Showing 18001 words to 21000 words out of 44092 words

Chapter 7 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3812

posting, zai iya yuwa ma na dakata da rubuta book ɗin, thank you all*








*SHALELEN ALHAZAWA*


*Writing and story*




*By*

*Asmeetar Hydar*




(Asma'u Ayuba)




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*








P. 4




Tun da suka fara ratsa kowacce unguwar mutane ke kallonsu har suka shigo arean su Najmeer, kasancewar motoci basa iya shiga ne ya sa suka dakata, cikin tsawa Sultan ya ce "What the heck, me kuma ya faru?"


"Alhaji ƙarami hanyar ce motoci basa shiga"


Da mamaki Sultan ya ce "What do you mean? wai anan ne arean da zamu tsaya?"


Drivern ne ya kuma cewa "Eh anan ne"


Cike da ƙasaita ya fito motar ba tare da jiran a buɗe masa ba, daidai lokacin da ya hangi adaidaita sahu na tsala gudu har ya iso ta gefensu, kamar an ce ya juya ai kuwa ya hangi su Najmeer suna faɗin me adaidaita ya ƙara gudu, suna haɗa ido Najmeer ta sakar masa murmushin da ke kama da na mugunta, tabbas ba zan mance da wannan fuskar ba ko da kuwa zan mutu na dawo ne, ya faɗa a ransa yana ƙare musu kallo, ganin cewa suna neman tserawa ne ya sa Sultan bada umarnin a bi bayan me adaidaitan, cikin sauri ya shige motar yana dakawa Drivensa tsawa, da kafurin gudu suka rufawa su Najmeer baya a lokacin har sun yi nisa sosai.




Gudu suke kan titi wanda ya tashi hankalin mutane, kasanacewar akwai tazara me yawa tsakanin motocin Sultan da adaidaitan da su Najmeer ke ciki ne ya sa basu riske su ba.








Maleek da duk fuskarsa ke manne da bandeji ne ya biyo kan mashin ya fito daga asibiti, ai idanuwansa na kaiwa kan su Meera da Najmeer da ke cikin adaidaita suna ba me adaidaita umarnin ya ƙara gudu ne ya sa Maleek faɗin "Dan Ubanka me mashin shiga bayan waɗan can Karuwan tun kafin su ɓullewa ganinmu" Ai kuwa me mashin da duk tsoron Maleek ya rufe sa ne ya sa shi karya kan mashin ɗin nasa ya shiga bayan su Najmeer da mugun gudu.


Meera da duk hankalinta ya tashi ne ta ƙara leƙa bayansu tana faɗin "Yau mun shiga uku wallahi ga Maleek nan a bayanmu, anya ba shine ya sanarwa su Sultan inda mike ba?"


"Kinga Meera duk wannan zancen zamu yi shi daga baya, yanzu neman tsira mike yi, amma ki sani ba wai tsoron Sultan ne ya sa nake gudu ba, ina son na yi masa tanadi na musamman wallahi sai na koya masa hankali"


Shuru Meera ta yi dan ita ganin take duk magana ɗaya Sultan na iya jin abin da suke faɗa.


Ta bayan layinsu Najmeer me adaidaita ya shigo, inda ta bashi umarnin ya rinƙa shiga kwanar da motoci basa iya shigowa, ganin hakan ya sa Sultan cewa a tsayar da motoci, da sauri ya fito tare da bin hanyar da matsanancin gudun da be taɓa sanin yanada irinsa ba har ya tsere su Maleek da ke kan mashin, cakkkkk ya tsaya yana kallon adaidaitar da ke tsaye kan hanya, tabbas ita ce wadda ke ɗauke da su Najmeer, abin mamakin shine ba bu kowa a ciki, Maleek da ke ƙarasowa ne ya ce me mashin ya tsaya ɗan nesa da inda Sultan ke tsaye, cikin ƙasa da murya kamar me raɗa Maleek ya cewa me mashin "Wai wancan ba Sultan Chief ba ne?"




Me mashin na jin haka ya saki mashin ɗinsa tare da runtumawa da gudu gurin Sultan yana masa kirari, ai kuwa mutane suka cika gurin ana faɗin ga Sultan Chief ga Sultan Chief, kafin ka ce me gaba ɗaya unguwar ta cika da mutane, su Majeed da masu tsaronsa ne suka ƙaraso ana tattare mutanen da ke ƙoƙarin isa gurinsa, Sultan kuwa duk baƙin ciki ya cika shi ganin babu kowa a cikin adaidaita har me tuƙin nata, a tsawace ya kalli mutanen da ke gurin yana faɗin "Dallah Malamai kun ishemu da surutun banza da wofi, wannan ai hauka ne sai hayaniya ku ke min a kunne" Ya ƙarasa maganar yana barin gurin cikin tsananin fusata, mutane sai jayewa ake ana bashi hanya ganin yanda ransa ya ɓaci.


Sultan na isa gurin motocinsu ya daki glass ɗin mota ɗaya da hannunsa da ƙarfi, nan take glass ɗin ya tarwatse hannunsa kuwa ya ɓalle da jini, Majeed ne ya yi saurin kama sa "Sultan what is this please? za ka halaka kanka saboda wata macen"


Idanun Sultan sun ciko da ƙwalla but taurin rai be bari sun zubo ba, ya ɗago kafuran idanuwan nasa da suka yi jajir ya sauke kan fuskar Majeed, ai kuwa Majeed ya sake masa hannu yana mai ja da baya a mugun tsorace, tun da Allah ya halicce sa be taɓa ganin ɓacin ran Sultan irin haka ba, wata irin razananniyar ƙara Sultan ya saki wadda ta haddasa watsewar duk mutanen da suka taru a gun, waɗan da ke cikin gida kuwa suka rinƙa kulle ƙofofinsu dan sun yi tsammanin ɓarayi ne suka shigo unguwar tasu.


Kan gwuiwoyinsa ya durƙusa yana dafe kansa jikinsa kuwa ya hau ɓari tamkar me jin sanyi, duk wata jijiya ta jikinsa sai da ta fito, jin an dafa kafaɗarsa ne ya sa ya naɗa naushi me zafin gaske ya doki wanda ke bayansa, amma sai ya ji an riƙe naushin nasa, da mugun fusace ya ɗago dan ganin wani me ƙarar kwana ne ya riƙe masa hannu, Junaid ya gani a tsaye cikin suit baƙaƙe, kayan sun masifar yi masa kyau musamman da ya ɗora glass ɗan ƙarami me kyau da ɗaukar ido, gashin kansa ya haɗe ya ƙara kyau, da mamaki Sultan ke kallonsa dan be san yanda aka yi yayan nasa ya san sun zo nan ba.


Hugging ɗinsa ya yi yana mai sauke ajiyar zuciya me zafi, cikin muryar da shi kansa be san yana da ba ya ce "Bro wallahi idan har ban kashe yarinyar nan ba zan iya kashe kaina, dan Allah ka nemo min inda take, yanzu ma na sake rasa ta"


Bubbuga bayansa Junaid ya shiga dan ya san duk abin da Sultan zai faɗa a yanzu baya cikin hayyacinsa, Junaid ne ya shigar da shi mota sannan ya bada umarnin su koma gida.


Tun da suka fara tafiya Sultan ke kwance kan cinyar Yayan nasa, duk hankalinsa baya jikinsa daga zaran ya rufe ido sai ya rinƙa ganin lokacin da Najmeer ke sakar masa murmushin mugunta, duk ya rasa abin da ke masa daɗi a rayuwa, sun ɗauki ɗan lokaci l
kafin suka ƙarasa gida kasancewar akwai jayewa.




Suna shiga Junaid ya kama Sultan suka nufi room ɗinsa, Allah ya sa babu kowa a parlourn.


Majeed na bayansu jikinsa duk a sanyaye, kan bed Junaid ya kwantar da Sultan sannan ya shiga aikin gyara masa gannunsa da ke fitar da jini, bayan ya gama ne ya maida kallonsa kan Majeed da duk ya tsure guri ɗaya, cikin muryarsa me ɗan karen daɗi gami da uban miskilanci kamar me ciyon magana ya ce "Majeed wai wacece wannan yarinyar da duk Sultan ya tada hankalinsa saboda ita?"


Ɗan sosa kai Majeed ya yi alamun rashin gaskiya "Bro Karuwa ce fa, me zaman kanta"


A razane Junaid ya waro rikitattun idanuwansa me ƙara masa kyau cikin mamaki "Karuwa kuma? meye haɗinku da Karuwa?"


Sanin halin Junaid ɗin ne ya sa Majeed kwashe duk abin da ya faru ya sanar masa daga farkon haɗuwar Sultan ɗin da Najmeer har yau.


Jinjina kai Junaid ya yi "Tun ina kan hanya na hangi motocinku na gudu kamar za ku tashi sama, shine na bi bayanku dan ganin inda za ku tafi, ashe Karuwa ku ke bi ya subhanallah"


Sultan da ke kwance ne ya ɗan kalli yayan nasa, sai kuma ya mayar da kansa wani gefen dan ya rasa abin da ke masa daɗi a halin yanzu, zuciyarsa kuwa sai ƙara fusata take.


Junaid ne ya kuma cewa "Majeed a ina yarinyar take kuma me ka sani game da ita?"


"Shalelen Alhazawa kenan wadda bata harka da yara sai manyan masu kuɗin da ke ji da kansu, cikakkiyar ƴar bariki ce me zaman kanta, wani lokacin har Clup take kwana idan har bata ra'ayin kwana da wani namijin......"


Saurin ɗaga masa hannu Junaid ya yi zuciyarsa na mugun duka da ƙarfi, a rayuwarsa ya tsani mace marar kamun kai, wani irin mugun zafi zuciyarsa ke masa tamkar zata faso ƙirjinsa, "Allah ya shirya su" Ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da barin ɗakin.


Sun kai mintuna biyar a haka ba wanda ya ce uffan, shima Majeed ɗin be yi yunƙurin magana ba dan ya san Sultan ba zai amsa masa ba, Sallamar Mom ce ta sa Majeed miƙewa yana gaisheta tare da ficewa daga ɗakin.


Da sauri ta ƙaraso tana mai zama gefen bed ɗin "Sweetheart me ya sameka ne? na shiga ukuna wai me yake faruwa ne kwanakinnan"


Mom ta faɗa cikin damuwa da ɗan nata, Sultan da ke kwance ya ɗago kansa a hankali ya ɗora kan cinyar Mom yana mai fashewa da kukan da ya daɗe a zuciyarsa, cikin tsananin tashin hankali Mom ta shiga rarrashinsa dan ta san yau kam ran maza ya ɓaci, abin da zai saka Sultan kuka ba ƙarami ba ne, sai da ya yi me isarsa kafin ya ɗago rinannun idanuwansa masu masifar ban tsoro "Mom please ku nemo mun ita duk inda take, idan ba haka ba za ku rasa ni, na tsaneta Mom wallahi na tsaneta...." Ya ƙarasa maganar muryarsa na sarƙewa, bubbuga bayansa ta shiga yi cikin tausayawa tana faɗin "Wacece ita? faɗa mun ko ƴar gidan uban waye sai an kawota har nan gidan ka zartar mata da hukunci"
Saurin ɗagowa ya yi "Da gaske Mom?"


Hawayen da ya zubo mata ta share cikin gazgatawa ta ce "Na yi maka alƙawari duk inda take a faɗin garinnan sai an nemo ta, ka saka wannan a ranka idan har ba'a kawo maka ita ba ka canza mun suna, amma meye sunan yarinyar?"


Ɓata fuska Sultan ya yi "Wai Shalele na ji ana kiranta, amma ki tambayi Majeed zai sanar da ke" "Alright ka kwantar da hankalinka ni ce nan na shaida maka cewar ka gama ganinta?" Mom ta ƙarasa maganar tana murmushi.
Wani mugun farinciki ne ya lulluɓe Sultan dan ya san babu abin da Mom zata masa alƙwari bata cika ba, kwanciyarsa ya yi kan cinyarta suka cigaba da fira kamar ba abin da ya faru.






........................
A ɓangaren su Najmeer kuwa, me adaidaita na sauke su suka shige ƙwanar da zata sada su da hanyar gidansu Mamu, ai kuwa da sauri suka shige, me adaidaita ko ya ɓoye dan ceton ransa.


Lokacin da suka shiga ba kowa dan haka Najmeer ta ja hannun Meera zuwa ɗakin Mamu, kwance suka sameta tana rawar sanyi cikin sauri Najmeer ta ƙarasa tana mai tallafota "Mamu lafiya? me yake damunki?"


A ruɗe Najmeer ta jero mata tambayoyin, duk da cewar Mamu na jin jiki amma hakan be hanata gane wadda ke gabanta ba, "Najmeer......?"


Ta faɗa cikin muryarta da bata fita sosai.


"Na'am Mamu sannu, bari na ɗaga ki ko za ki samu ƙarfin jikinki" Kamata ta yi tare da ɗorata kan gado, Meera ce ta ɗora mata pilo a bayanta, Najmeer kuwa ta fito tsakar gidan ko zata samu abin da zata dafa mata, dan alamun yunwa sun bayyana a jikinta.


Cikin ƙanƙanin lokaci Najmeer ta yi tuwo da miyar ganye, duk abin da take buƙata akwai shi a kitchen ɗin, sai da ta tabbata ta gama tasss kafin ta kwaso abincin zuwa ɗaki.


A nan ta samu Meera da Mamu na fira, duk da cewar Mamu sama-sama take magana amma Meera na jin daɗin firar sai washe baki take, har Najmeer ta aje girkin.


Da ƙyar ta samu Mamu ta ci tuwon, Meera kam sai da ta lashe kwano.


Bayan sun gama ne Najmeer ta kwashe kayan ta wanke.


Duk abin da take Mamu na kallonta, dan bata taɓa zaton Najmeer zata dawo ba, cikin sallama Najmeer ta shigo tana mai zama kusa da Mamu "Sannu Mamu ya ki ke jin jikin naki yanzu?"




"Mtsssss wai da waye take magana?" Cewar Mamu tana kallon Meera, bushewa da dariya Meera ta yi "Da ke take, tana tambayar ya jikin naki"


Najmeer ce ta ce "Haba Mamu yanzu kuma me na yi? idan bakya son dawowar nawa sai na koma" A ruɗe Mamu ta ɗago tana kallonta sai kuma ta fashe da kuka tare da rungumeta, itama Najmeer ɗin rumgeta ta yi tana rarrashinta, duk tausayinsu ya kama Meera bata san lokacin da ƙwalla ta zuba mata ba.


Cikin kuka Mamu ta ce "Najmeer me na yi miki ki ka nemi kashe ni tun lokacin mutuwata be yi ba?" Jin abin da ta ce ne ya sa Najmeer da Meera fashewa da dariya, cikin fushi Mamu ta janye jikinta tana ɓata rai "Yoooo na ga iyashege dariyar me ku ke min?"




Tun kafin waninsu ya kuma cewa komi suka ji an banko ƙofar gida da ƙarfi, Najmeer na jin haka ta koma bayan ƙofa ta ɓoye, Meera dai sai zare ido take dan ta kasa matsawa ko'ina, Kawu ne ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi cikin masifa ya ce "Ina shegiyar yarinyar ne? an ce mun ta zo gidannan"


"Wa ya faɗa maka hakan Jamilu? ni kaina ina neman Jinkanyata ido rufe amma kun korar mun ita, Allah sai ya saka mun" Mamu ta ƙarasa maganar tana sharɓe hawaye kamar gaske.


Sai a lokacin Kawu ya lura da Meera da ke zaune tana kallon yanda Mamu ke kuka, "Ke kuma daga ina?" Ya faɗa yana lashe baki kamar tsohon maye.


Haɗe fuska Meera ta yi dan ganin yanda yake kallonta, "Am....am....ni sunana Meera kuma na zo ganin Mamu ne"


"To to to ya yi kyau har wanne lokacin za ki kai anan gidan?"


"No ba daɗewa zan yi ba ziyara ce kawai na kawo mata".


Kawu na washe baki ya ce "Hakan nada kyau, ko za ki je gidana ku gaisa da matana"


Saurin karɓe zancen Mamu ta yi da faɗin "Kai Jamilu kai Jamilu ka shiga hankalinka, kuma ka nemo mun Jikanyata duk inda ku ka kai mun ita idan ba haka ba, hukuma ce zata raba ni da kai"


Jin Mamu ta ambaci hukuma ya sa Kawu ficewa da sauri yana zage-zage, sai da Najmeer ta tabbatar ya yi nisa kafin ta fito tana murmushi.


"Meera ashe mun kusa shan biki"


Harara Meera ta gallawa Najmeer "Bikin waye kuma?"


"Naki mana na ji yanda Kawu ke rawar ƙafa kamar da wata a ƙasa"


"Hmmm kin ga Najmeer bana son haka fa, Mamu kina jinta ko?"


Murmushin ƙarfin hali Mamu ta yi dan jikinta ya fara zafi, zazzaɓi take ji sannu a hankali yana shiga jikinta, amma sai ta daure saboda bata son hankalin Najmeer ya tashi "Nikam ku ake ji, ku koma can ɗakin nata ku ƙarasa ni zan samu na kwanta"


Fita Meera suka yi suna dariya jin yanda Mamu ke magana.


Da kallo Mamu ta bisu tana mamakin inda Najmeer ta samo budurwa kamar haka, tana son tambayarsu amma sai sun samu natsuwa.


Ɗakin Najmeer suka koma cikin mintuna talatin suka gyara shi tassss, duk jikin Meera ya saki kasancewar ɓarin da ta yi, kan bed suka baje suna maida numfashi "Wai nikam Najmeer me Docotor ya ce game da jinin da ya zuba a jikina"


Cikin alamun tsoro Najmeer ta ce "Dama...dama...."


"Dama me? faɗa mun mana ai babu abin da zai sa mu ɓoyewa juna sirrinmu a yanzu"


Duk da jikin Meera ya yi sanyi amma cikin dauriya ta ƙurawa Najmeer ido dan jin amsar tambayarta, "Cikin jikinki ne ya zube Meera"


A mugun tsorace Meera ta zazzaro ido "Cikin jikina kuma? ban fahimce ki ba Najmeer" Meera ta ƙarasa maganar tana jijjiga Najmeer da ƙarfi.
"Yes Meera kina da ciki amma ya zube sanadiyar zubar jinin da ki ka yi" Kuka Meera ta fashe da shi tare da rungume Najmeer cikin tausayin kanta, "Shikenan duk farincikin rayuwata ya ƙare, waye zai aureni a haka? bayan Karuwa ma har ciki na yi" Sosai Meera ke kukan tana dukan jikinta, da sauri Najmeer ta riƙeta ta shiga rarrashinta tare da yi mata nasiha me ratsa jiki "Meera ki sani cewar kowanne bawa da tasa ƙaddarar, kuma duk iskancin mace baza ta rasa me aurenta ba idan har Allah ya zaɓa mata, ina son ki kasance me ɗaukar ƙaddara a kowanne lokaci...."




Jin kiran sallar ƙarfe huɗu ne ya sa suka miƙe dan yin ibadah.




Wanka suka fara sannan suka yi sallah, sosai Najmeer ta yi musu addu'a.


Bayan sun gama ne ta kunna wayarta tana mai danna wata number, bugu uku aka ɗaga.


"Hi My Alhaj....." Najmeer ta faɗa cikin wata arniyar murya me ɗaukar hankali, wanda aka kira da Alhaj ne ya saki murmushi me sauti yana faɗin "Shalelen Alhazawa, ai wannan muryar taki baza ta ɓace mun ba, gaskiya na shiga wani halin na rashinki a kusa da ni, please ki bani dama na zo na ganki"


Cike da makirci Najmeer ta ce "No ba yau ba sai zuwa gobe yanzu haka ina cikin Airport zamu tafi Dubai karɓo wasu kaya"


"Wow that's why i love you, ki tura mun account numberki yanzu"


"Okay yanzu kuwa, anjima zan kira ka byeee"


Kashe wayar ta yi tana dariyar mugunta, Meera kam sai kallon Najmeer ta ke jin ƙaryar da ta zuba, account number Najmeer ta tura masa, ko minti ɗaya bata yi da turawa ba ta ji saukar alart na 10million.


Ihu Meera ta yi cikin mugun mamaki, "Kai Najmeer amma wannan waye haka? wanda be san zafin kuɗi ba"


Har Najmeer ta buɗe baki da niyar magana suka ji faɗuwar abu a tsakar gida, a tare suka fito dan ganin meye, da gudu Najmeer da Meera suka ƙarasa gun da Mamu ke kwance a sume, cikin sauri suka kamata jikinta ya ɗauki zafi sosai alamun zazzaɓi ya shigeta.


A ruɗe Najmeer ta ce "Kama mun ita mu tafi Asibiti jikinta ne ya tashi"


Ba ɓata lokaci suka nufi babban Hospital ɗin da ke cikin gari, suna isa aka shiga da Mamu dan bata taimakon gaggawa, Najmeer da Meera sai zarya suke har aka kira sallar magrib, a nan suka yi sallah har Nurse ɗin ta fito tana mai ƙarasowa inda suke "Ku biyo ni office ɗina" Jiki a sanyaye suka bita har zuwa office, sai da ta gama rubuce-rubucenta kafin ta maida kallonta kan Najmeer "Ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login