Showing 69001 words to 72000 words out of 130495 words

Chapter 24 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

da sauri, ganinsa tsaye bisa kanta yasa ta dan sukuyar da kanta "idan kinga dama ki koma bedroom ki kwanta"ya fada yai gaba hannunsa dauke da cup da flask din tea


Ta dauki a qalla minti talatin a zaune tana doubting din aliyyu ne kuwa ma ya tasheta?idan shi din ne ma ya zata iya kwana daki guda da aliyyu? Aliyyun da yaqi jininta? Bai sonta bai qaunarta?,wani benefit nata kawai yake so tayi masa girki da shara ba wai ainihin ita fadilan ba,ganin babu mafita ga wani sanyi da yake sirarowa falin saboda kashe na'urar falon da yayi ya sanyata miqewa jiki a salube ta njfi bedroom din


Kamar wata munafuka ta tura ta shiga,ga mamakinta yana kwance ne aqasa saman dan qaramun carfet din nan na gaba gado mai dauke da center table ya sauke center din shi kuma ya maye gurbinsa,trouser ne kawai ajikinsa da singlet,yayi ruf da ciki,hannun hagunsa da damansa duka pillow ne ya jajjerasu ya kuma matsesu ajikinsa,faffadan bayansa mai cike da siffar qarfi ya bayyana,ta dauke kanta cikin sanda ta zagayeshi gami da hayewa kan gadon tana mamaki cikin ranta shi kam wannn baijin sanyin garin nan ne?


Ga kuma sofa a dakin doguwa amma bazai hau kai ba?bata da courage din da zata magana don haka ta maida gulmarta ciki ta tattara tafukan hannayenta tayi addu'ar bacci ta shafe ilahirin jikinta da ita ta jawk bargon ta rufa tayi matashin kai da hannunta kasancewar duka filon dake kan gadon aliyu ya kwashesu zasu taya shi kwana😜😜


Idanunta fes a kansa tana gain yadda yake ta mutsu mutsu cikin ranta take munafuncin haka yake wai baccinsa ne shi,tun tana kallonsa har bacci ya rufe idanun nata,taso tayi daddan bacci mai tsawo a a lokacin saidai saidai hakan ya gaza samuwa don ta tashi yakai sau nawa saboda rashin sabo duk kuma tashin da zata yin idanunta na kan aliyyu sau uku tana ganinsa yana canza gurin kwanciya ana hudu ne ta ruskeshi yana qiyamul laili tuni ta miqe don ita din ma lokacin tashi yin tata sallar yayi


Aliyyu na bisa darduma yaga tashinta a zatonsa fitsari zata yi sai yaga bayan ta fito ta tayar da sallah shi da zuciyarsa yaje gulmar isha'i ne bata yi ba kota tsammaci asuba ce tayi?,shi kadai ke kida da rawarsa ita kam ta kafu gaban ubangiji,har ta idar idanunsa na kan fejin qur'anin dake hannunsa yana karantawa yana shafin qarshe ne cikin suratu anbiya'i,kusan yare suka sake miqewa suka tada sallar asuba kowa yayi tasa,yana so ya samu falalar jam'i sai dai girman kansa bazai barshi yayi mata tayi ba,bata jima da soma azkar dinta ba bacci ya sureta ko gamawa bata yi ba


🔅🔅🔅🔅🔅


Sanda ta farka ta duba agogon dake ajjiye kan side drawer tayi mamakin yawan baccin da tayi,ta yunqura da niyyar tashi sai ta ganshi shima kwance kan abun sallarsa yana baccinsa cikin nutsuwa da alama shima surarsa yayi bai shirya ba kamar yadda yayi mata,ta dan zubawa kyakkyawar fuskarsa ido wanda da idonsa biyu bata isa ba🙊,fuskatsa tayi mata kyau tayi wani fresh,ta dan girgiza kai ta miqe tsaye ta soma gyara gadona a nutse cikin taka tsantsan don kada ta sheshi sai da ta kammala tayi mopping ta wanke bandaki duk da baiyi komai ba ta sake kintsa falo,ta koma ta buda jakarta ta fiddo da turaren wuta ta jona abun turaren wuta mai amfani da wutar lantarki ta zuba cikin qanqanin lokaci gidan ya dumame da qamshi har ya leqa moqata ma,cikin sanda ta koma dakin gadon tayi saurin shiga wanka tun kafin aliyyu ya farka ta kasa sakewa


Shigar shadda tayi pink dinkin riga da skert ne sun mata cif sun zuna das ajikinta babu inda yayi kwarara kai ka rantse a jikinta aka dinka su,hida lip glosses sai kwalli kawai ta saka ta taje dogo kuma baqin gashinta ta kameshi da ribbon pink,ta ware dankwalinta tayi daurinta na zamani wanda ake sokeshi(ture kaga tsiya)hakan ya bawa jelar gashin nata damar zubowa ta qasan daurin,rigar sanyi ce wadda ko ciki bata rufe ba mai gashi dogon hannu ne da ita ita ta sanya light blue,ita kanta sai da ta juya ta sake kallin kanta duk da ba wani make up tayi ba amma ta zuba kyau


ta dauko turarenta ta shafe lungu da saqo na jikinta,har ga Allah tana jin dadin qamshin turaren yayi mata ta maida shi sannan ta koma kitchen din shirya break


Mrs muhammad ce👑


📚📚📝📝✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:56 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


3⃣3⃣&3⃣4⃣


Tun acikin baccin ya soma jin qamshin na ratsa qofofin hancinsa,duk zuqar numfashi daya da zaiyi yana zuqarsa ne tare da qamshin,qamshin yayi masa,tun yana tsammanin ko amafarki ne har ya soma gasgata cewa a zahiri ne ido biyu ne,sannu a ahankali idanun suka ci gaba da buduwa ya soma zagaye dakin da idanun nasa 👀,ko ina fes sai qamshin turaren wuta ke tashi da na wannan turaren nata da har yanzu ragowar qamshin bai bar dakin ba


Komai na dakin a kintse neat " I like it" ya fada can qasa,hakan yakeso ko da wani lokaci area din da yake rayuwa ta kasance,ya dan miqa hannunsa ya jawo wayoyinsa da ya dora kan center ya duba agogo,lokaci ya gani ya ja sosai din kuwa qarfe goma sha daya agogon china qarfe shida agogon gida nijeria,ya duba call logs nan ya tadda missed call na mr lin,babban dan kasuwa ne dan qasar china saidai sananne ne a qasashen duniya hakanan yana da companies anan gida nijeria sai missed call din andi biyu sai na salima guda biyar da ya biyo baya,duka baiji ba don a silent wayar take mantawa ma yayi bai kasheta ba don baya kwana da waya a bude saida babban dalili


A hanzarce ya miqe ya watsar da fulallukan da yake kai ya nufi toilet,as usual tun a gida a nan ma haka ya tadda ruwan wanka ready cikin bathtub shigewa yayi kawai abinsa,mintina talatin ya kammala wankan a gurguje ya fito ya shirya kansa cikin baqaqen suit harda baqar safar hannu saboda sanyi sunyi matuqar haska farar fatarsa yayi kyau kamar wani bature tabbas aliyyu badai kyau ba


Da hanzarinsa ya wuce kitchen kai tsaye kamar yadda ya zame masa aladarsa shan ruwa cup guda da safe kafin yaci komai,tun daga falon qamshin girki ya marabceshi,hancinsa ya bude sosai yana sheqar qamshin son ransa👃🏻😋,cikin kuzari ya qarasa kitchen din tana tsaye gabn gas tana kwashe chips don shi kadai ya rage mata dama ta kammala,bayanta yake bi da kallo tayi kyau kamar wata 'yartsana don kayan sun mata cif cif ajiki ya bi gashinta da kallo wanda ke reto a bayanta sai ya tsinci kansa cikin birgeshi da hakan yayi don shi kam ma'abocin son gashi ne tun yana qarami,ya dauke idonsa ya maida kan freezer bayan ya budeta yana jawa kansa kunne


Sam bata san da shigowarsa ba qarar rufe freezer din ita ta ankarar da ita,ta dago ta dubeshi yana shirin ficewa ya dan lumshe idanunsa sanda yake qoqarin barin kitchen din saboda feeling da yake ji sosai irin na jiya da ya hanashi sukuni da bacci mai dadi,bata ce komai ba ta biyo bayansa,har ya samu hannun kujera ya zauna numfashinsa na fita da sauri da sauri,cikin hanzari ya balle hancin gorar ruwan ya kai bakinsa ya soma daddaka


Bai ajjiye ba har sai da ya shanye tas ya wurga robar cikin dust bin dake kusa da shi yana maida numfashi bayan ya rufe idanunsa


"Your breakfast is ready"yaji muryarta kusa da shi tana fada,a hankali ya bude idonsa bai ganta ba don tuni ta wuce sai ragowar bayanta da ya gani sanda take qarasa shigewa kitchen,bai sake komai ba illa wucewa dining da yayi don gwada cin abincin


Ta zuba masa komai hatta tea ta hada masa a cup ya sanya cokali yana motsa shi,mamakin kanshi yake yana kuma tambayar kanshi *meke faruwa?* da shi,ta fito daga kitchen hannunta dauke da dan qaramin cup data hada black tea☕ta zauna cikin falon tana kurba a hankali qamshin ne yaci gana da buwayarsa ta hanyar iska dake kado mishi shi


Ya maida hankalinshi kan tea dinsa yana kurba kadan kadan,comfortably yake jin zamansa kan dining din shi daya,ya debi chips da pork ya kai bakinsa yana ci gaba da monitoring movement dinta da idanunsa,"hey" taji yace ta dago da kanta ya dan dago hannunsa ba tare da ya dubeta ba"come here"ya kirata sai taji ban barakwai,ta ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa dining din,ya sake kurbar tea din idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta ja kujerar gami da kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata


Bai ce komai ba har ya kammala breakfast dinsa,qamshin da yake ji ne ke rudashi ya rasa wanne irin mayen turare take amfani da shi ya zaro tissue daga cikin tissue dice box yana dan goge hannunsa inda ya bacin "as from today kada ki sake kawomin abinci ki bar gun har sai na kammala understand?"(nikam cewa nayi hmmmmm,fadi gaskiyarka na daure.......) "mutum sai shegen mulkin tsiya ba haka nake masa ba a nijeria wani lokacin bai taba cewa don me ba sai yanzu?wato zai fara fidda sabon salo don yaga ba'a gida muke ba"cewar fadila ita da zuciyarta,a fili kuwa gyada kai tayikata na a qasa "hey" ya sake cewa ta dago ta dubesa ta sake sadda kai "open ur mouth u r not a bruise" to tace masa cikin qosawa da zaman


Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina a gaba bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin gangar jikinsa is very strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata amma girman kai ya hana, yana ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da wani abu nata,he feel he can sustain whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da shi daga tashin da yayi niyya


Mrs muhammad ce 👑


📚📚📚📝📝✍🏻✍🏻
[10/16, 1:57 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


3⃣5⃣&3⃣6⃣


Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi pressing ok,sunan da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima ce,hira take yi masa sosai yana dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba daya launin idanunsa sun canza muryarsa ta sake zama so cool


Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu salama daga mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda yasa fadila daje shirin sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa da sukayi returning zuwa ja ya lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka taji saidai ba yadda ta iya ta koma din


Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun tayi tanajin wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya kitsa mata komai ba ta soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta gani yana tsatstsafo masa ya maida jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin jikinsa


ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya dinga sakin 'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar kallonsa tana mamakin meke damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few minutes,ya sauke doguwar ajiyar zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin da rai yana ganin kamar tasan meke damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark handkerchief ya share ragowar zufar fuskarsa


Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya sake fitowa wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya canza koma wanka yayi ne oho wa yasan masa😜😜😜,hannunsa riqe da brief case yana amsa wayar mr lien a hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa ya zaro yuan dari ya ajjiye mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin qasarsu?tabdijan" ta fada a fili amma qasa qasa kamar mai gunguni


Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen budeshin *maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka sara masa kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don dabbaqa value ba addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar motar ya shiga suka rufa masa baya


Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga yueyang hotel yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda ya bawa contract na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu wanda ya narkar da maqudan kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga manufacturing kayan babies blouses na maza da mata


Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka masa sosai gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren fadila ta wuni kwanciya sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga kitchen,pepe chicken couse couse da miyar qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin abincinta na dare


Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da turaren wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi wani dumi mai dadi daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka saboda sanyin dake damunta na garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta rufe cikinta jacket ta saka mai kauri ta mata wanda ta sauko har qasan gwiwarta tana da dogon hannu sai manyan maballai guda shida masu fadi da aka jera daga gaban rigar kusan sune kadai adonta,rigace da yawanci a turai matansu ke amfani da ita musamman lokacin sanyi


Gashinta ta gyara sosai ta kamashi da band ta saya socks qafa da hannu ko zata samu sauqin sanyin,da turarenta ta shafe jikinta ko ina ciki da waje,ta maida ta tattare abinda ya dan yamutse a dakin ta gyara shi sannan ta ciro jakar laptop dinta da sam ta manta da ita ta cirota tasan saqonnin email na nan na jiranta jingim ta dauki wayarta ta dawo falo


Sai da ta zauna sannan ta duba agogo don ganin ko lakacin sallah yayi don bata tsammanin akwai masallaci anan inda suke tun da tazo bata ji kira ba da agogo kawai take amfani ko dazun ma sauran kadan sallar azahar ta qwace mata,lokaci kadan ya rage lokacin sallar ya shiga don haka sai ta jona chargy na laptop din nata sannan ta zira hijabi ta shimfida dadduma ta tada salla


Bayan ta kammala ne ta ninke hijabin hadi da daddumar ta maida daki sannan ta dawo kan computer din tata,aikam ta tarar da saqonni masu yawa anty hafiza sumayya rabi'ah na sister farida ne akan gaba harda pictures din baby humaira masu yawa har da na ya ahmad ragowar kuma duka na masoya ne na gari dake qaunarta ,na 'yan uwanta ta soma dubawa kowanne na tambayarta ne sun iso lafiya? Da makamantansu,dai sai taji kewarsu ta cikata take ta shiga maida masu amsa lallai duk wanda yabar gida gida ya barshi,sai data gama da su sannan ta soma duba na sauran jama'a wanda ke da muhimmanci ta maida masa amsa mara amfani ta goge shi


A hankali ta daga kai karo na farko ta duba agogo,tara da mintina goma sha biyar,duk da cewa unguwar da haske ta dan soma duhu alamun dare ya soma kenan wasu sun kashe qwayayensu "me ya tsaida shi tun safe har yanzu?" Fadika kewa kanta wannan tambayar da ita kanta bata san amsarta ba,fargaba ta dan soma shigarta da tsoro lokacin da idanunta ke ganin kamar ana gilmawa ta cikin balcony dinsu,ta miqe a dan tsorace ta maida hijabinta bayan ta zare computer din daga jikin socket ta maida daki ta dawo falon ta tayar da isha'i


Har ta idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce sosai ta kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake kalla ya nuna mata qarfe goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji unguwar ya sake yin shiru ba komai ke tashi sai haushin karnuka🐕da keta kai kawo


Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule guri guda tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan


Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar falon hadi da tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya daga baya aka kashe,ai bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai itama taji,cewa take shikenan na banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk gidan da zata matuqar suna da kare to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan daman yaya lafiyar kura,yana daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata zuwa kenan da can suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su


Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a rude ,ji tayi an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda Allah zai sa ya kawo mata dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata yake kallonta ya zuba mata qwayoyin idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login