kamar a baya ba,Daga qarshe har godiya suka miqa ga fadilΓ 






Qawaye kuwa nata irin na da a yanzu babu burbushinsu ko daya,Tun tuni ta fatattakesu daya da daya,tayi wa tayi kyau ta sauya


πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰


Tana cikin kitchen yau ita daya ce,ita dai Tun safe take jiΓ± kaya kayar yaran suna ta shiri,abbun su na bada direction na inda za'a kai kowa,aslam da Muslim dama na Egypt su na shiru shiryen shiga *jami'atu al azhar* bayan sun kammala secondary dinsu kenan






Zuhra Islam da iftihal yasa aka kaisu gidan ummi,faruq da saddiq Kuma aka kaisu gidan uncle abba,afrah da amrah Kuma sukayi gidan farida,sai gidan yayi tsit,baba talatu na sashenta,samira kuwa tayi gidan su itΓ mΓ  bikin qanwarta,can zata kwana






Ita kam batasan tafiyar tasu duka ta kwana bace don haka har da su take girkin,tanayi tana mita cikin zuciyarta an kwashe mata 'yan aikin,don idan su na gida bata yin komai banda Gyara bedroom dinta da part din abbunsu,nata bada umarni ne da yin gyara inda aka kuskure












*Mrs Muhammad ce*πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸŽŠπŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰
πŸ“•πŸ“•πŸ“—πŸ“—πŸ“˜πŸ“˜βœπŸ»βœπŸ»βœπŸ»
[1/29, 5:39 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*part 3*






4⃣9⃣






πŸ‘¬πŸ‘«πŸ‘­πŸ‘«πŸ‘¬πŸ‘«πŸ‘­πŸ‘­πŸ‘«
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*wannan page din naku ne HUGUMA NOVELS READERS tare da iyalanku gaba daya*
*Allah ya bar qauna ina godiya*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»










Ta juya don dauka abarba cikin freezer zata niqa ta hada zobo,sai riga mutum tsaye a bakin qofa,sqnye yake da long sleeve t.shirt maroon colour wadda tayi masa dai dai jikinsa,sai trouser baqi,idanunshi tsaye da gilashinsa nan,hannayensa duka harde a qirjinsa,gaba daya ya zuba Mata mayatattun idanunshin nan masu shegen maganadisu,






Tayi masa kyau matuqa da gaske,ba zai iya tuna lokacin da yazo ya sameta ba cikin ado da kwalliya ba,haka itamq din a dan Kallon sakqnnin da tayi masa,aliyyu bai tsufa,ko yaushe kamar ana sabuntashi,idan ka ganshi tare da su aslam sai Kayi tsammanin yayansu ne ba wai mahaifi ba,Duk wani kyau kwarjini da farin jini nashi sunyo shi,ginshira gaji da shan qamshi tamkar shi da su din tagwayene,shine gamboΓ±su






Sai ta kawar da kanta tamkar ba yanzun suke qarewa juna kallo ba,ta duqa don ciro abinda tazo daukan,ya saki lafiyayyen murmushin nan nasa,wato har yanzu fadilan nan tashi ce dai,miskilar nan,mai shan qamshi jan aji da dauke kai,yana jin shima ya kamata ya tuna Mata aliyyun nan nata, *Aliyyu Salim maitΓ ma* mai qarfin hΓ lin nan da yawan qaunarta






Kafin ta kai ga ciro abarbar taji caraf an riqo hannunta,da sauri ta dago gami da juyowa,sai dai tuni yayi mata masauki cikin qirjinsa,yasa hannayensa ya rufeta,kafin ta kai ga furta koma ya hade bakinsa cikin nata






Sai da ya zare mata laka baki daya,tuni tsaiwa ta gagaresu suka zube saman tiles din kitchen,ganin yana qoqarin wuce makΓ di da rawa yasa tayi qarfin halin tureshi
"Abbu so kake muyi abun kunya?,yara fa zasu iya dawowa kowaΓ±ne lokaci"
"Eh shi yasa ai na korasu don kada su hanamin cin amarci da matata,ke da ki gaΓ±su sai after three days"






Harararsa take saidai da ka kalli tsabar qwayar idontΓ  zaka gane cike hararar take da qauna da bege
"Wanne amarci kuma?,mutumin dake shirye shiryen aurar da first born dinshi"
"Haka kika ce,to zamu gani?"yace da ita gami da sungumeta da hannayenshi,bai sauketa a ko ina ba sai a fadarshi,Kallon juna suke suna murmushi cike da shauqi,sake rungume ta yayi cikin faffadan qirjinsa yana rada mata
"Fushinki kashni yakeyi *HASKEN IDΓ€NIYATA*,zuciyata rΓ guwa ce a kanki,zan iya jure koma amma banda lamuran da suka shΓ feki,na tuba *RAYUWA TΓ€*,kace *GATA NA*






itama cikin salon radar take ce masa"idan na dau ke ma wata tamkar ina hukunta kaina ne bisa ga Kasa bin ra'ayinka da nayi,mijina Kaine *DUNIYA TA*gaba daya,na gode wa Allah da ka zamo *uban 'ya'yana*"
Da sauri ya tari numfashinta "ni yafi cancanta na godiya ga Allah da ya rufamin asiri ya hana inyi asararki,da haka ta faru Fadeelah na,........da tuni na dade a kushewa ta"
Sai jin qauri suka cikin kitchen,da sauri suka rige rigen isa kitchen din












*Mrs Muhammad ceπŸ‘‘*
πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠ
πŸ“—πŸ“—πŸ“•πŸ“•πŸ“˜πŸ“˜βœπŸ»βœπŸ»βœπŸ»
[1/29, 5:44 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*YASAN GOBE?........*
πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠπŸŽ‰πŸŽŠ






*PART 3*




5⃣0⃣


πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜πŸ’πŸ’˜


*_I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY HUSBAND,MAY ALLAH HELP AND GUIDE YOU,I LOVE YOU_*😍😍😘😘






Shi yayi nasarar kashe gas din,suka kalli tukunyar miyar da tuni ta qone sannan suka kalli juna,dariya sukayi a tare,ya kama hannunta yasa cikin nashi tafin hannun bayan ya dage girarsa
"Kwanaki ukun nan na amarci ne
Babu girki.......
Babu aiki.......
Babu hayaniya.......
Babu yara.........
Ba surutu........
*just Fadeelah and aliyyu* kawai zasu more duniyarsu"
Itama girar ta daga "wow....I like it, *duniyar Fadeelah da aliyyunta kenan ko?*"ya gyada kai
"Yes!,yes my own"






Riqo hannunta yayi suka jero Tun Daga kitchen din,tafiya Duke very slowly kamar ba zasu isa bedroom din ba,kowanne jikinsa da zuciyarsa ta mutu da qwayar son dan uwanshi


*"na miki alqawarin kasancewa dake har bada"*


*"na maka alqawarin zamowa kusa da kai duk rintsi duk wuya"*


*"na miki alqawarin bata wa zuciyarki da gangar jikinki*"


*"na maka alqawarin zamo wa wata babbar duniya a gareka"*


*"na miki alqawarin dawwamar dake cikin farinciki har qarshen numfashin mu*"


*na miki alqawarin........*
*na miki alqawarin*.........




Haka aliyyu ya dinga hero mata har ta Gaza fadin koma,kukan dadi ya kufce mata,ta samu aliyyu fiye da yadda take zato hasashe ko tsammani,tabbas
*BABU WANDA YASAN GOBE SAI ALLAH*






Tana tsaye tana Hawaye ya zube a gabanta kan gwiwoyinsa,ya lalubo qwayar idonta ya sanya nashi ciki,ya soma girgiza kai
"Um.....um baby, *No more tears* kin manta?, *na miki alqawarin ba zaki sake kuka ba fa har abada*"
Dai dai lokaΓ§in da hawayen idonta suka silmiyo su na qoqΓ rin dinga a tiles,yayi maza yasa tafin hanΓ±uΓ±shi ya tareshi,tas ya lashe hawayen kan fuskΓ rta






" *NURY* kukan farinciki samun ka a matsayin miki nake,irin mijin da ke wa mata tsada da wuyar samu a wannan lokaΓ§in"


"Kamar yadda mata irinki ke tsada a wannan lokaci ko
ladabi,biyayyatsafta,dadi ni,haquri juriya da kawaici
Kyau,Zubi diri,kullum kamΓ r ana dada miki yarinta da wani dadi na......."
Da Sauri ta rufe masa baki da tafin hannunta cikin kunya tana boye fuskarta cikin qirjinsa
"Kai dear don Allah"
"Yes,zancena haka yake wlh *qurratu ainy*"






Bakinsu ya subuce a tare suka fadi *ALHAMDULILLAHIL LAZI BINI'IMATIHI TA TIMMUS SALIHAAT*
Sai suka hada ido kowaΓ±Γ±ensu ya sakarwa dan uwansa amintaccen murmushi






*tammat alhamdulillah*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»




*dukkanin wani yabo da godiya sun tabbΓ ta ga Allah madaukakin sarki*


*tsira da aminci su sake tabbata ga dan gatan Allah shugaban dukkan wata halitta baki daya annabi Muhammad s.a.w*




*bakina bazai iya fasalta tarin godiyΓ  ta ga dubban masoya na ba masoyΓ  littafina,Wanda goyon bayΓ nku haquri da juriyΓ rku ya kΓ ini gΓ  bigiren da nake kai yanzu,Allah yayi muku sakamako mafifici,mutane Daga qasashe da garuruwa daban daban*




*ina Neman afuwa da yafiya ga duk Wanda na bata wa ko littafina ya batawa rai,duk dan Adam ajizi ne,ba lallai Kuma mu sake saduwa bΓ *






*fatan alkhairi ga mahaifana*




*godiya mai qima ga HUGUMA novels readers*




*shin cikin littafina waye gwaninki?*


*wa kika fi so?*


*wa kika fi tsana?*


*me yafi burgeki?*


*me yafi bata miki rai?*


*wanne darasi kika gano cikin littafiΓ±?*


*mene yafi baki dariya?*


*mene ra'ayinki kan wa yasan gobe?*


*ina jiraΓ± saqonninku ta watsapp dina*
08187255862


*Alhamdulillah* *Alhamdulillah*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»




*Mrs Muhammad dinku ce*
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ˜˜πŸ˜




πŸ“•πŸ“•πŸ“—πŸ“—πŸ“˜πŸ“˜βœπŸ»βœπŸ»

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login