Showing 27001 words to 30000 words out of 44092 words

Chapter 10 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3805

so ba.




Sai wajen ƙarfe biyar na yamma ta fito cikin wata arniyar riga daidai cinyarta, kayan sun masifar yi mata kyau musamman yanda shape ɗinta ya bayyana, gashinta ta ɗaure shi yana rito a baya, kunnenta ɗauke da waya da alama magana take, Meera na bayanta ɗauke da basket na kayan motsa baki.




A babban parlour suka shirya kayan cikin tsari da ɗaukar ido, ba jimawa Alhajin ya iso harabar gidan, cike da makirci Najmeer ta fito tana ɗaga masa hannu, ko kunyar Meera da ke wajen be yi ba ya rungumota yana mai manna mata kiss a kumatu "Shalelena wallahi na yi kewarki sosai, yanzu ne na ƙara tabbatar da cewar ke ta musamman ce" Fari da ido Najmeer ta yi sannan ta shafo gefen fuskarsa "Godiya nake my Alhaj, nima kewar ce ta sa na baro Dubai dan kawai na haɗu da kai"


Sosai kalamanta ya yi masa daɗi, sai a lokacin ya lura da Meera da ke kallon ikon Allah, cike da mamaki suka gaisa kafin Najmeer ta masa iso zuwa parlourn.




Meera na gefe tana kallon yanda Najmeer ke zuba makirci da kalaman soyayya kamar daga gareta aka fara sarrafosu.


Sun jima a hakan suna fira, kayan marmarin da drinks ɗin ma kaɗan ya sha.


Wata ƴar bag da ya shigo da ita ya miƙawa Najmeer yana murmushi "Shalelena ga wannan ko? i know you will like it" Itama murmushin ta sakar masa tana buɗe bag ɗin, waya ce ƙirar iphone 15promax sai ɗayar 13promax, ɗayar ledar kuwa agogo ne na gold me masifar tsada irin na ƴaƴan manya.


Cikin farinciki Najmeer ta ƙara ƙanƙame shi, "Thank you so much, kamar ka san ina buƙatar agogo, but wannan be mun ba anjima zamu tafi na zaɓi wanda nake ra'ayi, and ga friend ɗina itama ya kamata a saya mata"


"Ba ki da matsala as you wish, ai ke ɗin kin wuce hakan"




Jin saukowar mutum ne ya sa dukkaninsu kallon gurin, Mamu ce sanye cikin kayan da Najmeer ta bata, atamfa ce me kyau da tsada sai mayafi kalar atamfar, sosai kayan suka yi mata kyau, zaro ido Meera da Najmeer suka yi, dan sai da Najmeer ta hana mata fitowa dan kar ta basu kunya.


Ƙarasowa Mamu ta yi tana washe baki ganin kayan marmari zube kan tire, da sauri Alhajin ya rusuna yana gaisheta, ba tare da Mamu ta amsa masa ba ta ɗauki lemu ɗaya tana zama kusa da Najmeer "Lafiya ƙalau ɗannan ya gidan?"


Alhajin na sunkuyar da kai ya amsa da "Alhamdllh"


Ganin yanda Mamu ke wulla ido gashi tana neman yarfasu ne ya sa Najmeer miƙewa a fusace ta damƙo hannun Mamu tana faɗin "Keeeee rashin kunyar taki ta ƴan aiki har ta kai haka? waye ya ba ki izinin shigowa har parlourna gaban baƙona, kuma ki ka saka mana ƙazamin hannunki cikin abincinsa"




Meera ce ta karɓe zancen da faɗin "Hmmm gaskiya wannan tsohuwar akwai rigima, shiyasa na ce miki ki kawo matashiya wadda zata iya aiki cikin natsuwa amma kin kwaso mana me taɓin hankali"


Daga Alhajin har Mamu kallon su Najmeer suke, musamman Mamu da duk tsoron Allah ya kamata, har ta buɗe baki da niyar magana sai ta ji tamkar an saka mata makulli, duk iya ƙoƙarinta na ganin ta yi magana amma ina, Meera ce ta kama hannunta ta nufi sama da ita, "Am sorry Alhaj ka san halin talakawa da rashin wayewa"


Cewar Najmeer tana zama gefensa.


"Auuu kar ki damu, ai haka wasu suke basa sanin inda ke musu ciyo daga zaran sun fara tsufa"


Ba ƙaramin zafi maganar ta yiwa Najmeer ba, amma sai ta dake tare da faɗin "Sosai kuwa, dole zan canja ƴar aiki, yau ina ganin anan gidan zamu kwana, anjima da ƙarfe goma na dare ka shigo sai mu tafi na zaɓi kayan da nake so ko?"


"Yes ma, kuma ina son ayi mun wanka na ɗaukar hankali, amma ina son na faɗa miki wata magana idan baza ki damu ba"




"Ina sauraronka" Najmeer ta faɗa tana mai danna wayarta, "Aurenki nake so"


Wani irin tari ne ya ƙwace mata, sai da ta gama kafin ta ɗago blue eyes ɗinta masu firgitarwa ta ce "Aurenaaaaa?"


"Eh aurenki nake so, wallahi na kamu da matuƙar ƙaunarki, ki amince mun na tura gidanku a yi magana"


Gaban Najmeer ne ya shiga dukan uku-uku, tabbas asirinta ya kusa tonuwa, da farko ta masa ƙaryar family, sannan ta ɓoye masa cewar ita matar aure ce.


"Tunanin me ki ke haka? duk abin da ki ke so zan miki ko menene, matana biyu ina son ki zamo ta uku, idan ma kina son a watsa su waje ne sai ayi yanda ki ke so"


Waro ido Najmeer ta yi "Waneni, su ma ai iyaye ne, bana buƙatar a kori ɗaya daga cikinsu amma ina buƙatar ka bani lokaci na yi tunani"


"Baza ki iya auren me shekaruna ba ne?"


"Ba haka ba ne ka san komi sai da shawara, ina ganin kamar Dad ɗina zai kawo mana matsala"


"Kar ki samu matsala da shi, idan har kuɗi na aiki ba abin da zai hana ya bani ke"




"Amma ka san cewa Dad ɗina ya fi ka dukiya da matsayi, baza ka iya sayensa da kuɗi ba, dukiyarka tamkar ƙwarar zarra ce ga dukiyar mahaifina"


Jin abin da ta ce ya sa jikin Alhajin yin sanyi, dan ya san idan har Dad ɗinta ya fishi kuɗi da wahala ya aura masa ita.






"Zan iya ganin Dad ɗin naki a gobe"


"Why not, Allah ya kai mu goben" Cewar Najmeer tana miƙewa, "Ni zan shiga daga ciki idan ka gama zaka iya tafiya" Bata jira abin da zai ce ba ta haura sama cikin tafiyarta da ke ƙara mata kyau.




Alhajin kuwa wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana danna wata number, sai da wayar ta yanke ba'a ɗaga ba, ƙara dannawa ya yi amma sai da ta kusa yankewa kafin aka ɗaga, cikin girmamawa Alhajin ya ce "Allah ya ƙara maka nisan kwana ta shigo hannu, amma mahaifinta ne kawai zai bamu matsala" Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa, amma Alhajin ya yi shuru da alama magana ake, sai da ya kai kusan mintuna biyu suna waya kafin ya yi masa sallama tare da ficewa daga gidan.




..........................
A masifance Sultan ke saukowa daga uptairs yana kiran duk ƴan aikin da ke gidan, gaba ɗaya hankalin kowa ya tashi jin yanda yake ɗaga murya.


Mom da ke part ɗinta ne ta fito dan ganin abin da ke faruwa, a babban parlour ta sami Sultan zaune kan kujera me zaman mutum ɗaya, duk masu aikin na zageye da shi sun rusuna jikinsu sai rawa yake.


Sanye yake cikin suit blue me kyau sai glass ɗin da ya ɗora gaban aljihun rigar tasa, gashin kansa ya sha gyara sosai, ba bu wani alamu da ya nuna akwai abin da ya faru da shi a daren jiya, kana ganinsa ka san dawowarsa daga aiki kenan, cikin ɓacin rai ya ce "Waye ya shiga room ɗin da na hana kowa shiga?"


Cikin alamun tsoro kowa ya ce bashi ba ne, "Sultan wanne room ka ke magana?"


Mom ta faɗa tana dafa kafaɗarsa, cikin ɗaga murya kamar ba mahaifiyarsa ba ya ce "What are you saying Mom? kamar ba ki san ɗakin da nake magana ba, gaba ɗaya na duba amma banga waccan yarinyar ba"


Rarrashinsa Mom ta shiga tana mai faɗin "Kai a cikinku waye ya taimaka mata har ta fita, idan ba ku faɗa mun ba wallahi zan ɗauki mataki me tsauri game da ku"


Sumayya ce ta yi saurin cewa "Wallahi Hajiya ba bu wanda ya san yarinyar da ku ke magana, asalima tun jiya ba wanda ya haura hawa na huɗu"


Maganganun Sumayya ba abin da suka ƙarawa Sultan face baƙin ciki da ɓacin rai, a mugun hasale ya miƙe tare da ɗauketa da mahaukatan maru "Ke dabba shashasha ke ce me bakin magana ko? dallah ku ɓace mun da gani kafin na koya muku hankali"




Tun kafin ya gama rufe baki kowa ya arce.


Dafe kansa ya yi yana mai zama gefen Mom "Sorry Sultan insha Allah zan sa a dawo maka da ita a duk inda take"


"How Mom? ta ri ga ta gudu bansan yanda aka yi ta fice gidannan ba tare da wani ya ganta ba"




Har Mom ta buɗe baki da niyar magana Sultan ya ɗaga mata hannu "No Mom bana son jin komi a yanzu, ina buƙatar hutu" Be jira abin da zata ce ba ya haura sama cike da ƙasaita.




Junaid da ke tsaye bakin ƙofa ne ya sauke ajiyar zuciya, ƙarasowa daga ciki ya yi tare da zama kusa da Mom yana mai riƙe hannunta "Kin ga abin da Dad ke magana ko, wannan shine dalilin da ya sa Dad yake yiwa Sultan faɗa, yanzu ki kalli yanda yake miki magana kamar ba mahaifiyarsa ba, gaba ɗaya ba bu tarbiyya a ciki"


"Look Junaid waya faɗa maka Sultan baya da tarbiyya? ransa ne kawai ya ɓaci amma zuwa anjima zai sauko"


"Amma...."




"Shhhhhhhh....., yanzu ka dawo daga gun aiki ka je ka hutu"


Ba musu Junaid ya nufi ɗakinsa dan ba zai iya jayayya da Mom ɗin nasu ba.




Har zai nufi part ɗinsa sai kuma ya karya hanya zuwa part ɗin Sultan, daga bakin ƙofa ya fara jin maganganu ƙasa-ƙasa kamar ana meeting, be ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya rinƙa jin gurnani kamar na Zakuna da kuma kuka irin na jarirai, hannun Junaid na rawa ya murɗa ƙofar ɗakin, kamar daga sama ya ji an doko shi ji ka ke timmmm ya zube ƙasa, cikin azaba Junaid ya ce "Ya Allah......." Yana dafe bayansa da ke masa mugun zugi, ɗagowar da zai yi suka haɗa ido da Sultan tsaye yana sakar masa murmushi "Bro lafiya dai na ganka a ƙasa" Hannu ya kai da niyar taimaka masa Junaid ya galla masa harara yana miƙewa cike da jarumta, ba tare da ya kuma kallon inda yake ba ya bar gurin cikin mugun al'ajabi.


Sultan kuwa ya shige ɗakinsa tare da rufo ƙofa.






Tun da Junaid ya shiga ɗakinsa ya kasa samun natsuwa, gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake.




Ya rasa abin da ke shirin faruwa a gidan, kuma ba wanda ya faɗawa zacen ƙanin nasa, sai da ya watsa ruwa kafin ya shirya cikin ƙananan kaya masu kyau, yau ko turaren da yake sakawa ma be tsaya sakawa ba ya sauko ƙasa dan sanarwa Mom abin da idanuwansa su ka gani duk abin da zai faru ya faru.




A dianing ya same su, Sultal kuwa na video call da alama da ƴar London yake waya dan har Mom sai da suka yi magana da ita, fuskar Junaid ɗauke da damuwa ya zauna tare da ƙara gaida Mom, cikin kulawa ta ce "Junaid lafiya na ga kamar ba ka cikin natsuwa?"




Murmushin yaƙe Junaid ya saki "No Mom lafiya ƙalau kawai gajiya ce ke damuna"


Gyaɗa kai Mom ta yi alamun gamsuwa.




Maleeka da ke video call da Sultan ta ce "Love waye nake jin muryarsa, voice ɗinku ya so ya yi iri ɗaya"


"Brother Junaid kenan wanda nake ba ki labari"


"Wow can i talk to him?"


"Yeah sure love gashi ku gaisa" Sultan ya faɗa yana miƙawa Junaid waya, ba musu Junaid ya karɓa, ganin shigar jikin Maleeka ne ya sa ya ɗan kalli Sultan yana mai girgiza kai, Maleeka kuwa ta gama ruɗewa da ganin mahaukacin kyan da Junaid ke da, sai take ganin kamar ya fi Sultan ɗin nata kyau, bakinta har rawa yake gurin faɗin "Hi dear how are you?"


Sai da Junaid ya daidaita natsuwarsa kafin ya haɗe fuska alamar ba rahama kafin ya ce "Fine how's London?"


"London is amazing when you guys will come?"


Cike da gajiya da zancen Junaid ya cije pink lips ɗinsa yana faɗin "Very soon, kema kin kusa zuwa saboda ƙanina zai dawo mana da ke gaba ɗaya"


Ɗan taɓe baki Maleeka ta yi tana mai kashe masa ido "Hakane ni kaina na matsu na dawo Nigeria"


Duk maganar da suke idanun Junaid na ƙasa dan baya iya kallon shigar da ke jikinta, Maleeka kam ta ƙura masa ido ko ƙyaftawa bata yi, sai da ta gaji surutunta Junaid be amsa mata ba, daga ƙarshe ya miƙawa Sultan wayar.




Ba wani abinci Junaid ya ci ba dan yanzu ba abin da ke masa daɗi a baki, bayan sun gama ne ya maida kallonsa kan Mom yana gyara zama "Mom ina son mu yi magana idan ba damuwa"




"Okay ina jinka" Cewar Mom tana kallonsa.


Sallamar da suka ji ne ya hana Junaid faɗin abin da ke ransa, Surayya ce da Mommynta sai yayanta da ke bayansu fuskarsa ɗauke da murmushi, Junaid na ganinsa ya miƙe cikin farinciki suka rungume juna, bayan sun gaisa ne kowanne ya koma kan dianing, Junaid da Yayan Surayya me suna Imran kuwa suka nufi part ɗinsa.


Sultan da tun da ya gaida Mommyn Surayya kansa ke ƙasa ne ya miƙe cike da gadara ya nufi sama, kamar wadda aka tsikara ta tashi tana faɗin "Hi Babe wannan shan ƙamshin fa?"


Cewar Surayya tana matsawa kusa da Sultan.




Ko kallon inda take be yi ba ya nufi room ɗinsa, ai kuwa ta rufa masa baya tana surutu.


Mommynta me suna Hajiya Habiba ce ta ce "Hmmm Surayya ikon Allah, anya yarannan ba auren dangi za'ayi musu ba"


Mom na jin abin da Hajiya Habiba ta ce ta haɗe fuska kamar wadda bata taɓa dariya ba "Uhmmm ai Sultan ya fitar da wadda zai aura, im banda abinki Habiba kin san cewa ban son auren dangi ko kaɗan ɓata zumunci yake yi"


Cikin mamaki Hajiya Habiba ta ce "Salma kenan, ke yayata ce uwa ɗaya uba ɗaya amma ki ke gudun haɗa zuri'a da ni, ina laifin ki ce Sultan ya fitar da matar da zai aura ai ba sai kin nuna min ba ki son haɗin aurensu ba, imma ba Surayya da shegen nacin tsiya ba a kullum sai an wulaƙantata amma kamar marar zuciya"


"Nima shi na gani sai nacewa yaro take, ta je ta nemi wani mana ko za'a dace"


Ba ƙaramin zafi maganar ta yiwa Hajiya Habiba ba, amma sai ta saki murmushin da ya fi kuka ciyo "Allah ya sa mu dace, wai ina Daddyn Junaid ɗin ne ko an fita ne?"


"Ya tafi neman na halak"


Mom ta faɗa taƙaice.


Sanin halin Ƴar uwar tata ne ya sa Hajiya Habiba canza wata firar duk da cewar ranta ya ɓaci sosai.




Junaid da Imran kuwa a room suka baje suna firar yaushe gamo, sosai Imran ya gane ɗan uwan nasa na cikin damuwa, Imran fari ne amma ba can ba, ba laifi akwai kyau da ɗaukar wanka ga ibadah sosai shiyasa suke shiri da Junaid, kallonsa ya maida kan Junaid yana faɗin "Junaid faɗa mun damuwarka ko zan iya taimakonka da shawara"


Ajiyar zuciya me ƙarfi Junaid ya sauke yana dafa kafaɗar Imran, cike da miskilanci ya ce "Imran ina cikin damuwa gaskiya, kuma wannan ba maganar ɓoyewa ba ne" Cikin natsuwa Junaid ya kwashe duk abin da ya faru a daren jiya ya shaidawa Imran, a mugun firgice Imran ke saurasonsa har ya dasa aya.




Sun kai kusan mintuna uku ba wanda ya kuma cewa uffan kafin Imran ya ce "Zan iya taimaka maka Mom ta ga asalin wanene Sultan, amma bayan haka banada wani taimakon"


Murna fal a ran Junaid ya ce "Yaya kenan hakan zata faru?"


"Akwai addu'ar da zan ba ka wadda zaka karanta cikin gidannan anjima da dare, ina shaida maka cewar ba Sultan ba hatta wannan Magen sai ta zo gidannan, ina ganin akwai wani sirri da ke tsakanin Magen da Kadan"


Jinjina kai Junaid ya yi kafin ya ce "Na gode sosai Imran, insha Allah zan aikata kuwa saboda Mom ta san abin da ake ciki"


Addu'ar Imran ya rubuta masa a takadda har ƙarshe, sannan suka cigaba da fira.




A ɓangaren Sultan kuwa yana shiga ɗakinsa Surayya ta rufa masa baya tare da rungomosa tana mai sauke ajiyar zuciya, wani irin yanayi ne ya fara shigar Sultan wanda hakan ya hana shi dakatar da Surayya ga abin da take ƙoƙarin yi.




Ita kuwa tana ganin Sultan be dakatar da ita ba ya sa ta ƙara shigewa jikinsa tana mai shafo ƙirjinsa a hankali ta ce "Ina sonka Sultan......." Yanda ta furta sunan ne ya sa Sultan janyota zuwa gabansa, da ƙarfin tsiya ya matseta a ƙirjinsa har sai da ta saki ƙara.


Mazaunanta ya shafo yana ɓata fuska "Mtsss wai ina kayan da maza ke buƙata anan? wallahi Surayya ba ki da duk wani abin da zan soki saboda shi, asalima aurena ya kusa, daga Dad ya dawo ƙasar waje zamu tafi ayi bikina"




Ya ƙarasa maganar yana haɗe bakinsu, hakan ya sa Surayya danne kukan da ke ƙoƙarin zo mata, sosai yake kissing ɗinta har suka zube kan bed, sai da ya gama yagalgalata kafin ya yi jifa da ita gefe yana mai sauke numfashi, cike da jaraba Surayya ta koma jikinsa tana mai fashewa da kuka "Haba Sultan yanzu kana nufin baza ka aureni ba?"




"Eh ba zan aureki ba, kuma bana da ra'ayin auren mata biyu"






"Haba Sultan......"


"Get out please"


Ganin zata sake magana ne ya sa shi daka matsa tsawa "Na ce ki fita before na canja miki kamanni" Da gudu Surayya ta fice tana kuka.




Dafe mararsa ya yi da ƙarfi jin yanda take juya masa, rabonsa da mace tun da ya dawo Nigeria, sosai zufa ke karyo masa miƙewa ya yi ya ɗauko maganinsa, cikin dauriya ya isa gun fridge ya zuba ruwa tare da watsa maganin a bakinsa.




Ahankali kuma ya zame ƙasa yana sauke numfashi.




Sai bayan isha su Imran suka fito domin tafiya, har harabar gida inda motarsu ke ajiye su Junaid suka yi musu rakiya sai da suka fice daga gidan kafin su Mom suka koma ciki, a lokacin Sultan na saukowa daga room ɗinsa cikin shirin ƙananan kaya ya ci uban ado da alama fita zai yi, fuskar nan tasa ɗauke da murmushi kamar wanda aka yiwa albishir da gida Aljannah.






Junaid ne ya ce "Sultan ina zuwa haka?"


Ɗan sosa kai ya yi kafin ya ce "Clup ko akwai abin da ka ke so ne?"


Ya faɗa yana nufar hanyar fita, da sauri Junaid ya ciro addu'ar da ke aljihunsa ya fara karantawa yana mai tofawa da ƙarfi, ba Sultan ba hatta Mom sai da ta tsorata da yanda gidan ke juyawa, Junaid ko be daina karanta addu'ar ba sai ma ƙara ɗaga murya da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login