Showing 30001 words to 33000 words out of 44092 words
Chapter 11 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt
yi.
Nan take Sultan ya fara rikiɗewa zuwa ƙatuwar Kada me girman gaske, Mom da ke tsaye kuwa ta zube ƙasa cikin mugun tashin hankali.
A gaban idonsu Sultan ya koma jibgegiyar Kada me ban tsoro, idanuwansa jajir kamar garwashin wuta, ba zato kuma suka fara jin kukan Mage na tashi, gurnanin magen ne ya ƙara yawa kamar na Zaki, tafiyar Magen kuwa tamkar Doki, a ruɗe Mom ta maida kallonta inda kukan ke tashi dan ganin meye.
*Ku yi sharing saboda Allah, mu je zuwa yanzu aka fara, ku dai ku kasance da alƙalamin Asmeey ta haidar domin jin yanda zata kasance*
*SHALELEN ALHAZAWA*
*Writing and story*
*By*
*Asmeetar Hydar*
(Asma'u Ayuba)
*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*
P. 8
Ido huɗu suka yi da Sultan da ke watsa mata mugun kallo cike da tsana, "Ka mareni da wanne dalilin?"
Najmeer ta faɗa tana kallon Junaid da Meera.
Junaid ne ya ce "Keeeee.... wai dama ke ce me driving ɗin? ba shakka shiyasa ki ke tuƙin hauka"
"Kai ne dai mahaukaci"
Cewar Najmeer tana murguɗa masa baki.
Hannu ya ɗaga da niyar shafa mata mari cikin sauri ta damƙe hannun tana girgiza masa kai, duk da cewar hannunta na ƙonewa sosai kamar ta saka shi cikin wuta amma hakan be hanata daurewa ta fara faɗin "Ban da wannan lokacin, kar ka sake izgilancin ɗaga ƙazamin hannunka na ƴaƴan talakawa a jikina, idan a lokacin baya ka dakeni na barka wannan lokacin ba zan ɗaga maka ƙafa ba, zan yi maka uzuri yanzu saboda na lura har yanzu kai ƙaramin yaro ne wanda be isa na tsaya sa'insa da shi ba" Ta ƙarasa maganar tana mai sauke hannunsa a hankali, a lokacin har hannayenta sun yi jajir kamar wadda ta saka hannun a wuta.
Kallonta ta maida kan Sultan tana mai sakin murmushin da ita kawai ta san manufarsa "Kai kuma marin da ka yi mun bashi ka ɗauka, ka san cewa haɗuwarmu baza ta yi kyau ba, but next time sai na koya maka yanda ake girmama manya"
Junaid ne ya katseta da faɗin "Wai ke lafiyarki kuwa? kin ga sa'anki anan ne da ki ke kiran kanki da babba, na lura cewar Sultan kaine ka janyo wannan yarinyar ta rainani amma zan ɗaukar miki mataki" Ya faɗa yana barin furin a fusace, Najmeer kuwa ta kama hannun Meera suka shige mota, da kallo Sultan ya bisu har suka bar gurin cikin matsanancin gudu.
Tun da Junaid suka fara tafiya Sultan ke jan tsaki kamar wanda aka ce hanyar samun abincinsa kenan, gajiya da tsakin ne ya sa Junaid faɗin "Malan ka isheni fa, duk kaine silar wannan abin wallahi"
Cikin haɗe fuska da takaici Sultan ya cije lips ɗinsa yana mai faɗin "How's that my fault? yarinyar nan fa na kasa gane inda ta dosa, ga shegen rainin tsiya"
"Ai kuwa akwai raini sosai dan cikin jininta yake, ina ganin baza ta fi shekaru sha uku ba amma take faɗa mun baƙaƙen maganganu haka"
Junaid ya faɗa yana dafe kansa dan ya gaji da magana.
"Sha uku fa Bro? yarinyar zata fi shekaru sha uku ko kallon tsoro ka ke yi mata ne"
"Ina ruwana da ita? da har zan ƙare mata kallo mtsssss" Junaid ya ja tsaki.
Taɓe baki Sultan ya yi ba tare da ya kuma cewa uffan ba har suka iso gida, a parlour suka taradda Mom zaune tana kallon program ɗinta, bakin Junaid ɗauke da sallama ya shigo barin Sultan da be da niyar yin sallamar, Mom na ganin Sultan ta fara sunne kai tana ƙoƙarin barin parourn ganin haka ya sa Sultan nufota da sauri yana faɗin "Wai Mom lafiya kuwa? ko wani laifin na yi miki please ki daina gudu na haka"
Tun kafin ya rufe baki Mom ta kai ƙarshen steps da gudu.
Junaid ne ya bushe da dariya har da riƙe ciki abin da ya jima a rayuwarsa be yi ba kenan, sosai yake dariyar wadda ta ƙara masa kyau matuƙa, shi ko Sultan in ransa ya yi dubu ya ɓaci hakan ya sa ya haura room ɗinsa yana mai ƙara haɗe fuska.
Da ƙarfi ya daki ƙofar tare da faɗawa ɗakin.
A zaune ya sameta ta naɗe jelarta da ke kwance a ƙasa har tana jan ƙasa, a hankali Zakanyar ta wangame baki tana ɗaga kai sama alamar barka da zuwa, ɗan ɓata fuska Sultan ya yi tare da zama kan bed ɗin ba tare da ya ce uffan ba, miƙewa Zakanyar ta yi tana mai taku cikin izza har ta ƙaraso gabansa, Sultan ne ya ƙara haɗe fuska alamar ba rahama "Please ki tafi yau bana son dogon surutu, duk ke ce silar abin da ke faruwa a yanzu sai da na ce miki mu kashe wannan yarinyar amma kin ce mu bari har sai lokaci ya yi, yaushe kenan lokacin zai yi?"
Kallonsa Zakanyar ta yi sai kuma ta girgiza kai alamun aa tana mai juya masa baya, "Idan har muka kasheta a yanzu burinka da nawa ba zai cika ba, bayan haka aurenku ya zama dole kamar yanda ka sani ya kamata ka koyawa kanka rayuwa da ita tun yanzu"
"Okay fine zan yi ƙoƙarin yin hakan, but yarinyar akwai rainin hankali"
"A haka za ka canja ta har mu samu biyan buƙata" Zakanyar ta faɗa tana mai ɓacewa.
Dafe kai Sultan ya yi da ƙarfi yana mai jin mugun tsanar Najmeer daga ƙasan ƙafarsa har ƙwaƙwalwarsa.
Cikin dauriya ya shige toilet dan sakarwa kansa ruwa.
....................
A ɓangaren Prince kuwa yau tun safe ya fito dan neman unguwar da su Najmeer ke zama, sosai aka baza tsaro ana nemansu ai kuwa cikin ikon Allah Dogaransa suka samo addrees na gidan, zaune yake cikin mota sanye cikin kayan Sarauta kamar kullum ba ƙaramin kyau ya yi ba musamman yau da ya ɗora alkyabba a saman kayan nasa, ya sha rawani har kusa da kyawawan idanunsa masu kyau da ɗaukar ido, ba ka ganin fuskarsa sai dai da alama ya gaji da zaman da yake yi.
Cikin biyayya ɗaya daga cikin masu tsaronsa ya ƙaraso yana faɗin "Allah ya ba ka nasara mun samu gidan da take"
Kamar wanda aka tsikara ya ɗago yana ƙara lumshe ido "Ina buƙatar ku kaini yanzunnan"
Cike da biyayya Dogarin ya amsa da an gama yana mai shigewa motar, motoci ashirin ne suke take masa baya har haɗaɗɗar unguwar da su Najmeer ke zama, bakin gate ɗin suka tsaya kamar yanda Prince ya bada umarni, sosai yake kallon gidan kafin ya fito tare da nufar gate ɗin, Dogaran ne suka fiffito suna bin bayansa amma ya ɗaga musu hannu alamun baya buƙata, ya jima yana buga bell ɗin gate har ya fara fusata dan babu wanda ya buɗe, juyawa ya yi da niyar tafiya ya ji an buɗe gate ɗin ana faɗin "Waye ne......?" Cakkkk ya tsaya ba tare da ya juya ba, ita kuwa Najmeer da ke bakin ƙofa da mamaki take kallonsa tana son tunano inda ta san me wannan kamannin, kawar da tunanin ta yi kafin ta ɗan juya ciki tana kallon gate Man da fitowarsa bayi kenan "Baba ina ka shiga ana buga ƙofa tun ɗazu"
Cikin biyayya gate Man ya ce "Hajiya ayi haƙuri na zaga ne"
"Haƙuri fa ka ce, ai hauka ne da rashin hankali wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe" Ta faɗa a tsawace, haƙuri ya kuma bata yana mai sunkuyar da kai, duk abin da suke Prince na jinsu sosai ya ji zafin yanda take wulaƙanta masu aikinta, cikin ƙasaita ya juyo yana mai watsa mata mugun kallo, ai kasa magana ya yi ganin kayan da ke jikinta kamar ba musulma ba, wata ƴar ƙaramar riga ce da kaɗan ta wuce mazaunanta, rigar me hannun vest ce daga baya a buɗe, gashin kanta ya baje amma ya sha gyara sosai, bakinsa na rawa ya ce "Ke.... wannan wanne irin iskanci ne"
Najmeer kam tsoro ne ya shigeta ganin wanda ke gabanta tabbas shine wanda suka haɗu a gurin shaƙatawa, a tsorace ta runtuma da gudu cikin gida tana kiran sunan Mamu, yanda take gudun ne ya sa duk wata halittar jikinta motsawa, da sauri ya kawar da kansa ƙasa har ta shige sannan ya bi bayanta.
Najmeer na shiga parlour ta sami Mamu da Meera suna kallo, da gudu ta faɗa bayan Mamu tana faɗin "Na shiga uku ga Miyar yauƙi har a gidanmu"
Meera na jin haka ta fashe da dariya dan ta san wa Najmeer ke nufi, sallamar Prince ne ya sa ta ƙara daburcewa tana mai noke kai cikin jikin Mamu, Mamu kuwa sai zuba masifa take amma Najmeer taƙi fitowa, cikin biyayya Prince ya gaishe da Mamu yana mai kallon Najmeer ƙasa-ƙasa, Meera ce ta gaida shi ya amsa ciki-ciki yana mai zama nesa kaɗan da inda suke zaune, Mamu ce ta ce "Ɗannan sannu da zuwa"
Lumshe ido Prince ya yi a karo na farko yana faɗin "Sannu Hajiya ya gidan?"
"Lafiya ƙalau ka zo tafiya da ita ne ko? to dan Allah kar ka kwana da ita idan kun gama duk abin da za ku yi ku dawo a yau ɗinnan"
Waro ido Prince ya yi yana mai dafe saitin zuciyarsa, Najmeer kam ƙara hargitsewa ta yi jin Mamu ta lalata mata shiri, dariya ce ta hana Meera miƙewa sai ƙara sunne kai da ta yi, cikin biyayya Prince ya ce "Hajiya ba tafiya da ita na zo na yi ba magana nake son mu yi da ita"
"Wallahi ƙarya yake azzalumi jiya har fyaɗe ya tashi min a cikin bainar jama'a, hmmm ai Mamu idan na nuna miki yanda ya mayar da jikina sai kin sha mamaki, shine fa ya biyo ni har gida"
"Keeee waye ya tashi yi miki fyaɗen?"
Prince ya faɗa cikin mugun mamaki.
Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai yi masa gwalo sai kuma ta fashe da kuka har da birgima a ƙasa tamkar ƙaramar yarinya, hawaye kuwa daki-daki a idanuwanta, rarrashinta Mamu ta shiga yi tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un yanzu bawan Allah jikanyar tawa ka tashi lalatawa? yarinya kamila me tsoron Allah shine za ka yi mata fyaɗe, Allah ya fika da izininsa"
Cewar Mamu itama tana fashewa da kukan, majina Najmeer ta sharce kafin ta ce "Ina faɗa miki Mamu sai riƙe sa ake mutane na bashi haƙuri amma haka ya rinƙa ture kowa da ke gabansa cikin tasha ya nufo kaina da niyar ɓata min rayuwa"
Wannan karon kasa haƙuri Meera ta yi ta bushe da dariya har da riƙe ciki, Prince kam kasa magana ya yi idanuwansa sun rine jajir ransa ya mugun ɓaci jin sharrin da Najmeer ta laƙa masa, kuma daga zaran ya ɗago ido sai ta kawar da kai dan babu abin da take tsoro sama da kallon idanuwansa.
"Kin gani ko Mamu wai na zo"
Najmeer ta faɗa tana lailaya ido.
Tsammm Prince ya miƙe yana mai ficewa waje ransa a mugun ɓace.
Najmeer na ganin haka ta bi bayansa da gudu a lokacin har ya kusa gate, "Hi Mr Prince Miyar yauƙi"
Ta faɗa tana kama ƙugu.
Ran Prince a matuƙar ɓace ya juyo "Waye Miyar yauƙin?" Ya faɗa yana mai tsalle ɗaya ya damƙo gashin kanta, ihu Najmeer ta kurma kamar wadda ake cirewa rai "Sunan da ki ka samun kenan? ai kuwa zan koya miki hankali" Ya faɗa yana mai ƙara matse gashin kanta, sosai zafin ke shiga har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, "Washhhh Allah please ka sake min gashina"
Ba tare da ya saurareta ba ya cigaba da jijjiga kanta tsabagen mugunta, ai kuwa Najmeer ta rinƙa rafka ihu har su Mamu suka fito, Mamu ce a gaban Meera har tana ƙoƙarin zamewa ita ala dole an taɓa mata kamilar jikanya, Prince na ganin Hajiya Mamu na yanka gudu ta nufo inda suke ne ya sa ya sake Najmeer tare da ficewa da sauri.
Sosai kan Najmeer ke sarawa tana ganin Mamu ta ƙaraso ai kuwa ta zube ƙasa tare da runtuma ihu "Wayyooo Allah kaina, wayyo Allah jama'a ya kasheni ku duba min ƙwaƙwalwar kaina ina ganin ya tafi da shi"
Kamata Mamu ta yi tana duba gashin kan nata, "Mtssss ke rabani da shirmen banza ba abin da ya samu kan naki"
"Dama Mamu na san kin daina ƙaunata imba haka ba ga kwanya na zuba ƙasa amma za ki ce ba abin da ya sameni"
Najmeer ta faɗa tana dalalo yawu wai shine kwanya, Meera ce ta ce "Kai Najmeer ai wannan yawu ne ba kwanya ba, kuma dama idan an kama gashin kan mutum da ƙarfi sosai har zubar yawu zai rinƙa yi tsawon sati ɗaya"
Najmeer na jin haka ta ƙara tattaro yawu ta cigaba da dalalowa tana ɗaga kai sama "Kin ji ko Mamu, shikenan Miyar yauƙi ya gama da ni haka kawai ya tasa ni gaba"
Ɗagata Mamu ta yi tana zuba masifa ta inda take shiga ba tanan take fita ba, zagi kuwa babu wanda Prince be sha ba gurin Mamu har suka koma daga ciki.
Suna shiga Najmeer ta yi baje-baje kan kujera tana ɗaga harshe sama, Mamu kuwa sai sannu take yi mata har da ɗauko tsumma ana goge yawun da ke zuba, sarai Meera ta san Najmeer ƙarya take ita da kanta take zubar da yawun, kamar me ciyon farfaɗiya Najmeer ta ce "Mamu na san cewa mutuwa zan yi tun da har ki ka ga ban daina zubda yawu ba, yanzu haka idona sun fara rufewa da buɗewa ina ganinki ne uku-uku dan Allah ki yafe min duk abin da na yi miki"
Mamu na jin haka ta matso ƙwalla gami da sarce majina "Baza ki mutu ba Najmeer sai na ga ƴaƴanki da yardar Allah, ai shi ciyo ba mutuwa ba ne"
"A a mutuwa zan yi Mamu, ina ji a jikina dan har wani sanyi-sanyi ke tashi daga tsakiyar kaina da alama mu ne gaba a gidan Aljannah"
Najmeer ta faɗa tana wuwwula ido.
"Ƙwarai kuwa ku ne a gaba ƴarnan, ai ina ji a jikina, amma dan Allah kar ki mutu har sai kin kaini umrar da ki ka ce"
Daga Najmeer har Meera bushewa da dariya suka yi, cikin dariya Najmeer ta ce "Wai dama duk wannan tarairayar da ki ke min dan kawai zuwa umra ne? na zata duk cikin soyayya ce"
"Mtsssss rabani dan Allah da shirmen banza da wofi, yooooo ni meye abin tarairaya gurinki idan ba wani abin nake so ba"
"Ƙara narke fuska Najmeer ta yi tana mai karkace baki ta cigaba da magana kamar ɗazu "Wayyyooo Allah kwanyar kaina na zuba Mamu ki taimaka min ya raunatani"
Ko kallonta Mamu bata yi ba ta haura sama.
Wayar Najmeer da ke gefe ne ta ɗauki ƙara cikin hanzari ta duba tana mai jan dogon tsaki, sai da ta kusa yankewa kafin ta ɗaga.
Daga can ɓangaren Alhaji ya ce "Shalelena sai kira nake ba'a ɗagawa"
Ɗan taɓe baki Najmeer ta yi cike da salo ta ce "Yes mun tafi Abuja ne da Mom ɗina amma anjima zamu dawo"
"Okay dama zamu zo da iyayena gobe da safe neman aurenki kamar yanda mu ka yi magana a baya, kasancewar wasu abubuwan ne suka tsayar da ni"
Wani irin juyawa cikin Najmeer ya yi amma sai ta dake "Okay ƙarfe nawa za ku shigo goben?"
"Misalin sha ɗaya na safe"
"Allah ya kaimu" Najmeer ta faɗa tana kashe waya.
Duk gumi ya wanke mata jiki, "Lafiya dai Najmeer?"
Cewar Meera.
Sai da Najmeer ta ƙara sharce gumi kafin ta ce "Wai Alhaji ne zai shigo neman aurena gobe"
"Mun shiga uku, kina nufin zai gane ƙarya ki ke masa duk tsawon wannan lokacin"
"Ba ma hakan ba Meera ina da auren Jabir a kaina fa"
"What.........?"
Meera ta faɗa da ƙarfi.
"Yes Meera ranar da na koma gidan da ku ke zama a ranar aka ɗaura aurena da Jabir, shine dalilin da ya sa na bar gidanmu"
"Amma Mamu ta ce min ba'a ri ga da an ɗaura auren ba"
Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai kallon Meera "Kin tabbata hakan ta ce miki"
"Sosai kuwa na tabbata dan mun yi firar sosai, ta sanar da ni cewar an fasa ɗaurin auren saboda kin bar gida"
Hamdala Najmeer ta yi tare da godewa Allah, dama wannan dalilin ne ya sa a kullum take jin ɓacin rai, gyara zama ta yi kafin ta kuma cewa "Ya ki ke ganin za'a yi, ni da iyayena sun rasu duk ƙarya ce nake shirya masa yanzu idan ya zo ya samu ba hakan ba ne fa"
"Wai kina nufin aurensa za ki yi?" Meera ta tambaya.
Murmushi Najmeer ta saki me ƙarawa fuskarta kyau "Sosai ma kuwa aurensa zan yi, meye a ciki? daga zaran na yi sati ɗaya zan kwashe duk wata dukiyarsa sannan ya sakeni"
Bushewa da dariya Meera ta yi "Kina nufin be da hankali ne zai sakeki"
"Kin ga Meera duk wannan zancen mu aje shi a gefe, hankalina a tashe yake kar fa asiri ya tonu"
"Zamu yi tunani zuwa anjima yunwa nake ji yanzu, bari na kira Maryam ta ɗora mana girki"
Meera ta faɗa tana miƙewa.
..................
Yau ta kama Monday kuma a yau su Dad suka shirya zuwa London neman auren ɗansu Sultan, daga Junaid har Mom tare za'a tafi da su.
Dukkaninsu sun haɗe cikin kayan alfarma kana ganinsu ka san cewa ba ƙaramar dukiya ce tare da su ba, yau Junaid wankan ƙananan kaya ya yi wanda hakan ya masifar karɓar jikinsa, Sultan kuwa an sha manyan kaya sai washe baki ake.
Motoci hamsin ne suka nufi airport cikin tafiyar ɗaukar hankalin me kallonsu, jirgi ɗaya aka kama wanda zai ɗauke su, a can suka sami Surayya da Imran sai Alhaji Hafiz ƙanin Dad kasancewar da su za'a yi tafiyar.
Kana ganin Surayya zaka san hankalinta baya kanta, duk ta rame ta tsigale sai kallon Sultan take har lokacin tafiyarsu ya yi, wanda Sultan ɗin be sakar mata fiska ba, Imran da Junaid kuwa suna tare da juna sai magana suke ƙasa-ƙasa da alama akwai abin da suke tattaunawa.
Ba ɓata lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar London.
Basu jima suna tafiya ba Sultan ya miƙe dan shiga toilet, hakan ya sa Surayya ta faki idanu ta bi bayansa jiki na rawa, kamar an ce ya juya kawai ya ga mutun tsaye a gabansa.
"Surayya lafiya?"
Ya faɗa yana haɗe fuska.
"Ba lafiya ba Sultan, tabbas ka san matsalata kuma kaine maganinsa"
"Kin ga kar ki soma please, yanzu fa ni mijin wata ne, ki yi haƙuri da ni ko kuma ki koma