Showing 15001 words to 18000 words out of 119289 words

Chapter 6 - JIKAR MAGUZAWA COMPLETE BOOK BY Asma Baffa.txt

14 Jan 2025

9444

fita a ranki ba, Mama Daddy yafi Baba komai wlh,Fuska Mama ta bata da sauri na furta Sorry na daina,Slifas din kafarta ta zare da Niyyar dukana na mike da gudu na Shige bedroom dina tare da fadawa saman bed Dina nayi doguwar Mika Ina murna da ihu tare da cewa wayyo kudiiiii....kudiiiiiiiii yazo Zan Zama hajiya very soon,Bari na Kira kawayena Hamziyya da Farisa mu Fara shiri,mikewa nayi tare da jawo wayata na Kira wayar Hamziyya tana dagawa nace hello Hajiya Najla ce,Dariya tayi tace yaushe Kika Zama Hajiya ban sani ba,hmm ke dai Bari Hamzy ai Hajju ma ba Hajiya ba Zan Zama Nan da 2wks,kwana nan nice Dubai nice China idan nayi zuciya kuji ni a America,Hamzy tayi dariya tare da furta kin fiye hauka Najla da shegen buri.


Dariya nayi nace to ki fara shiri wlh biki na idan ba ayi shi Nan da 2wks ba to Nan da 3wks za ayi,Lagos za a kaini,wani hadadde na samu Ina fada Miki sunansa kin San sunan,joke apart Najla Wai da gaske kike? Wlh I'm serious ku fara shiri wani me kudi ne kwana Nan Zan daki Kan wasu kudade,Murna Hamzy ta fara nace da Yamma zanzo muje mu fito da anko,Allah ya kaimu cewar Hamzy,Haka na Kira Farisa itama Farisa tace Kinga dai mu talakawa ne a fito Mana da anko Atamfa leda,nace yo dama ai ita za a siya cikin sauki dukkan kawayenmu babu Yar me kudi sabo da haka abinmu na talaka.muna Gama waya na Kira kawayena Yan Uwana na kauye su Kadada Ina fadawa Kadada ta dura ashar tafi goma kala kala nima sai dana dan dura ashar guda Uku Kadada tace ana fito da atamfar ki turo Mana nace ai a yau ma Inshaallah Amma Leda zamu fitar dubu Daya da dari shida ko takwas ta biya Mana bukata,Kadada ta sake dannowa Atamfa me tsada ashar tace bura....atamfar me tsada,nace uwar masu kudi mu ko muna da kudi baza mu siyi me tsadar ba,Kadada tace Muna jiran anko yau da Wayar Nadare Zan kwana a hannuna sabo da jiran anko a zabo Mana me kyau nace Inshaallah...Mene Inshaallah ma a addininku? Kadada ta tambaya nace in Allah ya yarda nake nufi,Tace uhm tare da kashe wayarta Yar kwakwura.


Mama bata San me nake ba sai Kira nake Ina fada mu tuni mun Fara shiri bata sani ba Yamma lis na shirya nace da Mama gidan su Hamzy zanje zamuyi pics na candy an hada walima tace a dawo lafiya,sanye nake cikin doguwar rigar lace pink na sa hijab me Hannu pink da Yar jakata ta talakawa me Dan kyau da takalminta flat na fita na shiga Napep a hanya na hadu da Hamzy tare da Farisa Suka Shiga Napep sai kasuwa.
Kudin da Asif ya bani ban bawa Mama ba na hada da Wanda na Tara a banki na cike dubu arba'in da biyar,Muna zuwa sharp sharp Muka zabo atamfar anko Leda me kyau sea blue and dark pink,sannan Na siyi lace Dan dubu Sha Uku na Amarya,na siyi Shaddata wacce zanyi doguwar Riga yadi hudu dubu goma Sha biyu sai na siyi mayafai masu kyau nace takalmi sai na dawo,yanzu Saura dubu biyar,Farisa tace ki Kara Atamfa Yar dubu biyar Kinga ko kala Uku sun isheki tunda ba dinner za ayi ba maybe,idan ma za ayi ai shi zai siyi wannan Amma wannan dai duk tsiya karki sa na lefe idan an kawo naku Zaki sa na gidan ubanki bare danginsa su Raina miki hankali.


Nace Saura maganin gyaran Wajen Kar azo ayi biki yaki daga min kafa,Dariya mukayi na sake cewa mazan Nan ba Imani garesu ba da alama Kuma area dinsa me tsayi ce dole ta kamo Chanel da yawa,Dariya su Hamzy suka dingayi a kasuwa ana kallonmu kamar sabon kamu ba a San me muke cewa ba,nace wannan magana fa bata Dariya bace dole na gyara receiver yanda za a kamo Channel da yawa,Farisa tace a gidan ubanwa Kika ga area dinsa? Nace haba ai da gani ba sai an fada ba doguwa ce ta kirki Allah dai ya Mata Albarka duk da ita aka Samar damu gamu a duniya Allah ya karawa ta Daddy Lafiya shima ya haifi dansa kullum sai kamo Chanel amma shuru,Dan Allah muje naci bashin kayan gyara in yazo Zan kawo Mata kudin kayan gyaranta,Mu Fara kaiwa tela dinki sai mu je,ai Kuwa tela Muka kaiwa dinki na barwa su Hamzy anko da mayafan Dana siya nace ku ajiye Hamzy gidanku sabo da Kun San karyar dana yi,ku nunawa dukkan kawaye anko Nima zanyi waya da su muje gidan.


Daga nan Muka tafi gidan me gyaran jiki dake mun santa sosai kanwar Babar Hamzy ce tace ba matsala ta hada min abubuwa na gaske Wanda Zan fara a amfani da shi, nace iceko dai na Infection akwai da yawa yanda Receiver zata Yi garau sai Kuma yanda Zan dinga zuwa kullum ana gyara min skin dina shima Aunty bashi zamu Fara kafin su zo tace to Najla,a jaka na zuba komai na boye yanda Mama baza ta gane ba sannan Muna Fitowa su Hamzy suka shiga Napep Nima na shiga na layinmu sai gida.


Lokacin dana Zo gida har magriba ta wuce,Mama tace kin dade Najla har Ina Shirin kiranki Kun Sha walima,Nace ai Kuwa Mama tayi Dadi munci mun sha, Mashaallah cewar Mama,bayan na shiga dakinmu na ajiye jakata Alwala nayi na gabatar da Sallah,Ina Jin yunwa amma Haka na kasa cin abinci sabo da Kar mama ta ganeni sai can dare na zubo naci.
Ina kwanciya a dakina Farisa ta kirani tace Saura kwana Uku fa za ayi second Interview akwai cika ciki,nace Ina sane na shirya zamu je ai cikinmu sai yayi kuka Allah ya kaimu


Jawad Yana Katafaran Office dinsa aiki ya Masa yawa,juice yasa Secretariat dinsa ta kawo masa Yana Sha yana aiki ana ta kawo Masa takardardu Yana signing,Asif ne yayi knocking Kamar bazai Yi magana ba yace come in sai yaga Asif ya Manta ma da zancen auren da sukayi sai yanzu ya tuna,Zama Asif yayi Yana facing dinsa,ba tare da Jawad ya kalle shi ba yace yaushe ka dawo?dazu Ina ta kiranka kaki picking,Yana aiki a laptop yace I'm busy yanzu ma kana gani dai Yaya kuka Yi?Asif ya bashi labarin komai yace da kyar ta yarda zata ta kauyen,Murmushi me Kayatarwa Jawad ya saki sannan yace kana bani mamaki ai Kaine na kauyen da ake bugarwa anyway tana da sa'a ta yiwa kanta gata data amshi tayin ka fada Mata jibi zamuje coz Zan tsaya a Kano na karasa Interview duk hadawa zanyi nayi ta kwana ukun a kwana daya zanje Sweeden zanyi 1week kafin bikin Zan dawo,Okay bari naje gida na huta cewar Asif ya wuce abinsa.










Sharhi fans












08033933642


AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


16-20


Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA
ZAINAB GARBA BUTALAWA




Karanta kasa kiji yanda Zaki siyi wannan novel


SHIN KIN SAN SHAHARARRAN GROUP ƊIN NAN DAYA SHAHARA WAJEN KAWO SHAHARARRIN FINA-FINAN DA SUKA SHAHARA WAJEN SAKA MA’ABOCIN KALLONSA A CIKIN NISHAƊI DA FARIN CIKI?
IDAN HAR BAKI SANI BA LALLAI KUWA ANA YI BABU KE!
KODA YAKE HAR YANZU AKWAI BABBAR DAMAR ZUWANKI DON A CIGABA DA DAMAWA DA KE IDAN HAR KIKA JONE DA MU!

Kuna ina ma’abota kallon shirye-shiryen Arewa24 na ƙasashen waje da suka fara ba su ƙarasa ba? Yi Maza ka garzayo wannan maƙala don ƙarasq kallon shirye-shiryen.


Kuna ina ma’abota karatun lobayya wato ma’abota karatun littafan hausa? Shin na tambayeku akwai wani novel da kuka karanta har yau baka samu karashensa ba? Ko kuwa akwai novel ɗin da kake nema ruwa a jallo ka rasa? To kaima garzayo wannan maƙala domin dacewa da haziƙan fasahan littattafai.


‘Yan gayu sam! Bamu barku ba! Kina son koyon kwalliya ɗaurin dankwali kala-kala? Yi maza ki jone da mu kin ji? In sha Allahu sai dai ki koyawa wasu, domin an tanadar muku kyawawan vedios wanda zasu taimaka ki koyi kwalliya da kanki, ki koyi ɗauri da kanki.


Anzo wajen! Wato fannin girki! Ayyuriririiiii!
Duk kyan mace sai ta iya girki ta cika sunanta kyakkyawa! Maza-maza yar’uwa ki jone da mu don kuwa muna kawo manyan-manyan girki masu daɗi da ɗanɗano wanda ba su da wuya balle ma ace sai ankashe musu kuɗi. Ke dai shigo ki ganewa idonki!


Ƙarshen-ƙarshe kenan! Wato ba anan fa aka tsaya ba akwai wani babban albishir ga masu son group ɗin, shi ne babban tanadin da akai don kawai a faranta muku! Tanadin kuwa shi ne, akwai haɗaɗɗan novel da ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa da aka yi shi musamman dan ku, wato wanda ake sakinsa a iya group ɗin kacal, wanda wasu manyan marubuta ne ke rubuta su, duk dai sai kin antayo zaki ganewa idonki. Wannan ma na ɗaya daga cikin littafan.
Kalli katsa kaɗan!






*TSARE TSAREN WOMEN24 TV WHATSAPP DA WOMEN24 TV VIP👇🏾*


DAURE KI KARANTA DAKYAU


Akwai groups guda biyar(5) da muke tura littafi wanda marubuta keyi kyauta da kuma littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24


Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro


*KUDIN WOMEN24 TV VIP*
Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada
Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne


*KUDIN WOMEN24 TV*
*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in


Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv




*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*


1.WOMEN24 TV VIP NOVELS
2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS
3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS
4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS
A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa'in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu


5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE
Kinajin sunan groups innan kinsan meye za'a dungayi a groups in
DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.


Account number.




2065301650
Zubairu Hayat Iman
Uba bank.




Number waya.
09030159301










Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN


Kada kibari gara basannan ta wuceki.


YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39




A Yi min afwa jiya Ina so nace Alhaji Nasir nace Umar abin ne sai a slow🤣




Page Naku ne


BESTYNBEELAT
UMMI
UMMI LATEEPHA
UMMU ILHAM
MAMAN D
NICE GIRL










Yana ta aiki bai bar Office ba sai 6pm sannan direct gidan Abba ya shigo Yana shigowa ya ji kukan su Meenat a room dinsu room din ya nufa tare da budewa Yana budewa ya iske Hajara Yar aiki tana Zane Meenat Wai ta zubar da Madara Kamar zata kashe yarinya,Jawad Yana shiga ta saki bulalar a kasa tare da yin Miki miki jikinta ya hau rawa ga kamshinsa ya cika ko Ina ga uwa uba kyau da kwarjininsa ba bata lokaci ya kwashe Matashiyar yar aikin da Mari har biyu sannan ya dauki bulalar ya fara tsula Mata tana ihu ta fice a guje su Meenat sai faman kyalkyala dariya suke sun daina kuka sai lokacin manyan Suka shugo Jawad ya dinga musu masifa su daina barin yaran Indai ba school ba Suka amsa da to,kudi ya basu masu yawa sannan ya fita ko Abba da Umma bai Nema ba ya wuce abinsa zuwa gidansa.


Bayan kwana biyu da ranar data Kama su Jawad zasu Zo da wuri Mama ta fara Shirin girke girke Ina tayata muka gama komai tare da gyara gidan fes,bangaren Babana ma Yana gida Bai fita ba,Daddy ma Haka,muna kammalawa mukayi wanka Mama Tasha Atamfarta purple ta zuba kyau Ni Kuwa materia na Sha wani cotton riga da skert dai dai talakawa masu rufin asiri haka Muka fito fes damu muna jira har 11am sannan Naga Kiran Asif Ina dagawa yace Muna kofar gidanku fito,gabana naji ya yanke ya fadi masifar tsoron Jawad nake ji da kunyarsa yana mugun min kwarjini haka na daure na yafa mayafin Kalar kayana tare da zura dan takalmi na me dan tudu nace Mama sunzo Zan shugo da su,to ta furta sannan ta koma dakin Daddy ni kuma na fita domin shigo da su,sai da na Isa bakin kofar gidan mu sannan na dan leka naga motocin guda Uku lafiyayyu sunyi parking ba kowa daya fito sai guards da suke zaga wajen sabo da tsaro a raina nace to fa,sai nayi Kamar Zan fita sai na dawo na rabe jikin katanga tare da dafe kirjina sabo da yanda yake bugawa,a hankali nayi deciding fita Kawai idona na runtse sannan nace komai ta famjama fanjam Kawai na fito kaina a kasa har nazo jikin motar ban San nazo ba sai ji nayi na bigi jikin mota Saura kadan na Fadi Allah ya tsare


Asif ne ya fito daga motar Yana dariya yace me kike kallo a kasan dan rusunuwa nayi tare da gaisar da Asif ya amsa Fuska a sake sannan nace ku shigo, okay ya furta tare da budewa ogan motarsa wani kamshi da sanyi ya bigeni sanna ya fito fuskar nan tam babu faraga,ko kallona baiyi ba bare na sa rai zai min Murmushi,tun daga nan jikina yayi mugun sanyi a sabule nace Ina kwana ba tare da ya kalleni ba ya amsa Alhmdllh Yana latsa waya Fuska na kwabe sosai kamar Zan narke na kalli Asif,yasan me nake nufi yace Chill a hankali, Gogan na kalla yasha uban shadda me tsada silver ya diga kyau ya coka hula a gaban goshi irin na matasan zamani Yana kamshi da sheki a raina nace ke ki godewa Allah ma da zai iya aurenki daga haka na musu jagora zuwa cikin gidan Ina gaba suna baya gashi kayan sun kamani sosai ana ganin mazaunaina Kamar zasu Fado sai faman gyara mayafin nake Ina jansa,Jawad ya kalli abinda nake yaja tsaki a ransa ya furta Flat ko kyau,Ni ban San me yake Yi ba har muka Shiga sallama Asif yayi Muka Shiga palonmu dan gujul da Yan kujerunmu duk sun lalace wani wajen ma ya burma sai ledar tsakar daki sai dai komai Kal kal akwai tsafta Yana kamshi,Mama na Kira ta fito sanye da Hijab ta zauna, har Jawad kasa suka sauka tare da yiwa Mama gaisuwa ta ban girma,Daddy ma ya shigo Suka gaisa Ni Kuma na Shiga jera musu kayan abinci dana Sha a gabansu


Daddy Yana ta jansu da hira Yana yiwa Jawad Yan tambayoyi duk da cewar Daddy yayi bincike a Kansa Yana da asali me kyau ga addini baida makusa, Mama Kuwa tace Bismillah ga abinci ni dai na Shige bedroom lemo Kawai suka Sha da ruwa da kyar Daddy ya tursasu sai da Suka Sha fura me yawa Suka ci Dan abincin kadan sannan Jawad a hankali yace zamu koma,da wuri Haka to ku tsaya a kaiku wajen mahaifinta ku gaisa nan fa Daddy ya kwala min Kira na fito yace fito muje ki rakasu wajen babanki,Mama tace barta suje Kawai,haka Jawad ya mike tare da Ajiyewa su Mama dubu dari.


Daddy yace wannan kudi haka dan Allah ka barshi,Jawad yace ai ba yawa Suka fita Ina binsu a baya Muna Fitowa da sauri aka budewa Jawad mota ya Shiga ni Kuma Asif yace zaga ranki ya dade Ina zagawa ta dayan side din aka bude min motar Jawad daya gefen na zauna shima Yana can gefen,wani sanyi da kamshi Kamar Kar na fita a motar,wayarsa ya fara dannawa ya harde kafafunsa na kalle shi shima lokacin ya dago karaf muka hada ido,nace kaji dadinka dan Allah ka dinga tasbihi kana godewa Allah kaji? Fuska ya tamke yaci gaba da danna wayarsa


Asif shike driving Yana kallon mu ta glass dan kwanciya nayi Nan take bacci ya kwashe ni,Jawad yasha mamaki ganin har nayi bacci Dariya ta kamashi a ransa taji sanyin ac,ai sai na Fara mafarki ban sani ba ashe a fili nake surutai na cikin mafarkin Ina cewa Farisa Kun karbo dinkin ankon ko? Ya bace wajen tela? Wayyoo Allah kayan Amarya....au Jawad ya kawo wasu kayan na Amarya?.......Hamziyya make up,ina cikin mafarkin Kawai na ganni ana min makeup powder ta Fadi me tsada na buga ihu ashe ihu a fili nayi sai da Asif ya taka birki hakan shi yasa na farka da ihu nace Powder ta.....Jawad kunnensa ya toshe da sauri sakamakon ihun dana Yi,ai tuni na dawo hayyacina tuna a inda nake na zauna sosai kunya naji nayi Miki Miki,Asif sai dariya yake yace Amarya harda mafarkin biki please inane hanyar gidan Baban naki? Baki na bude da sauri nace ai mun bar hanyar a baya wani wawan tsaki Jawad ya ja cike da masifa yace ke tunaninki bani da time ne kamarki daga Shiga motar mutane kin Fara iskancin baccin banza to uban waye zai nuna Mana gidan yaja tsaki


Asif kida ya kunna ya Kuna wakar hausa Jawad ya ja tsaki yace dalla Malam cire Mana wannan Yar iskar wakokin,Asif Yana lailaya mota ya fara rawa da Kansa Yana bin wakar Nima Ina sonta na haddace ta tsaf amma sabo da kwar jinin Jawad na kasa ko motsi,Ina nunawa Asif har muka je katafaren gidan Mahaifina dake G.R.A sunyi mamaki Muna Isa na fito daga motar na shiga gidan direct sallama nayi na daure Fuska ba Rahma na Shiga kanne na da muke Uwa Daya uba daya na gani a Palo tare da sauran yaran gidan,Fawaz ne ya taho da gudu tare da rungumeni,sai Samahir da Wahida Auta Suka taho Suma tare Ina ta murnar ganinsu fes da su da gani kasan basu da matsala sai abinda ba a rasa ba tunda a hannun kishiyoyi suke,Dakin Baba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login