Showing 3001 words to 6000 words out of 44092 words

Chapter 2 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3815

a halin yanzu mutane suna ɗaukar cewa na sakar miki jiki kin lalace saboda ke marainiya ce, Allah ya kare ki a duk inda ki ke kuma Allah ya shiryeki".
Mamu ta ƙarasa maganar tana mai share ƙwallan da ke zubo mata kamar an buɗe pampo.






Su Namjeer kam a wani tangamemen gida suka shiga wanda ya gaji da haɗuwa, kasancewar Namjeer ta saba shiga manya-manyan gidajen Alhazawa ne ya sa take ganin wannan gidan ma ba komi ba ne, ɗakinsa suka nufa Najmeer na gefensa ya rungumota ta baya, har rawa jikinsa ke yi tsabagen jaraba, dan ba ƙaramin tafiya da iamaninsa ta yi ba.


Tamkar aljannar duniya haka ɗakin ya tsaru, komi na ɗakin da Gold aka yi shi, hatta bed ɗin na Gold ne barin ma ƙofofin gidan, hasken ɗakin da ya gauraye ne yasa Alhajin ƙara zubawa Najmeer ido, a ransa ya ce tabbas Allah ya zuba halitta a anan, wannan ƙwayar idon nata tamkar zinari, ajiyar zuciyar da Najmeer ta sauke ne ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga, cikin ƙasaita ta nufi Frigd ɗin da ke ɗakin ta ɗauko drinks da Cup, kamar wani soko haka Alhajin ya miƙe tare da karɓar kayan da ke hannunta "Baby ai wannan aikin ba irin na mata kamar ki ba ne, let me help you with it, amma ba bu abin da ki ke son ci kuwa?"


Zama kan bed Najmeer ta yi, ta ɗauki mintuna biyu kafin ta ce "Akwai Shawarma?"


"Yes akwai Shawarma" Alhajin ya faɗa yana latsa wata ƙararrawa, ɗaya daga cikin masu aikin ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, kallon Namjeer ta yi tana mai mamakin ganin ƙaramar yarinya kamar wannan tare da Dattijo irin me gidanta, tsawar da Najmeer ta daka mata ne yasa matashiyar matar da zata kai shekaru talatin razana cikin tsananin tsoro, a fusace Najmeer ta miƙe tana mai ɗauketa da mahaukacin mari, "Ke dabba jaka me ki ke kallo? kinga na yi kama da wadda za ki zubawa ido kamar wata tsohuwar mayya, tom bari na ba ki amsar abin da ki ke son sani, kallon da ki ke mun ya nuna cewar kina son sanin meya kawoni gidannan ko?"


A hankali ta koma tana mai zama kan cinyar Alhajin cikin iya barikanci ta shafo gefen fuskarsa tana faɗin "Ni Karuwa ce, cikakkiyar ƴar tasha me zaman kanta, idan kuma da abin da ki ke son sani za ki iya faɗa mun" Jikin matashiyar na ƙyarma ta ce "Allah ya ba ki haƙuri insha Allah hakan baza ta ƙara faruwa ba, Sir me ka ke da buƙata?" Ta ƙarasa maganar tana kallon me gidanta.


"Shawarma za ki kawo mata na ba ki minti ɗaya" Cikin biyayya ƴar aikin ta fice tana mai rufo ƙofar, ko cikakken minti ɗayan bata yi ba ta dawo hannunta ɗauke da plate, a gaban Najmeer ta aje sannan ta fice daga ɗakin, har yanzu Najmeer na kan cinyarsa sai yamusta fuska take, cike da makirci ta ce "Ka haɗa mun ruwan wanka kafin na gama" Tun kafin ta gama magana Alhajin ya miƙe dan cika umarni, ita kuwa ta fara cin Shawarmar tana lumshe ido saboda daɗin da ke ratsa ta.




A haka Alhajin ya fito ya sameta, ko kallon inda yake bata yi ba ta cigaba da abin da take, "Ranki ya daɗe na haɗa miki idan kin gama sai ki shiga daga ciki" Najmeer ta kai kusan mintuna uku kafin ta ce "Okay" Tana mai miƙewa dan rage kayan jikinta, kasa haƙuri Alhajin ya yi domin ta gama firgita shi, a ruɗe ya rungumota yana mai kissing ɗin gefen wuyanta jin wani ƙamshin da ke tashi a jikinta, Najmeer kuwa bata hana shi ba sai ma murmushin muguntar da take a zuciya har suka zube ƙasa, a wannan lokacin ne ta samu damar ɗaukar hankacif ɗin da ke aljihun wandonta ta shaƙa masa a hanci, lokaci ɗaya ya ja numfashi tare da zubewa a sume.


Wata irin dariyar mugunta Najmeer ta saki tana faɗin "Yanzu aka fara Alhaji" Wanka ta shige abinta, ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, kamar yanda ta barshi hakan ta same shi, sai da ta gama duk shirin baccinta hankali kwance, ɗakin ta fara bincikawa cikin ƙwarewa da iya sata, duk wasu Gold da kuɗaɗensa sai da ta kwashe, sannan ta yiwa kanta tranfer na kuɗaɗe tana mai cigaba da dariya.


A hankali ta nufi ƙofar fita ta danna mata key, dan ta san idan ta ce zata bar gidan a yanzu asirinta zai iya tonuwa, dan haka ta koma ken bed ta yi kwanciyarta tare da addu'ar bacci, cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita.


Asubar fari ta farka har tana zamewa, a gaggauce ta shiga bayi, har ila yanzu Alhaji na kwance yanda ta barshi, bayan ta fito ne ta duba hijab a wadrop da mamaki ta samu sabon hijab har ƙasa, sai da ta gama sallah kafin ta kama hannayensa ta ja shi zuwa ƙarƙashin bed sannan ta rufe shi da zanin gado, toilet ta koma tana mai kunna shawa sannan ta fito.


A daidai lokacin da aka fara buga ƙofar room ɗin, sai da Najmeer ta daidaita natsuwarta sannan ta ɗauki jakkar da ta zuba kayan da ta sata tana faɗin "Am coming" Ƙofar ta buɗe da mamaki take kallonsa "Waye kai?" Cewar Najmeer a taƙaice "Ni ne me kula da Sir a kullum safiyar Allah"


"Okay ya shiga wanka already mun yi sallama da shi ni zan tafi" Kamar matashin be yarda ba sai kuma ya gyaɗa kai saboda jin ƙarar ruwa daga toilet ɗin.


"Okay Shalele za ki iya tafiya, idan ba damuwa mu tafi na kaiki gida" A tsorace Najmeer ta ce "Ya aka yi ka san sunan da ake kirana"


Murmushi Matashin ya yi "Ai yanda naga Sir ya laƙe miki daga jiya zuwa yau ne ya sa na ba ki wannan sunan" Cikin samun natsuwa Najmeer ta ce "Bana buƙatar rakiyarka" Ba tare da jiran abin da zai ce ba ta bar gurin.




Tun da ta yi nisa da gidan hankalinta ya fara kwanciya a lokacin haske ya fara, adaidaita ta samu tare da yi masa kwantancen inda zai sauke ta, a can bayan layinsu ya aje ta.


Allah ya sa Mamu tana ɗaki cikin sanɗa ta shige nata ɗakin tana rufo ƙofa, kamar daga sama ta tsinkayo muryar Mamu na faɗin "Idan kin gama laɓe-laɓen sai ki fito ki faɗa mun gidan Uban da ki ka kwana"


"Dan Allah Mamu ki shafa mun lafiya, gidan Ubana na kwana mana, shikenan ba zan leƙa waje ba sai ki rinƙa zargin ina kwana a waje, to baza a fito ba idan kuma akwai wanda ya isa ya fito da ni"


"La'ilaha illallahu mahammadan rasulillah, Najmeer ni ki ke faɗawa magana haka? laaaaa biri ya yi kama da mutum, ashe bancin Karuwanci har shaye-shaye ki ka fara"


Banza Najmeer ta yi tana mai kwanciya domin bacci take ji.


Mamu ta jima tana zuba masifa amma ko uffan Najmeer bata kuma cewa ba har ta gaji ta koma nata ɗakin.




Yau kwana biyu kenan Najmeer bata fita koda nan da waje ba, ba ƙaramin daɗi Mamu ta ji ba hakan ya ƙara mata natsuwa duk a tunaninta Najmeer ta shiryu, sallamar da yaro ya yi ne yasa Mamu amsawa tana faɗin "Wa ka ke nema?"


"Wai Jabir yana sallama da Najmeer" Najmeer da fitowarta daga bayi kenan cikin shigar doguwar riga irin ta larabawa me adon duwatsu rigar ta masifar yi mata kyau, pink colour wadda zata kai kimanin dubu ɗari, gashin kanta ta laulaya shi sannan da ɗora mayafi ƙarami a kai, ƙafarta sanye cikin silifas me taushi "Tafi ka ce masa ko Ubansa Bukar be isa ya kira ni na tafi ba balle shi ɗan Akuya" Cewar Najmeer tana jifar Yaron da aka aiko da butar da ke hannunta, da gudu yaron ya fita yana ihu, salati Mamu ta rafka "Yoooo ni Mamu naga ta kaina, ke Najmeer surukin naki ki ka ambata haka?"


Tun kafin Najmeer ta amsa wani yaron ya sake shigowa "Wai dan Allah ta yi haƙuri ta fito" Da mugun gudu Najmeer ta nufi randar ruwan da ke tsakar gidan har takalmanta na cirewa, sai da ta cika wata roba da ruwa ta nufi hanyar waje, Mamu na ganin haka ta miƙe tana kiran sunanta amma ina har Najmeer ta fice, wani matashi ne da zai kai kimanin shekaru ashirin da bakwai sanye cikin fararen kayansa, ɗan mashin ɗinsa na gefe ya sha wanki, fuskarsa ɗauke da murmushi, ba zato ba tsammani ya ji an kwara masa ruwa, ai be ankara ba ya ji an zuba masa ƙasa a jikinsa, sai da Najmeer ta shafe mashin ɗinsa da duk jikinsa da ƙasa tana mai banka masa harara, Mamu da ƙarasowarta kenan ta damƙo hannun Najmeer tare da sharara mata mari, ai tun kafin Mamu ta sauke hannu Najmeer ta watsawa Jabir mari cikin mugun rashin kunya ta ce "Ƙarya ne wallahi, baza a mareni saboda kai ba, munafukin banza yau sai na illataka jira ni kaga" A fusace ta shiga gida tana surutai kamar zararra, gaba ɗaya mutane sun taru a ƙofar gidan, Jabir kam kasa magana ya yi Mamu sai haƙuri take bashi, duk mutanen da ke wajen suna yi ta cewa ya gudu tun kafin ta fito, ihun Najmeer suka jiyo daga bayansu ta nufo shi da Wuƙa a hannu fuskarta banu alamun wasa, ai kuwa ƙafa me naci ban baki ba, Jabir ya runtuma da gudu ko ta kan Mashin ɗinsa be bi ba, mutanen da ke gurin suma duk sun watse dan sun san cewa ba shakka Najmeer na iya dawowa kansu.


Mamu kam zaman dirshan ta yi tare da dafe kanta tana mai karanta duk addu'ar da ta zo bakinta.






Labari ko har ya kai kunnen Kawun Najmeer, a fusace ya nufi gidansu Jabir, tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo Mahaifin Jabir na zuba ashar, da sallama Kawu Jamilu ya shiga gidan "Kar ka tako ƙafarka cikin gidana idan ba haka ba wallahi sai ran kowa ya ɓace, har ni wata Karuwa za ta wulaƙantawa yaro? yoooooo me ake da wata ƴar tasha wadda bata gaji mutunci ba, daga yau na saka wuƙa na datse alaƙar Jabir da shashashar yarinyarku" Haƙuri Kawu Jamilu ya shiga bashi yana mai neman afwa, "Haba Bukar me ya yi zafi haka? wallahi idan a yau ku ke son aurennan za'a iya ɗaurawa" Zumbur Jabir ya ce "Eh a ɗaura a yau kowa ya huta, Baba dan Allah ka yarda na aureta ina msifar son Najmeer" Ba ƙaramin so Bukar ke yiwa Yaron nasa ba kasancewar shi ɗaya Allah ya mallaka masa, ba wata dukiya ce da su ba amma duk Unguwar sun fi kowa rufin asiri shiyasa ma Kawu Jamilu ya liƙe musu domin ya lashi arziƙi.


"Shikenan a ɗaura a yau ɗin, amma idan har ta ƙara wulaƙanta min Yaro babu wanda ya isa ya haɗa aurennan" Godiya Jabir da Kawu Jamilu suka shiga yi, miƙewa Jabir ya yi yana mai faɗin "Bari na shiga na shirya, Baba a samu a ba Kawu kuɗin sayen goron ɗaurin aure" Jikin Kawu na rawa ya ce "Yawwa yaron kirki ashe ka gane" Dubu goma aka miƙa masa, carafffff ya karɓe yana washe baki.






Ƙarfe huɗu suka isa gidansu Najmeer, wannan karon har da limamin Unguwar da wasu dattijai uku ƴan uwan Mahaifin Jabir.




A lokacin Najmeer na zaune tsakar gida tana cin shinkafa da miya sai naman kajin da ke saman abincin, gefe ɗaya kuwa drinks ne masu sanyi, sai sautin waƙar M-Sharif ke tashi wadda ta kunna a wayarta, Mamu na zaune tana linke kayanta wanda ta karɓo daga gun wanki.


Sallamar su Kawu ne ya sa Mamu ɗagowa tana amsawa fuskarta ɗauke da murmushi, amma tana ganin su Bukar da Yaronsa har ma da Liman ta ji gabanta ya faɗi, maraba ta yi musu tare da nuna musu shimfiɗa, duk bidirin da ake Najmeer bata saniba saboda ƙarar waƙar da ke tashi, bayan sun gaisa ne Kawu ya kalli gefen da Najmeer ke zaune tare da daka mata tsawa ganin abin nata yana son wuce gona da iri "Ke dan Ubanki ba kiga mutane ba ne? ki ke wannan haukar" A tsorace Najmeer ta miƙe jikinta na ɓari, sanye take cikin wando da kaɗan ya wuce mazaunanta sai ƴar rigarta marar hannu wadda ko cibiyarta bata rufe ba, gashin ganta ya sauko yana rito fuskarta ɗauke da simple makeup, ba Jabir ba har Liman da sauran mutanen sai da suka gigice, ji ka ke kawai Liman da Mahaifin Jabir sun buga salati, Liman ya ce "Subhanallahi, Allah ya shirya"


Sai a lokacin Najmeer ta tuna da kayan da ke jikinta, da sauri ta nufi ɗaki ƙirjinta na dukan uku-uku kar dai a ce ƙararta Jabir ya kai gurin Kawunta, to idan ƙarar ta ya kai meyesa Liman ya zo gidansu abin da bata taɓa ganiba.




Gaba ɗaya ta kasa ba kanta amsar waɗannan tambayoyin, Mamu ce ta ce "Sannunku da zuwa, Allah dai ya sa lafiya naga har da su Liman" Murmushi Liman ya yi "Lafiya ƙalau alkhairi ne ke tafe da mu, da farko dai ga goron ɗaurin aure, yanzu haka na saka a tara jama'a a ƙofar gida domin su shaida auren Jikanyarki Najmeer da ɗan wajen Malan Bukar Jabiru" Wata irin muguwar ashar Najmeer da ke laɓe bakin ƙofa ta ja, "Allah ya tsinewa mutanen da ka tara a ƙofar gidanmu daidai gwargwado, kai Liman har ka isa ka ɗaura mun aure, wallahi duk sai na shuka muku rashin mutunci" Jikin Jibir ne ya fara rawa dan yanzu kam tsoronta yake, Kawu Jamilu ne ya miƙe rai ɓace ya nufi ɗakin, Najmeer na ganin haka ta kwasa da gudu, ai kuwa ya rufa mata baya, daga waje kana jiyo ihunta taja faɗin wallahi ta yarda da auren, kuka take kamar ranta zai fita, ita kanta Mamu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, ba ƙaramin tausayin Najmeer take ba, ta san cewa dukanta Kawu Jamilu ya yi, a duniya ba abin da take son gani fiye da farincikin Jikanyar tata.




Fuska a murtuƙe Kawu ya dawo tare da zama kusa da Jabir "Kwantar da hankalinka Najmeer ta zama matarka, ke kuma Mamu ga naki goron ki rabawa mutanenki, mu zamu tafi daga waje mutane na jira" Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Malan Bukar da su Liman ma suka rufa masa baya, suna fita Mamu ta nufi ɗakin Najmeer dan har yanzu tana jin sautin kukanta.








LONDON
.................


Wani irin numfashi ya sauke wanda ya sa matashiyar da ke kwance sauke ajiyar zuciya, sun jima a haka kafin ya ƙara ƙanƙameta a jikinsa na tsawon mintuna biyar, a hankali ya koma gefe yana sauke numfashi.




Cikin salo da iyayi matashiyar ta ƙara haurawa saman jikinsa ta shafo haɗaɗɗen sajensa, "Love you are so sweet, but why do u want to go back to Nigeria?" Ta tambayesa tana shafa ƙasan mararsa, kyakykyawan matashin da zai kai kimanin shekaru ashirin da takwas ne ya ce "Colm down Babe you know my Dad said i should go back, and yau satina ɗaya da ƙare School amma kin hana mun komawa"


"Amma Love........"


"Shhhhhhhhhh......." Ya ɗora yatsarsa a lips ɗinta "Not another word Babe, anjima jirginmu zai ɗaga zan shiga wanka" Ya faɗa yana miƙewa daga kan bed ɗin, sanin halinsa ne ya sa ta kasa magana, zubawa halittarsa ido ta yi tamkar yau ta fara ganinsa, dogo ne daidai gwargwado me faffaɗan ƙirji, gashin kansa kamar na larabawa, shi ya ƙara bawa fatar jikinsa da ke fari tassss damar fito da kyawunta, yana da manyan idanu farare masu jan hankali ɗauke da gashi zara-zara, idan ya motsa bakinsa kuwa zaka iya ɗauke muntuna biyar ba ka daina kallon bakin nasa ba, ɗauke yake da red lips me laushi tare da fararen haƙora masu jan hankalin me kallonsa, dogon hancinsa kuwa har ya ɗan kwanta a sama kuwa ya yi tsayi gwanin sha'awa, gashin girarsa baƙi ne wulikk ga cika ga kyau, yatsun ƙafarsa zara-zara ne masu ɗaukar hankali, kamar yanda gashin ƙirjinsa ya kwanta luff-lufff kana gani ka san cikakken namiji ne me tsafta da kwarjini, cigaba da ƙura masa ido matashiyar ta yi har ya shige ƙayataccen toilet ɗin da ke ɗakin, duk da cewar itama ba ƙaramin kyau ne da ita ba, haskenta ma har ya haɗa da sirkin ja, saboda gashin kanta ba wani baƙi ba ne, kana ganinta ka san Baturiya ce cikakkiya, kamar wadda aka tsikara ta miƙe tare da shigewa toilet ɗin, sun ɗauki kusan mintuna talatin a ciki, sannan suka fito a tare daidai lokacin da wayarsa ta fara ƙara, cikin taƙama ya ƙarasa yana mai kallon screen ɗin, ganin sunan Dad ne ya sa shi saurin ɗagawa amma be ce komi ba.


Daga can ɓangaren Dattijon ya ce "Sultan baza ka yi magana ba ne? har yanzu kana London kamar wanda aka jona jininsa a ƙasar, to na ba ka nan da anjima ka shigo Nigeria if not sai na ɓata maka rai" Ba tare da jiran abin da Sultan ɗin zai ce ba ya Dad kashe waya, da ƙarfin tsiya Sultan ya buga wayar tasa a ƙasa ƙirar iphone 15promax nan take ta yi kaca-kaca, wani irin mugun huci ya furzar yana dafe saitin zuciyarsa, a kiɗime Matashiyar ta ja baya ganin halin da ya shiga, ba tare da ya kalleta ba ya fara shiryawa cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya masu masifar kyau da ɗaukar ido, wani ƙayataccen agogo ya saka na Gold yana mai fesa turarukka masu daɗin ƙamshin, a lokacin zuciyarsa ta fara sanyi amma idanuwansa sun rine sun yi jajir, "Malika what are you waiting for?" Ya faɗa a tsawace.


Jikin wadda aka kira da Malika na rawa ta ce "Am......am......am waiting for you".


"What.......? idan na buɗe idona na ganki a nan sai na kakkarya ƙasussan jikinki" Tun kafin ya gama rufe baki ta kwashi kayanta a hannu tare da barin ɗakin cikin mugun gudu, dan ta san cewa yau ransa ya ɓace.






Cikin ƙanƙanin lokaci ya nufi airport, ba ɓata lokaci jirginsu ya tashi, gaba ɗaya mutanen da ke cikin jirgin kallonsa suke musamman mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login