Showing 24001 words to 27000 words out of 119289 words
Allah ya kaimu zamu ga kuka ashe? Nace sosai ma ai farilla ne na fashe da kuka,Asif Yana ta dariya,Hamziyya tace banga laifinki ba,nace karfa kice na manta da dukan da nace Zan miki ba aure ba ko haihuwa nayi sau talatin Ina nan akan baka na duk Sanda na samu lokaci Allah sai na naci ubanki harda Maggi,Muna dariya Hamziyya tace ko Mene kiyi tunda ya bawa Aunty Haleesa babban matsayi Albashi dubu dari duk wata ai ko balla ni kika Yi ban fadi ba,matar fa Wanda ya bawa Yaya ta Aiki ai ba matsala, Asif Yana jinmu sai dariya yake har kofar gidan da Ango yake da abokansa yayi parking
duk suna ciki matasa da dangina dana ango Yan Mata da samari ana jira na.
Muna Fitowa su Kadada Suka narka wata ashariya Wai duk ta yabon kyauna ce,na koma gefe Ina rokonsu Kar suyi ashar a gaban angwaye Suka ce to sannan Muka shiga gaba daya sai wani guda Kadada sukeyi sun cikawa kowa kunne ga kida na tashi,Kowa ya juyo tare da zuba min Ido ,Ango na hango zaune Asmau da Nawwara suna gefensa Yana tsakiyarsu,Hafeez duk sun zuba min Ido suna murna yayansu ya zabo me kyau,abokan ango sai kallona sukeyi kamar zasu cinyeni,su Hafeez daga Jin an canja kida Suka Mike Suka dinga casa uban rawa Kamar Mata harda girgiza Ina ta dariya sun sani a tsakiya kallo ya koma kansu ana ta dariya kannen Ango,Nawwara suna ganin haka Suka taho Suma suka Shige sunayi Yan kallo suka taru ana ta Shan Dariya kannen Ango kana kallonsu kasan kannensa ne suna Kama,Nawwara ta rike Hannu na tana rada min Aunty kiyi ana ta Mana video nima ban San Sanda na Fara ba bilhakki da gaskiya ana ta dariya danginmu Suka dinga Mana liki masu resturant suna kwashewa Ina tsakiya suna zagani Naija music aka saka mana duk da ba wani jijjiga jikina nakeyi ba kowa yasan na Dan iya su Hafeez Kuwa sun kware Yan banzan yara,Ango duk da baiyi niyya ba sai da ya juyo Yana Shan kallo,Hafeez yace Aunty Kinga ya nuna wacce zamuyi iri Daya Muka fara Yi iri daya Jawad harda zuba tagumi Yana kallo Su Nawwara Suka je Suka dinga jawo shi ana ihu sai ya tashi ala dole ya taso ana ihu da tafi yazo wajen shi bai San ta ya ake rawa ba ma,na dan nuna Masa da hannaye nace ko haka kayi Mana,harara ya watsa min,su Asmau Suka rike hannayensa suna Masa rawar da Hannu aka dinga liki Kamar hauka,Nawwara ta kamo hannuna ta hada da nasa naji wani mugun laushi da taushi, shima haka duka dayan hannun ma muka rike Hannu biyu biyu Muna facing juna ana Mana pics da videos,masu liki suna Yi har kawayena sannan aka ce kowa ya zauna,tuni ya saki hannuna Yana wani bata Rai,kujerata kusa da ta sa Ina gefensa sai kannensa ga Asif da matarsa mun gaisa har pics duk anyi Mana har kawayena da kannensa munsha pics,Kowa abinda yake so ya karba naman kaji sosayye a saman Fried rice bargaza bargaza ga couslow,gurasa Tasha hadi,gasu faten Irish,ga farfesun Naman rago,lemuka da ruwa sai ka gaji da shi,ga wata dark brown spargetti etc, Ango ma abinda yake so aka kawo Masa wani kala kamar na turawa Ni Kuwa nace komai a zubo min ai Kuwa aka tara min tarkace kowanne kadan a gefe,nace Ina furar da nace a bawa kowa,duk son Jawad da fura kin Sha yayi Wai Allah ya kiyaye ya sake Shan furar Maguzawa ba Yan Fulani ba.
Anyi tsit ana ci ana Sha sai kida ke tashi shima kasa kasa an rage vol duk Wanda yayi magana ko ya sai anji me yace,Kadada da Tahantsi Wai zasuyi rada Basu San ana ji ba,Kadada ta kundumo ashariya tace Tahantsi kinji dadi wayyo inama Muna da Yan Uwa a birni to Bamu da uban kowa, Tahantsi tace uban wa garemu ko munje sai dai mu tsaya a randa (Round) sai fa su Fara Amarya gidan Ummiyanta su Kuwa ai ba abirni suke ba Darajar dodon tsafi gwara na Kauye dana rayu a gidan su Najla Amarya ji unguwa gwara gidan yari da ita ko Ina kwata sai wari da doyi,wannan angwayen ai sune suke a birni ba su Najla ba....Kasa jurewa nayi nace Dan uwarku Ina jinku munafukai kune kuke bani ci da sha ai sai ku tafi gidan Yan birnin ku zauna Yan Iska Arna,aka kwashe da dariya,Kadada tace kutmar....mune Arnan ai kema haka a ciki kuke danginmu Daya uwa Daya uba daya muke dan bura....Kuma maguzawan ne daga baya kakanku ya bijire ya koma musulmi, Tahantsi tace kai Dangin Ango Kar ayi muku rufa rufa gaba dayanmu jinin Maguzawa ne ashariya Kamar teku haka Najla ta iya gadonmu ce......Muryar ta aka ji nace music da karfi dan Kar a saurari su Kadada,sukayi Shuru sai masu Aiki Suka ware kida,Najla na kule da takaicin su Kadada ko abincin kasa ci nayi na kalli Kadada nace Yau sai min shata layi bari mutane su tafi
Sai da aka gama cin abinci Amarya ina ta kunci dama gani da saurin Fushi da rikon masifa na kalli su Kadada nace Kun haramtawa kanku shiga jirgi baku ba zuwa gidana ,Su Kadada Suka Fara bani hakuri nayi banza da su na wuce Asif ya Kira abokansu su Hussain da Ango Suka Shiga gidan su Amarya aka gaisar da iyayen Amarya Kawai maguzuwan Nan ashar ke tashi a gidan abokai suyi dariya a wani abun wani abin Kuma ya basu mamaki,Jawad Kuwa sai haushin Asif yake ji ya ja Masa ya auri Yar Dangin marasa mutunci yanzu a haka zata iya wani tarbiyya itama tana bukatarta bare ta bawa wani a bari ya auri me hankali yace Masa tana da hankali Yar mutunci ce in banda ashar me zata koyawa kannensa a haka zai biyata milliyoyin kudi sabo da takaici Yana Fitowa mota ya shiga ya wuce airport abinsa,ko kannensa baibi ta kansu ba,abokan ma duk sun tafi tare Suka koma da shi,Asif da matarsa sai kannen Jawad su aka bari sai Yamma zasu taho da Amarya da kawayenta biyu sai Yan Uwa mutum uku su Kawai Ummiya tace zasu je ciki Kuma harda Ummiya uwar Amarya da Daddy sabo da su ganewa idonsu komai inda yarsu zata zauna.
Kannen Ango har mazan duk inda Amarya ta sa kafa suna wajen har na Saba da su da rana bayan munyi Sallah na canja wani lace me kyau,Uwar Amarya Kuwa Shadda ta canja me kyau,Zuhriyya matar Asif itama ta Saba da Amarya da kawayenta ana ta harka da ita zuwa Yamma aka hada lefen Amarya da kayana kaf za a tafi da su,kawayena duk muka yi wanka tare da canja kaya,Amarya na sha Wani material fari kal komai fari nayi na Sha kyau aka dan Yi min kwalliya sama sama tare da dauri me kyau na daura mayafina a sama nayi kyau matuka,a cikin masu Kai Amary an Kara mace daya uwar gidan Babana,Haka Motata da kawayena su biyu Farisa Hamziyya daban tasu Mama da sauran daban sai ta kannen Miji data su Asif,Muna zuwa aka Mana screening Muka shiga jirgi nan ma Sai da aka Mana pics da videos mun Sha kyau babu Wanda zai raina mu,Muna jirgi harda Kadada a ciki ta makale sai zare Ido mu keyi har Muka Isa lafiya Lagos sai lokacin naji nutsuwa,Muna Fitowa Already motoci na jiranmu muka wuce gidan Abba direct duk mun ga gari me kyau da gidan mun rude mayafina Yana saman kaina muka Shiga har palo
A tsakiyar Palo aka zaunar dani dangin Jawad na bangaren Jawad Suka taru suna ta faman Yi min Nasiha iri iri Dangin uwa Kuwa Kaka Aisha ce kadai ta iya min Nasiha sabo da itace ke Jin hausa,Umma ce ta fito tare da Zama tace to Amarya sai a nutsu aure dai shi ba Dadi ake zuwa ji ba,mijinki me zafin zuciyane da izza sai ayi hakuri da halinsa,Wannan maguzancin sai a ajiyeshi gefe mu Fulani ne,Kadada ranta ya baci Nan take ta lailayo wata shahararriyar ashariya Mai maiko tace karfa ayi Mana hauka fa zamu hargitsa gida ba Sallah Muke ba ato...Ummiya ce ta bige bakinta tayi Shuru Haka dai kowa ya fuske Umma tayi mukus akayi Addua sannan Kaka Aisha tace aje a kaita dakin mijinta na zaci a gidan Zan zauna sai Naga mun fito mun sake shiga mota an kaini wata rantsataiyar unguwa ka rantse a turai kake wani hadadden gida Muka Shiga wow katon gaske gaskiya Naira tayi kuka a nan fadin irin gidan sai an dauki lokaci Mai tsawo ana bayani.
Part dina aka wuce Dani ya gaji da haduwa komai Arsh,wani sanyi da kamshi ne ke tashi Kawai abin sai Wanda ya gani,Dan guntun murmushi nayi kawai sai Murna nakeyi a raina irin wannan gida haka,a hankali na radawa Farisa idan Zaku fita dan Allah ku kulle Nigeria gaba daya ba kofa ba, Dariya tayi tace kasar gaba daya za a kulle ma lallai kin samu matsala.
a gurguje su Ummiya Suka ga gidan ko sallama basu Yi min ba ashe cewa Suka Yi tunda jirgi ne lallai yau zasu koma haka Asif ya kaisu suka tafi gida ni ban sani ba sai gani nayi Shuru Shuru
Gajiya nayi na sauke mayafina zuwa kafada ta Ina zaune saman bed Ina kalle kalle
Ina cikin kalle kallena Nan take na tuna da kuka na da nayi Alkawari zanyi gashi a gaban su Kadada nace zanyi baki na tabe nace kunwa kanku Kun tafi ba sallama da Kunga Kukana,hawayena ya huta bari na adana kukan,Ina wannan tunani naji motsi ana taku dai dai,Ina zaune naji an Murda handle,kaina na sadda kasa a hankali,Kamshi naji na musamman a hankali na dago da kaina na ga Jawad a tsaye jikin kofa ya Sha wani danyen yard me tsada brown,Yana sheki da walwali ga wani shegen gyaran gashi na musamman,Kallonsa na sake Yi Karo na biyu Muka hada Ido baki ya tabe ya min wani kallon baki Kai matsayin ba sannan a hankali ya bude baki tare da furta kinzo rainon? Zaki ga masu Aiki zasu Zo masu taimaka miki,rule dina Daya ne bana son shishigi karki shiga harkata yarinya ce ke ki tsaya iya matsayinki komai akwai a gidan kiyi abinda Kika ga dama a gidan,ki kula da aikinki rainon kannena ki saka Ido a kansu komai na gansu neat bana son kazanta,Banda shirme irin naku na yara, na tsani Yarinyar da yake ce min Nan take cikin masifa nace malam
tunda ni yarinya ce ai sai ka bani plunboti Feeder na fara tsotsa
Ya kusa dariya ya fuske yace za a siyo Miki Indai Feeder ce ya juya zai fita nace dan Allah tsaya,tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba nace Yau ba interview ne? Dan Allah kayi min Interview irin abincin Interview da muke ci shi nake nufi,ai ke ba Amarya bace,nace dan dai Kawai kaga bamu da kudi ne shi yasa kake min kallon hadarin kaza sabo da kaga Allah yasa Iska bata yaye ginin Yan birni ba irin gidanmu ba,Iyayen mu wasu ginin da suke ciki ya girme su Suma haka Suka tashi Suka gaje shi har aka haife mu muna ciki dole Iska tayi gaba da shi ko ruwa ya rushe shi dama wa'adinsa ya cika lokacinsa yayi shi yasa sai unguwar Talakawa ko Kauye Iska ke yayewa,ai shike nan a kawo min Yara gobe na Fara raino Kuma Albashina a Kan lokaci yawa duk wata on 25 zaka biya tunda aikin company ne ba na gomnati,kallona yake kawai yanda nake tsara zance bai ko ce komai ba ya juya tare da ficewa abinsa.
Wayata na jawo tare da Kiran Ummiya nace fatan Kun sauka lafiya? tace tun dazu ma kowa lafiya Suma na Kauye duk sun tafi Kadada ce Kawai ta dawo wajena da Zama,nace Alhmdllh yace Yana muku ban gajiya na furta kawai,Ummiya tace to Muna amsawa kice Muna Kara godiya da hidima,Yana jinki Ummiya,Ummiya kunya ta kamata ta surukinta ta kashe wayar nan take na dinga dariya ni daya bata San karya nayi ba,cikina naji yayi kugin yunwa ba shiri nayi fancakali da mayafin Amarci na nayi waje,part dina ya gaji da haduwa na rasa Ina Zan bi na shiga kitchen,steps na biyo a hankali na sauka main Palo na Ina duba each and Every room dake palon har na bude bedroom na uku ashe katon kitchen na gaske ya gaji da haduwa Kaya masu tsada har gas komai an hada min bani da matsala,wata kofa na gani a kulle a cikin kitchen daga gefe,bude kofar nayi sai naga katon store shake da duk wani kayan nau'i na abincin sarrafawa, kitchen na dawo na fridge ga freezer katuwar gaske daya na kayan sha,Daya Kuma shake da nama iri iri ga abubuwan gongoni barkatai,Dubawa nayi Naga babu kayan Miya Amma har su albasa gasu nan sosai,abubuwan da Ummiya ta daka min irin su yajin Maggi dana daddawa,ga kukar Miya,kubewa busashiya,gyadar Miya da sauran tarkace dai na gargajiya dukkansu na kwaso su na shirya kitchen din a daren duk wani abu na shirya shi komai na kitchen
Ganin ba kayan Miya sai na soya dankalin turawa tare da dafa indomie ta Sha Albasa sannan na hada tea me shegen kauri naga banza ta Fadi Palo na fito na duba ko ina ba bread har na zauna Zan fara ci sai na tuna ban soya kwai ba,kitchen din na koma a gurguje na soya kwai Guda Uku na fito na zauna a Kan center carpet na Alfarma,Fara ci na kenan naga mutum ya fito daga wani kofa ta cikin Palona mamaki nakeyi ta Ina yake oho,sanye Jawad yake cikin 3qtr da t-shirt orange color,Mamaki yayi ganin har na shirya girki zanci da uban dare haka,tunaninsa ma nayi bacci tunda 11:30pm bai San yau murnar haduwar gida ce ta hanani bacci, kallo daya yayi min sai Naga ashe Leda ce a hannunsa fara a gabana ya ajiye yace ga abinci,kallonsa nayi Naga waya yake dannawa nace Dan girma Allah idan kana yiwa Allah ka rage kallon waya karka makance da wuri wallahi sai ka makance da wuri wannan wacce rayuwa ce da Qur'ani kake karantawa da Sauki,Baki ya saki Yana kallona sabo da na raina sa Ina fada Masa banzar magana anyhow,cike da gadara ya daka min tsawa tare da furta keee...Ni kike ma magana haka? Tsoro naji nace a'a... ae..a'a..ledar daya bani na bude naga wani Kalar nama me ruwa ruwa yasha hadi gasu yogourt,da Wasu kalolin fruids a cikin wani glass abu kamar rubber, Daya ledar Kuma wasu snacks ne Kamar biredi,kaina na dago Muka sake hada Ido Karo na biyu sabo da farin ciki ban sanda na masa yare na Yan India ba nace Bayya na gode,Yaya kenan da Indianci na sake cewa
Bayya Jawad dama Kai mutumin kirki ne miji na gari zanyi aikina na gaskiya kannenka duk sai sunyi saukar Qur'ani cikin gaggawa karka damu kaji har su Tajweed duk zasu iya,da bulugu,ishmawi da iziya da risala,na basu tarihin sayyadina Aliyu mijin Nana Fatima,Ga Sayyadina Abubakar surukin manzon Allah baban Aisha da Asmau,tarihin Nana Khadija uwar gida a gidanmanzon Allah uwar gida ran gida Allah bamu ya tasu ba kishiya
Dake baya magana sosai sai dai ya jini Kawai na bashi dariya Wai Bayya Kamar ya mareta, a hankali yace ki daina min magana ni bana son yawan magana,nace to na ture abinda na dafa gefe na jawo abubuwan da ya siyo min, Ina ta jira naga ya tafi sai naga yaki tafiya Kuma bai zauna ba,tsoro ya kamani ko dai hakkinsa zai karba ne tun yau jira yake naci ya kaini Kan gado,Kamar yasan me nake ji a raina sai na tsinci muryarsa yace nafi karfin wacce ta fiki ma bare ke,babu Yan aiki a gidan nan sai masu gadi sai gobe zasu dawo nan idan kin iya dafa tea shi nake so banda Madara kayan tea din ai kin San inda suke
Da sauri nace to na mike tare da Shiga kitchen na barshi a tsaye kamar soja,lekowa nayi daga kitchen nace na sa Na'a na'a? Kai ya gyada min Kawai na gane naje na daura Masa nasa daban sabanin Nawa ruwa na tafasa Kawai na zuba Madara, vt etc, palon na fito bayan na dora na dawo Palo na ganshi ya zauna har ya kunna tv yana kallon wani dan iskan Amarican film na soyayya
Yankan nama Uku na dauka na juya Zan koma kitchen naji ya min wata uwar tsawa sai dana tsorata ban San Sanda na saki naman ba na fashe da kuka,masifa ya fara min wacce ban taba sanin ya Iya ba karni Zaki saka min a jikin cup din tea,nace ai Zan wanke Hannu na furta Ina goge guntun hawaye na,Tsaki ya ja tare da furta go and wash your hands very well idan yayi turanci sai kace baturen England wlh simple abu yake fada amma sai ka nutsu zaka gane me yake nufi da kyar na tantance me yace,na tafi kitchen sumi sumi na wanke hannu na da wani lemon liquid soap sannan na sake leko da kaina nace a flask Zan zuba? Sai da ya dauki 5mnt bai kulani ba bai ko kalli inda nake Maganar ba ko juyowa baiyi ba a haka da kyar ya furta cup,da sauri na koma kitchen na dauki wani hadadden glass cup na tea da dan spoon dinsa na hada Masa da sugar kadan na fito Ina tafiya Ina Waka Amarya me dadin tuwo da Miya.... zuwa nayi tare da Mika Masa a hannuna nace dan dana sugar yayi ,Spoon ya dauka ya dan eba jikina sai rawa yake sakamakon turaren da ya saka me arnen kamshi,yana Sha yace Sugar bai ji ba,komawa nayi na dakko Masa sugar cube ya saka da Kansa