Showing 57001 words to 60000 words out of 130495 words

Chapter 20 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi musa huguma

sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin kasuwanci da masana'antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria da indian


Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa yakance"alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?"shi kama aliyyu ya dage aiko kaya yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da mahaifinsa ke da shi ba


Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar addu'ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi ga wannan matsayin da yake kai


Haduwar su da salima ta kasance ne sanadiyyar hutun qarshen zangon karatu da daliban instute din pashwar suka samu ciki harda,wadanda ba 'yan qasar ba kuma suke da sha'awar zuwa qasashensu hutu nata shirye shiryen zuwa gidan ciki kuwa harda saliman,wasunsu na ahiga kasuwannin dake cikin mumbai don yiwa yan uwa tsaraba


Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta 'yar nijeria sa'adiyya abikan karatunta biyu 'yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude kamfaninsa


Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da abinda ya kawoshi shagon


Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke shi don hankalinta na kan alin


Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta sosai sannan taga ashe wata 'yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta *adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda su muta nene da komai ka siya ko kayi mu'amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa da makarantarsu yake


Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata


Ku biyo
Mrs muhammad👑😘


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:47 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 2*


1⃣7⃣&1⃣8⃣


Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da murmushi😃 yayin da tasa take a tsuke😠 kamar hadari,"sannu ko?"tace da shi cikin fara'a"yauwa sannu" ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace "I hope lafiya dai ko?"ta sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse👛 dinta dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace"wannan ka yar dazun a mall din paras mahal collection"ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana cewa"thank you verry much"ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe


Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa"haaabaaa haabaa malam babu ko goron tsintuwa?😊" a qagauce ya dakata ya juyo yana cewa"nawa kike buqata?"t saki wani mayaudarin murmushi"ba kudi nake so ka bani ba,kawai passport nake so na cikin wallet naka sai kuma phone number dinka shikenan abunda nake buqata🤗"


Girgiza kai yayi hadi"it can't ki zabi wani abun dai daban banda wadannan"ta kanne ido daya😉 tace"ni su din dai nake so"kafewa yayi kai da fata bazai bata ba"i told you ba zaki samu ba"itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa


Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin"idan kamin haka baka min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar kudinka


Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi da imaninta 100%


Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra'a yinta sannu a hankali har ya minta da ita ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa


Asalin salima 'yan katsina ne mahaifanta,yan boko ne na bugawa a jarida irin mutanen nan ne da ake cewa"yan boko aqida"wato ga karatun bokon ga kuma bin duk wasu aqidu nasu, bokon suke da gaske babu sirkin addini ko kada cikin mu'amalar rayuwarsu ta yau da gobe bokon kawai akasa agaba shine madubi,hakan yasa tun a nijeria salima ke alalace don babu kwaba balle hantara da zarar kin kai shekaru goma sha takwas a gidansu to kina da yancin yin komai da kika ga dama,iyayenta na da arziqi daidai gwargwado don su suka dau nauyin karatunta ta fita indian


Mutum daya ne salima ta yarda da shi ta sallama masa jikinta a nijeria suke harkarsu duk da tana bawa wanda taga dama kanta yayi tabe tabensa don a cewarta ita babbar harka take,sai kuma zuwanta india ne wani abokin karatunta rahul,shima din tunda ta hadu da aliyyu tayi mishi fata fata sukayi handing over don kuwa tunda ta ga aliyyun tayi amanna ta samu kalar namijin da take so ya zama miji a gareta ya hada komai hundred percent


Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya sauqaqa abun ma babu fara'a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle kice zaki kawo masa wargi


Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun


Ba qaramin tashin hankali aliyun ya shiga ba yadda ya sameta ba budurwa ba duk da bai san ya budurwar take ba hakanan tasha stitches duk don ta matse,yafi aqalla sama da wata abun ma dukansa amma kasancewar sa mutum mai tsananin kishi da baijin zai iya auren mace ya saketa wani ya aureta yasa ya qyaleta,bugu da qari tsantsar qauna da take masa tamkar ta fidda ranta ta bashi,yayi imanin idan ya rabu da ita mawuyaci ne taci gaba da rayuwa parfectly


Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce *cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan


Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu


Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce masa"gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da wahalar 'ya'ya?,am just 25 fa"ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye


Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace"that's my salima,wannan tunanin naki fake ne it's not real,haihuwa ai ni'imace daga Allah wanda kudi ko mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi"


Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams


A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba'a dole shi kuma yace zai mata dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji take kamar tasa hannu ta fisgo abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa


Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa,


Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa


Cikin haka ne ranar wata juma'a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin doctor sa'adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa'adah bata nan ne da ko bakin salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun


Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da tofeta da addu'o'in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi


Suna akayi na tserewa sa'a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta tayi murmushi tace ta bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa


Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule


Mrs muhammad ce👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:48 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*Part 2*


1⃣9⃣&2⃣0⃣


Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara ba tare da masaniyar aliyyu ba


Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da rashin kunya salima tace"ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan...........


Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa cikin matsanancin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login