Showing 63001 words to 66000 words out of 130495 words

Chapter 22 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

ko kada ya yarda kina da muhammanci da wani tasiri a rayuwarsa komai qanqantarsa koda kuwa ya qaryata hakan da bakinsa,sister a iya hangena da tunani na na fuskanci cewa don kada ya aliyyu yayi missing girkinki ne baya so yayi nesa da abincinki wanda yasan zaiyi wuya ya samu kamarsa nima shaida ce"ta qarashe maganar cikin sigar tsokana wadda ta zame mata jiki


Ta nuna fadila da yatsa 👉�sannan ta dora ke zaki canza wannan manufar ke zaki sauyata da kanki,ke zaki canza wa aliyyu wannan lafazin nasa na bazai soki ba har abada ki qaryata lafazin nasa ta hanyar nuna masa ba wanda *_yasan gobe_* sai Allah,sosai ta gamsu da maganar farida dari bisa dari kaso sittin cikin dari na damuwarta ya tafi,ta jinjina kai hadi da sakin ajiyar zuciya sannan tace"batun aikina fa sister?" "So easy"inji farida ta gada tana murmushi😊"k8na iya daukar excuse a gurinsu ki musu bayani tafiyar gaggawa ce ta sameki zuwa china zaki ajiye aiki amma da manufar zaki je course ne na wata hudu,idan hakan bai samu ba su barki a matsayin wakiliuarsu ta qasar china ta tsawon wata hudu" "great sister!"fadila ta fada cike da farinciki,tabbas dan uwa na gari dadi ne da ahi gashi xikin 'yan mintina qalilan ta warware mata damuwarta,ta rungume faridan tana cewa"thank you sister ya barmu tare ya raya mana humaira"tace "amin Allah yasa kema ki samo mana tsarabar dan china nan da wata tara ko goma mu dauki sabon baby " dariya sosai ta bawa fadila tana jinta ne kawai


Sanda ta dawo gida yana zaune cikin balcony dinsa,tayi maza ta dauke kai gami da qara sauri don ta shige shi


⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Washegari qarfe 6:40 pm ta dawo daga aiki sun gama settling komai da managing director na express da freedom sai damuwarta ta sake raguwa qwarai da gaske,tana toilet din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi🍺,ta dan langabe kai kamar bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom


A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya samà ya rufe su ruf hadi da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin anguwarsu fadila


Muje zuwa masu karatu🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻


Mrs muhammad ce👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:50 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


2⃣3⃣&2⃣4⃣


A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu


Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen cikin zuciyarta tana cewa"ummi na bakya tsufa kullum gida kamar na budurwa" (haka haj amina take ma'abociyar tsafta ce da gayu,don bata yarda wai don tana da manyan yara harda jikoki ta zauna haka ba,baka raba qafarta da hannunta da jan lalle mai ado irin na yanzun wanda akeyi,hakanan kullum kalolin girkinta daban ne masu dannkaren dadi hakan ne yasa yaranta sukayi gadonta suma,tun aurensu ita da alhj abbas koda wasa bai taba tunanin qaro aure ba donba cewarsa ta isheshi duk dashi qarin aure qaddara ce rubutacciya idan Allah ya qaddaro maka sai kayi


Muhammad ta tarar ciki riqe da babban spoon na qarfe yana ta faman juya fried rice,dariyar da fadila ta tuntsure da ita ita ta saka shi juyowa don bai ankara da shigowarta ba sai lokacin,ya saki murmushi yace"anty fadila yaushe kika zo?" Ta kama baki"🤔ina zaka san na shigo ka taqarqare kana ta jagwal gwalawa ummi abinci,wai yaushe ma ka fara shiga kitchen?"ya saki spoon dinnyana share zufa a goshinsa"😊 ni wallahi ma gwara da Allah ya kawomin dauki ,please anty karbi girkin nan,haka yanzu ummi kemin ko ta daina sona ne ma oho?,amma don Allah anty fadila ina ni ina wani kitchen?,wai gwara na iya tunda ku kun tafi saura ni da ita kawai a gidan"dariya fadila ta sake saki ,ta qaraso kan girkin tana gyara wasu abubuwa sai da ta hada komai ta rufe ta rage mata wuta don ta turara sannan ta tambayeshi ya haye saman freezer yayi zamansa"ina ummi" "tana gun Abba yanzu ya dawo daga kasuwa ne amma tunda an fara kiran sallah yanzu zaki gansu"


Yana rufe baki kuwa saiga dariyarsu cikin falo,da hannu Muhammad yayi mata nuni da falon cikin salin gulma,dariya ma ya bata ta miqe da sauri ta isa falon,ita da abban ne kuwa yana tsaye riqe da abun sallah ummin kuma na dauke da hularsa,da murmushi suke kallonta ta durqusa ta gaida su abban na tambayarta yanzu take tafe?,ta gyada kai yace masha Allah ya mai gidan?,tace abba tare muke yana waje,"ashshsha banda abin fadila shima ai gidansu ne amma don sakarci kika barshi a waje "ummi tayi saurin qwalawa Muhammad kira tace ya zo ya shiga da shi,abba yace barshi naje na sameshi in yaso idan mun idar da salla sai mi shigo tare,a shirya mana abinci kafin mu shigo din


Ummin ta dan rusuna tana miqa masa hularsa tace"insha Allah abban Muhammad a dawo lafiya"ya karba yana dora ta a kansa yace "Allah yasa Allah yayi miki albarka" cikin dariya yaran suka taya ta amsawa da amin


Sai da fadila ta taya ummin suka shirya komai kan dining sannan suka tafi yin sallah ummi ta ahige dakinta fadila ma tsohon nata dakin ta bude ta shiga,bin dakin tayi da kallo komai yana nan kamar yadda yake,dan fridge dinta na boye ice cream 'yar kwanar da take ibadunta,inda take boye kanta idan zatayi kukan Aliyyu,sai komai yake dawo mata"Allah sarki" ta fada a fili tana shafa filonta da take cusa kanta a qasansa ,qwalla ta dan taran mata a ido ta sa yatsanta ta dauketa,toilet ta tura ta shiga ta daura alwala ta dawo inda ta saba yin sallarta tayi,bayan ta idar ta duba kan mirror dinta powder ce kawai akai ita ta dauka ta sake gyara fuskarta sannn ta mutstsika turare ya sauka qasan


Muhammad ne kawai zaune kan table din yana buga game a wayarsa ta zauna kusa da shi hadi sa dan dukan kafadarsa,ya dago ya dubeta yana murmushi, "ka shiga aji nawa ne har ummi ta yarda aka baka waya,cikin dariya yace "haba anty nafa zama senior ina s.s one fa,kuma ma yanzu nine babba a gidan nan"dariya ya bata sosai tana cikin darawar ne ummi ta fito,tuni har ta yi wanka ta canza shiga tayi kyau duk da ba make up take yi ba,fadila na shirin tsokanarta tace tayi kyau sallamar abba da ta aliyyu ta karade falon wadda ta yake hirar da suka so farawa


Abban ne a gaba aliyyu na biye da shi har suka qaraso dining space din abba ya fara cewa da aliyyu bismillah kai tsaye taga yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna sai tayi duru duru har rudewarta taso ta fito,ji tayi ya take mata qafa ta danji zafi ta dago kai suka hada ido yayi mata alama da ido na ta nutsu,sannan ya duqar da kansa ya gaida ummi cikin girmamawa,ita kuma ta amsa masa cikin kulawa tana tambayarsa mutanen gidan


Fadila ita tayi serving kowa banda ummi don tasan ba zata ci ba,tazo kan aliyyu sai ya rasa mai zata zuba masa idonta na kan warmer tace "mai zaka ci?" "Zuba min duk abinda zaki ci" ya fada abunsa tamkar ba shi yayi maganarba,da sauri ta dago kai ta kalleshi saboda wata kunya da ya bata amma sai taga shi ko ajikinsa,ta saci kallonsu ummi sai taga hirar su ma suke da abba kamar basu san da su agun ba,sai kawai ya zuba masa fried rice da farfesun naman kaza mai yawa tana son qureshi taga zai cin?


Sai kuwa ya shayar da ita mamaki don abincinsa yake ci hankli kwance duk da baici da wani yawa ba yafi shan lemo,bayan sun kammala ita ta kwashe kayan ta kaisu kitchen ta hada ta wankesu kamar yadda ta saba tanayiwa ummin tun kafin tayi aure,tana aikin cikin ranta tana gulmar aliyyu bai da kunya


Saman kujera ta tadda su ta parlour ta samu gefan umminta ta rakube,aliyyu ne ya dora kan maganar da sukeyi da abban "sallama mukazo yi muku abba saboda gobe insha Allah zamu wuce china" abban yace "zancan bude kamfanin ne ya taso kenan munyi maganar da abban naku ai wancan watan yake gayamin an dan samu tasgaro ne da tuni cikin wannan watan company n ya fara aiki" aliyyu ya gayada kai yace "eh abba insha Allah wanna karon za'a kammala komai a budeshi daman cike ciken takaddu ne na yarjejeniya tsakani na da gwamnatin qasar ya kawo tsaiko amma yanzun al'a muran saun daidaita


Mrs Muhammad ce 👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


1:41 pm 29/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*


2⃣5⃣&2⃣6⃣


Abban ya jinjina kai yana cewa "kasan qasa ce mai tsari da doka ba irin namu qasaahen ba da sai dai muce inna lillahi wa 'inna ilaihi raji'un,Allahbya taimaka ali ya kuma yi jagora yasa a budeshi a sa'a,Allah yayi ma jagora a dukkanin lamuranka"ummi na amsawa da amin yayin da shima yayi qasa da kansa yana cewa "ameen ameen abba na gode Allah ya qara girma" yana shirin miqewa yasa hannu cikin aljihun kuftanshi na riga ya zaro turare yan ubansu designers ya ajjiue wa abban,albarka yasa masa tare suka qarasa miqewa abban zai masa tattaki kasancewar alhj abbas mutum mai sauqin kai ba ruwansa da wai shi mai shekarune babba ne kowa nasa ne


Sai lokacin fadila ta janye idanunta daga kan aliyyu kallonsa tayi sosai don bata taba ganin sa yayi doguwar magana irin haka ba,yanayin yadda yake maganar cike da girmamawa sai ya sake burgeta ta sake lafewa jikin ummin tana saukar da ajiyar zuciya,ummin ta kalleta sanda suka gama ficewa "au sake ma wani rabewa kike ajikina ke da ake jiranki?" Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kuwa ta saki kuka,ummin ta saki baki tana kallonta "wai wannan wane irin sakarci ne ko wata matsala kike da ita?" Kai fadilan ta girgiza,ance tsakanin d'a da uwa sai Allah hakanan sai tausayin gadilan ya kama ummin don yasan duk mace kimai jin dadinki baki rasa matsala ta zamantakewar aure,a da rance take mata nasiha hadi da lallashi


Ganin hankalin ummin ya tashi sai tace cikin son kawar da hankalin ummi daga tunanin ko tana da wata matsala tunda tasan halin iyaye yanzu sai ta fita shiga damuwa"ummi bana son na barku ne har wata hudu" ta saku ajiyar zuciya tana godewa Allah "idan banda quruciya irin taki fadila ko kina nan din ma basai ki kusa wata biyu ma baki gan mu ba ummm.....kiyi addu'a kinji Allah ya kaiku lpy ya dawo da ku lafiya kawai" tace amin tana share hawayen cikin dakiya


Ta zuge zif din jakarta ta fito da kudaden nan ta dorasu cinyar ummin,ummin ta kalli kudin sannan ta dubeta "wannan fa na meye?" "Naki ne ke da abba" "ina kika samo su fadila?yaushe kwata kwat kika soma aikin? Ina fatan ba roqonsa kike ba dai ko?", ta girgiza kai "a'ah ummi shi yake bamu kullum idan zai fita" ta dauke kudin ta ajjiye a gefe tana cewa "za'a dai juya miki zan bawa abbanki ko yayanki zasu san inda zasu sa miki su" ta langabar da kai tace "don allah ummi to ko dan wani abu 👌🏼 ne ki cira aciki ke da abban ku samin albarka" ta bita da "to naji"


Idonta fal da hawaye zuciyarta a raunane ta fito ,suna tsaye jikin motar aliyun ta qaraso ta tsugunna har qasa idanunta rau rau muryarta na rawa tana yiwa abban sallama "to fadila Allah yayi muku albarka ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya,ki zauna lafiya agidanki bana son fitina kada na ji kada na gani" tuni kukan ya qwace mata "insha Allahu abba"kasa tashi tayi har sai da abban ya daga ta da kansa,aliyyun ya zuba musu ido wani abu yaji ya taba ransa shi ya bude mata motar Abban ya sata ciki da kansa,aliyun ya rufe qofar sukayi sallama da abba ya zagaya ya shiga gun zamansa ya tada motar


Shiru cikin motar sai sautin kukanta danke tashi kadan kadan hadi da sheshsheqa,burki taji yaja bayan ya gangara gefan tati ya kashe motar sannan ya dan kwantar da kujerar da yake kai din ya kwanta rigingine idanunsa alumshe yana sauraran sautin kukan,sai da suka kusan kwashe awa guda ahaka lokacin tuni har kukan nata ya tsagaita,ya miqe a kasalance ya gyara zaman kujerar baice uffan ba ya tada motar suka wuce


Cikin daren bata kwanta ba sai da ta hada duk abinda take da buqata cikin babbar trolly dinta sannan ta kwanta zuciyarta fal da saqe saqe kala kala


⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Cike da kasala take janye da akwatin nata har ta iso bakin motar qirar sienna dake fake a harabar gidan,yadine a jikinta mai sulbi blue 🔷 tayi rolling da red din mayafi🔴🔵,sosai rigar ta bude daga qasa takalminta red ne hill sosai 👠,motar na bude duk suna ciki nasiru na mazaunin driver aliyu na kusa da shi sai salima dake sit din can baya bisa dukkan alamu ga fuskarta nan ta sha kuka,fuskar samira ba yabo ba fallasa tana sit din tsakiya,yayin da fadila ta zauna a sit din farko nasiru ya karbi troly din nata ya sanya a baya


Cikin hanzari nasiru ke ruqin aliyyu ya sake duba gaogonsa yace "nasiru qara sauri zamu iya missing flight" ya sake qarawa motar gudu don bin umarnin ogansa


Ba dadewa suka isa aminu kano international airport nasiru ya ajjiye motar inda aka tanada don ajiyar motoci,dukkaninsu suka fito daidai lokacin da airport din ta karade da sanarwa neman masu tashi a jirgin ethopian airline,hakan ya tabbatar ma da aliyu sun kusa makarar kam,tuni nasiru ya ciro musu jakankunansu,ya dubi samira da salima da fuska take adinke musamman salima da takejin kamar ta dora hannu aka ta zunduma ihu,"sai na dawo" yace kamar mai jira salima ta fashe da kuka ta taho a guje ta fada jikinsa,ya saki dan qaramin murmushi hadi da sa tafin hannunsa yana dan bubbuga bayanta alamar rarrashi,ya miqawa samira daya hannun alamar ta taho,dauke kai tayi tana turo baki zuciyarta babu wani takaici sosai Idan ta tuna da maqudan kudaden daya barwa kowaccensu tasan zasu sha bushasha don ma yayi misu gqrgadi da jan kunnen akan fita"sai ka dawo"tace kawai,ya dan janye salima daga jikinsa sukayi sallama da nasiru,ya wuve fadila ta rufa masa baya saluma ta bita da harara kamar ta fincikota,batasan itama fama take da fargabar bin aliyyun ba


Reception suka wuce suka qarasa departure ta farko suka shiga layin screening,aka kammala da su aka basu boarding pass suka qara gaba,immigration suka sake duba visa dinsu suka buga musu stamp suka shiga dan dakin jiran jirgi,mintina qalilan jirgi yayi ready suka bi layin shiga jirgi tana gabansa yana tsaye a bayanta


Mrs muhammad ce😘


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻












[10/16, 1:51 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


2⃣7⃣&2⃣8⃣


25 and 26 ne number din sit din nasu don haka sune maqotan junansu,aliyyu ya daga yar trolly din da aka barsu suka shigo da ita saboda kilo din ba wani mai yawa bane ya sanyata a inda mayafiyan ke ajjiye jakankunan nasu,yan kallo fadila nata kiciniyar sanya tata saboda ta dan yi mata nauyi,sai da ta soma gajiya sannan ya sa hannu ya janyeta ya fada kan kujerarta ya daga trolly din tata ya sanya mata ya koma sit dinsa ya zauna yana gyara zaman suit din jikinsa


Kowa ya zauna a mazauninsu,fadila na bakin window ta zubawa filin airport din ido tana fargabar yadda jirgin zai Lula da su sararin subhana duk da yawansu kasancewar wannan shine shigarta jirgi na farko a arayuwarta


A hankali aka zare matattakalar aka maida qofar jirgin aka rufe bayan sun gama duk wasu yan tsarabe tsarabensu suka bada sanarwar daura belt,fadila ta jawo belt din saidai bata san yadda zata sata ba,tana satar kallon aliyyu ta gefan ido yana daura tasa,ya kammala ya fito sa laptop dinsa ya dora bisa cinyarsa


A hanakali jirgin ya soma qugi hadi da shawagi a doron qasa na kimanin minti goma sha biyar sannan ya yunqura don rabuwa daa doron qasa,fadila ta runtse idonta saboda wani tsoro da ya kamata,ta qanqame belt din dake hannunta wadda ta kasa daurawa jin jirgin na niyyar dawowa qasa ya tarwatse da su😂😂😜😜 lol har naga idon masu karatu aliyyu salim mai tama da fadila zasu mutu😂😂


Ta qanqame belt din dake hannunta jin tana niyyar subucewa daga kan sit din ta,cikin zafin nama aliyyu ya kareta da hannunsa sannan ya amshe belt din ya zagayeta da hannayensa ya daura mata hadi da cewa "silly girl" ya gama ya koma kan danne dannen da yake kan laptop abinsa ba tare da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login