Showing 84001 words to 87000 words out of 130495 words
Chapter 29 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
suka gaya mata kudin da zasu cajeta suyi mata printing ticket?,cikin sauri ta gyada masa kai tun kan ya kammala printing din ta fito da kudaden ta ajjiye masa a gabansa,yana miqo mata da rawar jiki ta karba tana duba time da jirgin zai tashi awa guda ta rage mata
*mrs muhammad ce*๏ฟผ๐
๐๐๐๏ฟผ๐๏ฟผ๐โ๐ปโ๐ป
[10/16, 2:04 PM] ๐๐ฌ๐Salma๐๐ฌ๐: ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*WA YASAN GOBE?...*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*PART 2*
5โฃ5โฃ&5โฃ6โฃ
Da sauri ta koma gun mai taxi ta shige gidan gidan baya tana bashi umarnin su wuce airport,koda suka je kasa zaune tayi babu abinda take banda duba agogo hadi da sharar qwalla
๐
๐
๐
๐
๐
๐
Da qyar aliyyu ya samu ya yage aiki da kuma jama'ar dake dakonsa,ya bawa jumong umarnin ya maidashi gida,cikin motar ya zaro wayoyinsa ya kira lukas yace kada a nemeshi ko menene ya taso shi ko mukhtar yayi handling dinsa,ya wuce gida ne madam ba lafiya,cikin girmamawa ya amsa masa,ya cire wayar daga kunnensa ya hada da wadda ke ajjiye kan cinyarsa ya kashe su gaba daya,ya zuba su cikin 'yar jakar laptop dinsa
Jumong ya tsaida motar aliyyun ya fice,jumong din nata yi masa sallama amma hannu kawai ya iya daga masa ya shige gidan,fuskarta kawai yake da muradin kallo,ita kadai yake son gani,ta bashi wani abu mai tsada muhimmanci da daraja agun 'ya mace,ta bashi abunda ya kasa samu shekaru masu dama,abinda ya debe tsammanin ana samunsa gun matan yanzu,yana jinta sosai cikin jikinsa zuciyarsa ruhinsa...yana kuma jin wani matsayi da daraja mai girma nata cikin idanunsa
Wullar da jakar tasa yayi kai tsaye ya nufi bedroom don yafi tsammanin samunta a can,yanayin yadda dakin ya dan yamutse ya danji mamakin ganin hakan,saboda bai saba gani ba ko tsinke bai taba katarin tsinta cikin kitchen dinta ba ballantana bedroom,to amma bai kawo komai cikin ransa ba sai ya dan ganta hakan da yanayin raahin jin dadin jikinta,saboda haka ya juya ya koma ya duba kitchen,shi yana nan kamar yadda ya barshi da safen babu wani abu da ya canza,sai ya sake komawa bedroom din yana bawa ransa tana toilet to
Gefan gadon ya zauna yana zaman jiranta wanda daidai yake da a kirashi da zaman jiran gawon shanu,har sai da ya dan soma qosawa ya miqe bayansa sama gadon fuskarsa na kallon ceiling,sai yaji qayau qayau kamar ya kwanta kan wani abu,yasa hannun nasa qasan bayansa ya zaro ta yadan jujjuyata sai ya wullata daya gefan gadon,ya mirgina kansa da niyyar duban qofar toilet din sai idanunsa suka sake kaiwa kan takaddar,sai ya tsinci kansa da son budeta yaga mene a ciki don bata barin komai saman gadonsu
Yana daga kwancen ya jawota ya warwareta yakai idanunsa ciki ganinta cike taf da rubutu ya bashi mamaki,paragraph din farko kawai ya karanta sai gashi zaune dirshan tsakiyar gadon ba tare da ya san yaushe ya tashi ba,kafin aliyyu ya kammala karanta saqon tuni ya jiqe da gumi duk da ragowar sanyin dake qasar ta sin,ya kammala karanta layin qarshe na takardar gami da cukuikuyeta cikin tafin hannunsa da qarfi,rawa kawai jikinsa yake tamkar sojan da aka bugawa kugen yaqi,launin idanunsa tuni sun canza daga ainihin fararen nan qal masu haske zuwa jajaye,babu launin na alamun tashin hankali a lokacin da bai bayyana bisa fuskarsa ba,tsananin tashin hankalin da yake ji a lokacin bazai misaltu ba "why?why fadilah?me yasa kika yimin gurguwar fahimta?,me yasa kika fahimceni a abaibai?,ina zaki tafi?ina zaki tafi ki barni?,ba haka bane fadilah....ba haka bane abinda kike zato"shi kadai keta wadannan sumbatun ya dunqule hannayensa cikin junansu takardar na tsakiya
Wurgi yayi da takardar,tamkar an zungureshi ya fice daga dakin cikin matsanancin sauri,"ina zata yanzun?batasan kowa ba cikin qasar? " Tambayar daya takura yake ta faman nanatawa kansa ita bayan yasan shi kansa ba sanin amsad yayi ba,yana gab da fita a gidan wani tunani ya fado masa,cikin zadin nama ya juya ya koma ,kai tsaye inda yaga passport dinta shekaran jiya ya nufa ya hau dubawa wayam baya gurin,cikin zafin nama ya juya ya fice daga gidan,taxi ya tsayar ya shige shaf yama manta da cewar ana gayawa mai abun hawa inda za'a,gani yake ma tamkar taxi driver din yasan inda zai kaishi,saida yayi ta nanata Tambayar inda zai kaishi sannan ya tuna ya gaya masa airport zasu je
Safa da marwa take cikin departure din,hankalinta a tashe yake gani take tamkar aliyyu zai biyota ne ya hanata tafiya,wani bangare na zuciyarta ke tunatar mata babu yadda za'ayi aliyyun ya biyota,abunda kake qauna shi kake nunawa kulawa da damuwa da halin da kake ciki,koda sace ta akayi bata tsammanin aliyyun zai biyo sawunta bare tafiya tayi da qafafunta,duk da haka hankalinta bai kwanta din ba sai da suka hau layin shiga jirgi,ko anan din ma bata fasa sharar hawaye ba,sam bata damu da yadda jama'ar keta kallonta ba har wasu kan gaza shiru suce mata "sorry" kallon da suke mata bai dadata da qasa ba don ji take tamkar ansa mata wani hijabi ne cikin zuciyarta,tuni kowa ya kama sit din sa ya zauna tana sit 34 A,sanarwar daura belt ta biyo baya bayan an rufe qofar jirgin,a lokacin ta tuna tahowarsu da aliyyu qasar ranar da ta kasa daura belt dinta,kuka ne sabo ya sake qwace mata *kukan baqincikin rabuwa da shi ne ko kuma na farincikin rabuwa da shi ne?kukan shaquwa ne ko kuwa na kewa ne?* oho ita kanta bata sani ba,ita dai kawai ta tsincin kanta tana yinsa,a hankali jirgin ya soma qugi yana motsawa sannu sannu har ya ware sosai ya fara shawagi kan kwaltar dake doron qasa
Ko ta kan security dake ta tareshi da tambayoyi bai bi ba har sai fa ya dangane da inda yake son zuwan,duk ma'aikatan gun suka miqe saboda girmamawa don tuni garin na guangzhou ya soma gane wane aliyyu cikin qasar ta sin,sanarwar bikin bude katafaren kamfaninsa ya riga ya karade ko ina cikin qasar,cikin sakanni qalilan ya basu umarnin duba masa list na sunayen mutanen da suka tashi zuwa Nigeria tun daga safe zuwa yanzu,girmansa yasa suka masa haka don kuwa ba kowa ke samun haka ba sai idan jami'in tsaro ne da kyakkyawar shaidar neman wani mai laifi
Tafi yafi har suka zo list din qarashe wanda suka sanar masa jirgin yana daf da cillawa sama,daga qarshe sunan fadila Abbas Bashir ya bayyana,cikin azama ya dakatar da su yana fadin"mai wannan sunan nake nema" "ai tana cikin wadanda jirgi zai daga da su nan da yan sakonni" cikin sauri ya tashi yana fadin yana son a dakatar da tashin jirgin,cikin girmamawa yace "sorry sir bazai yiwu ba mun riga mun gama handling din komai,duk ma'aikatan mu sun san da tashin nasa,haka na qasar da zai sauka" da qarfi ya doki sama table din cikin zafi yace " I said stop the flight now!!!" Ya sake rusunar da kansa yace "sorry sir it can't,but idan kana buqatan tafiya zuwa nijerian ne sai amaka printing ticket"
Ya harde hannayensa a qirji ya lumshe ido yana maida numfashi,shi kadai yasan yadda zuciyarsa ke masa zafi da quna,shiru yayi tamkar baza ya furta komai ba "hasbunallahu wa ni'imal wakeel" yake karantawa cikin zuciyarsa,a hankali ya soma jin temper din na nasa na raguwa,still idanun nasa na alumshen yace"ok ina son jirgin da zai kuma tashi anjima" "sorry sir yau babu jirgin da zai kuma zuwa nijeria" "gobe da safe " "sai da yamma sir" "noooo!!!" Ya fadi sa qarfi hadi da bude idaunsa wadanda suka kuma zama manya ya ware su sosai kan ma'aikacin,ya sake dan rusunar da kansa gami da cewa"sir sai da yamma kayi haquri"shirun ya sake yi yana ci gaba da kallonsa,cikin ransa yake dana sanin rashin mallakar jirgi na kansa da yaqi yi a baya bayan yana da damar hakan,sai da ya gaji don kansa sanan ya sanya hannu cikin aljihunsa ya fito da kudi wanda baisan nawa bane ya ajjiye masa,ya miqa masa ticket sannan cikin sauri ya irgi kudin su ya muqawa aliyyun sauran saboda gudun kada ya karya dokar qasarsa,wani irin wawan kallo aliyyun ya watsa masa wanda ya sashi janye hannunsa shi kuma ya fice abinsa
Tafiya ce mai tsawo tamkar a zuwan ta kawosu airport din addis ababa,hamdala tayi da taji cewar nan da awanni biyu jirgi zai sake kwasarsu ya miqa su nijeria kanon dabo babu batun kwana kenan a ethopia,hakan yayi mata dadi sosai don burinta kawai shine ta bude idanunta ta ganta cikin nijeria zuwa lokacin idanunta sun sake yin luhu luhu saboda kuka wanda ta kasa tsaida shi
๐
๐
๐
๐
๐
๐
Qarfe takwas na dare agogon nijeria jirginsu fadila ya landing cikin aminu kano international airport,sannu a hankali passengers suka soma saukowa,tun sanda suke kusa da sauka ta soma tunanin ina zata nufa?gata dai a nijeria?,ba zata nufi gidansu ba ko giyar wake ta sha,ta sani idan dai har taje din babu shakka babu ruwan abbanta ko umminta zasu maidata ne gidan aliyyu hankali kwance,ta tabbata ko ta bakinta ba zasu buqaci ji ba,bayan ta riga ta yiwa aliyyu da ita kanta alqawarin yanke zamansu,ta masa alqawarin yin nesa da rayuwarshi,a yanzun bata da muradi ko digo kan ci gaba da zama da shi
*"ta inda aka hau ta nan ake sauka"* haka zuciyarta ta gaya mata,take ta amince da batun zuciyar tata,ta yiwa daya daga cikin direbobin airport din magana kan inda zaya kaita,take ya amince tare da tsula mata kudi,bata damu ba ko a duska din ita ba wannan ne a gabanta ba,ba ta wannan take ba ta kanta kurum take yi
Har a lokacin hawaye bai daina bin fuskarta ba kamar yadda bata fasa gogeshi ba,har ta soma jin babu dadi saboda kukan da take,har qofar get din gidan mai taxi din ya ajjiyeta,ta fidda kudinshi ta bashi,unguwar ba kowa shiru kasancewar haka yanayinta yake koda da rana ma balle dare,ta qarasa ta qwanqwasa get din,mai gadin ya yaso yana tambayar wane? dare ya soma a lokacin don tara ma ta gota,"nice" ta amsa masa bai dai gane wace din ba har sai da ya leqo ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin get din,cikin rawar jiki ya soma ture wagegen get din yana fadin sannu da zuwa hajiya,ga tsammaninsa a mota take,shigewa kurum tayi ta ajjiye masa dari biyar canjin da mai mota ya bata bisa bencinsa tana cewa "rufe get dinka bada mota nazo ba"yawan kyauta da fadila ke dashi yasa yake daukin zuwanta din bata taba ahiga ta fita bata yi musu ihsani ba
Tana shiga anty hauwa na fitowa daga kitchen da yake qofar shigowa falon opposite qofar kitchen din ta ne na qasan,hannunta dauke da food flask guda biyu,baki ta saki galala bayan ta tsaya cak tana kallon fadila,har ta bude baki zata yi magana sai ta lura da yanayinta a hargitse taje ba kamar yadda ta santa ba ba lamaun nutsuwa tare da ita,mamakinta yaushe suka dawo daga china babu labari?,kan tace komai din fadilan ta share wani qwallar "subhanallahi" anty hauwa tace ta qaraso da sauri ta dire flask din saman kujera ta kama hannayen fadilan tana fadin "lafiya fadilah?"a rude,"daga ina haka?" "Daga airport nake anty" ta bata amsa murya a dashe
Bata kuma cewa komai ba don tasan ba lafiya ba ta ja hannunta suka bi ta wani dan madaidaicin corridor dake hannun hagun falon,dakunan bacci ne ciki guda uku,daya na baqi wadanda baza'a kaisu boys quarters ba daya na yaranta wanda du sun kwanta bacci kasancewar da wuri take sasu suna yi saboda makaranta,daya kuma nata ne duk da ba kwana take ciki ba sosai ko yaushe suna sama a tare da mi gidan ta saidai idan yayi tafiya ne,ta tura qofar dakin suka shiga tare,daki ne mai kyau kamar sauran dakunan bakin gado ta zaunar da fadilan hadi da cewa"kiyi wanka kiyi sallolinki,nasan cewa ba lafiya ba lo baki gayamin ba"ta miqe ta fita jim kadan ta dawo dauke da wani cooler madaidaita guda biyu na baincin daya hannun nata kuma sabuwar abaya ce ta ajjiye mata,"ga abinci kici,ga kaya ki sauya don kifi jin dadin jikinki,zani na sallami abbansu kausar right?"ta qarashe da tambayar fadilan,kai kawai ta gyada mata kamar qadangaruwa a sanyaye anty hauwan ta juya ta fice
Cikin abinda anty hauwan tace tayi abu uku ta iya wanka canza kaya sai sallah,tana zaune akan darduma tana share hawayen dai nata,ta yanke hukuncin da taga shine daidai saidai ta rasa me yasa zuciyarta ke son bijere ma umarninta?,anty hauwa ta turo qofar ta shigo ,a sanyaye fadilan ta dago kanta tana masa mata sallamar sai kuma wani dan kukan mai dan qaramin sauti ya kubce mata ta sunkui da kai,dirshan anty hauwan ta zauna gabanta ta riqo hannayenta "cool down fadila mana,ki nutsu ko gayamin me yake faruwa?,ni kuma na miki alqawari tunda kika zabeni kika kawomin matsalarki zanyi qoqarin warware miki ita"cikin sigar lallashi har anty hauwa ta ciyo kanta ta tsagaita kukan duk da hawayen dai basu bar zuba ba
Ta danja majina irin ta mai kuka tace "anty so nake na rabu da aliyyu"zaro ido antyn tayi har da sakin hannun fadilan,daga bisani ta tattro kalaman tambayarta "saboda me fadila?,me ya shiga tsakaninku haka bayan kowa na ma ali murnar morewa aure yanzu?kowa sha'awar zamanku yake?,"murmushin takaici ne ya kama fadila ta girgiza kai "anty zaman mu abun sha'awa ne ga wanda baisan halin da nake ciki ba,ni da nasan me nake ciki banga abun sha'awar ba,banga sha'awa ga tilastawa wanda bai sonka ya zauna tare da kai ba,kin taba ganin inda anty wuta da ruwa suka hadu suka cakuda suka zauna kuma suka rayu suka wanzu gu daya?,banga abin shaawa ga zamantakewar auren da babu soyayya cikinta ba sai zallar qiyayya,anty aliyyu na cutar da ni ta hanyar rashin samun soyayya da kulawarsa,hakana ina matuqar cutar da shi ta hanyar tilasta masa zama da ni baya baya so,baya sona,ina cutatsa ta hanyar sashi kallona a matsayin matarsa,bayan ya gayamin baya sona bakuma zai taba sona ba,don me zan zauna anty allah ya kamani da haqqin cutar da shi?" Ido ta kuma zarowa tace"kamar yaya fadila,kimin gwari gwari ki daina min zancen kurma da bebe"
Ta dago tsaf tana kallkn antin don mafita yanzu take nema,so take ta canza rayuwarta yanzu,so take ta bude sabon babin rayuwa ta manta komai,rayuwartatake so ta maida ta ta mafarki ta fara ta gaske,tana so ne ta manta da aliyyu ta manta ta taba sonsa,baya sonta(a zatonta) itama ya kamata ta qishi(nikam nace hmmm zaiyiwu kuwa????)hmmmmm muje dai zuwa ga *part 3*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*alhamdulillahi rabbil alamin,wassalatu wassalamu ala man talaqqal qur'nu mi ladun hakimul khabir*
๐๐๐๐๐๐
*godiya ga mahaifana*
*sannan godiya ga dukka members din group dina huguma novels readers da dukkan wani masoyi na wa yasan gobe,Allahbya bar qauna ameen summa ameen*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*kuci gaba da bina da jin yadda wannan rikita rikita zata kasance,meye ra'ayinku game da jaruman wannan littafi?ina saurarenku ta number wayata*
*na gode*
*mrs muhammad ce*๐
๐๐๐๐โ๐ปโ๐ปโ๐ป
[10/16, 2:08 PM] ๐๐ฌ๐Salma๐๐ฌ๐: ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*WA YASAN GOBE?...*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ๏ฟผ๐บ
WA YASAN GOBE?....**WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HIGUMA*๐
๐ผ*PART 3*๐๐ผ0โฃ1โฃ
A hankali ta bude bakinta tace "anty *ta inda aka hau ta nan ake sauka* ,kece silar qulluwar igiyar aure na da aliyyu,ranar wanka kuma ba'a boye cibi"............A nutse cikin hikima ta soma labarta mata tun ranarhaduwarsu da aliyyu,ta fara sonshi tun kafin tasan waye ne shi,hakanan tun kafin shima ya san tana yi,ta rufe da cewa "sai ajiya na sake tabbatarwa aliyu ba sona anty yake ba bisa wani qwaqqwaran dalili nawa"(ta rufe ba tare da ta gaya mata ba),tayi shiru hawaye na diga a fuskartaShuru anty hauwa tayi don ta kasa cewa komai,ta jima cikin jimami,ta jima tana gyada kai kafin daga bisani ta saki nanauyan ajiyan zuciya "fadila sannunki da qoqari,ba shakka ke din jarumar mace ce mai son farincikin iyayenta,kin cika 'ya ta gari kuma 'yar halak,dama wannan zaman kike amma bamu taba gani ko a fuska kin nuna alamu ba?,tabbas aliyyu zaici qaniyarsa duk hukuncin da kika daukar masa ya dace da shi,wanne taimako kike da buqata a guna fadila fadeshi,kowanneiri ne zan iya miki shi,nayi da na sanin zamowa silar hada aurenku,na zamo silar xamanki cikin qunci bayan ni ima zaune cikin walwala"anty hauwan ta fadi cikin takaiciGirgiza mata kai fadilan tayi "kada ki soma dana sani anty,domin kuwa qaddarar Allah ce,ya hukunta hakan dole sai ya faru koda babu ke anty......alfarma daya nake so anty....bana son kowa ya san ina gidan nan koda kuwa 'yan gidan mu ne,bana son in sake tozali da aliyyu har sai ya ban sakina,rabuwa nake son nayi da shi saboda na barshi ya sake yayi rayuwarsa ba takura,in barshi ya rayu da masoyansa don rayuwa tare da miqiyi cikin inuwa guda ciwo ne da ita"ta fadi maganar tana jin wani daci har kan harshentaSosai anty hauwa taji wani tausayi nata har cikin ranta ta girgiza kai gami da kama kafadarta"indaiwannan alfarmar kawai kike nema fadila baki da matsala,kin samu dari bisa dari,amma in one condition.....sai kin min alqawarim cire wannan damuwar daga zuciyarki,kin bar wannan dan banzan kukan da kike,ba lokacin ki bane na kuka yanzu lokacin aliyyu ne har taya shi ya kamata ayi saboda asarar mace irinki da yake shirin yi,asarar da bazai taba maye gurbinta ba,dubi fuskarki yadda ta canza saboda tsananin kukaMurmushin yaqe tayi"insha Allahu na bar kukan anty daga yau,bazan sake zub da hawayena ba akan aliyyu,yadda bay sona ni din ma na bar sonsa kenan har abada" "good" anty hauwa tace tana dariya hadi da girgiza hannayen fadilan,sai kuma kunya ta dan kamata yadda ta taqarqare tana gaya mata bata son dan uwanta ita kuma ta kuma tana bata goyon baya ba tare da son kai ko zuciya ba ta sunkui da kai,Murmushi anty hauwan tayi "kada ki ji kunyata fadila gaskiyarki kike fadi,kowanne hukuncikuma da kikayi yayi daidai,don wallahi kinji na rantse miki mace dai dai ce zata iya irin zaman da kikayi ba"๐
๐
๐
๐
๐
Ya sallami mai taxi din da kudin da shi kansa baisanyawansu ba sannan ya shige gidan,bisa kujerar falo ya zube yana maida numfashi,wani azabar ganinta yake son yi ,a hankali ya kai idonsa inda ta saba ajjiye masa ruwa da drinks wayam gun yau ba komai,ba qamshin girkinta babu na freshner dinta,sai yaji gidan tamakar kango garin ya koma masa tamkar maqabarta,burinsa kawai gobe tayi yafice ya bar qasar,wayarsa ta soma karadi ya cirota don takaici bai san sanda ya bugata