Showing 87001 words to 90000 words out of 130495 words
Chapter 30 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma
da qasa ba ta bude komai ya tarwatse a saman centerA sanyaye ya zauna gefan gadon hadi da zubawa farin bedsheet din nasu ido yadda ya baci da jini haryanzu yana bisa gadon,bai son tayar da ita ne a jiya shi yasa ya tureshi gefe ya kwantar da ita,idanunsa suka sake kaiwa kan tray na breakfast da ya hada mata tun safen kafin ya fita,yana nan yadda ya shigo da shi dai dai da cup ba'a juya shi yadda ya saka shi ba da alamun babu abinda taci kenan?Ya daga zanin gadon yana qarewa jinin jiki kallo,shi kansa bedsheet din wata qimarsa yake gani,daga qarshe ya duqunquneshi a qirjinsa da dukka hannayensa biyu idanunsa na a lumshe,wata mahaukaciyar soyayyarta ke ratsa shi,baisan lokacin da ya kwanta saman gadon ba,fuksarta ce kawai ke masa yawo cikin idanunsa,zanen fuskar yake gani sanda suka kasace a lokaci mafi tsada dadaraja a rayuwarsa,lokacin da bazaya taba barin tunaninsa saidai mutuwa ta cire masa shi,lokacin da bazai taba daina ganin darajarsa ba saidi mutuwa ta hana shi,qamshinta ya dinga ji sosai kan pillow din da ta kwata tamkar tana gurin,da sauri ya bude idonsa,vest din ta ce ta jiyan daya yaga saitin hancinsa,da sauri yasa hannunsa ya dauko ta yana sake mannata cikin hancin nasa,tamkar zai shide tamkar zai zuqo fadilan daga jikin vest dinJuyi yake sosai cikin wai irin shauqin qauna da soyayya da bai taba zaton akwai makamanciyarta ba a duniyarmu "why u leave me?why?,I cannot sustain missing you,I can't,me yasa sai da kika mun kyautar abu mai tsada da daraja baki tsaya kin karbikema abu mafi tsada da daraja aguna ba kika barni?,me yasa ba zaki tsaya na saka miki dimbin kyautatawarki gareni ba?,why baki sanar da ni sirrin zuciyarki ba sai lokacin da kika barni why?....." shi kadai qwal cikin gidan harma a dakin yake ta wadannan sumbatuSam ya kasa hassalawa kansa komai,koda suit dinsaya gaza cirewa bare akai ga yin wanka ballantana kuma batun abinci,koda yana da buqatarsa bazai iya ci din ba don harshensa bai gamsuwa da girkin kowa idan ba natan baSai yanzu ya soma tantance son da yame mata ashe yafi wanda yake ma girkin ta?,sai yanzu ya fara ankara da dalilin da yasa yake hasala da yawa idan bata gyara masa part ko bata masa girki ba fiye da yadda yake jin zafi yake hasala fiye da su samira?,sai yanzu ya gane dalilin da yasa yake jin haushi idan ta kammala girki ta bar masa bangarensa kafin ya dawo?,sai yanzu ya fuskanci dalilun da yasa yake qin cin abinci har sai ya tilasta ta ta zauna by his side har sai ya kammala?,ashe sone hakan?,wani irin salon sone wanda bai farga da wane lokaci da kuma yaushe ya shiga zuciyarsa ba sai yanzu?,ba abun mamaki bane don bai taba kamuwa a akaran kansa da *SO* din ba sai a kanta,tamkar ya taso ne ya saba da cusa masa shi ake ta qarfin tuwoKamar ya jawo goben haka yake ji,daren gaba daya ji yayi yayi wani mugun tsawo a gunsa kamar jansa aka dada yi,gani yake kamar gari bazai waye ba,kayanta dake cikin cupboard gana daya ya watsosu ya barbazasu kan gadon ya kwanta akai yana shaqarsu ko zai samu sa'idar zugi da zillo da zuciyarsa ke masa game da ita,saidai inaa....kama da wane bata wane,tamkar wani zautacce haka ya koma idanunsa jazur bashin baccin jiya da yau gabadaya kuma bacci bai ziyarceshi ba sai gab da subaπ
π
π
π
π
π
Kiran wayarsa su mr lun ke tayi amma gaa daya layukan switched off,suna baqatarsa sosai don awanni uku kacal ya rage a soma gudanar da bikin,baqi masu zuwa nata tambayarsa,hakan yasa andi da kansa ya taho gidan takanas ba shiriCikin bacci yaji anataba qararrawa da alamun neman izinin shigowa ake,tsaki yaja ya maida kansasaman filon hadi da maida fuskarsa hannun hagu maimakon dama a yadda take dazu bashi da ko niyyar tashi,saidai mai danna qararrawar yaci gaba da matsata kamar babu gobe har sai da mijin nadiya ya fito abdul basid,hakanne ya sashi miqewaa fusace ya zare rigar saman ya cire tie din ya wurgar ya bar 'yar ciki ya fito cikin haushin kaza huce kan damiSuna hada ido da andin yasan cewa babu lafiya fa,don kalli daya zaka yima aliyyun kasan ya koma wani hargitsatstsen aliyyu,cikin tsawa yace "what doyou want?!" Cikin girmamawa yace "sir d time is passing,u have to prepare........." "leave me alone!" Aliyyun ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu cikin wata tsawar,ya ja qofarsa garam ya kulleta ya koma cikiSaman kujera ya koma ya zauna yana nishi,sai a alokacin idanunsa suka sauka kan wayarsa da ya tarwatsa jiya,yasa hannunsa ya tsince ya maida layukan ya sanya batirin ya kunnata,servicena gama hawa massage suka yita shigowa sun kusa hamsin,ko guda baiyi sha'awar budewa ba bare ya karanta,hasalima hankalinsa bai kanta nashi tunanin daban,cikin haka kira ya shigo,bai ko kalli wayar ba bare akai ga batun dagawa,sai da tayi ta katse har sau biyu,cikin jan tsaki ya sanya hannu ya janyo wayar da niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden bugu kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan wasu lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake sashi cikin wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?" Cikin rawar murya yace "abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya dakatar da shi"ya isa bana son jin komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka ka koreshi,damar da ka ka jima kana jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da ita?,maza ka ahirya kafin lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki ya maida bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar samun nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai kalleshi ba,cikin kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da kanshi don cika umarnin abban nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai da yakeyi babu walwala a fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan babu kuzari ko qanqani tattare da shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta ne domin wannan rana,maqudan kudade aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta ba sai angaya maka ta lashi kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi rigar ciki kuma da tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma kawai abun kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam babu nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar sabuwar baqar mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga cikin kutane na farko da suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya watsa musu harara don yana ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna yayin da ragowar biyun suka bishi da gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu sake cewa komai ba suka shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad* mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a nutse cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon isowar aliyyu,babu wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall dinShigowar tasa ya sanya duk wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya zura da gudu ya bar hall din haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya hau step din da ka tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss sisineo ce hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka kmmla zama sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai gabatarwa ya yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron yadda aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da bindiga aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce kawai zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba lokaci,jawabai masu muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya yi,sai ya bada uzirin baijin dadi sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya tantance yana sha'awarsu ko baya yi bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka sannan aka zo gangara,su mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga dimbin al'ummar da suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka mukhtar ya manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin a halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention nasu,ido kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni matuqa cikin rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar soyayyar gareta",ya danyi jim sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a lokacin da ya bayyana gareni na dade nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta barni a lokacin da nake da buqatar yi mata mafificiyar soyayyar da ba'a taba gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi mai azabar nauyi cikim zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta zama ruhina da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu duka biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe cikin kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake bayyana bankwana da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai sun yimin nauyi fiye da littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan hannayensa guri guda yana yinsa ya sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga ainihin zuciyarsa yake fita ba daga harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya fadi yana qoqarin komawa ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya burgesu,fuskarsu da zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai girmama soyayya komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na gwal guda biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai siya mata ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa hannu ya dauke yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce*ππππβπ»βπ»βπ»β?
ππΌ *PART 3*ππΌ
3β£&4β£
Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka zagaye shi da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a gaba a tsaye andi ya miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya datse,tafi aka saki sannan suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga shiga daya bayan daya cikin kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa
Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake kamar yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi ba,sam hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa wanda aka tanadar masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan ya koma ya kulle ya koma saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya tashi,baya tsammanin zai iya zaman jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira jumong da mukhtar
Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna yayin da jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka kaini airport" "ok sir" ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa me zaya yi a airport?,bai bashi wannan damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya tambayeshi ba "nijeria zan wuce mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka kayi handling dinsa,bazan yi sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin fahimta yake dubansa "like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u cannot help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is ok,is ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin jakan sa,yaga komai na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card platinum ya ajjiyewa mukhtar din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a gaggauce sannan ya bude qofar ya fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa
Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai tsaida shi daga tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma gani yake jumong baya sauri laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da ya soma masa maaifa kan ya qara gudu "sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin ya tuna ba'a nijeria yake ba dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani yake ba sauri yake ba shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan kwana kan sai gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai yake yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai washegarin
π
π
π
π
π
Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don daukarshi,gidansu yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga cikin motar saiga sumayya ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman fadila,"yauwa" yace yana sanyo qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani ajiya kikemin leqe leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana ba,kwananta biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin komawa ciki tace "bari na fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da labarin ma ta dawo to me yake faruwa ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani mai nagge(unguwar su fadila)
Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar bakinshi fal addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito daga inda suke ajiyar motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan shuka,nasiru ne ya qwala masa kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa "kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana washe baki da son jin amsar inda yayarsa take,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana fadin "bari nakira abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da jakarsa
Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata zo gidan ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje lafiya an dawo lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya abba" abinda ya iya fada kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira ba ya sallameshi shima ya fice kasuwa
Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa ya tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me suke fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar yana shirin shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa don hajin wanda aka bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne cikin motar,wata dabance ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a baya,dariya suke ta sheqawa sam basu ma kula da wani aliyyu ba har suka yo parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka yiwa albishir din ba zata mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata ido,suma qawayen dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya bayan daya suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake kallonta ba ya shiga bangaransa
Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa anyi kiran sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani tunaninsa na ina zai sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin tissue fari tas ya shirya,yayi kyau sosai duk