Showing 111001 words to 114000 words out of 130495 words

Chapter 38 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

maca ce ce zata San Wayne ainihin aliyyun ba ta kada kishinsa,musamman ma ita da kunsan tafi kuwa saninsa zahiri da badininsa






Salima nata rawar kai ta shige gaban,Aliyyu ya tada Motar yana qoqarin gyara madubin motar ta yadda zai samu sukunin gano fuskarta sai dai sam taqi yarda da hakan don tuni ta kautar da fuskarta,dole ya haqura ya soma tuqin hankalinda na rabe gida biyu






Duk yadda salima yaso ta janye hankalinsa suyi hira mai tsawo da dadi ko don ta cusa musu haushi abun ya faskara,dole daga qarshe itama ta haqura ta ja bakinta tayi shiru
Ko da suka shi go harabar gidan tamkar dama Allah Allah take su iso tuni ta rigasu ficewa tamkar bata jin nauyin jikinta,ya biya da ido don ba haka yaso ba






Yaso ne ya datseta a cikin Motar ya mannata da jikinsa ya dan rage mata temper,don a matakin da take ciki tana buqàtar wannan,salima dake lure da shi takaici ya cikata,ta sake qullatar Fadila,ta Kuma sake lasar takobin hana abun dake cikinta tayuwa kota halin qaqa






Ya dauke idanunsa lokacin da ta bace wa gàninsa,bai bai ta kan yadda suke kàllonsa kamar zasu cinyeshi danye ba ya jaw wayarsa dake gefensa ya latsa number din Anty hauwa ya kira,bugu uku ta daga
"Hello mummyn kausar,ga ajiyata nan as usual, pls abata kulawa ta musamman Anty na"dariya ta saka
"Ho,aliyyyuuuu.......to naji,mene tukuicina?"
"IPhone 7 da kike son siya ki bar kudinki ni Zan Waya miki"ta sake dariya"lallai Ashe abun na yine,to ba Matsala,kada ka damu dan qanina"
"Thanks Anty",ya fadi yana kashe wayar






"Amma fisabilillahi tuni yaushe bace maka ina son iPhone 7 din nañ ,kowa cikin qawayena ita suke riqewa ammavkaqi siya mini,sai ganshi rana tsaka kace zata siyawa Waya",Kallon da yayi mata ya sanyata yin dañasañin yin furucin,tuni kafin yace wani Abu ta balle murfin Motar ta fice tana qunquni cikin ranta Wanda ta bata isa ta yishi a fili ba,don ba qaramin wuya ta ci ba lokaciñ da ya amshe mata key din mota da wayarta bakamin ya dawo matà da su






Ya maida idonsa kan salima,tayi qoqarin hadiye bacin ranta don son cimma qudirinta kan fadila cikin ruwan sanyi ba tare da an gano komai ba,ta bude motar itama ta fice ranta na mata wata iriyar suya,tanajin zata iya koda kawar da fadilah ne don ta shigar mata hanci da qudundune da yawa,tasa ta rasa fili da gurbin da ada take jin tana da shi a zuçiyàrsa






Cikin falon ma kowa sannu yake mata,ciki wata bakwai amma sai ka dauka da ka bar gun za'a bika ace ta haihu,haushi,takaici,kishi,qyashi da hassada ta cika zuciyoyinsu,Samira da bata iya shiru ba tace"mu sai a tsine mana albarka ai tunda bamu iya daukan ciki ba"ciki ciki tayi maganar amma wani abun ya dan fito,madina tayi yunqurin magana Momi tayi mata inkiya da tayi shiru kada tabi ta kanta,sama dakinsu sumayya ta haye abinta tayi kwanciyarta Anty hauwa ta cika mata plate da ayaba ta bawa bilkisu ta miqa mata,Momi kuwa tayi ruwa tayi tsaki hawa,hana kuwa hawa,fada ma ta dinga don me yasa bà'a barta ta zauna a gida ba tana fama da kanta haka,batasan ita ta rage lallai sai ta so ba






Baccin kuwa take sonyi,don matuqar ba ranar girkinta bace bata ita wani baccin arziqi,ta riga ta saba bacci jikinsa,yana làllabata kamar qwai harda tausa yake Gara mata,baya runtsawa har sai ta rigashi yin baccin






Kira ya shi go wayàrta tana kwance lamp da tsammanin zuwan bacci,ta duba sai taga sunan *darling blood* sunan da ta sama number dinsa kenan,sosai take da muradin jin muryarsa sai dai tana sane tayi banza da wayarta,sau biyu tana rurinta tana katsewa sai a Kira na uku ta sdaga,ta kara a kunnenta ba tare da tace koma ba,ajiyar zuçiya ya soma saki wadda ta ratsa Fadila har ta tayar mata da tsigar jiki
"Babyyyy..."ya kirata Murya qasa qasa cikin Jan sunan,itama ajiyar zuciyar ta soma saki"I missed you badly"abinda ta iya fadi kenan cikin narkakkiyar murya,ya sani sarai akwai kewarsa dake damunta,kwana hudu ba tare da juñañsu ba abune ba mai sàuqi qwarai da gàske,sai tausayintà da sonta ya sake kamashi,iya kawaici tana da shi,gashi nan da kwana biyu zasu wuce umara shi da salima da Samira harda doctor sa'adah wadda ya mata alqawari






"I know baby na,saidai hankalina na tashi idan na ganki cikin rashin walwala,please smile my dearest wife,ko da bana kuwa nasan zànji a jikina"
Bata San lkcn da murmushin ya subuce mata din ba,musayar kalaman soyayya suka dinga yi masu tsuma zukatan ma'aurata,aliyyu yaqi barinta har sai da yaji shiru alamun baccin ya dauketa






*Mrs Muhammad ce 👑*




📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺






*part 3*

2⃣7⃣






Kai kawo take a bangaren nata don tuni aliyyu ya sawwaqe mata zuwa nasa bangaren anan bangaren nata yake yada zango har ya kammala yi mata kwanakinta,yayi hakan ne don hanata yin aiki Wanda ta saba da shi Duk ran girkinta sai ta qalqale bangaren nasa da su suke barinshi babu kintsi








Amma Duk da hakan bata fasa Duk wa ni shirye shirye na karbar mai gidan nata duk ranar girkinta,yayi mitar yayi fushin har ya gaji,ta Riga da ta saba bazata iya zaman ba,bata jin nauyin da tayi,uban cikinta bai damunta Kuma bai hanata duk wani abu d ya kamata ba,sosai aliyyu ke yabawa jàrumta da juriyarta






kamar yanzun ma ta kammala komai,sanye take cikin wata gown mai azabar kyau,budaddiya ce sosai daga qugu zuwa qasa,hakan yasa bata takurawa turtsetsen cikinta ba sai damar fitowa ma da ta bashi,yayi das a jikinta,qaramin hannu ne da rigar,ta tattara gashinta a tsakiyar kanta ta daureshi da ribbon Kalmar rigar,fuskarta tayi fayau tayi kyau cikin simple makeup, sai qamshin nan nata take zubawa,






Ta jita da niyyar shiga kitchen don dauko banana taji sàllamarshi yavshigo parlour din nata hancinsa na sheqar daddadan qamshinta,da sauri suka nufi Kuma kuwa na qoqarin tar bar dan uwansa,shi ya soma nasarar cimmata ya rungumeta ta bata yana sansanar wuyanta cike da farinciki
Fuskarta qunshe da murmushi tace"Baka da dawowa gida mijina"
"Yauwa matata abar alfaharina"ya mayor mata cikin salon qauna da kulawa,sunfi kusan mint I biyar a haka sannan ta juyo da niyyar amsar jakarsa su qarasa daki,zullewa yayi yana noqe kafada"naqi wayo nan naki,a waysnce fa kike Karya min doka daya bayan daya,bayan na hanaki dawainiya da ni"
Murmushi ta saki,ya Dora lebensa a goshinta ya sumbaceta






Qoqarin ta rage masa kayan jikinsa take don ya samu yashiga wanka Sam ya hanata ta gajiyar kama hannuwanta ya zaunar da ita gefen gado,tana kallonsa har ya gama ya daura towel ya shige wankañ,tuni ya tadda ta ta fiddo masa da kayan da zai sa ta feshe masa su da turare,ya gama shiryawa tsaf sannañ ta taka masa ya fice sallah masàllaçi ita Kuma ta koma ta tayar da tata






Sai da ta cika masa ciki da abun ci shi Kuma ya ci ka mata nata da ayaba yana tsokanarta ta zama qanwar monkey, bata kulashi ba sai da ta qarasa cinyewa abarta sannan ta taqarqare ta tureshi ta haye kansa
"Wayo jama'a wayo mummy 'yar lukuta maman baby zàta karyani a kawo agàji"ya fada yana qyalqyala dariyar tsokana,ta turo baki"kyau sai ka gayawa aya zaqinta"
"Wayo 'yar matata ki taimakeni ki dagani kada nayi amai
"To zan daya ka ammà kan sharadi dayà"
"Naji fadi indai zaki dagàni nidai"yana riqe da cikinsa yana qoqarin boye dariyarsa hade da yi mata gwàlo a fakaice
"Ni ka yima gwalo?"ta na nuñà kanta da danyatsanta gami da shagwabe fuska,dariyar da yake boyewar ta subuce ta fito






"A'ah,ni da baby na da yake ciki fa muke wasa"ta kalli cikin nata sai aliyyun ya bata dàriya,sai ta sauka tana ce wa"sharadina kamin doki"tuni kafin ta qarasa ya juyo mata bayàn nasa"maza hau,kada ki sauka har sai kin gaji da kañki"ta tattare rigarta tana shirin hawa salima tàyi knocking,hakan yasa fadila sakin rigàrtata ta koma saman kujera ta zauna,da qyar sàlima ta samu ta hadiye wa ni dunqulallen Abu mai zafi da ya tokare mata maqoshi,a duniya ta tsani ta bude ido taga fadila dauke da cikin nan a jikinta,ji takeyi da ta dunga ganin Fadila da shi ta gwammace ta bude idoñta taga baqin kumurcin maciji






Babban Abu na gaba dàke tayar mata da hankali,so qauna kulawa màsu nauyi da take gaji guñ aliyyu akan Fadila da cikinta,ta sani tayi sake Kuma ta barar da damarta,ta kuma bar kari tuni ran tubani






dumbin kulawa da tarairàya babu wadda bata Samu ba guriñ Aliyyu,tuni yà bana mata hanya qwaya daya da zata sake samun damar mallakeshi shine ta hanyar cika masa gida da yara amma sai ta gaza yin hakan,ta watsa masa qasa a ido,a yanzun tana jin shiryawa yin hakan,ta shirya kawàr da duk wani Abu da zai zama mata shamaki tsakaninta da Aliyyu,Samira ba matsalarta bace lamarintà mai sauqi ne bata dameta ba kamar yadda Fadila ta tsole mata ido.......


(09063329635 SMS only pls)


*Mrs Muhammad ce👑*




📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺




*part 3*


2⃣8⃣






Ta qaraso falcon tana qaqalo murmushin dole
"Uwar biyu"ta sima ce wa da fadilan
"Maman biyu"fadilan ta mayar mata,ta kalli aliyyu dake zaune saman carfet ta zube a gabansa tana masa nacin kallo,qaunarsa na fisgrta tana ara mata qaimi kan qudirinta
"Dear barka da warhaka"fuskarsa sake ya amsa mata,ta turawa Fadila flask kamar koyaushe"ga wainar fulawa nan nasa an miki, itakam Fadila abun na daure mata kai,babu Ragnar Allah da zata fito ta fadi ba tare d Salima ta kawo mata wa ni abun ba,fara'a da kulawa take nuna mata,sai dai dan jarida da lawyer ba wasa bane,can qarqashin murmushinta fara'arta da kulawarta fadilan na tsakulo wa su yanayi boyayyu kan fuskar saliman,Saidai ita taimakon da Allah yayi mata cikin nata ba mai cite cite bane idan har taci ayabarta ta jiqa zobonta ta share to shikenan






"To na gode"kawai fadilan tace, ta Daki remote ta qaro sautin t.v tare da maida hankalinta kai,saboda jin wani kishi na taso mata yadda aliyyu ke hira da salima cikin sakin jiki ta soma ka ranta "hasbunallahu wa ni'imal wakeel",Samira ce ta shigo gamida ce wa"sllama" kanta tsaye ta nufi kusa da Fadila ta sauna don Neman magana,ta kalli aliyyun yayi da shi din ma ita yake kallo ,cikin ransa yana fadin"can za mutum sai Allah"baar doguwar Riga ce a jikinta kanta babu ko kallabi,d slipper sonta ta shigo har tsakar faloñ,hannunta Kuma ga ragowar miya da maiqo nan,ya sake fadin "yanzun haka qila ta taho har nan kenan"






"Gani,ina zaune zan fara cin abinci ka kirani,har na fara ci naga waccar ta taho bace Gwara na haqura da abincin inzo inji kake faruwa kada ayi bàbu ni,ko a yimin munafurci a cuceni ganin bani gun"sai Kuma ta maida kanta gun Fadila dake gefanta"ummm,anata mana Kallon banza ko"ta sani sarai da ita yake don ta saba gaya mata haka,wai tana mata Kallon banza tana ganin zata haihu






sau tari dariya Samira ke bata idan ta fadi haka,don ita dai bata ga wa ni Kallon banza da take musu ba,sai bata fiya damuwa da shirmen ta ba,bata da qullaci kanta tsaye take magana,haka idan zata ai kanta kanta tsaye take fadi ba boye boye






Maganar aliyyu ce ta dau ke hankalinta daga kan fadilan
"Jibi insha Allahu zamu wuce umra,za muyi sati biyu da yarda Allah"sai ya bude wa ni file dake Ajjiye kusa da shi ya ciro passport guda biyu ya miqawa salima da Samira,wani uban ihu da tsalle samiran tayi sai gata ta dire a gaba aliyyu,ta ruqunqumeshi,tuni har ta shafe masa ragowar miyar hannunta
"Da gaske don Allah sweet aly,za muje saudiyya,wayo dadi zamu keta hazo"sumbatun murna ta dinga yi,don kafin aurensu ya mata alqawarin fita honeymoon da ita har ta saka rai sosai don bata taba barin nijeria ba,sai Kuma ta barar da damarta






Salima ma murnar take yayin da Fadila tayi kamar Batasan me ake ba,don ta tsammaci zai miqo mata nata passport din tunda yana guriñsa,a hankali ya maida idanunsa kanta bayan fitarsu,ko motsi bata yi ba tana zaune a inda take kamar yadda taqi furta komai
"Babyyyy"ya kira ta ta juyo ta kalleshi,sai Kuma qwalla ta ciko idanunta,ya miqe tsam ya iska Kujerar da take kai
"Baby.......kuka?"kamar jira dama take sai kawai ta rushe da kunya
"Subhanallahi"yace ya kwantar da ita kan cinyarsa,a hankali ya dinga shafa gashin kanta da yasha gyara yana jin sautin kukanta na sauka a kunnensa,bai hanata ba don yasan ba yin kanta bane






sai da ta gama ta qoshi har tana sakin ajiyar zuciya sannan yace mata"baby me ya faru erhmmm?"
"Shine zakayi tafiyarka umra kai da kayan ka wato ni a barni a gida ko?"
Murmushi ya saki mai dan sauti,ai kuwa sai ta sake qufula
"Dariya ma kake mini?ai dole Kayi dariya saboda yanzu bani da mamora kenan"sai ta kuma sakin kuka,masifa ta hau zazzaga masa da bala'i,shi kam ma sakin baki yayi yana kallon dan qaramin bakinta daketa zazzaga masifar yarda qoqarin qwacewa daga jikinsa,sai ya hanata ya matseta a jikin nasa har sai dà ta gaji don kanta tayi shiru,sai Kuma ta dinga sakin ajiyar zuciya alamun ta fara sauka








Yana dagota yaga tuni Ashe bacci ya dauketa,murmushi ya saki ya dagata cak ita da uban cikinta ya kaita bedroom cikin dabara ya suya mata kayan bacci ya gyara mata kwanciyarta sannan ya dawo parlour ya gyara gun dà suka ci abun ci ya hada kwanukan ya wanke mata su tas,don yasan matuqar suka kai safiya saita wanke kafin ta hada breakfast






*Mrs Muhammad ce👑*




📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/28, 7:56 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺






*part 3*



2⃣9⃣




Lokacin da ya dawo tuni ta Dade da yin nisa cikin barcinta,ya jima zaune yana kallonta,ba qaramin tausayinta yake ji ba haka nan d wannan uban cikin nata da yafi watanninsa girma
"Har yau Baki gama sanin irin matsayin d kike d shi cikin zuciyata ba Fadeelah,sadai na sani lokaci zai ci gaba da nuna miki"ya fada a filing,bayanta ya koma ya kanta bayan ya janyota jikinsa ya sake tofesu da addu'o'in tsari na kwanciya barci,hannunsa daya na saman cikinta yana shafawa a hankali yana jin qaunar abinda ke cikin nata yana sake ratsashi


⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜


Qarfe goma su na falon zaune abinsu,Garin na lullube ne da hadari kadan don haka babu batun rana,sanyin a.c da qamshi mai taushi ne ke ganshi a falon,tun dazun ya tsura mata ido yana dariya qasa qasa,tun safe yake dawainiya da ita,wqnka,shiryata,bata ayabarta amma taqi yarda ko daya su hada ido,kunyar abinda tayi masa jiya ke cin ranta,tana ganin ta zaqe da yawa ta gaya masa maganganu da ya cancanci yayi fushi d a ita amma yaqi maimakon haka ma sai ya buge da yi mata hidima da dawainiya d ita






Zuwa can ya sake tsunkularta ta sa hannunta ta dan bugeshi ba tare da ta kalleshi ba,tasan dai abinda yake so,da dai yaga taqi kallonsa sai ya sure ta gaba daya ya azata bisa cinyarsa yana leqen fuskarta
"Haba baby nah,so kike ne yau na susuce ?,gaba daya yau kin hanamin Kallon sexy eyes dinki"
Sai ta fada qirjinsa tana Hawaye
"Ka yafemin miki na,na maka rashin kyau tsawa jiya,na mance lokacin da ni ka dauke ni mukà tafi Wata qasar tsawon watanni my biyu kacal,kishinka ne yamin yawa har na ai kanta hakan,amma......"






Da sauri ya tura harshansa cikin bakinta ya hanata qarasa maganar tun dazun dama lebunan nata ke bashi sha'awa,daga bisani ya cire yaba share mata qwalla"kada ki sake yamin asàrar hawayena masu tsada,bayan already na gayamiki ba zaki sake kuka ba har abada,ni baki yimin komai ba"aliyyu miki ne daya da daya Wanda sàmunshi a irin wannan zàmanin sai an tona,wuni sukayi tarairayar juna,ita tana qoqarin faranta masa shi yana qoqarin kyautata mata,ganin bashi da niyyar fita yasa ta tambayeshi
"Kyau babu inda Zani sai la'asar,ina tare da masoyiyata"dariya ma ya bata,aliyyu mayen Soyayya ne wani lokacin idan ya cikata da ita sai ta rasa inda zata tsoma ranta






Duk d cikinta hakan bai hanata sakarwa aliyyu kanta yayi yadda yake so ba Duk da qoqarin boye zalamarsa da yake hakan bai hanata dagoshi ba,shi Kansas mazewa kawai yake amma yasa zaiyi kewarta ita da babynsa ba kewa ba na wasa ba,ya yaba sosai da juriyarta d jarumtarta,sau tari taken danne farincikinta don shi ya samu nasa,hakan yake qara masa qaimi gun kula da duk wani abu da zai kawo naqasu ga walwalarta






Sai da yayi la'asar din sannan yàce zaije shi da nasiru yayi masu handling din koma,ana magariba zai dawo suje ta siyi abubuwan da take da buqata
Ta kashe hand drayer din da take busar da gashinta da ita"my haidar,ni bana guitar koma,kada ka wani kashe kudinka"ya dau ribbon sonta yana tayata faire gashinta "ban son in tafi in bar ruhina tana buqatar wa ni Abu"
Ta saki murmushi "bana tsammanin ko shekara hudu zakayi zan rasa wani abu cikin gidanñañ"ya sani Fadila akwai tattali ,ko kadan bata da almubazzaranci"nasan wace mata ta,amma Duk da haka a taimakeni a yimiñ alfarma aje Siyayyar nan"
"Kafi qarfin haka a wajena mijina ,nayi makà"






Yana fità ta shiga kitchen ta Debi fulawa ta kwaba cin cin d cake a mixer,ta Debi zallar tsokar nama ta gyara ta dora kan wuta,abun ka da harkar na'ura nan d nan ta kammala koma da wuri har dambun naman ta nade cikin papers masu kyau,sosai ta gaji don ta jima batayi aiki irin haka ba,don haka ko da ta fito wanka zaune tayi German gado tana daure da towel a haka ya shigo ya taddata
"Kinyi aiki bayan fitàta"tana dariya qasa qasa tace "waye ya gaya maka?"ya qaraso inda take"kin manta zuciyarmu a hade take?,Kuma ina shigowa naji wani qamshi kuma na tabbatar ke kadaice mai irin wannan girkin"cikin son bàsar da zancen tace"yanzun dai ka hañzarta Kayi wanka ruwanka na bayi,ya gano wayanta.....




N.b:pls Ku yimin afuwa kwana biyu nayi busy ne wlh,na gode muku da haqurin da kuke da ni,Allah yabar qauna




*Mrs Muhammad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login