Showing 15001 words to 18000 words out of 44092 words
Chapter 6 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt
ya saka shi murna, tun da yake be taɓa haɗuwa da macen da yake jin daɗin harka da ita ba kamar Maleeka, kuma shine namiji na farko da ya fara kwanciya da ita shiyasa yake ƙara daraja ta.
Mom da ke murmushi ne ta ce "Yawwa ai yanzu sai kowa ya fito da matar da yake son aura, kai Junaid ka tabbata ka nemo mata nan da wata ɗaya idan ba haka ba zan haɗaka da Humaira ƴar gidan ƙawata dan naga alamun tana masifar sonka kuma ita ba kalar matan banza ba ce"
Ɗan sosa kai Nunaid ya yi "A dai ƙara haƙuri Mom zan nemo da yardar Allah amma wata ɗaya kamar ya yi sauri"
Dad ne ya ce "Ai sati ɗaya ma nake so ka nemo mata"
Dariya suka yi gaba ɗayansu jin yanda Dad ya yi maganar.
.............................
Najmeer kuwa tun da suka shiga gida ba wanda ya leƙo waje har garin Allah ya waye, bayan sun gama karyawa ne suka baje a tsakiyar parlour suna firar abin da ya faru daren jiya, Meera ta kalli Najmeer da ke game a wayarta ta ce "Kai amma ke hatsabibiya ce, yanzu Sultan ki ka wulaƙanta haka? ai ni jiya na rasa bakin magana shiyasa ki ka ga muna dawowa na kwanta dan a tsorace nake"
Murmushi Najmeer ta saki wanda ya ƙarawa fuskarta kyau "Ke Meera im banda abinki waye zai taɓa mun ke ya zauna lafiya, daga jiya zuwa yau na yi saba da ke sosai, ina jinki kamar ƴar uwata ta jini"
"Hmmm nima haka na ɗaukeki, Allah ya bamu ikon riƙewa juna amana"
"Ameen ya Allah wai ina Maleek ne? rabon da na saka shi a ido tun jiya"
Cewar Najmeer tana ƙunshe dariyarta.
Dogon tsaki Meera ta ja har tana rufe ido "Allah ya tsare ai ni yanzu ganin kaina nake babbar celebrity na wuce sanin Maleek, anjima zan kwaso kayana dan ba zan iya kwanciya a part ɗinsa ba"
Dariyar da Najmeer ke riƙewa ce ta ƙwace mata "Wai da gaske ki ke? Maleek ɗin naki"
"Mtsss zan zageki fa Najmeer wallahi ki fita idona, salon na koma ya cigaba da dukana"
Cike da jin haushi Najmeer ta miƙe zaune tana dafa kafaɗar Meera ta jijjigata da ƙarfin tsiya "Ashe ba ki san abin da ki ke ba, kar ki mance ke macece wadda zata iya shiga ko'ina, kar ki taɓa barin wani kafurin namiji ya rinƙa dukanki a banza a wofi, ke ɗin macece wadda take da ikon kanta, idan har kina son zama da ni sai kin koyi yanda ake dakawa maza gumba a hannu, sai kin zama jajirtacciya marar tsoro, ni da ki ke gani nan......."
Numfashi Najmeer ta ja kafin ta cigaba da faɗin "Bana shakkun kowanne ɗan iskan, ni kaina tsoron kaina nake, shiyasa na nunawa wancan yaron cewar iskanci ma guri ya samu" Ta ƙarasa maganar tana mai komawa ta kwanta.
Sosai maganganunta suka shigi Meera, ai kuwa ta miƙe zumburrrrrr ta fice waje, a harabar gida suka ci karo da Maleek wannan karon be sha komi ba, kallonta ya yi sama da ƙasa kafin ya ce "Ke gidan Uwar wa ki ka kwana? a jiya ma na yi mafarkin kin samu wata ƴar tujara wadda ta zabgan mari, sai da na farka nake ganin ashe ba gaskiya ba ne dan na san babu wata ƴar tashar da zata iya taɓa jikina"
Cikin fusata Meera ta ɗaga hannu tare da saukewa Maleek maruka guda biyu tana nuna shi da yatsa ta ce "Kar ka sake kiran Ƙawata da waɗannnan mugayen kalaman, yanzu na daina tsoronka kuma zan kwashe kayana na bar maka gidan..."
Maleek da ke riƙe da kuncensa ne ya duba gabas da yamma kudu da arewa dan ganin wanda ya mare sa amma bega kowa ba, cikin mamaki ya maida kallonsa kan Meera da ke tsaye a gabansa ta riƙe ƙugu "Hehehehe Meera...., shin kinga wanda ya mareni kuwa?" Cewar Maleek yana ƙara duba gefe da gefe, harara Meera ta galla masa kafin ta ce "Uwar wa zata mareka imba ni ba, ni ce nan na wanke ka da maru, kuma wannan kaɗan kenan idan ba ka fita daga rayuwata ba......."
Ai tun kafin ta gama rufe baki Maleek ya ɗagata sama ya damɓarata da ƙasa ji ka ke timmmmmm, wata irin muguwar ƙara Meera ta saki tana cije lips ɗinta a lokacin jini ya ɓalle daga ƙasanta, Maleek kuwa ya shiga dukanta hannu da ƙafa, ihunta ya sa Najmeer fitowa da gudu, abin da ta gani ne ya mugun fusata ta, ai kuwa ta koma cikin ɗaki da sauri ta rarumo Wuƙa me kaifi ta fito kamar wata ƴar daba, tana isa ta daka tsalle tare da ɗanewa bayan Maleek da ƙarfin tsiya da yanka masa Wuƙar a fuska, nan ta shiga yayyaka masa Wuƙar tana cije baki, Maleek da ya gama ficewa a hayyacinsa ne ya fara runtuma ihu da neman taimako, sai da Najmeer ta yi masa mugun rauni kafin ta yi jifa da Wuƙar gefe, cike da jarumta ta ɗaga Maleek sama da hannu biyu ta buga a ƙasa, ruwan cikinsa ta hau ta rinƙa gwara masa maru, "Yau sai na illataka Maleek ka kawo ƙarshen dukan mace, dan kawai ana zuba maka ido kana iskancin da ka ga dama, ai mu tun iskanci be san kansa ba mike yinsa"
Marinsa ta cigaba da yi har sai da ya sume a gurin, Meera kam ta gama tsorata da lamarin Najmeer dan ta fara zargin anya Najmeer ba Namiji ba ce kuwa, dan bata taɓa ganin mace me ƙarfi kamarta ba"
Ƙarasowa Najmeer ta yi da sauri ta sunkuci Meera zuwa hanyar waje, Allah ya sa suna fita suka samu adaidaita, a baya suka shiga Najmeer ta ce ya kaisu hospital ɗin da ke kusa.
Suna isa aka shige da Meera dan sosai jini ke zuba, a kujerar da ke wajen Hospital ɗin ta zauna duk ta daburce, a ranta take faɗin anya ba kashe Meera Maleek ya yi ba.
An ɗauki awa ɗaya ana duba Meera kafin wata Nurse ta fito duk ta yi zufa, dirrect gurin Najmeer ta nufa "Ke ce wadda ta kawo wannan matashiyar ko?"
Da sauri Najmeer ta ce "Yes i'm the one, ya jikin nata ne?"
"Ki biyo ni a office" Nurse ɗin ta faɗa tana yin gaba, bayanta Najmeer ta nufa a zuci take roƙon Allah ya sa ba mutuwa Meera ta yi ba.
Bayan Nurse ɗin ta gama rubuce-rubcenta ne ta miƙawa Najmeer wata takaddar, "Am sorry to say ƴar uwarki ta yi ɓari, cikinta da ke wata ɗaya da kwana biyu ya zube saɓanin mugun faɗuwar da ta yi"
Waro ido Najmeer ta yi "Ciki.......?"
"Yes ciki ko bata da aure ne?"
Da sauri Najmeer ta sauya yanayin fuskarta "No matar aure ce, thank you zamu iya tafiya gida ko akwai abin da ya rage"
"No sai zuwa anjima saboda an saka mata ruwa yanzu, kuma tana buƙatar hutu sosai ina ganin ki koma gida anjima ki dawo"
Godiya Najmeer ta yi kafin ta fito daga Hospital ɗin, sai yanzu take tuna cewar ai bata ba me adaidaita kuɗinsa ba, dube-dube ta fara amma babu kowa, dan haka ta nufi bakin titi ko zata samu abun hawa, tun da ta fara tafiya take jin kamar ana bin bayanta, daga zaran da juyo sai taga ba kowa har ta kawo bakin titi.
Horn ɗin motar da aka yi ne ya sa ta ɗan janye gefe, da mamaki ta ga me motar ya tsaya a gabanta tare da sauke glass ɗin, wani Alhaji ne sanye cikin manya kaya masu tsadar gaske, Najmeer kam yanayin motar ne ya tafi da imaninta dan ba ƙaramin tsada zata yi ba.
Kasancewar tana da jan aji ne ya sa ta matsa gaba, shima ya ƙara matsowa idan ta matsa sai ya matso, a tsawace ta ce "Haba Malan wai meye haka ne?"
Kashe mata ido Alhajin ya yi kafin ya ciro wata ƙaramar bag da ke cikin motar ya fara watsa mata dollers "Ki kira ni da Alhaji me dala ba Malan ba, shigo daga ciki na shayar da ke ruwan dukiya da jin daɗin rayuwa".
Ya ƙarasa maganar yana dariya, Najmeer kam wani mugun daɗi ne ya kamata dan so ɗaya ta taɓa riƙe dollers, ai kuwa ta haɗe fuska tana mai faɗin "Ka fito ka kwashe kuɗinka, ko ka ga na yi maka kama da me neman kuɗi, ka kalleni sama da ƙasa kaffff matanka babu me kyawuna ko kyawun diri na"
Ƙara bushewa da dariya Alhajin ya yi kafin ya ce "Hakane maganarki ki shigo daga ciki zan kwashe kuɗin da kaina" Fitowa daga motar ya yi Najmeer kuwa ta zagaya ta shige bakinta ɗauke da addu'a.
Sai da Alhajin ya kwashe kuɗin kafin ya shigo motar yana mai kallon Najmeer da ta haɗe fuska kamar wadda aka yiwa saƙon mutuwa "Amma kinga yanda fushi ke miki kyau kuwa? a gaskiya ke ta musamman ce"
Murmushi Najmeer ta saki me ƙara mata kyau, a hankali ta ɗora hannunta saman ƙirjinsa tare da shafowa ta ce "Faɗa mun abin da ke tafe da kai"
Bakin Alhajin na rawa ya ce "Ke nake muradi"
"Ka samu Alhaji na Shalele, menene tukyuicina"
"Faɗamun duk abin da ki ke so duniyar nan ko menene a yau ɗinnan za ki samu"
Fari Najmeer ta yi da ido kafin ta maida kallonta gaban motar "Benz nake so wadda ake ya yi"
Dariya Alhajin ya yi kafin ya ce "Wannan shine kawai abin da ki ke so? to zan haɗa miki da ƙaton gida me hawa biyu, ina son ki zamo mallakina Shalele"
"Na riga da na zama taka ɗan Shalele"
Cewar Najmeer tana murmushi.
"Kinga muna yita magana ban sanar da ke wanene ni ba....." Saurin katse shi Najmeer ta yi da faɗin "Bana buƙatar sanin ko waye kai, abin da na sani shine kai nawa ne"
Wani mugun daɗi ne ya kama Alhajin wanda sai washe baki yake.
"Amma na ganki tsaye anan ina zuwa ne?"
"Ohhh ina jiran Driver na ne, ya tafi karɓo mun wasu kuɗi a bayan layinnan"
"So kina nufin a gidan iyayenki ki ke?"
"Yes a gidan iyayena nake amma zan iya kwana a waje ba tare da Dad ɗina ya hana ni ba"
"Wow i like your stile yanzu ina muka nufa"
"Inda zaka tafi"
Najmeer ta faɗa cike da gajiya da magana, lura da hakan ne ya sa Alhajin zube mata dollers ɗin a hannunta sannan ya tada motar tare da barin gurin.
Sai da suka wuce unguwa uku kafin ya tsaya bakin wani danƙareren gida me masifar kyau da tsada, ba ƙaramin girgiza Najmeer kyawun gidan ya yi ba ta tabbata cewa gidan zai zuba kuɗi sosai.
Ba tare da Alhajin ya fito ba ya ɗauki wayarsa yana mai danna wata number, bugu biyu aka ɗaga, shuru ya yi da alama ana gaida shi ne daga ɗayan ɓangaren kafin ya ce "Lafiya ƙalau ka fito mun da takaddun gidannan ina bakin gate" Ba tare da ya jira abin da za'a ce ba ya katse wayar, Najmeer dai ta zuba ido tana kallon ikon Allah.
Ba jimawa wani Dattijo ya fito daga gidan ɗauke da takaddu a hannunsa, sai da suka ƙara gaisawa kafin ya miƙa masa saƙon, karɓa Alhajin ya yi sannan ya ce "Zaka iya tafiya gida yau already na yi kyauta da wannan gidan, amma zan kira ka next week sai na ga yanda za'ayi" Godiya Dattijon ya yi kafin ya bar gurin, Alhajin kuwa kallonsa ya maida kan Najmeer tare da miƙa mata Keys da takaddun gidan.
Cike da ƙasaita ta karɓa tana mai sakin murmushi "Thank you my Alhaj"
"Don't worry idan kina tare da ni za ki samu fiye da wannan, mu shiga daga ciki na nuna miki motarki da kuma yanayin gidan"
A tare suka shiga cikin gidan, gida ne wanda ya amsa sunansa, gaba ɗaya tsarin ya tashi hankali, duk wani abin da ake buƙata na more rayuwa akwai shi, pearking space suka nufa inda wasu bagaggun mota ke baje kusan guda biyar, kallonta Alhajin ya kuma yi tare da kama hannunta "Ki zaɓi ra'ayinki cikin wannan"
Najmeer duk ta gigice dan murna, da sauri ta ƙarasa gurin wata arniyar Benz me halakakken kyau maroon colour.
Ai kuwa ya miƙa mata key ɗin motar, da gudu ta ƙaraso tana mai faɗawa jikinsa dan murna, "Thank you Alhaj and nice to meet you, yanzu lokacina ne da zan faranta maka fiye da yanda ka faranta mun" Najmeer ta faɗa tana janye jikinta cike da makirci.
Sai da ta shiga motar ta zauna tsawon mintuna biyu kafin ta fito, "Ni zan koma gida saboda akwai aikin da ke gabana and na san yanzu haka ƴan Maula sun cika ƙofar gidanmu zan je na raba musu abin da ya dace"
"Okay mu tafi na sauke ki ko"
"No need my Alhaj, kawai ka faɗa mun numberka zan kira idan na isa"
"Number Alhajin ya bata kafin suka fito daga gidan, a bakin titi ya sauke ta sai da ta tabbatar ya yi nisa kafin ta tari adaidaita ta nufi gidansu.
Koda ta shiga gidan babu kowa har Maleek ɗin da ta barshi a kwance bata same sa ba, a gaggauce ta ɗora shinkafa da miya wadda ta ji kayan haɗi, lemun kankana da apple ta haɗa tare da jerewa a basket, ta san cewa yanzu haka Meera ta isa farkawa, wanka ta shige da sauri a lokacin an fara kiraye-kirayen sallar ƙarfe biyu, bayan ta fito ne ta yi sallarta sannan ta shirya cikin doguwar riga daidai gwuiwarta black me kyau an yi mata adon duwatsuna na gold, haɗaɗɗen gashin kanta ta ɗaure tana mai yafa ɗan ƙaramin mayafi, sannan ta fesa turarukka masu daɗin ƙamshi, ba ƙaramin kyau ta yi ba musamman yanda hips ɗinta da mazaunanta suka bayyana, sai da ta tabbatar ta haɗu ta ko'ina kafin ta ɗauki handbag ɗinta da basket na abinci ta fito tare da rufe part ɗinta.
Har wannan lokacin ma bata ga alamun Maleek ba kuma bata damu da halin da yake ciki ba, dirrect titin unguwar ta nufa ta samu adaidaita.
Sai da ta fara biyansa sannan ta shige daga ciki, mintuna kaɗan suka iso bakin hospital ɗin, da sauri Najmeer ta fito tare da nufar cikin asibitin.
A bakin ƙofa suka haɗe da Nurse ɗin da ta duba Meera, Najmeer ce ta fara gaisheta kafin ta ce "Ya me jikin? ina fatar ta farka ko"
"Jiki Alhamdulillah har ma ta ci abincin da Yayanku ya kawo mata"
Nurse ɗin ta faɗa tana barin gurin, mamaki ne ya kama Najmeer jin abin da aka ce, waye kuma Yayanmu, ta tambayi kanta a zuci, ganin ba me bata amsar ne ya sa ta nufi ɗakin da Meera ke ciki.
A zaune ta same ta tana shan kankana, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Najmeer kin dawo? sannu da zuwa"
Shuru Najmeer ta yi tana mai zama kan kujerar da ke gurin, cikin alamun zargi ta ce "Maleek ya biyo ki ne?"
A tsorace Meera ta ce "What are you saying? me kuma zai kawo Maleek a nan?"
"Kamar ya me zai kawo shi? bayan an ce mun akwai wanda ya kawo miki abinci"
Ɗan murmushi Meera ta yi kafin ta ce "Waye zai kawo min bayan ke? nima lokacin da na tashi a haka na samu waɗannan kulolin cike da girke-girke kala-kala, na zata ke ki ka kawo mun"
Jin abin da ta ce ne ya sa Najmeer zaro ido a mamakince "Tashi tashi mu bar hospital ɗinnan"
Ta ƙarasa maganar tana kama hannun Meera, ko ta kan abincin da ta kawo basu kuma bi ba suka fice daga hospital ɗin.
......................
A ɓangaren Sultal kuwa wayarsa ce kan kunnensa da alama da Girlfriend ɗinsa ƴar London yake waya, anan yake shaida mata cewar Dad ɗinsa ya amince da aurensu.
Sosai Maleeka ta yi murna jin wannan haɗaɗɗen labarin, sun jima suna fira wanda duk yawan firar babu daɗin ji saboda abin ya ƙazanta, a haka har Sultal ya samu natsuwa.
Ƙarfe uku na rana ya sauko parlourn ƙasa sanye cikin gajeren wando da singlet fara sai ƙamshi ke tashi a jikinsa, saurin dakatawa ya yi jin an yi hugging ɗinsa ta baya tare da shafo ƙirjinsa, da ƙarfi Sultan ya gimtse ido jin wani yanayin da ya shige sa, Sumayya da ke manne a bayansa ne ta juyo a hankali tana mai shafa fuskarsa, sannu-sannu Sultan ya buɗe rikitattun idanunsa ya sauke kan fuskarta, cikin mugun ɓacin rai ya ture ta daga jikinsa yana mai zabga mata wawan marin da ya sa da buga kanta a ginar da ke gurin, wata irin ƙara Sumayya ta saki jin zafin da ya shigeta, "Are you okay? do i look like your type? idan ki ka sake gangancin kallona ba ma taɓa jikina ba sai na kawar da ke a doron ƙasa, dabba kawai ɓace mun da gani tun kafin na tattake ki".
Da gudu Sumayya ta haura sama tana rusa ihu, kasancewar Dad sun fita da Junaid ne ya sa gidan ya yi shuru sai masu aiki, Mom kuwa tana part ɗinta.
Har ya juya zai koma sama ya ji wayarsa ta ɗauki ƙara, sunan Majeed ya gani kan screen ɗin hakan ya sa ya ɗaga ba tare da yace uffan ba, Majeed ne ya ce "Sultan an samu gidan da Shalele suke zama, yanzu haka ina tare da addrees ɗin...."
Tun kafin Majeed ya rufe baki Sultal ya ce "Kana ina yanzu haka?"
"Ina bakin gate ɗinku".
Ɗiffff Sultan ya kashe wayar, da saurin tsiya ya fito harabar tare da dakawa masu tsaron gidan tsawa "Ina buƙatar motoci ashirin yanzunnan"
Ai kuwa duk sun daburce nan take aka jere motoci ashirin a harabar gidan, be damu da kayan da ke jikinsa ba ya shige motar da ta fi kowacce ɗaukar ido sannan ya bada umarnin su tafi.
Kasancewar Majeed ya zo da motarsa ne ya sa ya shige gaba, motocin Sultan kuwa na bayansa, da mahaukacin gudu suka bar unguwar tare da nufar gidansu Najmeer.
*Mu haɗe a next page, ina ganin ƙorafin rashin typing kullum da kuma ƙorafi kan cewa na ƙara yawan typing wannan baya isarku, maganar gaskiya ita ce ba zan iya ƙara yawan typing ba, sai ma ragewa da zan yi, saboda ina ƙoƙarin yin typing sosai, kuma ina da ayyuka da dama a gabana ciki kuwa harda haddar alqur'an, ba rubuta littafi nr kawai nake ba, ba zan zauna yin typing kullum ba ku yi haƙuri da duk randa ku ka samu