Showing 9001 words to 12000 words out of 44092 words

Chapter 4 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt

21 Mar 2025

3813

fa? how will you come out?"




Sai da Sultan ya ɗauki mintuna biyu ba tare da ya ce komi ba, sai can kuma ya ce "Don't worry i'll call you, mu haɗe a bakin gate by 10:00pm".


Ya faɗa yana kashe wayar.




.....................
A ɓangaren Najmeer kuwa sosai Mamu ta rarrasheta har ta shirya cikin tsadaddun kaya masu masifar kyau, duk jikinta ya mutu mafita kawai take nema.




A lokacin gaba ɗaya wajen gidan ya cika da mutane, Kawu kam sai raba goro yake yana mai washe baki.


Bayan an gama sanarwa ne Kawu Jamilu ya nemi izinin shigowa gida dan ya faɗawa Mamu za'a ɗaura auren, ihun da ya ji ne ya sa shi ƙarasawa cikin gidan da gudu dan ganin abin da ke faruwa.


A ƙasa ya samu Mamu na rusa kuka kamar ranta zai fita, nan da nan gidan ya cika da maza domin kukan Mamu ya tsananta, Kawu Jamilu kuwa ba kukan ne damuwarsa ba sai wulla ido yake inda zai hangi Najmeer amma babu ita babu alamunta, a mugun fusace ya damƙi wuyan Mamu kamar zai kasheta yana faɗin "Ina shegiyar yarinyar nan ne? kar ki ce mun ta gudu dan wallahi baza ta saɓu ba".


Mutanen da ke gurin ne suka rirriƙe Kawu ganin da gaske kashe Mamu zai yi, ai kuwa ya rarumi icce ya rinƙa dukan mutane yana kiran sunan Najmeer, duk waɗan da ke gurin sun watse dan kar ya illata su, ɗakin Najmeer ɗin ya nufa dan tabbatar da gaskiya, ai kuwa ko tsinke a cikin kayanta bata bari ba, duk wata sutura da kayan kwalliyarta ta kwashe, kayan ɗakin ne kawai bata taɓa komi ba, wani irin ihu Kawu ya daka wanda yasa su Jabir da iyayensa shigowa ɗakin da gudu, nan suka tarar da abin da ya rafu, ai kuwa Jabir ya rarumi Kawu Jamilu ya damɓara shi a ƙasa, ji ka ke timmmmm, Bukar Mahaifin Jabir da ƴan uwansa suka rufa masa baya, sai da suka yiwa Kawu mugun dukan tsiya, da mahaukacin gudu Kawu Jamilu ya bar gidan yana mai neman ceto, bayansa Jabir suka bi suna mai zage-zage kamar zautattu musmaman Jabir wanda ji yake duk burin rayuwarsa ya lalace.




Mamu kuwa na ɗaki ta gaza zaune balle tsaye sai hawayen da ke rito kan kuncinta, kamar an ce ta kalli gefen pilo sai ga baƙar leda, da sauri ta ƙarasa tana buɗewa.


Kuɗaɗe ta gani masu yawan gaske, zaro ido ta yi dan ta san aikin Najmeer ne, ai bata gama mamaki ba ta ji sallamar yaro a tsakar gida, cikin hanzari ta ɓoye kuɗin tare da fitowa, ɗan ƙaramin yaro ne wanda zai kai shekaru sha uku zuwa sha huɗu, bayan ya gaishe da Mamu ya ce "Wai ga saƙo in ji Shalele" Bakin Mamu na rawa ta ce "Tana ina ne?"


Wata takadda yaron ya ciro a aljihun wandonsa ya warware sannan ya fara karantawa kamar haka "Ina mai ba ki haƙuri da kuma neman yafiyarki ga watsa muku ƙasa da na yi tare da tozarta ku gaban mutane, amma ina mai tabbatar miki cewa zan dawo gare ki idan lokaci ya yi, bayan haka zan rinƙa turo miki da duk abubuwan buƙata......." Kukan da Mamu ta fashe da shi ne ya sa yaron tsagaitawa, bayan ta rage sautin kukan ne ya cigaba da faɗin "Kar ku yi wahalar nema na, domin baza ku taɓa samu na ba, ina cikin garin Jos na kama gida har zuwa lokacin da Kawu zai canja ƙudirinsa a kaina, sannan kuma ya sa Jabir ya sake ni, na san cewa yanzu am ɗaura aurena da Jabir amma ba zan taɓa yi masa biyayya ba, kuma ba zan taɓa zama a ƙarƙashinsa ba, daga ƙarshe ina miki fatan alkhairi da kuma roƙonki da ki taya ni da addu'a".




Yaron ya ƙarasa yana miƙa mata takaddar sannan ya fice daga gidan, in banda karkarwa babu abin da jikin Mamu ke yi, tsoro fargaba da kuma tashin hankali ne kwance kan fuskarta, a haka ta ja jiki zuwa ɗakinta.






................
Najmeer kuwa tun da ta bar Unguwarsu ta nufi wata unguwa me suna Dutse uku wadda tana da nisa sosai da unguwarsu dan sai ka shiga mota, wani ƙaramin gida ta kama haya me ɗakuna biyu da toilet ɗaya sai kichen, babu abin da zaka rasa a gidan kama daga bed kujeru da kayan kitchen, cikin ƙanƙanin lokaci ta jere kayanta a wadrop sannan ta ƙara gyara ko'ina ta yi mopping, wajen ƙarfe bakwai na dare ta kammala.




Wanka ta shige dan jikinta duk ciyo yake mata, sai da ta haɗa da alwala kafin ta fito sanye da ɗan ƙaramin tawul daidai santala-santalan cinyoyinta masu kyau da jan hankali.


Haɗaɗɗen man shafawarta ta ɗauka cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shafawa tare da saka ƙaton hijab ta kabatarta sallah.


Sallamewarta ke da wuya ta fara jiyo ihu da kuka tare da maganganu iri-iri, dama part biyu ne a gidan daga part ɗinta sai na wasu a can gafe, kuma daga nan take jiyo kukan, babu alamun tsoro ta tattara hijab ɗinta ta nufi part ɗin dan ganin abin da ke faruwa.


Abin da ta gani ne ya mugun firgitata, wani matashi ta gani wanda zai kai kimanin shekaru talatin daga ganinsa kaga mashayi, duk jikinsa kaca-kaca abun ƙazanta, a ƙasa kuwa wata budurwa ce wadda baza ta haura shekarun Najmeer ba, iya ƙarfinsa yake zuba mata iccen da ke hannunsa, a ɗayan hanun kuwa kwalbar giya ce ya yi mankass, cikin mugun ɓacin rai Najmeer ta ɗauki wani tiren da ke gefe a ƙasa ta buga masa, ai kuwa ya saki ƙara tare da zubewa ƙasa a sume, budurwar na ganin haka ta tashi da sauri ta nufi Najmeer tana mai rungumeta, duk da cewar Najmeer na iya jiyo warin jikin yarinyar ama hakan be hanata rungumeta ba, duk tausayinta ya kama ta, a hankali Najmeer ta janye jikinta tana faɗin "Zo mu shiga ɓangarena kafin ya tashi"


Bayanta matashiyar ta bi har parlour, sai da Najmeer ta haɗa mata ruwan wanka wanda ta zuba turarrukan ƙamshi sosai, sannan ta ce ta shiga ta watsa ruwa, cike da murna matashiyar ta shige toilet dan rabonta da wanka yau sati ɗaya kenan.




Ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul ɗin da Najmeer ta miƙa mata, cike da mamaki Najmeer ke kallonta a ranta take faɗin, wai dama fara ce kuma haka take da kyau, matashiyar ce ta katse mata zancen zucin da faɗin "Thank you so much and i can't forget the way u help me from that wicked Man"


Ƙura mata ido Najmeer ta yi dan bata san abin da ta ce ba, lura da hakan ne ya sa matashiyar zama a hankali tare da dafa Najmeer ta ce "Can you speak english?" Kasancewar Najmeer ta san wannan kalmar ne ya sa ta girgiza kai alamun bata jin turanci, murmushi matashiyar ta yi a karo na farko kafin ta ce "Da farko sunana Meera, ni ƴar garin Maiduguri ce, iyayena sun rasu dalilin wasu ƴan ta'adda da suka shigo garin, duk a cikin Family na babu wanda suka bari sun kashe mun kowa, ni ɗaya ce na rayu sannan na baro garinmu na dawo nan garin da zama, a lokacin da na shigo dubu ɗaya ce kawai ta rage mun kuma gashi dare ya yi, ina cikin tafiya na haɗu da wannan bawan Allah me suna Maleek, daga nan ya ce zai taimaka mun idan har ina so, a lokacin ba wani wayo ne da ni ba yasa na amince masa, ya kawo ni wannan gidan wanda a ranar ya keta mun haddina, na yi kuka marar iyaka tare da nadamar rayuwa, tun daga ranar Maleek ya mayar da ni kamar matarsa, kuma haka zai je ya sha giyarsa ya dawo ya mun dukan tsiya, wasu lokutan a hospital nake tsintar kaina, yanzu maganar da nake miki na zama cikakkiyar Karuwa me zaman kanta, shekaruna sha bakwai ina cikin sha takwas, zan iya sanin ko ke wacece?"




Meera ta faɗa tana kallon Najmeer da idanunta sun ciko da ƙwalla, sai da ta kai kusan mintuna uku kafin ta ɗago tana kallon Meera "An kira sallar isha, mu fara yin sallah kafin lokaci ya tafi"


"No bana sallah wahala take mun, ke ki yi kawai"


A mugun tsorace Najmeer ta ce "Sallar ce ke miki wahala?"


Itama Meera a tsoracen ta kalli Najmeer jin yanda ta ɗaga murya, "Yes ita ce ke mun wahala, sai ranar da na ji ina ra'ayi nake yi"


"Ya subhanallah"


Cewar Najmeer tana zama kusa da Meera tare da kama hannunta "Meera kin san hukuncin wanda ke wasa da sallah kuwa?"


Girgiza kai Meera ta yi alamun bata saniba.


Cike da basira Najmeer ta cigaba da faɗin "Meera a matsayinki na mace kuma wadda ki ke fatar Allah ya shiryi rayuwarki domin ki gina sabuwar rayuwa be dace ki kasance marar bautawa Allah ba, gara ma a ce bakya sallar gaba ɗaya da a ce kina wasa da ita, saboda wutar me wasa da sallah ta fi azaba fiye da wanda baya yi gaba ɗaya, kamar masu haɗa sallar asuba da ƙarfe biyu har ma sallar ƙarfe huɗu, Meera ina son ki sani cewa sallar da za ki rinƙa yi kina faɗawa Allah damuwarki zai iya silar shiriyarki, dan Allah ki yi mun alƙwarin baza ki ƙara wasa da sallah ba, saboda bana son ki tashi ranar lahira cikin mutanen da za'a saka su a wutar da ta fi kowacce azaba".




Jikin Meera ne ya yi sanyi jin kalaman Najmeer, sai a lokacin take fara nadamar rashin yin ibadah, kuma take ganin wasu matsalolinta sun haɗa da rashin bautawa Allah, saboda Ubangiji yana rabuwa da duk wanda ya daina saka shi a lamuransa.




"Na gode sosai kuma na yi miki alƙwarin daga yau zan cigaba da ibada, amma ba ki faɗa mun sunanki ba"


"Sunana Najmeer, ki tashi ki yi alwala bari na fito miki da hijab"


Miƙewa ta yi tana mai buɗe Wadrop ta ciro ƙaton hijab, ita kuwa Meera ta shiga toilet dan ta yi alwala.




Bayan ta fito ne Najmeer ta shiga ta sake canja alwala itama.




A tare suka kabbarta sallah, abin tashin hankalin shine gaba ɗaya Meera bata iya sallah ba, bayan sun gama Najmeer ta yi mata gyara sosai kafin suka cigaba da fira, duk iya wayon Meera dan ta san labarin Najmeer amma ta kasa samun dama, domin daga ta kawo zancen Najmeer ke saurin canja wani topic, a haka har tara na dare ya buga, Najmeer ce ta ce "Meera akwai shagon da ake sayar da kayan abinci a kusa haka?"


"Yes akwai da yawa ma, akwai abin da ki ke so ne?"


Miƙewa tsaye Najmeer ta yi tana faɗin "Eh mu tafi ki raka ni"


Itama miƙewa Meera ta yi tana nufar ƙofa, wani kallo Najmeer ta yi mata me kama da ina zuwa haka, sai kuma ta cire hijab ɗin da ke jikinta dama daga ita sai wata riga ta roba daidai gwuiwoyinta, riga ce me masifar kyau da ɗaukar ido red colour, gashin kanta ta sake shi ta baya tana mai gyara zaman rigar, duk abin da take Meera ta zuba mata ido daga bakin ƙofa tana kallon ikon Allah, ita kuwa Najmeer ta nufi ɗan ƙaramin trolynta ta ciro wando da riga masu kyau da tsada ta jefawa Meera, "Ki saka wannan dan baza ki fita da ni a cikin wannan ƙaton hijab ba.


Baki sake Meera ke kallon Najmeer, a haka har ta gama saka kayan, wando ne da kaɗan ya wuce gwuiwar Meera, sai rigar me gajeren hannu, kayan sun bala'in amsarta kasancewarta fara.


Ai Meera bata sake tsinkewa da lamarin Najmeer ba sai da taga sun fito a haka, a tsakar gida suka sami Maleek zaune yana dafe kansa, bishi-bishi yake kallonsu har suka fice daga gidan.




Tun da suka fara tafiya mutanen unguwar ke kallonsu, musamman Najmeer kamar zasu haɗiyeta da kallo.


A wani haɗaɗɗen shago suka shiga me girma, ba ɓata lokaci suka zazzaɓi kayan abinci masu yawa da tsada, duk abubuwan buƙata sai da suka ɗauka, a wajen shagon suka kira almajirai dan su kwashe musu kayan, lokacin da suka shigo goma daidai ta buga na dare, kuma lokaci ɗaya alarm ɗin wayarta ya fara ƙara.


Cikin gaggawa ta sallami almajiran sannan ta faɗa bayi, wani sabon wanka ta kuma yi sosai ta haɗe cikin wando da riga masu rikitattun kyau, duk da cewar Meera mace ce amma sai da ta kasa ɗauke idanunta daga kallon Najmeer, wandon kuwa da kaɗan ya wuce mazaunanta, a ƙasansa akwai rabaja sai rigar marar hannu me tsage ta baya, Najmeer na murmushi ta miƙowa Meera wasu kayan, itama cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya tana faɗin "Ina zamu je ne? gaskiya lamarinki abun tsoro da mamaki ne"




"Hmmm Meera kenan, a sannu za ki san ko wacece ni, inda zamu je kuwa be wuce Clup ba, na kwana biyu ban tafi ba kuma na san Guys ɗina sun yi missing ɗina sosai" Ihu Meera ta saki dan murna tana faɗin "Ki ce kema ƴar harka ce, gaskiya na ji daɗin haɗuwa da ke, nima ina zuwa Clup amma wanne ki ke zuwa?" Meera ta faɗa tana fari da ido.






"Secret Clup idan muka tafi za ki gani"


Daga haka Najmeer bata kuma cewa komi ba har suka gama shirinsu, sosai ta yi ɓarin turare a jikinta, ita kanta ta san bata taɓa yin kyau idan zata je Clup kamar yau ba.


Wasu arnayen takalma suka saka masu tsayi da kyau, Meera ce ta fara fita kafin Najmeer, sai da ta tabbatar ta rufe ko'ina na part ɗinta kafin ta saka keys ɗin a handbag tana mai nufar inda take jiyo surutun Maleek da Meera, da sauri ta ƙaraso ta shiga tsakaninsu "Lafiya dai Malan? wallahi kar hannunka ya yi izgilin taɓa jikinta idan ba haka ba sai na wulaƙantaka a garinnan" Najmeer ta faɗa a tsawace.


Gaba ɗaya Maleek be san abin da take faɗa ba, dan shi kyawunta da kyawun dirinta ne ya tafi da imaninsa har ta gama masifa ta ja hannun Meera suka fice daga gidan, da gudu ya bi bayansu yana kiran sunan Meera.




Shan gabansu ya yi a fusace ya damƙo gashin kan Meera tare da matsewa "Ke dan ubanki ina zuwa? har ni wannan Aljanar ƙawar taki zata gayawa munanan kalamai"


Cike da jin zafi Meera ta ƙwalla ƙara tana bashi haƙuri, wani gigitaccen marin da Najmeer ta watsa masa ne yasa shi sakin gashin a ruɗe tare da duba wanda ya mare shi, sai da ya kai mintuna biyu a haka kafin kunnensa ya dawo daidai, "Uban waye ya mareni? na ce wani ɗan hegiyar ne ya gallaramin mari"


Yanda yake ɗaga murya da zage-zage ne ya sa mutane taruwa gurin ana kallonsu, cike da gadara Najmeer ta kama hannun Meera tana nuna shi da yatsa "Wannan ya zama na ƙarshe da zaka kai hannunka jikin Ƙawata, idan kuwa ka ƙara jahilin gangancinnan sai dai Uwarka ta haifi wani amma ba kai ba" Ta ƙarasa maganar tana jan hannun Meera suka bar gurin, ihu da shewar mutane ne ta cika gurin, dan Samari da dama sun kamu da son Najmeer musamman yanda ta fara takawa Maleek burki a Uguwar kasancewar ya hana kowa shan iska, "Ku kuma Uwar waye ku kewa shewa anan?" Ya faɗa yana rarumar abun da zai dake su, da gudu kowa ya watse dan tsoron kar ya illata su.




A Restaurant suka fara zuwa dan gaba ɗayansu yunwa suke ji, a lokacin da suka shiga babu kowa sai masu sayar da abincin, dan haka suka yi Oder Julof na indomie wadda ta sha ƙwai, sai naman kaza da kuma drinks, rabon da Meera ta ci naman Kaza har ta mance, ai kuwa ta zage damtse ta ci har ta ture, Najmeer dai sai kallonta take tana murmushi.




Ƙarfe sha ɗaya ta yi musu ne a bakin Clup ɗin, tun daga waje ka ke jin ƙarar sauti na tashi, tabbas gurin ya tsaru wanda ƙarya ne kaga ɗiyan talakawa a nan, ido Meera ta waro da mugun firgici bakinta na rawa take nuna sunan Clup ɗin "Soultan Clup......."




"Yes Soultan Clup, wani abun ne ya faru?".


Najmeer ta tambaya.


Meera da duka ta daburce ta ce "Kin san waye Sultan kuwa, kin san waye Ubansa, kin san waye shi kuwa?"


Meera ta jero mata duk wannan tambayoyin a lokaci ɗaya tana ƙoƙarin komawa da baya, a fusace Najmeer ta damƙo hannunta a lokacin idanunta sun koma dark blue, gaba ɗaya farin idonta ya ɓace, cikin yarda da kai ce "Meera wannan ba shine lokaci na farko da na taɓa zuwa ba, asalima abokin me Clup ɗin muna shiri da shi sosai, me Clup ɗin ne kawai ban taɓa gani ba kuma ban san shi ba"


Ajiyar zuciya Meera ta sauke tana mai kawai da kai gefe ganin yanda idon Najmeer ya canja, ba tare da fargabar komi ba suka shige, cike da ƙasaita Najmeer ke taka steps kamar yanda ta saba.




Ba ƙaramin tsaruwa Clup ɗin ya yi ba, daga ƙofar shiga wasu manya manyan majiya ƙarfi ne suka nufo su, amma suna ganin Najmeer suka basu hanya cikin girmamawa har ma ɗayan na faɗin "Allah ya ja da ran Shalelen Alhazawa, ke ba sa'arsu ba ce ta manya ce, ke ɗin tauraruwa ce me haskaka duk wanda ya yi arba da ke"


Jin yanda ake zuba mata kirari ne ya ƙara ba Meera mamaki, Najmeer kuwa ta ciro kuɗaɗe ƴan dubu-dubu ta fara zuba musu, nan fa kirari ya ƙara yawa har mutanen da ke ciki suna jin yanda ake koɗata, hakan ya ƙara tabbatar musu cewa Shalele ta shigo, cikin sauri Majeed ya fito wanjen dan ganema idanunsa, ai kuwa ya yi arba da ita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙaraso suka rungume juna tare da kashe hannu, "Hi Shalele, gaskiya mun yi kewa sosai, ni na tabbata za ki shigo yau shiyasa ma na yiwa Oga na arbishir da samunki" Wani irin fari da ido ta yi tana mai faɗin "Waye kuma wannan da ba zai iya zuwa da kansa ba har sai ya turo ka?"


"Friend ɗina ne kuma shine me wannan Clup ɗin".


"Friend ɗinka fa ka ce? kaga na yi kama da wadda zata yi harka da low class masu irin shekarunka......"


Saurin rufe mata baki Majeed ya yi "Hold on Shalele dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login