Showing 39001 words to 42000 words out of 44092 words
Chapter 14 - Shalelen Alhazawa Book Document By Asmeetar Hydar .txt
komi na bikinki har da gidan da za ku zauna ke da mijinki, kuma na ɗauki nauyin komi naki ke da Kakarki za ku dawo gidana da zama duk abin da ku ke buƙata ki min magana, na lura sosai akwai babban al'amari tattare da ke"
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Kina makaranta ne?"
"Primary kawai na yi daga nan ban ƙarasa ba, a gefen islamiyya na yi haddar alqur'an da sauran littafai" Ba ƙaramin burge Dad ta yi ba jin ta yi karatun islamiyya sosai.
"Ya sunanki?"
Ya sake tambayarta.
"Sunana Najmeer"
"Masha Allah Najmeer daga yau kin zamo ƴata kuma na yi alƙwarin riƙe ki hannu bibbiyu, yanzu ku koma gida amma kafinnan ki bani address ɗin gidanku zamu shigo zuwa gobe"
Godiya sosai Najmeer ta yi masa tare da bashi address ɗinsu, haka kawai take jin Dattijon har cikin ranta, a zuciya take faɗin amma Sultan ya yi sa'ar Mahaifi ba kamar shi me mugun hali ba.
Sai da ta rufe fuska kafin suka fito daga ɗakin.
Ba su Meera ba hatta su Junaid sun sha mamakin ganin Dad da Najmeer na saukowa cikin fara'a da annashuwa kuma ba komi a hannunta alamun bata karɓi kuɗin da ta ce ba.
Ai basu ƙara tsinkewa ba sai da suka ga Dad ya ce "To sai da safe a gaida mutan gida"
Najmeer na murmushi ta ce "Mutan gida za su ji Alhaji"
Ɗan ɓata fuska Dad ya yi alamun ya yi fushi "Kar ki sake kirana Alhaji ki kirani da Dad kamar yanda sauran Ƴan uwanki ke kira na"
"Afwan Dad ba zan ƙara ba"
"Yaww Allah ya yi miki albaka"
"Ameen Dad" Najmeer ta amsa tana mai kallon su Meera ta ce "Mu tafi ko" Ficewa daga gidan ta yi su Malik na bayanta kamar raƙumi da akala cike da al'ajabi.
Sultan ne ya ce "Dad me nake shirin gani, kana nufin wannan ƴar fashi ka ke kira da ƴarka?"
Kusa da Mom Dad ya zauna yana faɗin "Ƙwarai kuwa labarinta abin tausayi ne, shiyasa na yanke hukuncin dawo da su gidana tare da ɗaukar nauyin aurenta saboda shine dalilin da ya sa ta shiga wannan halin"
"Wallahi ba zai taɓa yuwa ba, babu wanda zai kawo mana ƴar fashi cikin gida" Mom ta faɗa a zafafe.
Junaid de ya kasa furta komi sai kallonsu da yake, tashi Dad ya yi yana mai gyara zaman rigarsa "Magana ta rage gareku hukunci na yanke ba wanda ya isa ya karya dokar da na shimfiɗa, dole su dawo gidana da zama"
Ba tare da ya kuma cewa komi ba ya nufi room ɗinsa.
Mom na masa magana amma ko gefen da take be kalla ba, bayansa ta bi tana kiransa tare da faɗin ba wanda zai kawo musu ƴar fashi cikin gida amma Dad ko a jikinsa sai ma shigewa ɗakinsa da ya yi.
Tsananin takaici ne ya hana Junaid ɗagawa daga inda yake Sultan ko sai huci yake kamar kumurcin maciji.
Su Najmeer kuwa tun da suka fara tafiya ba wanda ya ce ƙala har suka iso ƙofar gidansu Malik, anan Najmeer ta tura masa kuɗin da ta yi masa alƙwari har ma da ƙari, sosai ya rinƙa yi mata godiya tare da sauran samarin.
Barin gurin suka yi ganin ukun dare ya yi, gudu Najmeer ke yi kan titi har suka iso gida, Meera dai ta aje tambayoyinta dan ta san baza ta samu amsa a yanzu ba.
A gajiye ta shige toilet dan watsa ruwa ga ciyon kai da ke damunta, nan kuma ta ji tunanin Prince ya faɗo mata a rai lokaci ɗaya ta saki murmushi tana mai lumshe ido, a hankali ta furta "Miyar yauƙi....." Yanda ta ja sunan ne ya bata dariya ai kuwa ta shiga dariya ita ɗaya a bayi, ta ɗauki mintuna goma kafin ta fito tana mai tsane gashin kanta.
Kan kujerar da ke gaban mirrow ta zauna sannan ta fara shafa mai, a hankali Meera ta ɗago tana faɗin "A gaskiya lamarinki na rikitani Najmeer"
"Meyesa ki ka ce hakan?"
"Kin san abin da nake nufi ai, shi kuma Dad ɗinsu Sultan a ina ki ka san shi? ko yana cikin Alhazawanki ne"
Bushewa da dariya Najmeer ta yi "Wai dama duk wannan ya sa ki ke faɗin haka? mtsss ni fa ko saninsa ban yi ba kawai taimaka mana zai yi"
Duk abin da ya faru Najmeer ta kawashe ta sanarwa Meera, cikin kiɗima Meera ta ce "Mun shiga uku kina nufin gidansu Sultan zamu koma da zama? ai kuwa akwai babban tashin hankali marar ƙarshe"
"Ke dallah Malama babu wani tashin hankali sai dai ayi ta gwarama duk rana ta Allah, dan ba zan raga musu ba har uwarsu me ɗaure musu suna yanda suke so, ke har Junaid sai na koya masa hankali a gidannan dan bawa zan maida shi"
Dariya Meera ta fara har da riƙe ciki "Junaid ɗin ne za ki mayar bawa? lallai akwai yaƙi a gabanki"
"Au kina ɗauka ba zan iya ba kenan? ai zamu gani sai ki zuba ido tun da tare da ke zamu zauna a gidan sai kin ce na faɗa miki"
Jinjina kai Meera ta yi "Hmmm nikam zan ga chakwakiya Sultan Junaid Meera a gida ɗaya ai kuwa sai gidannan ya kama da wuta"
"Hhhhhhh kin ga Meera barni haka dan Allah bacci nake ji gobe zamu ƙarasa wannan zancen" Najmeer ta faɗa tana mai hayewa kan bed.
..........................
A gefen su Sultan kuwa yau tun da garin Allah ya waye Mom ta hana masu aiki girka komi a gidan, Sultan da Junaid ma a office suka karya, Dad kam be ƙara bi ta kanta ba dan ya san duk wannan abin da take saboda su Najmeer da zai kawo gidan ne.
Har yamma ta yi Mom ta kasa samun natsuwa, wayarta ta ɗauka tare da latsa numbern ƙawarta Hajiya Halima bugu ɗaya ta ɗaga tana mai faɗin "Da girman kujerarki manya-manya maganin ƙanana"
Cikin damuwa Mom ta ce "Hajiya Halima ina da damuwa wallahi na rasa yanda zan ɓullowa wannan lamarin?"
"Subhanallahi me yake faruwa ne? fatar dai ba aure Alhaji zai ƙara ba?"
Mom ne ta ce "A a ko ɗaya amma kamar auren ne, dan duk wanda zai kwaso maka talakawa ƴan fashi da makami ya kawo cikin gida ai kamar kishiya ce ya ƙaro maka"
"Banganeba Hajiya Salma ki yi min yanda zan fahimta" Sai da Mom ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kwashe duk abin da ya faru ta zayyanawa Hajiya Halima.
"Kutumar ubancan, yanzu Alhajin ya rasa waɗan da zai kawo gidansa sai yarinyar da ta tashi kasheki da ƴaƴanki? wai tsaya ki ka ce ya maidata ƴarsa, bakya tsoron ya tattara dukiyarsa ya mallaka mata"
A rikice Mom ta ce "Ƙarya ne wallahi ai baza ta saɓu ba, idan har suka shigo gidannan da ƙafarsu za su koma dan sai na hana su zaman lafiya"
"Yawwa ƙawata ki hana su shan iska dan lamarinnan ya fi a zuba ido dole ki tashi tsaye tun kafin a rabaki da kowa naki"
Cewar Hajiya Halima tana mai ɗaga murya, sosai maganganunta suka shigi Mom har ta ƙara jin ƙarfin gwuiwa.
Sallama suka yi a kan cewa za su yi waya anjima.
Junaid ne ya shigo Sultan na rufa masa baya da alama daga aiki suka fito bakinsu ɗauke da sallama, yau an yi sa'a Sultan har da gaisuwa.
A gajiye Junaid ya ce "Mom ina wuni?"
"Lafiya ina Dad ɗin naku? ko da yake Sultan kai zan tambaya tun da a guri ɗaya ku ke"
Kallon Junaid Sultan ya yi alamun ya faɗa ko ya yi shuru, Mom ce ta kuma cewa "Sultan magana nake ina Dad ɗinku?"
"Ya tafi ɗauko ƴar fashi da ahalinta"
Sultan ya faɗa yana mai barin gurin, salati Mom ta rafka har da tafa hannu "Shikenan za su raba ni da mijina, saura kuma ƴaƴana da alama wannan shegiyar yarinyar masifa ce a rayuwarmu tun da har an fara ta kan uban ƴaƴana"
Junaid ne ya ce "Mom please ki kwantar da hankalinki Dad ya ce yarinyar nan ba halinta ba ne kuma ya ce aure ma zata yi"
"Kai amma shashasha ne marar tunani, kana ganin za'a raba ku da dukiyar mahaifinku amma ko a jikinka"
"Ki gafarceni Mom amma a ganina kamar taimako ne wannan"
"Taimakon ubanka na ce taimakon ubanka zai yi? ba dan Allah ya sa ina da rabon shan ruwa ba da yanzu na daɗe da mutuwa, a gaban idonka shegiyar yarinyar ta ɗoran bindiga a kai amma ka ke faɗin taimako tashi ka bani guri tun kafin ranka ya ɓaci, na lura kaine ka biyo halin uban naka gurin taimakonku wata rana sai kun haɗu da Aljana"
Mom ta ƙarasa maganar rai ɓace, haƙuri Junaid ya bata kafin ya nufi room ɗinsa, sanin cewa duk abin da zai faɗawa Mom a yanzu baza ta saurare shi ba balle ta yarda.
Dad kuwa har bakin gate ɗin suka isa tare da horn gate Man ya buɗe musu dan Najmeer ta faɗa masa cewar tana da baƙo, motoci hamsin ne masu uban kyau da ɗaukar ido, har pearking space suka isa sosai mamaki ya kama Dad ganin gidan da su Najmeer ke ciki.
A parlour Maryam ta masa rakiya tare da zube masa kayan abinci kala-kala, dan Najmeer ta dawo da Maryam nan gidan kafin su koma nasu gidan.
Ruwa kawai Dad ya sha dan baya jin yunwa, ba jimawa Meera da Najmeer suka shigo sai Mamu da ke bayansu, Najmeer ce kawai ta yi shigar banza dan wando ne daidai santala santalan cinyoyinta da ƴar ƙaramar riga me gajeren hannu, ba ƙaramin kyau shigar jikinta ta yi mata ba, kallo ɗaya Dad ya yi mata ya sauke kai ƙasa, Mamu kuwa har ƙasa ta tsuguna tana gaishe shi da sauri Dad ya miƙe yana mai faɗin "Haba Hajiya dan Allah ki miƙe ai ni ne ya dace na gaisheki, fatar mun sameku lafiya?"
Bakin Mamu na rawa ta amsa da "Lafiya ƙalau Cheif ya jama'a da hidima" Sai da Dad ya yi murmushi kafin ya ce "Alhamdulillah, amma Hajiya ya aka yi ki ka sanni har haka" Caraffff Mamu ta karɓe da cewa "Ai Najmeer ce ta ce za ka zo gidanmu a yau, na zata ƙaryar da ta saba ce ta sharara min ashe lamarin azimun ne, Allah ya yi da rabon zamu gana"
"Masha Allah abin da jikanyarki ta faɗa miki gaskiya ne tashi ki zauna kan Kujera" Dad ya faɗa yana nuna mata guri, Najmeer da Meera ko suka gaishe shi cikin girmamawa, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Najmeer je ki saka hijab ki dawo" Har zata yarfa masa magana sai kuma ta kasa saboda gwarjinin da ya yi mata, dole ta sa ta nufi room dan ɗauko hijab ba dan tana so ba.
Sanye cikin ƙaton hijab ɗinta ta fito tana tura baki, anan ta samu Mamu sai zuba zance take babu abin da bata sanarwa Dad ba har da auren da Najmeer zata yi da kuma iyayen ƙarya da ta hayo, sosai Dad ya girgiza jin cewar Najmeer ƴar bariki ce, a ransa ya ce shiyasa bata kunyar irin wannan shigar, kusa da Meera ta zauna tana mai haɗe fuska.
Sai da Dad ya ƙare mata kallo kafin ya ce "Najmeer gaskiya kin aikata babban kuskure, kuma kina cikin aikatawa, ina ki ka taɓa ganin mace ta sakawa kanta rayuwar ƙarya irin haka? bakya tsoron mijin da za ki aura ya gane ke wacece?"
Sunkuyar da kai Najmeer ta yi alamun kunya, sai kuma ta ɗago tana mai kallon Dad idanunta sun ciko da ƙwalla "Wallahi ban taɓa aikata zina ba, kuma bansan daɗin zina a rayuwata ba, ko wannan abin da nake ba yin kaina ba ne, addu'ar ku kawai nake nema amma ba zan iya daina yawo da rayuwar ƙarya ba ko da kuwa aure na yi"
"Hehehe haukar banza waye ki ke cewa ba ki taɓa aikata zinar ba? je ki faɗawa shashashu amma ba mu ba, wasu lokutan ko gida bakya kwana kina can gurin yawonki na banza da wofi shine za ki ce ba ki taɓa kwana da namiji ba, ashe haihuwar jiya-jiya ce mu da ki ke faɗa mana shirme"
Mamu ta faɗa tana mai jan dogon tsaki, Meera ce ta ce "Ni shaidata ce Najmeer bata taɓa aikata zina ba, saboda yanda take riƙo da addini ba zai barta ta aikata wannan babban laifin ba saboda ita sallah ma tana ƙarawa bawa imani a ransa musamman idan yana yinta cikin lokaci"
Harara Mamu ta gallawa Meera "Yooo ai duk halinku ɗaya kawai ƙarya ce Najmeer ta fiki iyawa da kuma wayewa, amma yanzu zata iya buga waya ta ce gasu nan hanyar zuwa wata ƙasar ita da ƴan gidansu alhalin ko hanyar da jirgi ke bi bata saniba" Dariya su Dad suka kwashe da shi har da Najmeer jin abin da Mamu ke faɗa, kuma sai ta haɗe fuska sosai tana ɓaro zance.
Dad ne ya ce "Okay yanzu dai shikenan, ni kaina duk da cewar daga jiya zuwa yau na san wannan jikanyar taki amma zan iya yarda da abin da ta faɗa, kuma na yanke shawarar za ku koma gidana da zama amma da sharaɗi"
"Faɗi sharaɗinka Alhaji da yardar Allah zamu kiyaye"
Cewar Mamu cikin zumuɗi.
Gyara zama Dad ya yi kafin ya maida kallonsa kan Najmeer ya fara da faɗin "Da farko za'a tsayar da maganar aurenki har lokacin da ki ka fara makaranta ina son ku shiga School ke da wannan ƙawar taki na ji kakarki ta ce sunanta Meera, sharaɗi na biyu za ki daina kwana waje har abada, sharaɗi na uku za ki daina ƙarya"
Waro ido Najmeer ta yi sai kuma ta girgiza kai alamun baza ta iya ba, "Nikam ba zan daina kwana waje ba, kuma bana son makarantar da za ka saka ni zancen ƙarya kuma sai dai idan ba'a kirani ba"
Meera da ke gefe ne ta danne dariyarta ganin Najmeer ta dage baza ta daina halayyarta ba, ajiyar zuciya Dad ya sauke kafin ya kuma cewa "Dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan matsayin ƴata da na ɗaukeki" Kallonsa Najmeer ta yi sai kuma ya bata tausayi, cikin shagwaɓa ta ce "Zan daina insha Allah amma sai kun bini a hankali saboda shi me hali a sannu yake dainawa"
"Shikenan na gode, zancen auren fa?"
Dad ya faɗa yana murmushi.
"Shima na fasa har sai na fara school, amma ni zan zaɓawa kaina makarantar da nake so"
"Okay fine duk makarantar da ki ke so zan saka ki da yardar Allah, ku shiya komi naku zuwa gobe zan turo a je da ku gida"
Cikin farinciki Najmeer ta rinƙa masa godiya, barin Mamu wadda har da kukanta, itama Meera ta masa godiya sosai da kuma addu'a.
Har gurin motocinsa suka yi masa rakiya kafin suka dawo ciki.
Tun a parloun Mamu ke sakawa Najmeer albaka, "Ƴar nan kin gama biya min Allah ya jiƙan magaba, wai yau ni ce zan shiga gidan Chief shugaban masu kuɗin garin Jos" Sai kuma ta ƙara fashewa da kuka har da kwanciya a ƙasa, taɓe baki Najmeer ta yi "Wai ke Mamu meye haka ne? idan na ga dama sai na ce ba inda zamu tafi"
Zumbur Mamu ta miƙe kamar zararra "Amma kin cika ƴar baƙin ciki me mugun hali, da farko kin cewa Cheif baza ki daina halayyarki ba yanzu kina faɗin za ki fasa zuwa gidan, idan kin fasa bakya wa Allah"
"Haka ki ka ce ko? shikenan na fasa zuwa"
"Au da gaske ki ke kenan? har da ƙara maimaitawa"
"Dama a zatonki ƙarya ne, yanzu ma zan bar gidannan sai na yi kwana uku kafin na dawo akwai wani suger Daddy wanda nake son mu shaƙata da shi"
"Waye kuma Sugari Daddyn?"
"Suger Daddy aka ce ba Sugari Daddy ba, saurayina kenan amma kuma ya haifeni a shekaru"
Najmeer ta faɗa tana mai jifa da hijab ɗin jikinta dama ya dameta sosai.
Bata jira abin da Mamu zata ce ba ta nufi room ɗinta tare da juya hips kamar wadda ke yin hakan da saninta.
...........
Tun a harabar gida Dad ya hangi Mom riƙe da ƙugu sai huci take har motocinsa suka tsaya, ba tare da ya ce uffan ba ya nufi hanyar parlour fuskarsa a ɗaure, ganin ba wanda ke biye da shi ne ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana mai bin bayansa, "Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya"
"Da ban dawo lafiya ba za ki ganni?"
Dad ya faɗa a taƙaice.
"Laifin me na yi haka? da ake ƙoƙarin sauke haushi kaina"
A fusace Dad ya juyo fuskarsa babu alamar wasa ya nunata da yatsa "Ki maida hankali ki saurareni da kyau Salma, na lura daga jiya zuwa yau akwai abin da ke damunki wallahi ki shiga hankainki bana cikin irin mazan da matansu ke juya su, idan har kina son zaman lafiya dole za ki girmama duk wanda na kawo gidannan a matsayin nawa"
"Amma Alhaji......." Saurin ɗaga mata hannu ya yi "Ban son jin komi daga gareki, in kina son zaman lafiya ki tabbata cewa gobe idan baƙina suka zo ki kama girmanki a matsayinki na uwa" Barin gurin ya yi cike da takaicin hali irin na matarsa, a rauwarta bata ƙaunar talaka balle wani ya zo gidanta.
Saukowar Sultan ne ya sa ta maida kallonta gurinsa, sanye yake cikin jallabiya fara me kyau gashin kansa ya sha gyara tamkar ba shi ba, ƙamshin turarensa ne ya baje gaba ɗaya parlourn har ya ƙaraso inda Mom ke tsaye kamar an dasa ta.
Ƙarar bell ɗin ƙofar ne ya sa Sultan faɗin "Majeed come in"
Shigowa Majeed ya yi bakinsa ɗauke da sallama, gaida Mom ya yi ta amsa sama-sama tana mai barin gurin jiki na rawa, dan har yanzu ba wani sakewa da Sultal ɗin ta yi ba.
Hannu Majeed ya miƙa ma Sultan suka tafa, "Guy wallahi yunwa nake ji please a kawo min wani abun kafin a kira sallar magrib"
Sai da Sultan ya hararesa kafin ya ce "Zan yi maka dan Allah ba dan ka isa ba"
Kichen ya nufa Majeed kuwa ya haura ɗakinsa yana dariya.
A hankali ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama jikinsa ne ya hau rawa bakinsa kuwa ya shiga ɓari kamar wanda aka kunnawa lantarki ganin Zakanya zaune tsakiyar ɗaki tana mai kallon ƙofar, suna haɗa ido da Majeed ta yi saurin ɓacewa daidai lokacin da Sultan ya ƙaraso gurin da gudu hannunsa ɗauke da basket, da ƙarfi ya janyo Majeed ta baya, a mugun tsorace Majeed ya ja dogon numfashi gami da sumewa