Showing 33001 words to 36000 words out of 44092 words

Chapter 12 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3806

gun Junaid tun da shi baya da wadda zai aura"


Waro ido Surayya ta yi a tsorace "Rufa min asiri, ai Juanid ɗin na fara so kafin kai amma sanin halinsa ne ya sa ban yarda ya san ina son sa ba, amma kai na bayyana maka soyayyata ka kasa amincewa, dan Allah Sultan ka aureni ko zuciyata zata samu sauƙi"


"Ke wai ya zan auri ballagaza kamar ki, kalleki dan Allah duk wani abin da nake buƙata a gurin mace bakya da shi, a hakan zan aureki"




Fashewa da kuka Surayya ta yi tana mai roƙon Sultan amma be saurareta ba ya shige bayi abinsa, jiki a mace ta koma tare da zama inda ta tashi, duk yanayinta ya canja Imran yayanta ne kawai ya san halin da take ciki dan bata ɓoye masa komi, sosai tausayin ƙanwar tasa ya kama shi ganin yanda lokacin ɗaya ta canja.






Misalin ƙarfe sha biyu suka isa ƙasar, inda suka tarar da hamshaƙan masu kuɗi an zo tarbarsu, motoci fiye da ɗari ne ke gurin masu masifar kyau da tsada, da farko iyayen Malika sun haɗe fuska suna jiran ganin waɗan da suka zo neman auren ƴarsu, amma suna ganin kayan jikinsu Dad sai kowannensu ya fara washe baki, dan gaba ɗaya taronsu babu wanda ya saka kaya me tsada da ɗaukar ido kamar su Dad, Malika da ke can gefe ne cikin shigar ƙananan kaya waɗan da suka ɗame mata jiki duk wata halittar jikinta ta bayyana, da gudu ta ƙaraso tare da hugging ɗin Sultan, kiss ta sakar masa a goshi "I love you Babe"




Daga Dad har su Junaid kasa magana suka yi, ganin rashin kunya a fili.


Surayya kuwa hawaye ta share a gefe tana mai jin mugun tsanar Malika a ranta musamman da ta ga kyawun da Allah ya yi mata, ɗan janyeta a jikinsa Sultan ya yi "Love you too Baby, ki gaida su Dad mana"


Sai da ta ɗan taɓe baki kafin ta ɗaga musu hannu tana faɗin "Hi guys welcome to London" Idanunta ne ya tsaya kan Juanid, ai kuwa ta nufesa da sauri har tana haɗawa da gudu-gudu, hannu ta ware da niyar rungumesa ya ɗaga mata yatsa tare da girgiza kai "Hi Malika ya ki ke?" Ya faɗa yana sakin murmushin yaƙe.


Hakan ya sa ta sha jinin jikinta, nan fa aka fara gaisuwa da yi musu barka da zuwa, duk da cewar Dad ya ga rashin tarbiyya a tattare da Family ɗin amma hakan be sa ya nuna ko a fuska ba, Surayya na gefen Mom a tare suka shiga mota, ba ɓata lokaci motocin suka bar gurin.


Kai daga ganin gidansu Malika ka san cewa ba ƙananan masu kuɗi ba ne, gida ne wanda ya amsa sunansa gida duk inda ka duba zubin dukiya ne tari-tari.


Wani ƙayataccen parlour aka sauke su tare da zube musu kayan more rayuwa, Malika idanuwanta na kan Junaid ko ƙyaftawa bata son yi har Junaid da Imra suka lura da hakan, Imran ne ya ɗan mitsini Junaid a hankali ya ce "Wai kana lura da wannan yarinyar kuwa? sai kallonka take nifa lamarinta ya fara bani mamaki"


Cikin cool voice Junaid ya ce "Ni kaina kallon ya isheni ka san bana son yawan kallo ai"


Daga haka suka bar zancen ganin mutane sun fara taruwa ana ƙara yi musu sannu da zuwa, baƙin ciki ne ya hana Surayya ɗaga ko cokali balle ta ci wani abun, ba laifi sun ci abinci amma ba sosai ba, nan aka kai kowannensu nasa ɗakin, sai dai Mom da Surayya ɗaki ɗaya suke Dad kuwa da ƙaninsa Junaid yana ɗaki ɗaya da Imran, gogan ne Sultan aka warewa ɗakinsa daban wanda ya mugun haɗuwa.




Ƙarfe huɗu za'ayi taro a harabar gida, wanda hakan al'adarsu ce idan har za'a zo neman aure sai an yi shagali tare da nunawa jama'a mijin da ya zo neman ƴarsu.




Kasancewar a gajiya Sultan yake ne ya sa yana shiga ya kwanta dan baccin da ke idonsa.




Dad kuwa tun da ya shiga ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa ɗaya wannan wanne irin Family ne Sultan zai haɗa zuri'a da su.




Kamar yanda Dad ke cikin wannan tunanin haka ma Junaid da Imran waɗan da ke mamakin rashin kamun kai irin na Malika.




Ƙarfe huɗu da rabi na yamma an gama shirya gurin taron tamkar baza'a mutu ba, komi na gurin white and pink ne, haka ma kowa ya saka kaya white and pink hatta su Mom, wanda anko ne da aka kawo musu na taron.


Malika ta yi shiga cikin doguwar riga har tana jan ƙasa, a kanta babu ɗan ƙwali balle mayafi duk rabin dukiyar fulaninta a waje, wannan shigar ba ƙaramin ɓatawa su Dad rai ya yi ba, cikin fushi ya ja hannun Sultan gefe ransa a mugun ɓace ya ce "Sultan wannan wanne irin hauka ne haka? ka rasa wadda zaka kawo a matsayin matar aure sai wadda bata san darajar kanta ba"


"Dad please wallahi ina sonta sosai and zan mayar da ita yanda ka ke so bayan aurenmu"


"Haukar banza kenan, bayan sunana da zaka ɓata a gari har sunan ƴaƴan da zaka haifa ma dan babu wanda zai so haɗa alaƙa da irin wannan gidan, dukiyarsu ta banza ce tun da babu tsoron Allah a ciki" Dad ya ƙarasa maganar yana barin gurin, daidai lokacin da aka ce ana buƙatar Malika ta kama hannun mijinta ta kawo shi gaban taro.


Cikin karairaya Malika ta miƙe tana mai tafiya a gadarance, kowa ya zuba mata ido sautin waƙa na tashi a hankali me daɗin dauraro, Sultan kuwa har da gyara tsayuwa yana mai sakin killer smile, da mamaki aka ga ta nufi Junaid fuskarta ɗauke da murmushi, nan fa kallo ya ƙara yawa dan mutane da dama sun san cewa ba Junaid ne angon ba.




Malika na isa ta kama hannunsa tare da jansa zuwa gaban taron, kamar wani wawa haka Junaid ke bin bayanta cike da mamaki kamar a mafarki, sai da suka isa kafin Malika ta ɗauki speaker tana mai ƙara gaida mutanen da ke gurin cikin harshen turanci, sannan ta cigaba da faɗin "Kamar yanda kowa ya sani a yau ne aka zo neman aurena daga Nigeria, kuma kowa ya buƙaci ganin wanda zan aura hakan ya sa na yanke hukuncin nuna muku wanda zuciyata ke ƙauna sannan nake fatar na aura"


Sai da ta kalli Sultan da duk idanunsa sun canja kala kafin ta cigaba da faɗin "Junaid nake so kuma nake burin na aura, dan haka a ɗaura min aure da shi ko na kashe kaina"




Tsittttttttt kiɗa ya tsaya mutanen da ke gurin duk suka ƙara yin shuru ana sauraren abin da Malika ke faɗi tamkar a mafarki.
























*Jiya na ce zan yi posting bansamu na yi ba saboda matsalar rashin wuta da mike fama da shi a yanzu, wutar mu ta samu matsala bama samu kamar kowanne lokaci, dan haka a ƙara haƙuri ba kullum mike samun wuta ba*






*SHALELEN ALHAZAWA*


*Writing and story*


*By*

*Asmeetar Hydar*


(Asma'u Ayuba)




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




P. 9










A fusace Sultan ya ƙarasa gurin yana mai ɗauketa da wani rikitaccen marin da yasa kowa miƙewa tsaye, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta jikinsa sai rawa yake tsabagen ɓacin rai, da yatsa ya nunata bakinsa na karkarwa ya ce "My Brother........, shine wanda za ki aura? wow Malika wow, ai bansan cewa ke ɗin marar tunani ba ce sai yau, and babban kuskurena shine yarda da ke da na yi, wallahi na yi nadamar saninki a rayuwata".


Sultan ya ƙarasa maganar yana mai barin gurin.




Dad da su Junaid suka rufa masa baya, aka bar Malika na rusa ihu kamar mahaukaciya, iyayenta kuwa sai zagin Sultan da Family ɗinsa suke, ko minti biyu masu kyau basu ƙara a gidan ba suka fito cikin shirin tafiya Nigeria, gaba ɗaya gidan ya ɗauka da surutun mutane sai kukan Malika da ya ƙara cika gidan ita ala dole Junaid take so idan ba haka ba zata rasa rayuwarta.




Jikin Junaid ya yi sanyi sosai ganin son da Sultan ke yiwa Malika, Surayya sai murna take a zuciya tare da zubawa Malika albarka dan ta gama biya mata komi.




Airport suka nufa ran kowa a ɓace musamman Dad da har suka isa Nigeria be ce ƙala ba, ransa ya masifar ɓaci dan ko Sultan ba zai nuna masa ɓacin rai a yau ba.




Tun a airport ɗin kowa ya kama gabansa, su Imran da sister ɗinsa suka nufi gida sai ƙanin Dad wanda shima be ji daɗin abin da ya faru ba, Mom kam sai rarrashin Dad take ganin yanda ransa ya ɓaci, a babban parlour suka sauka kowannensu da abin da yake tunani musamman Sultan, minti ɗaya be ƙara a zaune ba ya miƙe tare da nufar ɗakinsa.


Kamar yanda ya saba haka ya sameta a zaune tana mai kaɗa jelarta sautin dariya na tashi daga bakinta wanda ke ɗauke da mugayen haƙora masu kaifin gaske, cikin fushi Sultan ya damƙo wuyan Zakanyar da hannu ɗaya ya shaƙe har sai da ta fara zare ido "Bari na fara kashe ki kafin burin rayuwata ya gama rugujewa tun da ke ce silar duk halin da nake shiga, na tabbata cewa ke ki ka hana wannan auren ba kowa ba"


Sultan ya faɗa yana mai jifa da ita gefe.




Ɗagowa Zakanyar ta yi a hasale ta doki cikinsa da ƙafa, ai kuwa Sultan ya yi tsalle sama tare da faɗawa kan bed, itama Zakanyar tsallen ta yi tana mai dira kan bed ɗin ta kai masa cizo daidai wuyansa amma sai ta tsaya cakkkk ba tare da ta cije shi ba, a hankali kuma idanuwanta suka fara fitar da ƙwalla wanda hakan ya sa Sultan hugging ɗinta gami da fashewa da kuka shima, sosai suke kukan a tare wanda duk yanda ka kai ga rashin imani idan ka gansu sai ka tausaya musu, tabbas ba ƙaramin abu ke tsakaninsu ba musamman yanda fuskar Zakanyar ta sauya lokaci ɗaya.


Cikin sanyin jiki Sultan ya janyeta yana mai shafa gefen fuskarta "I'm sorry Habibaty na kasa daurewa ne"


Ɗaga kai Zakanyar ta yi tana mai juya fuska "Na sani Sahibina ina son ka ƙara haƙuri har lokacin da burinka da nawa zai cika".


Ta ƙarasa maganar tana mai ɓacewa.


Naushi Sultan ya kaiwa bed ɗinsa a lokacin Junaid ya yi sallama tare da zama fuskarsa a haɗe, ko kallon inda yake Sultan be yi ba ya juya masa baya, Junaid ne ya ce "Me hakan ke nufi? ko kana tsammanin ni na hana Malika aurenka?"




Ɗan sosa kai Sultan ya yi yana mai janyo blanket ya fara rufe jikinsa ganin ya fara sauya halitta zuwa Kada, kasacewar Junaid be lura da hakan ba ne ya sa ya cigaba da faɗin "Ya kamata ka yi magana da ita a yau domin tabbatar da abin da ke faruwa, but please kar ka ɗauki wannan a matsayin laifi"


Miƙewa tsaye ya yi gami da taku ɗaya inda Sultan ke kwance "Amma kamar abin farinciki ne ka rabu da ƴar marassa tabiyya"


Kafin ya ƙarasa maganar Sultan ya ɗaga jelarsa tare da kai masa duka a baya ji ka ke timmmmmm, "Ya subhanallah" Junaid ya faɗa yana mai dafe gurin da Kadan ya dakesa, da sauri kuma ya maida kallonsa kan Sultan da ya rikiɗe zuwa mummunar Kada me ban tsoro, yau lamarin ya fi muni dan har wani baƙin hayaƙi ke fita daga bakinsa, ganin hakan ya sa Junaid ficewa daga ɗakin da yana mai dafe bayansa da ke mugun zafi.




..................
A ɓangaren su Najmeer kuwa sun gama tsara komi har da iyayen ƙarya waɗan da ta saya musu kayan da za su saka masu mafisar tsada, unguwar Rimi suka samu hayar wani haɗaɗɗen gida me hawa uku, sosai gidan ya tsaru tamkar baza a mutu ba, misalin sha ɗaya su Najmeer suka shirya cikin wasu masifaffun kaya masu shegen kyau less ne me tsada milk, anko su ka yi da Meera sai dai kayan sun fi zama daram daƙam a jikin Nameer, mayafinsu black ne kalar handbag da takalmar ƙafarsu wanda ya gaji da haɗuwa.


Meera ce me driving Najmeer ne gefe Mamu kuwa tana bayan mota sai surutu take zubawa ba tare da sanin inda aka nufa da ita ba, suna isa ta yi horn Gate Man ya danna remote nan take ya ɗage masa Meera ta kunna kai ciki, bakin Mamu har yana dalalo yawu tsabagen kallo, kai daga gate ɗin zuwa harabar gidan ya isa tabbatar maka cewar an kashe dukiya me yawa.


"Aljannar duniya" Cewar Mamu tana fitowa.




Meera ta ce "Ai sai mun shiga daga ciki za ki tabbatar da gidan ƙarshe ne"




"Kina nufin wannan duk wasan yara ne? kin ga motoci kamar a gurin saidawa"




"Sosai kuwa Mamu ke dai mu ƙarasa daga ciki"




Meera ta faɗa tare da jan hannunta.




Najmeer na bayansu tana waya da Alhajinta har suka shigo ƙayataccen parlourn me ɗauke da duk wani abun da ake buƙata.


"Wai wai rangammm" Mamu ta kuma faɗa tana mai kama baki, parlour ne me ɗan karen kyau yana ɗauke da kujeru kala uku masu tsadaddun kyau.




Frigde kuwa uku ne ta kowanne ɓangere, sai Tv manya-manya guda biyu.




Bakin Najmeer ɗauke da sallama ta shigo tana mai katse wayar, "Yawwa Mamu kin ga wannan gidan zamu zauna na tsawon sati ɗaya saboda hidimar bikina, ina son ki kasance makauniya kuma kurma, ina nufin duk abin da ki ga gani ki kawar da kai kuma duk abin da ki ka ji ki yi kamar ba ki ji ba"




Mamu ce ta katseta da faɗin "Na boni na lalace ni Mamu tsohuwa ga Najmeer, ke dan ubanki auren ke za ki yiwa kanki da har za ki mayar da ni makauniya da kurma? yoooo ina uwayen da za su ɗaura miki auren bayan Kawunki Jamilu?"




"Mu ne uwayenta kuma jigo a gareta"




Cewar wasu Dattijai da ke saukowa daga upstairs cikin shigar alfarma, Namijin zai kai shekaru hamsin da ƴan kai, sai macen zata kai shekaru arba'in, fuskarsu ɗauke da murmushi.


Cike da tafiyar ƙasaita suka iso tare da zama kan kujera me zaman mutum uku, Mamu na ganin haka ta sauko har ƙasa ta rusuna sai da ta dunƙule hannu kamar me gaida Sarki ta ce "Barka da zuwa ranku ya daɗe, shugaba me daraja sannunku da saukowa"


Dariya ce ta kusa ƙwacewa Dattijan ganin yanda Mamu ke zuba gaisuwa amma sai suka ƙara haɗe fuska kamar yanda Najmeer ta tsara musu, Dattijon ne ya ce "Yawwa Hajiya ya hanya da mutanen gida?"




"Alhamdulillah ai mutane kune mutane ga kuɗi ga mulki, ku kam Allah ya sallemeku"


Mamu ta faɗa tana washe baki.




"To muna godiya tashi ki zauna a sama"


Dattijuwar ta faɗa tana mai murmushi, girgiza kai Mamu ta yi alamun aa, sai da aka yi da gaske kafin ta koma saman kujera, jin ƙarar motoci ne ya sa Meera kama hannun Mamu aka haura da ita sama, Najmeer kuwa ta ƙara tsara musu yanda za su yi sannan ta bi bayan su Meera.




Motoci hamsin ne aka shigo da su gidan wanda daga gani ka san ba ƙananan mutane ba ne, duk inda ka duba manyan Alhazawa ne ke fitowa cikin shigar kamala.




Daga gefe ɗaya Alhajin Najmeer ne sanye da farar shadda ya sha kyau sai murmushi yake, har babban parlour aka yi musu jagora inda suka tarar da Mahaifin Najmeer da Mahaifitarta na ƙarya da ta samo zaune suna mai yi musu maraba, cike da girmamawa aka gaisa kamar dama can iyayen gaskiya ne, ba ƙaramin mamaki Alhajin ya yi ba ganin iyayen Najmeer ko kaɗan basa kama da ita, amma hakan be sa ya kawo wani abun a ransa ba, wayarsa ce ta yi ƙara a ladabce ya nemi izinin fita sannn ya fice tare da ɗaga wayar.




Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa amma Alhajin ya yi shuru da alama ana magana ne, kusan mintuna uku yana saurara kafin ya ce "Idan muka nemi ɗaura auren a yau akwai matsala dan za su iya zargin wani abun, amma a saka ranar auren hakan zai fi"


Ƙara dakatawa ya yi alamun ana masa magana, sai can ya amsa da "Kar ka samu damuwa Najmeer ta zama mallakinka da yardar Allah ta shigo hannu" Sallama ya yi tare da kashe wayar, yana juyowa suka yi ido huɗu da Meera da ke tsaye tana mai sauraronsa, bakinta na rawa ta ce "Dama ba kai za ka auri Najmeer ba wani ka ke nemawa aurenta?"


Da sauri ta juya zata koma ya yi hanzarin kama hannunta "No Meera please ki tsaya ki fahimceni zan faɗa miki koma menene amma sai idan baza ki hana aurennan ba"




Mugun kallo Meera ta watsa masa tana mai ƙwace hannunta "Kana tsammanin za'a haɗa kai da ni a yaudari babbar aminiyata"




"Ba haka nake nufi ba ki fahimceni Meera Oga na ne ke son ƙawarki, kuma baya ƙasar nan kawai ina masa aiki ne har zuwa lokacin da zai bayyana kansa"




"Waye Ogan naka?"


Cewar Meera a fusace.


Sai da Alhajin ya duba gabas da yamma kudu da arewa kafin ya matsa kusa da Meera yana mai rage murya "Zan faɗa miki wannan alƙwari ne amma please kar ki sanar da Najmeer, ga number na sai ki kirani zuwa ajima bayan mun koma duk abin da ke faruwa zan sanar miki"


Ba dan Meera ta so ba ta karɓi numbersa tana mai barin gurin cike da fargaban abin da zai je ya dawo.




Komawa ciki Alhajin ya yi inda ya samu an tsayar da rana sati ɗaya Friday me zuwa za'a ɗaura aure, sosai ya ji daɗin lamarinnan ganin iyayen basu kawo matsala ba, kayan abinci da na sha kuwa sai da suka ture dan ba wani ci suka yi ba, duk abin da suke buƙata akwai shi a gurin, nama ko kala-kala ne kama daga naman shanu naman rago da sauransu.


Million ɗaya suka aje tare da ficewa, sai da suka fito kafin aka kira Najmeer da Meera dan su gaishe da mutane, Najmeer na sanye cikin mayafinta me girma kamar gaske sai sunne kai take, sosai mutanen suka yaba kyawunta da kuma natsuwarta.




Ba wata magana suka yi da Alhajin ba ta koma ciki, sosai ta ji daɗin yanda komi ya tafi yanda ta tsara, a parlour ta sami Mamu zaune ta haɗe ƙafa, ba tare da Najmeer ta kalleta ba ta maida dubanta kan Dattijan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login