Showing 6001 words to 9000 words out of 44092 words

Chapter 3 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3814

ganin tsananin kyawun halittarsa me matuƙar jan hankali.




Cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya sauka a babban airpor na garin Jos, wata Matashiya da ke bayansa ne ta ƙura masa ido har suka sauko daga kan matattakalar, daga nesa Drivernsa me suna Umar ya hangesa cikin hanzari ya ƙaraso yana mai karɓar Trolyn da ke hannunsa, "Ƙaramin Alhaji barka da zuwa?" Drivern ya faɗa yana murmushi ko kallonsa Sultan be yi ba ya bar gurin, bayansa Umar ya bi cikin rashin damuwa dan sun saba da halinsa a gidan, balle yanzu da ya tafi ƙasar turai ai dole zai ƙara hartsinewa.


Motoci uku ne masu masifar tsada suka zo tarbarsa, daga cikin motocin akwai ƙirar Loxes me jan hankali, glass ɗinta black ne ba ka ganin wanda ke ciki, amma da alama akwai mutun a cikinsa, cike da miskilanci Sultan ya kalli Drivern da ya saka troly a boot "Waye a cikin motar nan?"


"Ƙaramin Alhaji ai Oga Junaid ne tare da shi muka zo" Da sauri Sultan ya nufi motar cikin mamaki dan be yi tsammanin Brother ɗin nasa zai zo tarbarsa ba, Drivern da ke jan motar Junaid ne ya yi saurin buɗewa Sultan ƙofar motar, ai kuwa ya shige cike da ƙasaita.


A zaune ya same shi waya kare a kunnensa, ƙamshin turarensa ya gama hautsine gaba ɗaya motar, a cinyarsa kuwa Laptop ne da alama aiki yake yi, Matashi ne fari sol me matuƙar kyau wanda kana ganinsa ka san hutu da kuɗi sun gama baje hajarsu a jikinsa saurayi me taƙama da aji ɗan shekaru talatin daidai a duniya, kamanninsu ɗaya da Sultan har ma zaka kasa gane wanda ya fi wani kyau a cikinsu, sai dai shi Junaid lips ɗinsa pink ne saɓanin Sultan da nasa red ne, sanye yake cikin manyan kaya yadi me masifar tsada da ɗaukar ido wanda kana gani ka san kuɗi sun yi kuka, wayarsa ƙirar 15promax ce ya sauke a hankali yana mai kallon ɗan uwan nasa, cikin muryarsa me ɗan karen daɗi ya ce "Ba ka iya gaisuwa ba ne Sultan" Ɗan cije lips Sultan ya yi dan baya son abin da Brother ɗin nasa yake masa, amma babu yanda ya iya dole ya sosa gashin kansa fuska a haɗe ya ce "Barka da war haka"


Sai da Junaid ya ɗauki mintuna uku yana latsa Laptop ɗinsa wanda har jikin Sultan ya fara rawa tsabagen takaici babu abin da ya tsana irin wulaƙanci, kamar daga sama ya ji ya ce "Lafiya ya hanya"


"Hanya Alhamdulillah" Sultan ya amsa a taƙaice.


Ba tare da Junaid ya kuma cewa komi ba ya ce "Driver we can go because i have alot to do"


Cikin girmamawa Driver ya ja motar, nan take sauran motocin suka mara musu baya, tun da suka fara tafiya babu wanda ya sake magana daga Junaid har Sultan kowa na ji da kansa.




Wata arniyar Unguwa suka nufa wadda suke kira da G R A, babbar area ce a cikin garin Jos wanda duk wani me kuɗi da ke ji da kansa zaka same shi a unguwar, a bakin wani tangamemen gate motocin suka tsaya nan take gate ɗin gudu uku suka ɗage sama, gida ne wanda tun daga wajensa zaka tabbatar da cewa ba ƙaramin hamshin me kuɗi ne ya gina shi ba, gaba ɗaya ginar gidan Golding Colour ne, gate ɗin kuwa na Gold ne wanda kafin ya ɗage sama sai ya yi searching idan har ba ka ɗauke da wani mugun abu, a pearking place suka tsaya wanda duk iya gulmarka baza ka ga ƙarshen motocin da ke baje a gurin ba, and you can't even count it.




Every where security's ne kowannensu riƙe da bindiga suna tsaron lungu da saƙo na gidan.




Gida ne me hawa-hawa har huɗu lafiyayyu na faɗa a ji, kowanne hawa da kalar pentinsa kuma kowanne hawa da kalar tsarinsa, a iya binciken da aka yi gaba ɗaya garin Jos babu gidan da ya kai gidan Chif Muhammad kyau, gaba ɗaya gidan Flowers ne masu ɗaukar hankali Golding colour waɗan da idanu basu taɓa gani ba, grass carpet ne a baje me matuƙar ɗaukar hankali, guraren shaƙatawa kuwa ya fi biyar a gidan, kama daga swimming pool har gadin.


Da sauri wani matashi ya ƙaraso tare da buɗe musu motar.


Cikin gadara Sultan ya sauko da ɗayar ƙafarsa yana ƙarewa gidan kallo zuciyarsa na kaɗawa, sai da ya ɗauki tsawon mintuna uku a haka kafin ya fito a lokacin Junaid ya jima da isa haɗaɗɗen parlourn gidan wanda ko gidan shugaban ƙasa be kai shi haɗuwa ba, ta ko'ina kayan more rayuwa ne kamar basu san zafin dukiya ba, manya-manyan TV ne guda uku masu rai da lafiya manne a bangon parlourn, ɗaya daga cikin haɗaɗun royal ɗin da ke gurin Junaid ya zauna bakinsa ɗauke da bisimillah.


Daga sama ya ji ana faɗin "Where's he?"


A hankali Junaid ya sauke rikitattun idanunsa kan Dad ɗin nasu "He's coming Dad just wait a minute" Daga haka Junaid be sake cewa komi ba.


Dattijon mutumin kuwa da ke cikin kayan alfarma ne ya fara saukowa daga matattakalar fuskarsa a haɗe, kana ganinsa ka san shine Mahaifinsu dan kamanninsu ya nuna hakan, sai dai shi ya fi su tsufa ne kawai.




Kayan jikinsa sun isa tabbatar maka cewar babu wani abun da suke nema a duniya face gamawa da ita lafiya.


Saman kujera me zaman mutum ɗaya ya zauna yana mai duba agogon gold ɗin da ke hannunsa daidai lokacin da Sultan ya yi sallama cike da taƙama, dirrect gurin Dad ɗin nasa ya nufa yana mai ware hannayensa "Hi Dad am back......"




"You are very stupid Sultan, is that how za ka gaida mahaifinka? ashe ka watsar da tarbiyyar da na yi shekara da shekaru ina ba ku".


Idanun Sultan ne suka ƙanƙance tsabagen fusata har jikinsa ya fara rawa jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu-ruɗu, a fusace ya nufi matattakalar ba tare da ya ƙara magana ba, cikin tsawa Dad ya ce "Sultan don't add another step if not wallahi sai dai ka canja wani Uban amma ba ni ba......" Cakkkk ya tsaya yana mai damƙe hannunsa da ƙarfin tsiya, Junaid da ke jin duk abin da ke faruwa ne ya ɗago kyawawan idanunsa yana mai saukewa kan Sultan, lokaci ɗaya kuma ya miƙe tare da nufar Frigde ɗin da ke parlourn, robar ruwa ya ɓalle sannan ya zuba a Cup.


Cike da takunsa me jan hankali ya ƙaraso gaban Sultan da har yanzu tsaye yake kamar wanda aka dasa, "Take this ka sha ko zuciyarka zata yi sanyi, but remember one thing please he's our Dad not our mate". Hannunsa ya kama ya ɗora masa Cup ɗin sannan ya haura sama yana mai sakin murmushi.




A fusace Sultan ya ɗaga Cup ɗin ya kai bakinsa, kurɓa uku kawai ya shanye ruwan yana mai jingina bayansa kan ƙarfen da ke steps ɗin, duk abin da yake Dad na kallonsa yana mamakin zuciya irin ta ɗan nasa, sai da ya ƙara mintuna uku ahakan kafin ya fara saukowa kan steps ɗin a hankali, kujerar da ke fuskantar Mahaifin nasa ya zauna cikin sanyin murya kamar wanda ke ciyon magana ya ce "Ina wuni Dad ya gida" Sai da Dad ya ƙare masa kallo kafin ya ce "Lafiya lau ya karatun? ina fatar ka gama tattaro komi naka da yake can, saboda kai da ƙasar London har ƙarshen rayuwarka, waɗannan shekarun da ka yi ka gama sauya rayuwarka gaba ɗaya dama ko a can baya sai a hankali".


"Yes Dad amma na bar abu me muhimmanci da gaba ɗaya Family sai sun koma saboda shi"


"What are you saying Sultan, wanne abu ne haka da har zai sa Family su tafi wata ƙasar?"


"Dad wadda zan aura" Sultan ya faɗa cike da gajiya da magana dan ba ƙaramin wahala magana take yi masa ba.


Rai ɓace Dad ya ce "Ashe ka isa da kanka tun da har zaka tafi wata ƙasar ka kwaso mana wata macen acan, to bari ka ji na faɗa maka idan har na isa da kai kuma ni ne Ubanka babu kai babu wannam yarinyar" Ba tare da Dad ya jira abin da Sultan zai ce ba ya miƙe yana mai barin parlourn a lokacin da wata Dattijuwa ke saukowa daga saman bene fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Sultan, haɗaɗɗiyar atamfa ne jikinta me tsadar gaske duk jikin nata Gold ne, ba ƙaramin kyau ta yi ba, domin har hutu da jin daɗi na ƙoƙarin ɓoye tsufanta, Sultan na ganinta ya miƙe da sauri ya nufeta tare da hugging ɗinta kamar ƙaramin yaro ya ce "Hi Mom am back"


Ƙara faɗaɗa murmushinta ta yi "Hi Son welcome ya London ɗin?" Ta faɗa tana mai kama hannunsa suka koma kan kujera me zaman mutum uku.


Sultan na yamutsa fuska ya ce "So amazing but Mom kina jin Dad wai ba zai barni na yi aure a ƙasar waje ba"


Gefen fuskarsa ta shafa cikin so da ƙauna ta ce "Don't mind him babu wanda ya isa ya hana ka auren wadda ka ke so.


"Thank you so much Mom that's why i love you"


"Love you too Sweetheart ka je ka watsa ruwa kafin ka gama zan sa a haɗa mana abinci yau a babban parlour za'a ci abinci tun da ka dawo"


Fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙe yana faɗin "Okay Mom"


Cikin so da ƙaunar ɗan nata take kallonsa har ya haura sama cike da gadara.






A hawa na biyu ya isa wanda anan ne part ɗinsa, wani irin mashahurin room ne wanda komi nasa blue colour ne hatta penting ɗakin, ƙayataccen bed ne irin na manyan ƴaƴan masu kuɗi, komi na ɗakin set biyu ne hatta Mirrow, girman ɗakin kuwa ya wuce misali dan zaka iya tafiyar mintuna uku kafin ka kai ƙarshen ɗakin, dukiya ce a zube tamkar basu san zafinta ba, a bangon ɗakin kuwa wani tangamemen hotonsa ne sanye cikin manyan kaya ya masifar kyau amma fuskarnan a haɗe, a lokaci ɗaya kuma tunanin burdurwarsa ta London ta faɗo masa, wani irin juyi mararsa ta yi kamar zata bar jikinsa nan take jikinsa ya fara rawa, da ƙyar ya isa gun troly ɗinsa ya buɗe hannunsa dafe da mararsa idanuwansa sun yi jajir, Laptop ɗinsa ya ɗauka yana mai zama kan sofa, da sauri ya shiga wani chat yana mai typying kamar haka (Hi Guy am back and i really need a hort Girl urgent) ko minti ɗaya massage ɗin be yi ba aka yi reply da (Okay akwai wata Babe me zafi da take zuwa Clup a duk ranar yau na san you will like her saboda gaba ɗaya Jos babu me kyawunta balle kyawun surarta her name is Shalele suna kiranta Shalelen Alhazawa) jin sunan da aka kira yarinyar da shi ne ya sa Sultan jin muguwar faɗuwar gaba sai da ya ɗauki mintuna uku ba tare da ya yi reply ba daga ƙarshe ya tura masa (Okay am waiting for you Guy ka sameni a gida around 10:00pm wallahi a matse nake) Yana tura hakan ya kashe Laptop ɗin yana mai cije lips ɗinsa da ƙarfi dan wani zugin da mararsa ke masa, ya san cewa ba ƙaramin haƙuri ya yi ba tun da har ya kai wannan lokacin without havin sex, a daddafe ya miƙe tare da shigewa toilet yana mai rufo ƙofar.














*SHALELEN ALHAZAWA*


*Writing and story*


*By*

*Asmeetar Hydar*




(Asma'u Ayuba)




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*








P. 2










He took almost 40 to 50 minutes kafin ya fito ɗaure da tawul me laushi da ƙamshi, ɗayan kuma yana tsane haɗaɗɗen gashin kansa.
Ba wani lokaci ya ɗauka gurin shiri ba ya fito cikin jallabiya fara sol me kyau da tsada, rikitattun turarukkansa ya fesa waɗan da ya saya a ƙasar London masu sihirtaccen ƙamshi yana mai saukowa ƙasa cike da taƙama.


Ƴan aikin part ɗinsa mutane uku ne mata, a tsaye ya samu ɗaya daga cikinsu me suna Sumayya, cike da girmamawa ta gaida shi tana mai zuba masa ido, wani mugun kallon wulaƙanci ya yi mata ganin yanda take kallonsa, "Zo nan ke dan Ubanki" Ya faɗa a tsawace, jikinta na rawa ta ƙaraso tana mai sunkuyar da kai ƙasa, cike da jaraba ya janyota ta faɗo jikinsa, a ruɗe ya fara romance ɗinta kamar zai zaunce, ƴar aikin me suna Sumayya kuwa dama abin da take so kenan dan ta jima tana kwaɗayin jikin Sultan saboda ba ƙaramin so take masa ba, sosai yake yamutsa ta har suka zube ƙasa, sai ƙara shige masa take tana ƙoƙarin haɗe bakinsu, wata irin razananniyar tsawar da aka daka musu ne ya sa dukkaninsu dawowa cikin hayyacinsu a ruɗe.


A mugun rikice Sumayya ke kallon Junaid da hankalinsa ya gama tashi ganin abin da be taɓa zato daga gurin ƙanin nasa ba, tsawar da ya ƙara daka mata ne ya sa ta miƙe jiki na rawa "Idan na sake buɗe ido naga wannan ƙazamin jikin naki anan a bakin aikinki ballagaza mahaukaciya". Junaid ya faɗa yana mai dafe kansa da ke sarawa, babu abin da ya tsana irin yaga mutum na aikata zina ko kuma saɓon Allah.


Da gudu ta bar part ɗin har tana zamewa, Sultan kuwa haɗe fuska ya yi ganin abin da Junaid ya masa, a ƙufule ya raɓa ta gefensa yana ƙoƙarin wucewa, ba zato ya ji Junaid na faɗin "Sultan why......?" Cakkkk Sultan ya tsaya ba tare da ya ce uffan ba kuma ba tare da ya juya daga inda yake ba, "Sultan ƙanwar wani ce fa, kuma matar wani ce wadda idan har kana da ƙanwa aka yi mata hakan baza ka ji daɗi ba, kana son Allah ya yi fushi da kai ne?"


Junaid ya ƙarasa maganar hawaye na zuba kan kuncensa, a hankali Sultan ya maida kallonsa kan yayan nasa, ba ƙaramin mamaki ya yi ba ganin hawaye na zuba kan fuskar Junaid abin da tun da Allah ya haliccesa be taɓa gani ba, har Sultan ya kai hannu da niyar dafa kafaɗarsa Junaid ya ɗaga masa hannu rai ɓace "Don't......, ka je ka wanke janasar da ke jikinka" Ya ƙarasa maganar yana barin gurin cike da takaicin halin da ya sami ƙanin nasa, Sultan kuwa kafaɗa ya ɗage alamun ko a jikinsa.




A babban parlourn ya sami mutanen gidan amma banda Junaid, "Hi guys whtp?" Ya faɗa yana dunƙule hannu ya miƙawa Mom ɗinsa itama ta dunƙule hannu tare da miƙa masa suka haɗe suna murmushi, ko kallon inda suke Dad be yi ba ya cigaba da cin abincinsa yana mai nemawa ɗan nasa shiriya a zuciya.


Da sauri me seving abinci ta ƙaraso ta zuba masa haɗaɗɗar shinkafa julof wadda ta sha naman rago, sai dambun naman da ya ji kayan haɗi, ɗan ƙaramin Cup ɗin zinarin da ke gurin ta zuba masa juice na apple wanda ke tashin ƙamshi, ba zancen bismillah Sultan ya fara cin abincin yana lumshe ido, "Ina Junaid ne?" Mom ta tambaya tana kallon Sultan, sai da ya ɗauki mintuna biyu kafin ya ɗago yana yamutsa fuska "Maybe ya fita"


Daga haka be sake cewa komi ba, ba wani abincin ya ci ba dan Sultan be damu da abinci ba, miƙewa ya yi yana mai faɗin "Dad Mom ni zan fita"


"Babu inda zaka tafi" Dad ya faɗa kansa a ƙasa.


"What......why? Dad wayana ne ya samu matsala nake son a karɓo mun wata"




"Ka sami Junaid a ɗaki ba zai rasa waya ba, ɓace mun da gani please"


Sultan na ɓata fuska ya nufi ɗakin Junaid.


Mom da ke kallon Dad ne ta ɗan rai tana faɗin "Wai meyesa ka ke takurawa wannan yaron ne? tun kafin ya dawo ka ke nuna fushinka a kansa"


"Kina ganin hanyar da nake ɗora shi ba daidai ba ne?"


"Ba haka nake nufi ba Chif, amma a ganina tsananin ya yi yawa"




"Ai sai ki nuna mun cewa ke ce Uwarsa ni kuma ba Ubansa ba ne" Dad ya ƙarasa maganar yana miƙewa daga zaunen da yake.


Har Mom ta buɗe baki da niyar magana ya ɗaga mata hannu "Bana son jin komi" Shuru ka ke ji ta kama bakinta dan ta san halin Dad baya son yana magana ana amsa masa.




Sultan kuwa a kwance ya sami Junaid yana latsa wayarsa, a gefensa Coffee ne me zafi da ƙamshi wanda yake sha a duk rana ta Allah.


Ciki-ciki Sultan ya yi sallama sanin halin Junaid baya son a shigo masa ɗaki ba sallama, ɗaki ne wanda ya amsa sunansa, ɗakin ya masifar yin kyau, komi na ɗakin Golding ne hatta penting da aka masa, kamar yanda komi set biyu ne a room ɗin Sultan haka ma room ɗin Junaid sai dai room ɗin Junaid ɗin ya fi kyau nesa ba kusa ba, saboda yana yawan canja kayan ɗakin nasa lokaci zuwa lokaci, saɓanin Sultan da rabonsa da gida shekara ɗaya kenan.




Cike da ƙasaita Sultan ya ce "Bro wayana ne ya fashe ina hanyar dawowa can i get another phone with you"


"Ya hakan ta faru?"


Cewar Junaid.




Ɗan sosa kai Sultan ya yi cikin gajiya da zancen ya ce "Na zauna a kai ne a rashin sani"


"Ka duba a loka akwai 15promax da nake son na yi giveaway gobe insha Allah sai ka ɗauki ɗaya daga ciki"


Daga haka be sake cewa komi ba, shima Sultan ɗin gurin lokar ya tafi ba tare da ya amsa yayan nasa ba, wayar ya ɗauka cikin kwalinta sabuwa galllll yana mai ficewa daga ɗakin.






Room ɗinsa ya koma dan haƙurinsa ya fara ƙarewa, duk zaman da ya yi da su Mom daurewa kawai yake amma mararsa dammm take da feelings.




Layinsa na Nigeria ya ɗauko tare da sakawa a sabuwar wayarsa yana mai danna wata number me suna Majeed, bugu biyu aka ɗaga, cike da miskilanci Sultan ya ce "Guy how far yarinyar zata samu zuwa kuwa?"


Daga can ɓangaren ne aka ce "Ai babu Friday ɗin da bata zuwa Clup kawai ka zauna a shiri"


"Wait Guy ina fatar ba ƙazama ba ce ba"


"Haba My Sultan wannan yarinyar ko tsafta ta fika......" Wani mugun ashar Sultan ya narkawa Majeed yana faɗin "Har akwai wata tsinanniyar karuwar da ta fini tsafta a faɗin garinnan"


"Sultan calm down be kai haka ba, yanzu magrib ya kusa mu haɗu ƙarfe goma kamar yanda ka ce, amma Dad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login