Showing 66001 words to 69000 words out of 119289 words

Chapter 23 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9422

jefar da Zaki ce nayi asara ko Kuwa Maidawa ne ya mutu,Yaya Jawad ta saka turare da zata fito,yace Kyaleta Tahantsi zanyi maganinta gani take har yau budurwa ce,Kadada tace ki daina yaudarar kanki Fara da aurenki kibi musuluncinku sai ki dinga Iskanci iri iri


Sharesu nayi muna tafiya kowa Shuru su Tahantsi ne kawai suke surutunsu da Kadada jefi jefi Ina sa baki,Tahantsi tace na taho da babbar tsaraba tana jaka sai naje Zan kaiwa ko wanne a gidanmu,Muna wucewa ta layin wata Kasuwa Jawad yaga Hijabai a rataye yace tsaya a Nan aka tsaya,nasan me zaiyi Hijab ya siyo kato me Hannu ya dawo ya miko min,ta mudubi na kalleshi zanyi kuka,Kadada ta bigi kafadar Tahantsi tace Kinga soyayya,Ina gani Wai zata Yi kuka kema ki koya,Kadada tace na haddace na dauki darasi, Fara an Fadi ba nauyi,hijab din na karba na saka,sannan na cire mayafin na maida jaka, handkerchief ya Miko min Yana Murmushi na karba na goge jambaki.


Kaina na kifa a jikin kujera Ina ta goge hawaye su Kadada su kadai Suka San kuka nake suna ta tuntsira Dariya suna leka min fuska,Jawad yace ka Kara gudu lokacin Sallah ya kusa ai suna da masallaci a kauyen,Kadada tace kato ma kuwa Yana nan,har Muka Zo kwanar da zamu shiga Kauye mota bata Shiga sai dai ka bada ajiyar motarka a wajen masu machine ka hau machine,Kuma ba Napep,Muka fito gaba daya Jawad Yana mamakin daji irin wannan ace da mutane a ciki ko da yake Yana gani a kudu ma,masu machine biyar Suka taso, sai naga Daddy yazo shima an wuce da shi a machine, Hannu na daga Masa nace Daddyyy....ya dago min hannu,motoci Uku Muka gani masu tsada sunyi parking a wurin tamu ta hudu,ana zuwa Kadada data hantsi sune gaba sunyi nisa,Farooq ya hau nasa,Zan hau nawa jawad yace shi zai hau na hau bayansa,haka ya fara hawa na hau bayansa yace ki rikeni karki fado nace to ban rike ba ai akwai kunya,ana tafiya yace karfa ki Fado,nace a'a


Muna zuwa ana ta hudubar Sallar Juma'a Suka Yi Alwala zasu tafi liman har ya Kai karshen khuduba ya fara adduarsa yanda ya Saba wance da bata da lafiya Allah ya Kara Mata lafiya,wance.... Tahantsi tace wannan Liman din Anya na kirki ne kullum sai dai yayi ta zancen Mata,yaci gaba yaranmu da suke gida basu samu mijjn aure ba Allah ka kawo musu miji......Yarinyar Nan Kadada Allah ya shiryeta ta karbi musuluncin,Kadada ta sheke da dariya tace liman ya takura min shi yasa sai saka Hijab nake ya jaja min an karbi adduarsa,su Jawad suna ji suna ta dariya Suma,Farooq yace Ni na taba Jin liman haka kowa sai ka Fadi matsalarsa a gari,Jawad gefe ya Jani yace Wai Kinga Daddy ko? Nace ae yace yau Kadada za a musuluntar a daura Mata aure, na rigada tuni na sanar da iyayen Farooq komai Kuma sunji Dadi yanzu ma Babansa da dangi suna cikin masallacin,Kuma Farooq da Kadada basu sani ba fa,yace yanzu zanji ta bakin Kadada Farooq Kuwa mun gama da Iyayensa ba sai ya sani ba,Kadada ya Kira gefe yace yau gamu ranar Juma'a a garinku,kin shirya karbar musulunci yau a daura aure? Kadada tace ae amma shi ya yarda Farooq din? Ae yace,ki fadawa iyayenki,Kadada tace tab ai baza su yarda ba,Kawai bari na shiga mu gaisa daga masallaci sai cikin Kano idan ba Haka ba yau a gidan nan bazan kwana lafiya ba zasu iya kasheni, Farooq yace mun tafi Sallah ki gama kizo tace to,kallona tayi tace Fara ku shirya muje mu fito,Muka fadawa Tahantsi tace to ku muje Yara Suka dauki kayan da Kadada ta siyo tsaraba,Suna ta murna,Ina shiga Suka yayyameni Fara haka Kika koma balarabiya,a jirgin kuka sauka? Nace ae kawai,Gwamma harda shewa tana daga Hannu ta rike hanci Muka kalli Hammata Dariya ta kamamu muka kalli juna,Tahantsi ta fito da shaver da uban yawa ta dinga bawa kowa package Daya wajen Sha biyar kenan,Suka dinga tambaya mene ne,a dinga aske gashin hammata shi yasa duk na siyo muku duk da nasan kowa package Daya a rana zata kare sabo da ciyawa,Tashuka Kuwa karyewa ma zasu dinga Yi cewar Kadada,tace bari naje na kalli iyayena kafin suji na musu Tawaye,Gwamma ce ta fatalo shaver tace Naga Kamar Reza me mirki sai ta fashe da kuka amma yaran Nan bakwa kaunata so kuke na yanke jikina,Tahantsi ta dauka tace to Gwamma kyale abarki har ki bari maaskin dare ya gaji da gani shi yazo ai yayi Miki kwal kwal


Muna ji an idar da Sallah Muka fito Muka ji ance jama'a a tsaya akwai baiwar Allah da zata Musulunta bamagujiya Kuma za a daura Mata aure yanzu, Gwamma tace jama'a ku tsaya kuji wata jininmu zata shiga musulunci,kowa maza da Mata Yara da manya Suka kasa kunne suna Jin wace,Gwamma tace wannan kwai bankadaddiya ko wace,Kakannina Kuwa dadi Suka ji su dake musulmai ne,Muna zuwa Kadada ta shiga Masallaci aka bata Hanya ana kabbara Allahu Akbar, Tahantsi tace an rakata tabi bayan Kadada, suka shiga tare Liman ya Kalli Kadada yace Addua ta fada,sai ya bada sanarwa tace musulunci shine sadakin Aurenta,Farooq yayi zaune mamaki ya kamashi wato Jawad ne ya hada wannan tuggun zai Masa auren dole,tunda yaga Babansa da danginsa ya sare, bayan anyi khudubar aure da sharudansa nan take aka radawa Kadada kalmar shahada ta maimaita akace aure ya dauru,wanne suna kike so,Kadada ta karbi speaker tace Fatima Binta kowa zai iya kirana da Binta Sugar mangoro me Zaki,aka fara dariya


Aure ya dauru tsakanin Fatima Binta da Angonta Farooq Ibrahim Dangana, amma ango ya bawa amaryarsa kyautar kudi dubu dari biyar,Aminin ango ya bawa Amarya dubu dari biyar,Baban Farooq yace ya biya Mata aikin Hajji wata shekarar,ana ta kabbara kafin kace me Kadada ansha kyauta harda masu ishirin da Hamsim, Tahantsi tace a bata speaker aka Mika mata tace kowa ya sheda Kadada Ta koma Fatima Binta Sugar ta Musulunta Kuma an daura Mata aure,Nima Kadada ta Musulunta me ya rage nima mene amfanina Zan Musulunta a fada min me zance,masallaci aka kaure da kabbara yayin da can gida su Gwamma da duk Yan gida Suka haukace Kadada ce,Gwamma harda dirza kanta a kasa sabo da bakin ciki ta dinga goga goshinta a kasa sai da yayi jini sabo da bakin ciki,tace ayi maza a tarewa su Kadada Hanya,sai Jin sanarwa Suka sake Yi Tahantsi ta Musulunta ta koma Nana Khadija,liman harda cewa Tahantsi ta zabi suna me daraja sunan uwar gidan manzon Allah (s.a.w) Nana Khadija uwar gida ran gida shahidiya Allahu akbar, Tahantsi yanda aka yiwa Kadada kyauta itama Haka aka Mata har kujerar Makkah, liman yace zaku iya tafiya sai a samu masu koya musu addini yanda zasu fahimci Allah,Jawad a ransa yace uhmm kaji liman yasan kalmata, Farooq shi iyayin liman dinne yake bashi dariya, Tahantsi a gaban mutane tace to su Binta sugar anyi aure sai a daukin Dangana,Kadada tace bana son wulakanci sunan Surukina ne fa a gabanmu ai cin Fuska ne,aka kwashe da dariya sai lokacin mutane Suka tuno sunan baban Farooq Ibrahim Dangana,liman yace Alhmdllillahi yarinya tayi hankali tayi kunya, Fitowa sukayi Suka sameni nesa da masallacin na tari Jawad nace ga masu machine muje wlh naga Yan gidan nan sun Fara zagaye haushi zai sa su Mana duka, nace ga baban Kadada can da Adda, Farooq tuni ya dane machine sabo da tsoro,ta hantsi da Kadada Suka hau daya ni da Jawad Muka hau daya,Baban Kadada ya biyo ta da gudu tace me Machine tsaya ka Wana min machine din Nan ka bashi wuta,Ta hantsi tace juya kofar gidanmu Baban Kadada ya bisu da gudu,Me machine yace karfa ya muku Illa,ba abinda zaiyi Suka ce, Suka sauka a machine Kadada tace Zan biyaka saki salansa yanda zai cika garin nan da kara ka wuce ta kofar gidan damu sau Uku,Haka me machine ya sauka Suma Suka sauka ya balle salansa duk Yan gidan sun fito ba Wanda ya iya Kai Sara suna kallo aje a juyo da su Tahantsi har sau Uku da uban gudu,Gwamma ta fito da lemuka ta watso musu ku tafi bama sha ba mu ba ku,Kayi hakuri Baba Allah ne ya shiryeni,ka Taushi Babata Tashuka,Baban Kadada ya kutuntumo mata ashar, Me machine yaja Suka tafi,gidan Maguzawa Kuwa Gwamma sai rasgar kuka take jikokinta sun Musulunta sunyi abin kunya.


Suna karasowa Muka ji salansa a sake,Farooq yace yaran Nan basa ji,suna zuwa Muka wuce sai cikin kano,Muna hanya duk na gaji kaina ya fara ciwo na kwanta a jikin Kadada,Jawad ya juyo ya kalle da kullawa yace Mene ?nace kaina ne sai na Fara kuka,Haushi ya Kama Kadada tace dalla dagani raguwar banza daga ciwon Kai sai kuka,Farooq dai bai ce komai ba,Jawad yace ka sauri mu shiga gari a siya Mata magani,Farooq ya ware wuta amma Jawad yace Kai baka iya driving ba Yana ta masifa a haka har Muka Zo cikin Gari,ya tsaya a pharmacy ya siyo min maganin ya bani na Sha sannan aka Yi gaba zuwa hotel dinsa,yace min fito banyi musu ba na fita,yace ka mai da Tahantsi gida itace zata kular min da Baba,Binta sugar dinka Kuma kasan yanda zakayi da ita ni na gama maka sai godiya nake jira kazo Watarana ka min,Fitowa Farooq yayi tare da Jan Jawad gefe yace ka shammace ni yanzu asibitin da mukace zamuje fa a tsuma ni? Dariya sukayi harda tafawa yace sai a Lagos ya juya tare da rike hannuna Muka karasa ciki har room dinsa kafin mu shiga sai da yayi Mana order abinci,Ina Shiga na ajiye jakata a saman drawer Hijab Dina na cire na kwanta a saman gadon sabo da yanda kaina ke ciwo,wanka ya Shiga ya fito daga shi sai towel yaga na Fara gumi naji sauki sosai wuyana ya taba yace ya warke nace ae,yace je ki wanka to ko na Miki? Dariya nayi na tashi na Shiga da kayana duka,bayan nayi na dauki sabon brush nayi brush sosai Kamar yanda yayi,sannan na daura towel Dina na fito wannan towel din har yafi na gida guntu sai da naji kunya amma Kawai Fitowa nayi haka ya bini da kallo nace wanne kayan Zan sa lace din ya min nauyi,maadanar Kaya ya bude tare da furta ga kayanki na taho da su sabo da naji kala uku Kika dauka,naji Dadi na bude na dauki wata Yar Riga silk marar nauyi me siririn hannu na saka,da pant Kawai,na gyara gashina sannan nayi Sallah la'arsa Kamar yanda yayi shima,tuni an kawo abinci lafiyayye harda su Fruits,da Kansa ya dinga bani a baki har Muka koshi Muka Sha fruits sosai tare da kuskure bakinmu.


Kwanciya nayi Ina huce gajiya ya kwanta a gefena shima tare da jawoni jikinsa na rungumeshi Ina murmushi nayi missing dinsa sosai,maidani yayi kasansa na dawo Kamar Yar karama gashina me santsi yake shafawa a hankali Yana kissng saman lips Dina,jikina ya fara rawa yace ba abinda Zan Miki ni bacci na daukoki ki tayani trust me sai sanda Ummiya ta bani ke a dakina ranar to ba sauki bare rangwame na gaji da hakuri.


To muyi baccin Yamma tayi amma dai bari mu huta,ganin zai zame min rigata najuya bayana tare da dunkule jikina,hannunsa yasa ta tsakanin hannayena Ina kwacewa yace Dariya kike bani ke ganinki karfinki ne yasa in Kika janye hannuna nake cirewa,Hakuri na bashi yace ki bari tun kafin na canja mind na Miki warka warka,Dariya ya bani nace sai kace tsohuwar radio, please joke apart ya wani marairaice I miss you, Ina so na taba,me? So kike in fada Miki? tace ae a hankali ya rada Mata kyawawan nono abuna, Yana shagwaba ya sa hannayensa ta kasan nawa hakura nayi na nasan bazai hakura ba,sai da ya gama latse latsensa da tabe tabe,ya dawo Kan mazaunaina ya dinga latse su Wai massage yake musu nace na gaji










Ayi Hakuri da wannan




Maman Mujaheed Fans Muna... muna..muna
Muna da magunguna mata da supplement kaka kala na gyaran jiki da gyaran fata na Karin niima da matsi Ina uwargida da amarya da masu Shirin aure dama taku muna da kayan mata da supplement kala kala iya kudinka iya shagalin ks cikin sauki Mai kama da kyauta ba'a Nan mmn mujaheed ta tsaya ba tana yima marasa karfi adashen kayan gyara 500 duk weekly abaki kayan 5k 1k weekly abaki na 10k sai kin zabe abin kk so muna aikawa duk garinda kake


08066726866
















AsmaBaffa🌏 JIKAR MAGUZAWA🌏
66-70




NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP
IN KIN GANSHI A WAJE NA SATA NE




Official


By
AsmaBaffa






SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA




PAGE NAKU NE


Cutie
Bestynbeelat
Aidah Maman Tasnim
Maman Samha
Ummi H












Wayarsa ce tayi Kara ya dagani tare da dagawa Hello...muryar mace naji kasa kasa Yana ta faman cewa Okay...yeah..tana ta magana ban San me take cewa ba naji kishi na mike zumbur tsaye sai da ya kalleni yana wayarsa ya dade har ya gama ya kashe wayarsa,kallo na yayi tare da riko hannuna lafiya Fuska na hade tare da fisge hannu na nace mene na wani Okay baza ka bude baki kayi magana ba sabo da wato Kar na gane budurwarka ce ni Zan hanaka soyayya ne ko aure zaka Kara me na Isa nayi,wato sabo da bana gidanka shine ka fara soyayya,Jawad ya saki baki Yana kallona yace na yarda ke yarinya ce gaskiya,da sauri nace ae ai kace haka Mana tunda ka samo Babba tsohuwar banza ni dama nasan ba so na kake ba jikina kake bi,Dariya yayi kawai yace Wai da gaske kike? Raina a bace nace ae,yace tab Sannu da aiki to,ai haka kake ce min kullum yarinya yarinya na saka kuka,Jawad ya zaro Ido ya bude baki tare da furta ahhh....ke Mene haka? Yace yanzu ni wanne Mata ne ban gani ba a duniya Naga Fara,Naga baka,Naga wankan tarwada,Naga Yar lukuta,Naga siririya ke a siririya ma Naga wasu Kamar Sandar Snooker,


Naga larabawa,turawa,indiayawa duk na zagayesu nace Ina sonki,Ina son wata Zan tsaya na saurareki,ai kaji gashi Nan kace babu Kalar da baka sani ba dama kallonsu kakeyi, idan ma doguwa ce dai ka sani da wuya dogo ya zam me hankali kaje kaji wakar shata baza tayi hankali ba Indai doguwace Kuma baza ka taba samun nutsuwa ba,Dariya Jawad yayi yace to ke kenan tunda kema dai doguwa ce Kinga kin tonawa kanki asiri bana son shiririta zauna idan so kike kiji wace to a karkashina take aiki,wato har Mata kake dauka yace ae,to fire her taje ta nemi wajen aikinta,Baki Isa ba Kuma wannan bana son zargi fa ya bata rai sosai,Zauna bana son irin wannan karki sake min haka,kyaleshi nayi na koma na zauna,me yasa ku dukkanku kuke da taurin Kai ne, laaaa harda Ummiyata ko,kinji nace ita,kace dukanmu yace Ni nace ne ?ya wani Bata rai Shuru nayi na kwanta a gefensa, lokacin magriba nayi yayi Alwala tare da canja Kaya yace na tafi masallaci nace to,Yana fita na Kira su Farisa kawayena Muka gaisa Basu San Ina gida ba ban fada musu ba Nima,tashi nayi nayo Alwala tare da gabatar da Sallar magriba Ina Adduoi Jawad ya bude kofa ya Fado a guje yace ga Naroro nan,da gudu na tashi na fada toielt na kulle,Dariya ya dinga Yi yace tsokanarki nake,Fitowa nayi Ina dariya nace wlh naji tsoro su Kadada sun Musulunta ya kamamu ubanmu zaici,Sallayar hannunsa na karba na juya ashe bai saki sallayar ba ya jawo na juyo ya jawo ni na fada kirjinsa yayi huging dina nace Addua fa nake fuskata ya shafa da tafukan hannayensa Wai Ameen Inshaallah an karba ta wuce ya daukeni tare da kwantar dani saman bed.


Farooq Kuwa bayan ya sauke mu mota ya koma Kadada ta fito tare da komawa gaba Amarya,Farooq ya kalleta tace ae Amarya sai a gaban mota muje in Kuma so kake ka Zama driver to,Farooq yayi dariya yace ai hankalinki na gani da Kika dawo gaba,ya wuce da su wajen cin abinci Suka ci abinci suna ci Farooq Yana musu bayani akan Sallah da abinda ya dace mutum ya sani Wanda ya shiga musulunci,haka da Suka fito a mota ma, Tahantsi ya fara saukewa a bayan gidan Baba ta Shige gida tana shiga ta tambaya Baba ya dawo masu gadi Suka ce a'a taji dadi tare da Basu cin hanci dubu Daya Suka Yi godiya ta wuce ciki Kai tsaye,Matan Baba suna yin Tahantsi sabo da aikinta,kullum tayi ta musu aiki tana yiwa yaransu wanka,tana dawowa tayi sallama basu taba ji ba a bakinta sai yau,tace na Musulunta yau na koma Khadija ba Tahantsi ba idan ma Tala'asar ce ta fita daga bakinku daga yau na koma Khadija,Ke da gaske kike? tace fitar da nayi masallaci naje nida Yar uwata Kadada Muka musulunta,Kai amma mun tayaku murna Alhmdllh mun samu karuwa tace addinin musulunci ya samu karuwa,suna tayata murna ta koma bedroom ta fito tace ku Zo ku koya min Alwala da Sallah kafin na shiga makaranta,ai da sauri Suka shiga koyawa Tahantsi abubuwa taje zatayi alawala yanda Suka koya mata,Bata iya karatun Sallah ba,yaran gidan Yan manyan Suka dinga koya Mata karatu sai da ta iya Fatiha da kyar,da dare suka koyawa Mata suratul Iklas tafi sauki,sai tahiya da tasbihi da akeyi a sujjada da ruku'u,sai dagowa daga ruku'u ta iya sannan taje tayi Sallah tun daga wacce ta risketa Bayan ta Musulunta Tana idarwa ta bingire a wajen tana wash wahala wuyana wayyoooo..


Farooq Kuwa bayan yayi parking a kofar gidan Ummiya Kadada ta kalleshi ya juyo Yana kallonta shima fari tayi da fararen idanuwanta masu kyau Kadada ba dai kyan idanuwa ba,Farooq yace Amarya wannan Ido sai kace farin wata ,Dariya tayi tace hmm ba dai mutunci Zan maka,ana kawoni ka tabbata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login