Showing 21001 words to 24000 words out of 44092 words

Chapter 8 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3810

wannan takaddar sune magungunan da za ku saya, amma wannan baza ku samu a nan ba" Ta faɗa tana miƙa mata wata ƙaramar takkadar.


Karɓa Najmeer ta yi "Mun gode sosai, but ana buƙatar maganin a yanzu ne?"


"No ba yanzu ba sai zuwa gobe idan ta tashi daga bacci, mun yi mata allurar bacci ne"


Godiya suka ƙara yi kafin suka fito.






Har kusan goman dare ba wanda ya samu bacci a cikinsu, Najmeer ma kasa cin komi ta yi, Meera ce ta samu awara me zafi a bakin titi ta sayo.
A hospital ɗin suka kwana, sai wajen tara na safe Najmeer ta fito domin sayo maganin da ake buƙata, Meera da ke ƙoƙarin shiga ɗakin da Mamu ke ciki ne ta ce "Ina zuwa haka?"


"Zan siyo maganin da suka ce ne, ko za ki mun rakiya?"


"Aa sai kin dawo, ba bu kyau barin marar lafiya shi ɗaya, ki sayo mun abu me daɗi please"


Tsaki Najmeer ta ja tana mai barin gurin.


A harabar Hospital ɗin ta tsaya neman adaidaita saboda har ciki suna shigowa, amma da mamaki yau ba kowa, hakan ya sa ta fara tafiya har kan titi, duk wanda ta tare sai ta ga da mutane a ciki, babban titin ta iso tana mai duban inda zata samu abin hawa, kamar daga sama ta ji ƙarar motoci sun mugun rikita mata kunne, gaba ɗaya ƙura ta baje gurin tamkar wasar motoci ake, motoci hamsin ne masu kafuran kyau da tsada, a rikice Najmeer ta dafe kunnenta tana mai neman hanyar da zata wuce, cikin ƙanƙanin lokaci motocin suka zagayeta wasu majiya ƙarfin maza kusan su goma ne suka fito daga wata arniyar mota black, ba tare da ɓata lokaci ba gardawan suka kama Najmeer da ƙarfin tsiya zuwa mota, ihu take tana neman ceto amma ba bu me saurarenta wasu ma guduwa suke dan tsira da rayuwarsu, da sauri motocin suka bar gurin da ita cikin matsanancin gudu.




Duk Najmeer ta firgice dan bata san su waye ba, gashi sun rufe fuskarta da baƙin ƙyalle, sai da suka yi tafiya me ɗan nisa kafin suka tsaya bakin gate ɗin, cikin ƙasaita motocin suka fara shigewa har suka shige gaba ɗaya, Najmeer dai tun tana ihu har ta daina dan numfashinta ya fara ɗaukewa.
















*Mu je zuwa yanzu aka fara, sorry yau ba yawa, pleae share and ku min uzuri na faɗa muku cewa ina hadda, shiyasa bana samun typing akai-akai*












*SHALELEN ALHAZAWA*




*Writing and story*


*By*

*Asmeetar Hydar*




(Asma'u Ayuba)




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*














P.5








Da ƙarfin tsiya wani ƙaton ya fincikota daga motar yana mai jifa da ita gefe.


Duk da cewar numfashin Najmeer na sama da ƙasa amma hakan be sa ta kasa jin zafin faɗuwar ba.




Wani gigitaccen marin da aka ɗauke ta da shi ne ya sa ta saki ƙara me rikitarwa, lokaci ɗaya aka janye ƙyallen da ke rufe a fuskarta, Sultan ne a tsaye cikin baƙaƙen kaya idanuwansa manne da glass baƙi wulikk, fuskarnan kuwa ba bu alamun rahama ko kaɗan.

Gashin kanta ya damƙo da ƙarfi yana kallon Mom da ke murmushi "Thank you so much Mom, yau kin cika mun burina" Ya ƙarasa maganar yana yiwa mutanen da ke gurin alamun su wuce.

Ƙayataccen parlorsu ya nufa Najmeer kam ta fice a hayyacinta dan bata ganin fuskar kowa sai dishi-dishi, a hawa na ƙarshe ya nufa da ita tare da jefata cikin wani ɗakin da babu haske sai duhun da ke bayyane, cikin tsoro da fargaba Najmeer ta ƙwalla ƙara tana faɗin "Waye kai........? idan ka isa ka fiddani ɗakinnan wallahi sai na koya maka hankali"

Jin abin da take faɗi ne ya sa Sultal juyawa cikin ɓacin rai da niyar shiga ɗakin, Mom da ke bayansa ne ta yi saurin riƙe hannunsa "No Son kar ka shiga a yanzu, ka jira har Dad ɗinka ya bar ƙasar ya ce mun za su tafi meeting a Mali" Cije lips Sultan ya yi yana mai barin gurin, Mom kuwa ta rufe ɗakin tare da saukowa ƙasa, anan suka ci karo da Dad yana ƙoƙarin sauka ƙasa "Wai ina Junaid ne ya? ina son zai mun rakiya Aiport?"

"Sai dai Sultan shine kawai a gida"

"Kina nufin be tafi aiki yau ba? wai me Sultan yake son zama ne, kira mun shi yanzunnan" Cewar Dad yana barin gurin.


A harabar gidan ya sami Dad na jiransa fuska babu walwala "Dad barka da war haka"

Ko kallonsa Dad be yi ba dan ya tsani shiririta "Sultan aikin ne ba ka tafi ba lafiya dai ko?" Haɗaɗɗen gashin kansa ya sosa yana lumshe ido "Yes Dad bana jin daɗi ne, amma zan shiga gobe da yardar Allah" "Masha Allah, Allah ya yarda"

Ɗago kai Dad ya yi kafin ya kuma ce "Zan yi tafiya sai nan da one week mun yi sallama da Mom ɗinka, Junaid ne ban samu ganinsa ba idan ya dawo ka sanar masa" "Okay Dad a dawo lafiya" Da ameen Dad ya amsa yana shigewa motar da aka buɗe masa, da sauri motocin suka fice daga gidan, Sultan na ganin haka ya nufi cikin gidan da sauri dan ya matsu ya fara gallaza mata.

A parlour ya sami Mom na shan lemu me sanyi, kana ganinta ka san tana jin daɗin zaman, ba tare da ya kalli inda take ba ya nufi sama, "Sultan ina zuwa haka da sauri?" Ya tsinkayo muryar Mom "Ohhhhh Mom please kin san cewa wannan yarinyar na gidannan ina son na hukuntata ne daidai da laifinta, ni ina ganin kasheta zan yi kowa ya huta"
"Kisan kai......? no Sultan ban amince maka ba, idan har da wani hukuncin za ka iya yi mata amma banda kisan kai" "But Mom why?"

Ya faɗa yana mai dawowa inda take.


"Look Son ka san bana son na rasa ka, idan har ka kasheta wallahi Abbanka zai iya shige mata gaba har a hukuntaka".


"Okay fine"


Sultan ya faɗa tare da nufar room ɗin da Najmeer ke ciki.


Daga bakin ƙofa yake jin yanda ake tattaka tiles ɗin ɗakin kamar tafiyar doki, sai kuma kukan Mage me ban tsoro da firgitarwa, a ɗan tsorace Sultan ya tsaya yana sauraren yanda kukan Magen ke ƙara sauti, can kuma ya ji ihun Najmeer da surutai kamar zararra, cikin fushi ya daki ƙofar ai kuwa ta ƙara sautin ihun nata, kukan Magen da yake ji kuwa ya ɗauke chakkkk kamar ba abin da ya faru.


"Keeee Uwar wa ki ke wa ihu kamar kin samu gidan Ubanki?" Sultan ya faɗa yana danna hasken ɗakin, da sauri Najmeer ta rufe rikittatun idanuwanta da tafukan hannunta, ƙarasowa Sultan ya yi yana mai chakumo wuyanta da ƙarfi "Magana nake miki ƙaramar Karuwa" Sai yanzu Najmeer ke buƙatar ganin ko fuskar waye, ta tabbata cewa Sultan ne kawai zai iya yi mata hakan, amma sai ta ƙara runtse idanuwanta ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba.


Cikin muryar da ta tashi rikita shi ta ce "Har yanzu ba ka nuna mun kai namiji ba ne, tun da ka kasa bari mu haɗa jiki da kai, idan kana son tabbatar min kai cikakken ɗan iska ne ba sai ka saceni ba"


A fusace Sultan ya ɗaga hannu gami da sharara mata mari ji ka ke tasssss, "Keeee idan har kwanan baya kin faɗa mun son ranki, a yanzu ba zan lamunce miki ba, ke ba kowa ba ce face Karuwa"


"Kai kuma mazinaci ko?"


Kamassss ya buge mata baki yana mai sakin wuyan nata "Waye mazinacin? ina ganin wannan bakin naki ba zai daina surutu ba sai na koya masa hankali, wallahi na tsaneki Karuwar banza da wofi"


Caraffffff Najmeer ta karɓe zancen da faɗin "Ka mance da suna ɗaya" Zuba mata ido Sultan ya yi jiran abin da zata ce, har ila yanzu idanuwanta a rufe su ke, "Bayan Karuwa ni ɓarauniya ce, and soon zan nuna maka asalin ko wacece ni, sai na lalata maka rayuwa sai na mayar da kai abin tausayin da kai kanka sai ka zubarwa kanka da hawaye" A mugun fusace Sultan ya cire belt ɗinsa ya shiga dukanta ta ko'ina kamar Allah ya aiko shi, sai da ya yi mata shegen dukan da ta kasa tashi, tun Najmeer na ihu har ta kasa magana.


Sultan na layi kamar mashayi ya iso bakin ƙofa gami da kashe hasken ɗakin ya fice waje.


Kasancewar ɗakin ɓoyayye ne ya sa duk yanda za ka yi ihu ba bu me jinka, wannan dalilin ne ya sa ba wanda ya ji ƙarar da Najmeer ke yi.






Wani irin sarawa kansa ke masa a haka ya sauko ƙasa, inda ya sami Mom yanda ya barta amma wannan karon da wata matashiyar yarinya me kyau zaune cikin shigar ƙananan kaya, ita ba fara ba kuma ba baƙa ba, a kanta gashin doki ne ya sha gyara sai wayar da ke hannunta iphone 15promax tana latsawa.


Jin saukowar mutum ne ya sa ta ɗago da sauri, ai kuwa ta tashi da gudu ta nufi Sultan gami da hugging ɗinsa "Hi love am so happy to see you, jiya nake dawowa daga ƙasar nan ake ce mun ka shigo, welcome back sweetheart". Ta ƙarasa maganar tana ƙara shigewa jikinsa, cike da ɓacin rai Sultan ya tureta daga jikin nasa har sai da ta kusa faɗuwa, dama ba wani jikin take da ba, idan aka yi iska me ƙarfi zai iya ɗagewa da ita sama.




"Are you mad? Surayya sai yaushe za ki yi hankali ne?"




"What? haba love yanzu me nayi maka? Mom kina ganinsa ko, bansan meyesa Sultan ya tsane ni ba"




Cewar Matashiyar da ya kira da Surayya tana mai zama kusa da Mom cikin shagwaɓa.




"Ke kuma ban da abinki ai kin san Sultan baya son hauka, amma kin kasa hankali ai yanzu kin shiga taitaiyinki, ina ganin baya cikin good mood ki barshi kawai"




Turo baki Surayya ta yi kamar zata yi kuka "Sultan please ka mun magana ko so ɗaya ne" Wani mugun kallo Sultan ya jefa mata yana barin parlourn.






Sumayya da ke can sama tana kallon duk abin da ke faruwa ne ta taɓe baki tana faɗi a hankali "Shegiyar banza ai kin kawo ƙarshen iskanci, ai kuwa yanzu mun shiga uku tun da kin dawo Nigeria" Ta ƙarasa maganar tana jan tsaki yanda ba bu me jinta.




Surayya kam tana ganin Sultan ya shareta ne ta miƙe cike da fushi ta bar parlourn ko sallama bata yiwa Mom ba, Mom kam ko kallon inda take bata yi ba dan ta san dama gurin Sultan ta zo.




Kamar wadda ake turawa haka ta ƙarasa gurin bugaggar motarta tana dakawa gate Man tsawa cikin ɓacin rai.


Sanin halin Surayya ne ya sa gate Man danna remote da sauri, da mahaukacin gudu ta bar gidan kamar zata tashi sama.




Junaid da ke office kuwa gaba ɗaya yau gabansa faɗuwa yake ya rasa dalili, hakan ya sa ƙarfe biyar ya bar Hospital tare da nufo hanyar gida, Allah ne kawai ya kawo shi lafiya amma duk jikinsa ya gama mutuwa, koda ya shiga ba kowa a parlourn dan haka ya nufi nasa ɗakin, yana shiga ga faɗa toilet dan sakarwa kansa ruwa.








Ya kai kusan mintuna talatin kafin ya fito ɗaure da pink tawul me kyau da laushi, a hankali ya zauna kan Mirrow yana karanto alqur'an suratul Mulk, zazzaƙar muryarsa ta gama karaɗe ɗakin, har ya shirya cikin jallabiya ruwan toka me masifar kyau an yi mata ɗinkin wuta, jallabiyar irinta larabawannan ba ƙaramin fito da shi ta yi ba, kasancewar Junaid akwai sihirtaccen kyau.


Sai da ya gama gyara haɗɗen gashin kansa sannan ya fesa turarensa me ƙamshin daɗi.


Wayarsa da ke gefe ya ɗauka tare da nufar dianing dan yunwa yake ji.




Ƴar aikinsu me kula da ɓangaren abinci ce ta jere masa lafiyayyen girki cikin natsuwa dan ta san halin Junaid baya son garaje.




Hankali kwance ya yi bismillah ya fara cin abincin, be wani jima ba ya kamalla, bayan ta kwashe kayan ne ya ɗago kyawawan idanunsa masu kyau yana faɗin "Ina Mom ne?"


"Oga Junaid ina ganin tana part ɗin Alhaji ƙarami"


Ba tare da ya ce uffan ba ya ɗaga mata hannu alamun ta tafi.




Part ɗin Sultan ɗin ya nufa amma ba kowa hakan ya sa ya tafi ɓangaren Mom nan ma be sami kowa ba, da mamaki ya danna number Sultan ɗin but har ta tsinke be ɗaga ba, and yana jiyo ƙarar wayar daga bayansa.


Cikin tafiyarsa me jan hankali ya fara bin hanyar da yake jin ƙarar wayar.




Daidai koridon da zai sada shi da hawa na huɗu ne suka ci karo da Sultan da Mom na ƙoƙarin saukowa, Junaid ne ya ce "Lafiya kuwa? na ga kamar bakwa cikin natsuwa and Sultan kana ganin kirana shine baza ka ɗaga ba"




Sultan da ke cikin haɗaɗɗun manyan kaya masu kyau yadi wanda ya sha ɗinki ne ya sosa kai a hankali cikin alamun rashin gaskiya "Amm.....dama ina son na sameka da kaina ne"


"Dama ka san na dawo ne?" Junaid ya jefa masa tambaya.




Mom ce ta yi saurin katse zancen da faɗin "Kun ga mu koma ƙasa sai ku yi duk wannan surutun" Ta ƙarasa maganar tana jan Sultan tare da barin gurin.


Da kallo Junaid ya bisu yana mamakin abin da su ka je yi a hawa na huɗu, tabbas akwai abin da suke ɓoye mun amma da sannu zan gane ko meye.


Cewar Junaid a zuci yana mai bin bayansu.










....................


A gafensu Meera kuwa hankalinta ya mugun tashi ganin har yamma babu alamun Najmeer, kuma babu wani kuɗin da ke hannunta da zata karɓowa Mamu magani, wayar Najmeer da ke hannunta ne ta kalla da kyau gashi bata san pin ɗin ba balle ta yi tranfer a POS ta sayo magani.




Mamu da ke kallon Meera ne ta ce "Ƴarnan lafiya dai ko? har yanzu Najmeer ɗin bata dawo ba ne?"


Jikin Meera a sanyaye ta ce "Wallahi har yanzu, nikam ina ganin ba lafiya ba, dan Najmeer baza ta tafi yawo bayan ta san bakya da lafiya ba"




"Nima na san da hakan, Allah ya sa lafiya gaskiya na fara tsorata, amma ki tambayi likitoci ko za mu koma gida na gaji da kwanciyar nan"




Meera ce ta ce "Eh sun ce zamu iya tafiya tun ɗazu, dama rashin dawowar Najmeer ɗin ne ya tsaya mun a rai"


Sosai Mamu ta ji tausayin Meera ganin ko abinci ta kasa ci, rarrashinta ta shiga yi kafin suka haɗa tarkacensu zuwa gida.




Kuɗin adaidata ma rasawa suka yi sai da wani bawan Allah ya taimaka musu.






Har ƙofar gida aka sauke su, inda suka sami Jabir tsaye yana faman washe baki, "Affff har zan tafi sai gashi kun dawo" Ya faɗa yana ƙarasowa gurin su Mamu, Meera kam rashin sanin ko waye ya sa ta ja hannun Mamu suka shige gida, bayansu Jabir ya bi yana faɗin "Ina Najmeer ɗin ne? sai magana nake kun yi banza da ni" Daga Mamu har Meera ba wanda ya amsa masa, ganin hakan ne ya sa Jabir fusata, "Wai meye haka ne? ina matata zan shuka muku rashin mutunci fa sai magana nake ana shareni ita kuma wannan ƙanzon fa?" Ya ƙarasa maganar yana nuna Meera, cikin gajiya da hayaniya Meera ta ce "Bawan Allah me ka ke buƙata ne? dan Allah ka shafa mana lafiya idan Najmeer ce bata tare da mu, ka tafi nemanta wannan surutun banzan naka ya yi yawa" Jin abin da Meera ta ce ne ya sa Jabir laulayo ashar ya maka mata "Kutumar ubancan ke har kin isa ki gasa mun magana?"




Mamu ce ta yi saurin faɗin "Jabir kana da hankali kuwa? ko rashin auren Najmeer ɗin ne ya haukata ka? ka fice mun daga gida tun kafin na tara maka jama'a, bayan kun raba ni da Jikanyata shine za ka biyo bayan fage kana surutan banza, to duk inda ku ka kai mun ita sai kun nemota yawwa"


"Rufe mun baki munafukar tsohuwa ai duk munafurcin da ku ke haɗawa ya dawo kunnena, na ji labarin Najmeer ta dawo gidannan kuma an faɗa mun cewar an ga lokacin da ku ka fita tare, dan haka ki aje duk wani makirci ki fito mun da matata"




"Kai Jabir ne sunanka ko waye? zan ci Ubanka anan gun na fika akuyanci, Mamu ka ke faɗawa wannan maganar?" Cewar Meera tana ɗaukar wani icce da ke gurin cikin masifa, ganin da gaske zata iya dukansa ne ya sa ya matsa da baya yana faɗin "Ku jirani zan dawo wallahi sai na ɗauki mataki a kanku, musamman ƴar tashar yarinyar nan marar kunya sai nayi maganinki" Ficewa daga gidan ya yi yana surutai kamar zararre.


Meera kam ɗaki ta nufa da Mamu ba tare da ta koma bi ta kansa ba, har Meera ta yunƙura zata fita Mamu ta kama hannunta tana mai share ƙwallan da ya zubo mata "Ina zuwa ƴarnan Allah ya sa kema ba tafiya za ki yi ki barni ba" Mamu ta faɗa tana mai fashewa da kukan da take riƙewa.


Da sauri Meera ta zauna tana faɗin "Aa ba tafiya zan yi ba Mamu, idan na tafi waye zai kula mana da ke? kuma ni bana da kowa a yanzu daga ke sai Najmeer iyayena sun rasu, zan iya cewa ku ne dangina, dan Allah ki daina kuka kar ki saka ni nima" Cikin sauke ajiyar zuciya Mamu ta ce "Allah ya jiƙan waɗan da suka riga mu gidan gaskiya, kuma Allah ya bayyana mana Najmeer a duk inda take cikin ƙoshin lafiya" Da ameen Meera ta amsa kafin suka cigaba da fira sama-sama kasancewar kowa da abin da yake tunani a ransa.










Sai da aka kira sallar magrib kafin suka yi sallah Meera ta ɗora musu girgi, ba laifi jikin Mamu ya yi dama dan tana iya miƙewa amma babu ƙarfin jiki, wayar Najmeer kuwa sai kira ake amma ba bu me ɗagawa daga ƙarshe Meera ta kashe wayar.




Wajen tara na dare ne suna zaune da Mamu a tsakar gidan sun yi jugum-jugum jiran ganin Najmeer amma shuru ka ke ji.


Mamu ce ta ce "Nikam na fara tsorata sosai kan lamarinnan? anya kuwa ba Jamilu ne ya sace Yarinyar nan ba" Jin abin da Mamu ta ce ne ya sa Meera ɗagowa a firgice ta ce "Na san wanda ya sace ta"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login